Showing 15001 words to 18000 words out of 27623 words

Chapter 6 - Darajar Yayana Book 1 Complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt

na ce
tabdijan! Hauka. Na ce Mujidat kizo inji Yaya
Usman. Ta ce, in yazo ganin yarone ya shigo
mana, ni bazan fitoba. Na ce, Rago ya kawo
muku, shima sauri yakeyi. Ta mike tana yatsina
ta fito. Ni kam ban koma gurin su ba sai da na ji
yana kirana. Madam na tafi.,na fito nace to Yaya
mungode, amma lallai ina jiran Aunty, yayi dariya
zan fada mata kiyi ta hkr Kinji? Na ce ba komai.
Sati 1 Kawai da suka yi a gidan naga takaici,
gulma gurinsu ga shegiyar kazanta. Babanta wai
ya so ya ga Aliyu saboda a yi daurin aure su zasu
tafi ,kuma ganinsa baza su iya dawowa ba, shi
kuma yaya yace dansu Bazai bar aikinshiba sai
dai na lallabasu da cewa su tafi in Ya zo sai a je
can garin. Haka kuwa sai tafiya suka yi, ya so ma
har Mujidat ta bisu can, amma da yake ta san shi
in har ta sa kafarta tabisu to sam ba zai nemeta
ba, don haka tace aifa sam ina nan na baka lkc
ka gama zaman ka dawo muyi aure.
Yafi wata sannan ya dawo, lokacin Abdul-Hakeem
yayi wayo sai gogewa yake yi, don ma ba ta san
bashi nono sai madara, wai bata san nononta ya
lalace, na ce Allah Sarki wata rana ma ke kanki
sai kin lalace bare wani nononki. Aliyu kam
tuburewa yayi cewa ba zai auri mujidat ba, nima
na tubure cewa ban yardaba, matsalar da ta
janyo rigima har sai da Usman yazo gidan.Usman
ya cewa Aliyu, alkawari Kayi tun farko, kuma
musulmi ne kai ka san muhimmancin alkawari,
sannan matarka tana da gaskiya ba za ku rabu
ba. Mujidat da Ke daki tana jiyo wa kuwa ta
fito,ta ce, ai mutuwa ce Kawai zata raba su,
kuma ta dibarwa kanta lokaci in har ya cika bai
ce komai a kan auran su ba za ta maka shi a
kotu, sanan zata nemi yan jaridu manema labarai
ta ce shine a matsayin wanda yayi mata wayo
yayi mata ciki bisa alkawarin zaiaureta, amma
yanzu yaki cikawa.Take Aliyu ya tashi ya watsa
mata mari, sannan yace bazai auretaba, taje tayi
duk abinda take ganin zai fitar da ita,da kyar
Usman ya tausheshi, ni kam daki na shige ina
kukan takaici mijina wanda nake girmamashi da
daraja shi, amma ga wata banza datti tana
wulakantashi,a fili na ce shi ya jawa kanshi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sun yanke za'a kai sadakin ta can lagos, amma
tare zasu har da ita da Usman da kuma su Yaya
Suleiman. Aliyu ya ce amma sai dai ta fadawa
dangin ta kada suyi maganar jariri, duk ina daki
ina jiyo su,lokacin ne na soma sabon kuka
saboda kishin mijina ta dai tabbata lallai mijina
auran zai yi.
Ya same ni a daki bayan tafiyar Usman cikinn
halin kuka, ya tsorata mutuka, ya dagoni yana
tanbayata dalili, ce masa na yi kaina ne kurum ke
mini wani irin ciwo.ya kawo min magani ya bani a
baki, sannan ya kwantar da ni.
Cikin dare na farka naganshi zaune, na dafa
shi,lafiya Yaya?
Ya ce, Sadiya, ina ganin har in mutu ba zan daina
nadamar laifin da na aikataba, ina cikin dana
sanin zinar da na aikata da banyi ba da ban fada
cikin wannan halin ba, yanzu tunanina da wane
yare zan fahimtar da Iya cewar zan auri wannan
yarinyar? Tsoron tunkararta nake da zancen
Aunty wallahi,ban san me yasa a duk lokacin da
mijina ya shiga damuwa hankalina kan tashi
tausayinsa ya cikani,gaskiya da mutane suke
cewa In kana son mutum kana tausayinsa. Sai na
kwantar da kaina a kirjinsa, sannan nace. Don
wannan Yaya Kar Ka damu, in Allah ya kaimu da
safe zan samu Iya, ko kuma muje tare da kai. Ya
ce, Sadiya bana son yadda nake ta saki karya don
ki fitr da ni. Na ce, Allah zai dubani ya yafe min
karyar insha Allah, tunda dan gyara nayi ba don
batawaba,Ya rungumeni yana fadin, Sadiya Ke ce
rayuwata, Ke ce abar alfaharina. Na ce, nima
kaine rayuwata. Muka kwanta cike da damuwa a
zukatanmu.
