Showing 6001 words to 9000 words out of 16870 words
wai aure yakeso,to karka damu bari zuwa gobe se in shiga gurin dad dinta muyi maganar "
Murnace ta kama shaheed rungume dad din nas yayi,yana masa godiya,dan shi dama yafiso ayi auran inma laifi yay mata ya rarrashi abarsa sanda ya dorata akan cinyarshi.
Washe gari da safe,dad din shaheed yaje gurin gomna,sun tattauna gameda auran tunda dama kowa yasan suna soyayya.
Kamar yadda shaheed ya bukata,haka aka saka wato nan da sati guda.
Bayan sun rabu ne gomna ya shiga bangaren mtarshi inda yasmeta zaune dasu sanaya suna hira.
Be damuba yafara maganar data kawoshi.
"hajiya kinji mutananki ko,sanaya da shaheed yanzu sun fara mgnr auransu,dan yanzu mahaifinsa yabar gidannan shaheed ya matsa akan a daura auranshi da sanaya cikin satin nan to nasan da amincewarta shiyasa na amince a daura din"
"WHAT!!!!"cewar sanaya da taji maganar kamar saukar aradu.
azabure ta mike tana kuka tana faΙin.
"no daddy bazan aureshi ba,ko na aureshi ze sakenine,kafa tuna dad safwan yarigadaya batamin rayuwa,wlh ba namijin dazega mutuncina mtukar bashidin daya yimin fyaden ba,dan haka wlh banason shaheed inkuma kamin dole wlh sena kashe kaina"tana kaiwa nan ta juya ta shige dakinta tana kuka me tsuma zuciya.
wani gumine yashiga karyowa gomna,safwan ya cuce shi,cuta tahar abada taya ze iya yafe masa.
"Alhaji batun sanaya abun adubane fa,kasan fa budurcin mace shine mutuncinta dana iyayenta agurin miji da danginsa,pls kayi nazri sosai kar muzo muna dana sani"cewar mummy.
Shide yakasa mgn gumi kawai yakeyi dan ko giyar wake yasha baze bari sanaya ta auri safwan ba,inde shine ubanta.
Alamura sun cabe gaba daya dan yanzu sanaya kwananta biyu kenan kwance adakinta tarufe kofar baci basha,gaba daya ta fita hayyacinta.
Hankalin iyayenta duk yatashi ba ma kamar gomna tsoronshi kar yunwa da damuwa ta kashemishi sanayarsa.
Masu balla kofa ya kira suka balla kofar, a kwance suka hangota ko numfashi batayi,dagudu dad ya sungumeta,zuwamota mummy da munaya nabinshi.
Da sauri excorde dinshi suka bude musu motar,tuni jiniya ta fara tashi,suka fice a dari,zuwa asibitin Garden City.
Duk abun da ya dace shi aka mata,inda binciken farko yabada tabbacin jininta ya hau,sosai snnan damuwa tayi yawa a zuciyarta wanda gab take dahatsarin kamuwa da ciwon zuciya.
Kukane kawai gomna beyiba,amma mummy da munaya sunyi kuka har sun gaji.
Safwan ya gama cutar dasu,cuta ta har abada haka kawai suke maimaitawa.
Shaheed besan wainar da ake toyawa ba se yau dayaje gidan aka sanar dashi ay mutan gidan na Asibiti.
kai tsaye asibitin ya nufa,inda ya samu kowa jugum jugum ana jiran farkowar sanaya.
Ayko suna zaune ta farka.
"wlh banason shaheed bazan aureshiba,inko aka takuramin sena kashe kaina,na tsaneshi bana kaunarshi"itace kalmar dasanaya ta farka da ita akan bakinta.
A gigice shaheed ya mike yana ja da baya yana fadin
"No,no, no, sanaya kina sona duniya ma tasan hakan........"ji kake sharab ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,
wayyo tashin hankali baa sa maka rana gomna ko takalmi babu akafarsa π€£haka yake daba kafar akasa,
Emmergency aka shiga da shaheed rai a hannun Allah,itako sanaya bata masan anayi ba dan ci gaba tayi da fadin batasonshin cikin mayen ciwo.
muje zuwa
Surbajo for life
ππππππππ
*SANADIN KIDNAPPING*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
*Sometimes I forget 2 say hi, sometimes I forget to reply,sometimes my msg doesn reach u, but it doesn"t mean I forget u. I"m just giving u time to Miss meπ AUNTY ASMAU ABDULLAHI SHAREEF YAKO AND AUNTY ALIYA SHAREEF GAMBO YAKO,YOU GUYS I LOVE YOU IRIN SOSAI DINNANβ₯β₯β₯β₯β₯β₯β₯π*
*Dedicated to fatima Abubakar Radda*
*19-20*
Kan kace me an dukufa gurin ceto ran shaheed,dakyar akasamu numfashinshi yadawo shima seda taimakon oxygen.
