Showing 27001 words to 27623 words out of 27623 words
Chapter 10 - Darajar Yayana Book 1 Complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
Abdul yana
nuna murna da ganin jikanshi a cewar shi, har
ya kara da cewa yaron ya biyo jinin babanshi.
Aliyu ya ce to za su tafi,sai wanda yake amsa
Uncle din ya yi rokon shi kan cewa ya bar su su
yini. Da kyar ya yarda. Mujidat sun lalace da
saurayin ta yini guda, hankalin Aliyu ya kasa
kwanciya don haka uku daidai ya bar komai ya
nufo gurinsu,sam ba su zata ba sai dai an yi
sa'a sun fito falo suna hira,ya diro ya ce su
fito.sun fito, nan ya shaka mata kudi masu
yawa,sai dai dubu goma ta cewa Aliyu ya bata.
Bayan dawowarsu ne ta yi ta siye siyenta har ta
sai wayar da ta siya a boye tana chatting, ta ji
dadin zaman Abuja rayuwar da suka yi ta kwana
goma da mijinta, da ma ta fi so daga ita sai shi
da dansu. Don haka ta sha alwashin duk
yandaza ta yi ta raba ma'auratan dan ganin
cewa ita kadai ce ta mallaki mijinta. Lokacin ni
kuma na shiga zargin cewa shi ne ya ba ta
kudade,ta je gidansu Anty Ramatu gidan da
kullum take zuwa, da yake sun fi shiri da
Ramatu, sabida ita ce mai zuga ta a kan
kishiyarta, ta ce mata Hausawa mugaye ne in ba
ta yi wani abu ta kare ta ba, to ita za takoreki.
Mujidat ta ce ina Yusufu? Kanin AntyRamatu
kenan. Ramatu ta ce, Yana dakin shi. Mujidat ta
je gurin shi ta ce, Yusuf ya maganar mu? Yusufu
ya ce, Anty ai ke nake jira mun gama magana
da yaron Bahaushene, kudi kawai yake so. Tace,
Ko nawa ne zan ba shi. Ya daga waya 'Bari in
kira shi. Yaron ya zo, jamilu sunan shi ya san
kan computer sosai, hatsabibi ne. Mujidat ta ce
ina son a hadawa wata mata sharri ne ta hanyar
internet, yanda mijinta zai rabu da ita. Jamilu ya
ce ita ma tana hawa internet din ne? Mujidat ta
ce tana hawa,kuma mijin ya hana ta amma har
yanzun ina ganin ta.Ya ce tana saka hoto?
Mujidat ta cea'a, ya ce kina da hoton ta?
Mujidat ta ce a'a. Ya ce, To ba matsala nawa za
ki biya ni?Zan baka dubu uku. Ya ce, A'a ki ba
ni biyar, cikin sati daya zan ba ki mamaki. Ta
ciro dubu uku cikin 'yar jakarta ta hannu (post)
ta ce, Rike wannan zan cika maka in har ka yi
min wannan aikin da kyau,sannan duk lokacin
da irin haka ta taso zan yi maka magana. Ya ce,
An gama. Nan take ya bukaci ta fada masa
sunan da matar ta bude account din ta, ya
kuma ce ko ta san wani da matar ta sani?
Mujidat ta ce a'a,sai dai tana koyarwa a
primary. Ta yi ta yi masa bayanai a kan Sadiya,
sun rabu a kan cewa zai turo mata duk abin da
ya hada a nata account din ta gani.
Kamar an jeho shi ina kwance a tsakar dakina,
sabida kowa ya san mace mai ciki da jin zufa,
har bare ana cikin yanayin zafi. Ya tsallaka ni na
dago kai cikin faduwar gaba na ce, Lafiya Yaya?
Wayar da ke gefena yasa hannu ya dauka,sai
huci yake kamar kumurcin maciji na yunkura na
tashi zaune, ina sake cewa. Lafiya Yaya? Ya
dubeni idanunsa jajir 'Dama duk tsawon lokacin
da na ce ki rufe account dinki na facebook baki
rufe ba? Gabana ya yi mummunar faduwa,sam
na manta da shi, banama hawa. Na kalle shi.
Kawo in rufe wallahi ba na ma hawa kuma na
manta ne. Ya soma sintirin kai kawo a
dakin,sannan ya ce, 'Kin ba ni mamaki Sadiya in
wani ya fada min ba zan yarda ba..............
Abin tsoro sai na ga hawaye sun soma zuba
daga fuskarsa. 'KINA BIN WANI SADIYA, DA ME
NA RAGE KI, KI KE BIN MAZA??? KASH! Kash
amadadin HALIMA ABDULLAHI K/MASHI. Ni
ANaM Dorayi nake cewa dan jin yaddaza ta kaya
mu hadu kashi hudu wanda ya fito tare da na
ukun nagode,dan Allah inna barar addu'inku
Allah yayemin damuwar dake cina,kwarrai inna
cikin damu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100