Goma tagota muka fito zuwa gidan Iya. Yayaya yi
mutukar kyau cikin shadda waganbari mai kalar
sararin samaniya(sky blue), Hula mu hadu a
banki,itama kalar kayan, wanda kyan shi ya tona
tsadar shi, yana ta kamshi. Ni kuwa Atamfa na
sha Purple mai ratsin fari, Takalmi da Hijabina
kuma farare, muka jero tamkar sabon aure muka
nufi gidan Iya.
Tana zaune kan sallaya ta idar da salar walaha
da fara'ar ta dubemu tana cewa. Masha Allah ina
zaku haka tabarakallah amma kunyi kyau. Muka
sa 'yar dariyar yake dan nayi Imani yadda nake
tsananin fargaba, hakan nanma Yaya yake ciki.
Nace gurinki muka zo. Yaya ya ce daga nan za
mu je kasuwane ne sai muji ko kina son wani
abun?. Ta ce, bana bukatar komai Gadanga. Duk
wani abu da zan nema ka ajiye min, ga firji da ka
sai min ina ta saida ruwan sanyi ina samun na
batarwa, ba abunda nake bukata Allah ya shi
muku albarka yasa yayanku su goyaku.Muka ce
ameen,tace, yan uwnka sun zo sun fada min
cewa ka kai musu kayan abinci su duka ko?yayi
yar' dariya, 'Iya wannan aikin Sadiya ne, ta ce
duk wata in dinga sai musu kayan abinci shi ne
muka fara da wannan watan. Iya ta kalle ni da
dariya, 'Hali Dubu rubutun dutse, halinki dubu
duk na alkhairi, na san sai ke 'yata. 'Ta kalli
Aliyu. Dadin auran mace tagari kenan zata dinga
bai wa mijinta shawara ta gari. Aliyu ya dube ni,
sannan ya kalli Iya, 'Wannan gaskiyane Iya. Nace,
'Yanzun ma gurin ki muka zo kan wani
batu.....tace, to, ya aka yi? Na kalli Yaya, shi ma
ya kalle ni na ce, 'Ka fada mata. Ya ce, 'A'a ban
san ta inda zan fara ba ki fada mata kawai in ta
amince shi kenan. Iya ta ce, 'Ku fada min mana,
kun daga min hankali. Na sunkuyar da kai, 'Iya
dama mun yi shawara da Yaya ne a kan cewa zai
....za ya... 'Sai na yi shiru. Ta ce, 'Inajin ki. Na
ce, 'Zai auri bakuwar nan ta gidanmu sabida tana
da hankali kuma.....' Da tsawa ta katse ni, 'Ke!
Da kata kin san me ki ke fada kuwa? Waye zai
auri wa?
Na kalle ta 'In..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yaya ne (Na nuna shi) zai auri Mujidat, tana da
hankali Iya sosai. To ya ce yana son kara aure shi
ne na ce ya aure ta. Iya ta rabka salati,sannan ta
ce, 'Amma ban taba sanin ke mahaukaciya ba ce
sai yau, ni ban taba jin inda aka ce ga wata mace
ta ce mijinta ya yi mata kishiya? Ta sake zabga
salati tare da riqe haba tana kallona. 'Ko ni nan
da nake tsohuwa bakeba a ce babanku zai dawo
duniya zan amince ya yi min kishiya? Dan haka
ban yarda ba. Muka kalli juna da Yaya, ta ce,
'Meye matsalar ka da har kake son kara aure? Ko
har yanzu bata son haihuwar ne? Ya ce, 'A'a
wallahi bata da laipin komai kuma ba inda ta
kasa, dama sabida raya sunnah ne kamar yanda
yake cikin musulunci, yarinyar nan kuma Iya ta
musulunta ne in ta auri wanda ba na kwarai ba
za ta dauka haka halin musulmi yake, amma mu
za mu yi mata mu'amula ta kwarai yanda ba za
ta yi da ta sanin musulunci ba. Iya ta ce, Eh, ai
dama ke Sadiya ba a yada ke gurin magana,ni fa
dan ke nake fadan nan amma ke na lura kamar
zuga ki nake, wai ke ba kya kishin mijinki ne?nayi
'yar dariyar yake, sannan na ce 'Ina kishinsa
mana amma hakan ba zai hana shi ya kara aure
ba. Ta yi shiru tana kallon mu can ta ce, 'Ni fa
ban yarda da yarinyarba, kallonta nake kamar