Do kyar security din dad suka lallabeshi yasa takalmi,se masifa yake tayi.
Sanaya ko allurar bacci aka mata dan ta daina cewa batason shaheed.
tuni labari ya isarwa iyayensa tuni suka garzayo asibitin domin kawo masa agaji.
Sun kidima da ganin halin da dan nasu yake ciki,mumynshi in banda kuka ba abinda takeyi.
Munaya ko tausayin shaheed yafi komai sata kuka,dan tasan irin son da yakewa sanaya ba na wasa bane.
Bayan kwana biyu dukansu sun dan murmure,hakanne yasa daddy sawa asallamesu in yaso doctor yaje gida yaci gaba da duba su.
Batan an sallamesunne yasa aje azo masa dasafwan in yayitaurin kai,su babballasa su kawo shi.
Allah sarki bawan Allah yanacan gurin da yake faskare,yaga motoci kamar ana yaki dan harda igwaπ€£.
"ka bimu muje cikin aminci inba haka ba wlh se mun harbeka,me girma gomna ne keson ganinka"cewar daya daga cikin wainda aka turo.
Ba musu safwan yabisu dan dama yanaso yamasa warning na karsheπ³
Har cikin falon gidan suka shigar dashi,yayi mamakin ganin kowa zaune yana kallonsa.
Sanaya na ganinshi ta rushe da kuka,sabida tuno sharrin data mushi.
"meyasa kayiwa sanaya fyade?"
jin tambayar yayi kamar daga sama da sauri ya waiga yana kallon gomnan.
"tambayarka nake ko baka ji vane?"ya maimaita.
"katambayeta ni ban yi mata fyade ba,ay gatanan tana jinmu"cewar safwan.
"Sanaya,waye ya miki fyade?"gomna ya tambayeta batare da wasa ba.
kukanta ne ya karu inda cikin kukan tace.
"Daddy safwan ne yamin,wlh har so goma yana maimaitawa"t karasa maganar cikinkuka inda taci gaba da cewa.
"ka cuceni safwan,ka lalatamin rayuwa,kasa nida shaheed mun haramta ga juna dan ko na aureshi baze ga mutuncina ba,dan haka yazamemaka dole ka aureni tunda kaine ka fara Sanina"ta karasa maganar cikin gunji kuka.
A zabure safwan ya mike,ya nunata da dan yatsa yacr cikin fushi.
"naga alamun kamar yadda tsohonki yake dan giya kema kin fara korawa,agidan ubankine ni safwan nai miki fyade,wlh ki shiga taitayinki ni ba saan wasanki bane"
"wlh kaine,kuma dole ka aureni a hakan,in banda kaddara ma ni mezanti dakai kazamima irinka"cewar sanaya cikin kuka.
wata cafka yakai mata inda ya shako wuyan rigarta sega sanaya a sama ya ruketa da hannun daya,dan masifa hancinshi har budewa yake,yace.
"kin gama rabarwa atiti ne yasa kikeso ni na kwashi saura ko,to bari kiji ni nafi karfin ragowar wani,kuma wlh ko na aureki sanaya,senasa kin mance da waye ubanki,karuwa kawai"cillar da ita yayi,sanaya fitsari ne kawai batayiba dan tsananin tsoro.
"Nan gidanane dan samari ba naka ba,kuranka nayi dan na baka umarni,yazama dole kayi daya aciki,ko ka auri yata daka lalata ko kuma nasa atsareka anan na tura karti guda goma gidanku su yagalgalamin kanwarka kamar yadda kayi wa tawa yar,wlh ba wasa nakeba"cewar gomna yana huci.
kuyi hakuri da wannan abubuwanne se ahankali
surbajo for life.