wata 'yar bariki ko wadda ta buga duniya. Muka
kalli juna,Ya ce, 'Ai kin san zaman Lagos, sannan
ba ta dade da Musulunta ba.Nace, 'Eh, ba ruwan
ta Iya. Ta ce, 'Oho! In ma da ruwanta ke ki ka
sani tunda kin ji kin gani ai shi kenan, ni me zan
ce, Allah yasa alheri. Yauwa, kwanaki yayanku
kece min 'yan uwanta sun zo na ce shi ne don
rashin mutunci ai sazo su min godiya. Muka sake
kallon juna ni da Yaya, na ce, 'Af wannan laifina
ne Iya ni ce ya kamata in rako su kiyi hakuri. Ta
rike baki tare da cewa, 'Uhum! Abind ya same ki
kar Allah yasa ya samu sauran dangi. 'Na ce Iya
na gode bari mu tafi. Haka muka bar Iya baki
bude tana mamakina,ni kuma na ce masa mu
tafin dan kar ta canza ra'ayi,duk da ta amince,
amma ba wai ina murna ba, bani da yanda zanyi
da ya wuce in kauda da kai a yi auran, na san
mata da yawa za su ga baike na amma ina san
su sani DA KISHIYAR WAJE GARA TA GIDA.Daga
nan gidansu Anty Abida ya ce mu tafi,,ni dai
muna tafe ne ba kamar yandamuka taho dazu
ba, ba wata hira bare annuri. Mun samu Usman
a gida don haka muna shiga suka fita. Aliyu ya
kalli Usman 'Aboki, Iya fa ta yarda da batun
Mujidat. Cikin mamaki Usman ya kalle shi tare d
fadin, 'Kai haba? Aliyu ya ce, 'Allah da gaske.
Usman ya ce, 'Banzata ba, ya aka yi ta amince
da sauri haka? Ya ce, Kai bari kawai,yarinyar nan
Sadiya aboki ba ni d abind zan biya ta, ita ce ta
shawo min kan Iya har ta amince da batun,sai na
lura da akwai wasu shakku daga zuciyarta, Allah
yasa ba ta gane cikina Mujidat ta haifa ba.Usman
ya ce, 'Ka kara rike matarka da kyau,ina fada
maka a wannan zamanin ba za ka samu tamkar
ta ba, ina fada maka ko Abida matata ba za ta yi
wannan jan aikin ba, tana fada min sai dai ta ce
tana karfafawa Sadiyane dan tasan za ta iya
kuma hakanne mafita. Aliyu ya ce, Allah ya ba ni
ikon riqe ta da gaskiya. Usman ya ce, Ameen,
yanzun mu tafi gidan su Yaya Sulaiman mu ji
yanda za a yi. Aliyu ya ce to, Allah ya rufa asiri.
Abida ta dube ni ina kuka, kallo na kawai take yi
bata hana ni ba kuma bata bani hakuri ba. Sai da
nayi mai isa ta. Sanan na share hawaye na,
sanan ta dafa kafada ta. Sadiya kada kiga cewa
ban baki hakuri na barki ne ki rage radadin dake
zuciyarki, gaskiya ne in ka zubar da hawaye yana
rage bakin ciki, amma in tambaye ki mana? Na
kalle ta da jajayen idanuna, ta ce kukan nan na
menene kike yi? Murya ta a dishe tana rawa na
ce, anty... Abida ina da matukar kishin Yaya
Aliyu,Dan ban san irin son da nake yi mashi ba,
kukaba yakunshi abubuwa dadama, amma kishin
mijina shine a gaba, wai mijina zamu raba da
wata, inna tuna haka hanjina na kaduwa, da na
sani ban amince ya aure taba.... Sabon kuka ya
kubuce mun.Tace kijure, Allah yasan nufinki,
karki bari yaga karaya daga gareki, domin ba
mijinkiba har mijina ya ce kin burge shi kullum
cikin yabonki yake tare daba mijinki shawarar
cewa yayi maki kyakkyawar ruko, dan haka ki
cigaba da dannewa. Na ce, to anty zan kula,
yanzu na sha kanshi ya amince in nemi koyarwa,
sai dai ban san ta ina zan fara ba. Ta ce kada ki
damu shugabar makarantar firamare ta L.E.A
unguwar Mu'azu kawar yaya ta ce zanyi mata
magana sanan karamar hukumar Kaduna ta kudu
ma babban wan su Usman yana gurin ne kuma
nasan zai tai maka. Na ce, to, aikuwa nagode
Anty Abida Allah yabar kauna. Tace amin. Haba ai
ba komai wallahi. Nan muka wuni nakasa cin
komai, Anty Abida har Dan wake tayi min wai
taga inaso, amma da kyar naci uku ina taunawa
tamkar ina tauna magani, ko ruwa na sha sai
inga tamkar magani . Anty kanta ta shiga
damuwa tana min fadan kan in kashe kai na a
banxa. Na ce mata. Anty kiyi hakuri cikin
kwanakin nan ko gida na bana iya cin abinci in na
dauki littafin marubutan nan in dan duba sai
komai ya tsaya min inkasa fahimtar me nake
karantawa mai makon in karanta litafi sai dai shi
littafin ya dinga neman karantani da ko ina da
yar matsala inna karanta sai ya dan rinka debe
min kewa. Ta ce ai duk ki ajiye batun littafi
kirumgumi mai kankat wato, ALKUR'ANIR
KAREEM. Na sauke ajiyar zuciya,, tabbas Anty
Alkur'ani yana sanyaya zuciya mu kan musalmi
bamu da kaico sai godiya ga ubangijin da yayo
mu a musulmi. Ta ce haka ne Allah kasa mu
mutu a cikin musulumci muna a musulmai. Na ce
amin.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kafin su dawo ta sani na wanke fuskata nayi yar
kwalliya, duk da fara'ar da nadingayi sai da yaya
ya gane nayi kuka, duk lokacinda na kalle shi sai
in ga idanunsa na kan fuskata har dai ya kare ya
ce Sadiya kukan me kikeyi? Muka kalli juna da
Anty abida ta ce, sam bata yi kuka ba me kagani?
Yayi dan yake shi dole murmushi, ko ba jami'in
tsaro bane ni, kun san daini ba yaro bane. Na
share zan cen da cewa, yaya mu tashi dan yara
na jira na in daukosu. Ya ce madan saurareni.
Abida ta kalle shi ya ce, nifa bana son abin da
zata shiga matsala, in auren nan zai kawo mata
damuwa wallahi sai a fasa duk abin da zai faru
ya dade bai faruba kowa ya ji cewa nayi wa wata
ciki ta haihu, daga nan fa? Na runtse ido, don
Allah yaya mu bar maganan nan, nace maka ba
damuwa nake ciki ba, ka yarda dani. Usman ya
ce aboki ina ga dai na dawowa da hannun agogo
baya din nan a bar shi. Abida ta ce ai sadiya
jaruma ce bata cikin wata damuwa, kuma
malamai sun sha fada muna cawa in Allah ya
rufa maka asiri yayin da ka aikata wani laifi to kai
kada kayi kokarin tonawa kan ka don haka barin
batuna haka shine mafi a a'ala. Haka dai muka
baro gidan nasu bayan sun yi mana rakiya.
Saty daya bayan nan suka shirya tafiya lagos, sai
dai ban da ya Sulaiman saboda suna son yan da
haduwar su da dangin mujidat zai kasan ce, haka
nan basa son yanda ya Sulaiman ya san cewa dan
da ta haifa na shi ne. Sun tafi da Usman da shi
Aliyun da kuma Mujidat da Danta. Sai dai lissafin
da aka yi masa ya same wuce hankali, domin ko
auren Sadiya bai kashe wannan kudin ba, sannan
kudin sa da ke accout yayi shirin siyan wani gida
ne da aka yi masa tallansa can kasan su a
sabuwar unguwa da ke nan unguwar Mu'azun. Ya
kalli Usman ya ce aboki ni fa ba zan iya biyan
wayan nan kudinba. Usman ya ce, to ka kirata ta
fada musu baza ka iya yin al'ada ba. Ya kalli
waliyin ya ce a kirata. Sai suka ce ai su al'adar su
ba a magana da amarya sai su waliyanta. Usman
ya ce to su basa yin wanan al'adar sadaki kawai
zasu biya. Sauran suka ce sam ai tunda ta haihu
a tasu al'adar yin biki dolene, kuma abubuwan
al'ada dole ne, domin ita mai albarka ce mai
haihuwa ce, sannan ba dama ya ce ya fasa tunda
ta haihu.