ππππππππ
*SANADIN KIDNAPPING*
ππππππππ
*ZAHRA SURBAJO*
ππππππππ
*Don Allah kuyi hakuri na jina shuru da kukayi,wlh inada babban uzurine,daya sha kaina,ina fatan zakumin uzurin*
*Dedicated to Fatima Abubakar Raddaβ₯*
*21-22*
Shuru safwan yayi yana kallon sanaya,cikin matsanancin mamakin sharrin da ta masa.
Se yanzu yayi danasanin saninta a rayuwarshi,wasu hawayene masu dumikebin fuskarsa,dan yasan sabida kansa baze so ya tarwatsa rayuwar kanwarsa ba,uwa uba anashi ganin,da yakai rahama gidan miji ba cikakkiyar budurwa ba to gwamma shi yadauki second hand din koda hakan zeyi sanadin salwantar numfashinshi.
Zubewa yayi akan guiwowinsa yana kuka ya rike kafafun gomnan,yace.
"zan auri yarka domin kare mutuncin kanwata,bana son yarka bana kaunarta,na fada maka ne dan ka tabbatar da cewa kiyayya ba abunda bata sawa,dan haka in har ni kakeson na aureta to ka daura mana auran yanzu,dan wlh ya wuce yanzu bazan aureta ba,koda kuwa da naman jikina zaa dunga yin miya a gidanka kullum"ya karasa maganar cikin dakewar murya.
"kai dalla malam dakata,ubanwaye saanka anan,kabar ganin fa ina kyaleka,wlh ba tsoronka nake jiba,akwai lokacin da zakayi nadamaraykata min duk abinda kayi,kasan duk wanda ya rigaka dakwana dole ze rigaka tashi,yata ni nake da ikon saka ranar auranta ba kaiba dan haka bazan daura auran yanzu ba"
mikewa safwan yayi yace
"to naji,sede ka manta da cewa,sanayace yarka ba niba,kana daiko akanta amman banda ni,dan mulkin naka ba inda aka rubuta se gomnan jihaya amince dan jihar zeyi aure,kamar yaΙdana fada da farkoin na fita yanzu wlh bazan aureta Ba"yana kaiwa nan ya juya Ze bar falon.
Dawani mahaukacin gudu sanaya tazo tasha gabanshi har tana haki,sabida adan zamanta dashi ta fahimci shi kaifi dayane,inde ya fadi abu ti tabbas seya aykata,
ruko shi tayi tana kuka tace.
"Don Allah kar ka tafi,ka bari adaura auran yanzu"da sauri ta waiga gurin dad dinta tace cikin kuka.
"dad inde da gaske kana son farincikina toka Daura aure na yanzu anan gurin,"
"Sanaya..."cewar dad
"dad"ta katse shi da hanzari.
shiko safwan ko ajikinshi,so yake ta bashi guri kawai yawuce.
Ganinfa da gaske sanaya take ne yasa dad Yin abinda ta bukata badan shi yasobane.
Shide shaheed dake zaune kamar gawa inbanda kuka ba abinda yake.
Haka abban shaheed yayiwa sanaya wakilci sannan gomna yayiwa safwan aka daura kan sadaki dubu dari dahamsin .
an daura aure lfy,sanaya se murna take,ana gama daura auren taje gaban daddynta tace cikin kuka.
"daddy kuyi hakuri,zan sanar daku gaskiya,wlhsafwan beyimin fyade ba,kawai sonshine ya kama zuciyata ta yadda bazan iya hakuri dashi ba,ina son safwan dad fiye da raina,shaheed kayi hakuri,wlh nakasa jurewa ne"
Azabure kowa ya mike yana kallonta,cikin fushi dad yasa hannu ya dauketada mari,sannan cikin fushi yanufi safwan.
"nasan kunnenka yaji maka,cewa ba gaskiya bane sharrin data maka,dan haka yi hanzarin sakarmin ita yanzu dan baku dace da ita va"
Murmushi safwan yayi,ya mika hannu ya kamo sanaya suka tsaya gaban dad yadubeta yace
"Kina sona da gaske ko?"
kai kamar na kadangarw haka tashiga gyada shi.
murmushi yasakeyi Sannan yakai dubansa gun gomna yace.
"Baba a tayamu da addua dan nima.gaskiya ina son matata"yana kaiw nan yaja hannunta suka fice daga falon.
"sanaya in kika bi karen nan na tsmeki acikin yyana,bani bake har abada"cewar gomna kamr zeyi kuka.
Sanaya ko hawaye kawai takeyi dan tasan yanzu safwan yafi iyayenta iko da ita,dan haka ko waigowa bata yiba,tabi safwan suka fice daga gidan.
tofa
muje zuwa.
Surbajo for life.
*SANADIN KIDNAPPING*
*ZAHRA SURBAJO*
*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*
*23-24*
Har suka fice get safwan be saki sanaya ba,janta yake iya karfinshi.
Mahaifinta ganin sun fitane yasa ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,sabida in akwai abinda ya tsana a rayuwarsa to be wuce safwan.
Da gudu aka kwashe shu zuwa asibiti,rai a hannun Allah.
Koda likitoci suka dubasa tuni jininsa ya hau over dan haka taimakon da yadace suka shiga yimasa.
Safwan da sanaya ko suna fita ya saki hannunta,yaci gaba da tafiyarshi kai kace ba tafiyarsu daya ba.
Binshi take kamar bindi,dan batasan manufarsa rayin hakanba.
Ζankwalin kanta ta kwance ta rufa ajikinta,dan ko mayafi babu a tare da ita.
Safwan tafiyarshi kawai yakeyi,dan ko sisi bashi dashi dazasu hau mota.sanaya taga ta kanta,dan tun daga malali,har zuwa tudun wada kaduna akafa sukayi ta.
sanaya har jiri ke dibarta dan tunda tazo duniya bata taba yin irintaba,gashi sauri yake kamar ze tashi sama,haka ta dunga falla gudu tana binshi dan kar ya bace mata.
Gurin inno me icce dake gangaren bolar layin Ζosai ya nufa,yana zuwa gatarinshi ya dauka yaci gaba da faskarenshi.
Agurin akwai wani tsohon tankin mota da aka ajiye kusa da shagon deluwa me mangoro dan haka sanaya can ta nufa ta zauna tana kallon yadda yake faskaren.
Hawayene kebin fuskarta,na tausayin kanta,sanda takai dubanta kan kafar deluwa sannan ta dubi tata kafar,sosai ta deluwa tafita ta kyn gani,
Safwan be dena faskarenba se gefin magrib,sanaya na kallo inno tabashi dubu uku kudin aykinshi,fuskarshi kawai ta kalla tasan yana tsaka da murnar samun kudin.
Suna sallama da inno ya juya ya dau hanyar tafiya,batare dayayiwa sanaya magana ba,da sauri ta mike tabi bayanshi.
wani gida sanaya taga ya danna kai ciki,me kama da akurki a gurinta,da sauri itama tabishi.
Rahama ce ta taso da saurinta tana fadin.
"Sannu da zuwa yaya,ya ayki?"
Murmushin da sanaya bata taba gani safwan yayi ba,shi taga yayiwa rahama,gamida cewa.
"lafiya lau kanwata,ya zaman kadaici?"
murmushi rahama tayi,se alokacin ta hangi sanaya dake rakube a bayanshi,da sauri ta kalleshi tace.
"yaya bakuwa mukayine?"
be kulata ba illa wucewa da yayi ya dauki buta yayi alwala,yazo ya fice masallaci.
jiki a sanyaye rahama ta matso gurin sanaya,kirkiro murmushi tayi gamida cewa.
"sannu da zuwa bakuwa,tafiyarku daya da yayana ko?"
murmushi sanaya itama tayi gamida cewa.
"yauwa rahama,tafiyarmu daya dashi"
Mamakine ya kama rahama najin sunanta a bakin sanaya,tunda taga safwan be kira sunan ta ba bare tace anan taji.
Hakade ta jata zuwa Ιakinta,ruwa ta bata tai alwala,ba abinda yafi ba rahama mamaki,kamar ganin suturar jikin sanaya,wani leshine da kwanaki taga irinshi gurin jummai dillaliya 400k,
kwata kwata rahama ta kasa sakin jiki da sanaya,har zuwa sanda ta zubo musu abinci,suka ci rahama dari dari takeyi ta kosa safwan yadawo gidan.
sanaya ko tana gama cin abinci ta bingire a gurin s bacci,sadaf sadaf rahama ta mike tafice daga dakin,kofar gida taje ta tsaya
Bata jimaba yadawo gidan,yasameta a waje,ayko faΙa yarufeta dashi,dukar dakai tayi tacr kasa kasa.