Shi da Usman suka kalli juna a ran shi ya ce lallai
ya debowa kanshi ruwan dafa kanshi. Usman ya
ce kawai ka basu inya so sai ka sai fili bana son a
samu matsala. Nan dai ba da son ran shi ba ya
amince bayan sun fita suka tafi banki in da ya
ciro kudi suka dinga yi masa lissafi yana ba su,
nan fa suka ce jibi za su yi hutu, suka amince a
haka. Ni kam ko da suka dawo bai fada min ba
gurin Anty Abida na samu labarid Usman ke fada
mata, na ce shi dai ya sani can da yawarsa.
Idanu na zuba ina kallonsa yau da na ga yanzun
yana dan zakewa tare da rawar kai, sam ban zata
ba, ya sa a yi gyaran gida. An yi fenti na kwashe
kayan yarana daga dakin da ta zauna tunda nan
za'a sa ta, ya ce da ya so canza min gado,amma
in yi hakuri ko daga baya ne. Yaba ni dubu
talatin,na yara ashirin na karba na aje tare da
cewa mun gode. Na dauki waya ta ina dannawa
ya ce, Wai Sadiya akwai wani laifi da nayi
makine?na kalleshi' Me ka gani? Ya ce, Na ga tun
jiya da na zo ba wata fuska a gurinki?Na maida
kaina ga kallon wayata,sannan na ce, Akwai abin
da ban makaba daga cikin wanda na saba
yimaka?Yace, A'a,kin min komai MY CHOICE, sai
dai ni na gane kamar ba ki da walwala. Na ce, Ba
ka yi min komai ba. Ya ce, To anjima zan tafi, Na
ce, Allah ya kai mu. Har ya kai bakin kofa na ce,
Au! Na manta in fada maka an dauke ni amma
ba aprimary ta nan unguqar Ma'azu ba, ta can
Tudun wada. Ya tsaya yana kallona, nima shi
nake kallo don son jin ta bakin shi,a zuciyata ina
cewa yanzun dai a ce ya hana ni, tabdijan! Da sai
ya ji magana. Tamkar ya sani sai ya ce na san
kina zaton zan hana kineko? Ai ba ni da yanda
zan yi tunda na rigana yi miki alkawari,amma ki
sani raina baya so. Ban ce kala ba na ci gaba da
danna wayata shi kuma ya fita.
Ban tabbatar da cewa ina da kishi ba sai da
lokacin auran ya gabato,wallahi ko abinci kasa ci
nayi duk datausar da Aisha ke min da kuma Anty
Abida dan ganin na kwantar da hankalina, amma
na kasa, bana bacci sosai duk da cewa bana
nunawa Yaya damuwata sai dai shi duk lokacin
da muka yi waya sai ya yi min korafin in daina
damuwa in kwantar da hankali,To kurum nake ce
masa, amma zahirin gaskiya zantukansa ma soya
min rai suke yi.
Ana gobe daurin aure zasu tafi can Lagos din ina
kallo shi yana ta shige da fice yana shiri,an zuba
sababbin dinkuna an sai Huluna da Takalma sai
ina mamakin mutumin da na dinga shan kan shi
da kyar shi ne yake zumudi. A fili na ce Allah
yasa abin ya tsaya nan. Ya fito cikin shiri ina
kwance kan gadon yara ya ce 'My Choice mun
shirya,na dago na kalle shi, yayi matuqar kyau
cikin Shadda Wagambari Blue shar kaladaya da
hularsa mu hadu a banki, kamshinsa ya cika
gidan, kishi ya kama ni mai tsanani,na kau da kai
gefe. Ya ce, 'My choice yaya ne? Ban tanka masa
ba sai zuciyata ta ce gwada shi ki gani da yake
cewa in na ce ya fasa zai fasa,in ya so duk ma
abin da zai faru to ya faru. Ya tallabo fuskata.
'My Choice, yaya ne? Na ce, 'Ni fa gsky na sake
tunani a kan wannan auran, gaskiay ina tsoron
abin da zai biyo baya. Zai fi kyau a barshi.
Zumbur ya mike tsaye daga russunawar da ya yi,
na kalle shi ga mamakina fuskarshi daure, ya ce,
'Me ki ke nufin maidani? Karamin mutum? Kin sa
mun yi magana yanzun kuma kizo ki ce ke kina
jin tsoro, ya kamata ki fadi haka ne tun kafin
yau, sai dai ki yi hakuri,mamakida tsoro suka sa
na kasa daina kallonsa sannnan ga hawaye yana
ta zuba tamkar an bude famfo, na girgiza kai
tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya zauna
kusa da ni tare da dafa kafadata. My choice bana
nufin cutar da ke kece kika karfafani kika nuna
min yin auran nan shine mafita, to me zai sa
yanzun ki bijiro min da wani sabon batu bayan
aski

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login