"ba dole in fito ba kaje ka dauko budurwa kamar yar aljanu dan kyau kazo ka ajiyeta a gida bakamin bayanin ko ita wacece ba,"
Murmushi yayi yacr.
"wlh rahama kin bani da tsoro,yanzu macen ma tsoronta kikeji"
dariya tayi gamida kama hannunshi suka juya zuw cikin gidan.
a tsakar gida ya zauna kan tabarmar data shimfida masa.
abinci yaci tukuna,sannan bayan ya gama,ya kwashe duk abinda ya faru yafadamata.
Idon rahama kamar goruba tace.
"yaya kana nufin wannan yar gomnan garinnance Kuma matarka?"
tsaki yayi gamida cewa.
"to meye aciki na mamaki,da har kike wni zaro ido?"
Bata kulashiba da gudu ta mike ta koma dkinta tana karewa snya kallo cike da tsananin mamaki,dan ita ko me ayki. Gidan gomna bata tabazaton ganinta ba ko a mafarki bre yarshi.
muje zuwa
nifa Allah ya sni thanks dinna ce ta fama bana so nafiso ayi sharhi shine ke bani kwarin guiwar yin wani akan lokaci
Surbajo for life.
January 15 at 9:19pm Β· Public
*SANADIN KIDNAPPING*
*ZAHRA SURBAJO*
*Haba yan amanar surbajo,wato zahra surbajo novel group,don Allah ku dunga hakuri kunji,koda nice nai muku laifi don Allah kudena cewa left shine masalaha,bare in wanine yay muku,danni de nidaku mutu ka raba,dan duk wacce ta fita sena dawo da ita,duk da banfiye zuwa online ba yanzu amman inde nazo nasamu ba wata tofa zan dawo dake
don haka don Allah kuyi hakuri da juna,in kuka rushe nima na rushe ,kusha kuruminku register ta kiran suna zan muku sabida tsaro *
*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*
*25-26*
Sanaya jin mutum akantane yasa ta farka,wata kara tasaki na razana da gnin inda take,dan ta manta tabiyo safwn gidansu,azatonta saceta aka sakeyi
Jin ihun tane yasa safwan dake waje shiga dkin da gudu,rahama ko mannewa tayi da bango dan itama a tsorace take,dan bata san abind yasa sanaya yin ihu ba.
Sanaya ko ido a rufe take ta faman buge buge na neman hanyar gudu,da sauri safwan ya isa gareta akayi katari ko ta fado kirjinsa.
Rungumeta yayi tsaf a jikinshi,tuni sanaya ta dwo cikin hayyacinta dan jikin safwan ta jima d haddace yadda yanayinsa yake,dan haka bata bukatar karin bayanin ko waye ya rungumeta.
kwantar da kanta tayi akan kirjinshi,tana maida numfashi,kasancewarta shagwababbiyane yasa bata dena kukan kasa kasa ba.
yawan gashin kan sanaya ba safwan ba hatta rahama seda ta yi mamakinsa,dan gaba daya ya rufemata rabin bayanta,
Hannu safwan yasa ya yaye mata gashin da ya rufe mata ido,yadan sunkuyo daidai kunnanta yace a tausashe.
"me aka miki ne?"
sinne kai tayi gamida yan soshe soshe na alamun taji kunya,.
kara matseta yayi ajikin shi yace.
"oya tell me,whats wrong with you?"
A kunyace tace.
"Nothing"
"are you sure?"ya tambaya.
"very sure"ta bashi amsa.
Har alokcin be saketa ba,seda yaga ta ntsu sosai,yana sakinta,ya juya ze fice a dakin,ji yayi an ruko shi,kan ya juyo ita ta karaso gabanshi.
langabe kai tayi,ta kureshi da idanuwanta masu kama dana ashwairiyya,shima binta yayi da ido,tabe baki tayi alamun kuka tace.
"tsoron dakin nakeyi fa,kuma naga zaka fita ka barmu mu biyu"
Yasan zaa rina,dan ya fahimci shine abund ya firgitata dazu,
"to ya kike so nayi muku,munan shine inda muka saba rayuwa,so mu be bamu tsoro"ya bata amsa.
sakalo tayi tana kallonshi,dan ta fahimci akwai alamun bacin rai agame da amsar tashi.
"Allah ya baka hakuri ni ba nufina kenan ba"tace tana share hawaye sakinshi tayi ta koma gefe ta takure,
sa kai yayi ya fice,adakin.
Rahama cr ta karaso gurin sanaya tacr
"kiyi shuru kinji ba abinda ze sameki da yardar Allah ki kwanta kiyi bacci"
murmushi sanaya tayi gamida kwantawar kamar yadda rahama ta bukata.
itama rahaman kwanciya tayi abinta kan wani lokacu tuni tayi baccinta,sanaya ko idonta biyu,
ga aladar berayen gidan su safwan se cikin dare suke shagalinsu,dan haka yanzunma farawarsu kenan.
tim sanaya taji abu ya fado mata akanta,da sauri tamike,ta haska fitilar wayarta,wani rusheshen berane tagani yana kada bindinsa,
Wayyo sanaya,mikewa tayi tsaye tana ta guje gujenta,sabida berayen sunkai shida a tsakar dakin.
Rahama ga nauyin bacci sam batasan wainar da ake toyawa ba,sanaya se kuka take jikinta na bari,
Safwan daga dakinshi yajiyo karar guje guje,da kuma sautin kuka,da sauri ya fito daga dakinshi,yana fitowa ya fahimci daga inda karar ke fitowa,da sauri yaje ya tura kofar gamida haskawa da torchlight din hannunshi beraye n yaga suna guje guje tare da sanaya,wacce hatta zanin jikinta ya kwance,daga ita se pant sabida ita dama ba gwanar saka underwear bace.
Fararan cinyoyinta a waje se sheki suke,tayi gumi kashirban tana kuka.
A karo na farko da wani tausayinta me tsanani ya kamashi,da sauri yaje gurinta,yasa hannu ya dagata sama, da sauri ta kankameshi tana fadin.
"don Allah kataimakamin wlh bana kyamar gidanku amman wainnan halittun zasu hallakani"
bece mata komai ba ya juya ya fice da ita dauke a hannunshi,
Dakinshi yakaita,wanda shi akwai gado me rumfa aciki,dade sauran kayan afanin gida haka,sabida shine dakin ummansu kan ta rasu,Rahama ta guji dakin ne sabida tuno umma da takeyi aduk sanda ta kwanta aciki,babu yadda safwan beyi da itaba amman fafur taki aminta da dakin,shiyasa shi yake kwana aciki ita kuma ya bar mata nashi.
Kan gadon yaje ya dora sanaya,sannan ya koma ya rufewa rahama dakin shima yadawo ya rufe nashi.
Rawar sanyi sanaya takeyi sabida rigarta data jike da gumi batare da tunanin komai ba ta cire rigar ta cillar sannan ta shige cikin bargon nan irin na fulani me ruwan toka.wani dumi taji ya ratsata,
Safwan hawa gadon yayi shima sannan ya gyara net din dake jiki gudun haurowar berayen dan ko adakin nashi akwaisu.
bude bargon yayi da nufin ya rufa shima,arba yayi da boobs din sanaya da rabinsu basa cikin bra din,sunyi tirtsi tirtsi suna kallonshi,
wani abune kemasa yawo ajiki wanda yarasa ko menene,daurewa yayi ya kwanta amman idonsa na kansu.
A zatonshi tayi bacci ne, sede yana kwanciya ta mirgino jikinshi,ta dora kirjinta akan nashi,tacr cikin dasasshiyar murya.
"sanyi nakeji,pls ka rungumeni"
Shuru yayi kawai,dan shi kadai Yasan yanayin da yake ciki awannan lokacin,hannu yasa yaja bargon ya rufesu sannan ya gyara mata kwanciya ajikinshi ta yadda zataji dadin baccin.
muje zuwa
Surbajo for life.
January 16 at 9:38am Β· Public
*SANADIN KIDNAPPING*
*ZAHRA SURBAJO*
*ESHA MUSTAPHA, ALLAH YA SAUKEKI LFY,YADDA YA SHIGA ANA DARIYA ALLAH YASA YAFITA ANA DARIYAR
,DAKE DA SAURAN MATA MASU CIKI ALLAH YA SAUKEKU LFY DOMIN ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR'ANI AMEEN,KEDA UNBORN SURUKATA KULLUM KUNA RAINA,ALLAH YA KAWO MANA ITA LFY,IN KUMA SIRUKINE SHIMA MUNA MASA FATAN ISOWA CIKIN