Showing 15001 words to 16870 words out of 16870 words
cikin dakin tana kuka ,
Arazane sanaya take binta da kallo inda ta kasa daurewa tace.
"sister lafiyarki kuwa?"
Cikin kuka tace.
"aunty yayane nakirashi ina fada masa abinda ya faru dake nace yau saura kiris ki mutu be jira na karasa ba se ji nayi hayaniya agurin ana fadin wai akira ambulace ya fadi"ta karasa maganar tana kuka.
wata irin kara sanaya tayi itama ta koma ta kwanta sharab,agigice ayi kanta sede ina ba numfashi jikinta.
Daddy gurin gudun kiran doctor har faduwa yayi sabida rudewa .
Doctor na gaba daddy na binshi abaya gudu suke amman daddy har hankadashi yakeyi,dan ya raina gudun nasa.
Doctor be jira wata wata ba yasawa sanaya oxcygen,
Duk wani taimakon gaggawa shi aka mata,inda akasamu ta farko,sede fa ta dage ala dole se ankaita gurin mijinta,hankalin daddy in yayi dubu ya tashi,ko kadan taki jin rarrashi,ita sede akaita gurin safwan.
Shiko safwan yanacan rai ahannun Allah dan dan ji yayi rahama tace mishi sanaya ta mutu.
Koda aka kaishi asibiti babu sauyi,dan ko numfashi bayayi.
Rahama kuka tasa su daddy agaba itama tanayi akan ataimaki dan uwanta.
Akaro na farko da daddy yaji tausayin wani abu da ya shafi safwan,
Wayar babban sojan dake kula dasu safwan din ya kira,inda ya bukaci da asako safwan ajirgi zuwa kaduna yanzu yanzu.
Cikin awa biyu an iso da safwan kaduna,karkashin rakiyar sojoji,ciki harda babban sojan.
Ambulance ce ta daukoshi zuwa asibitin garden city dake kaduna.
wayyo sanaya jin ance an iso dashi da kyar ta iya mikewa rahama da munaya suka riketa zuwa inda aka doroshi akan gadon daukar marasa lfy,yayinda duk jikinshi an daureshi da belt,
Jiki na bari sanaya ta dora hannunta akanshi tana fadin,
"hubby pls katashi,karkaimin haka,ban mutuba gani nan da raina harda yaranmu katashi kazo muje ka gansu"ta fadi tana kuka.
Hmmm love magic ya wuce wasa,se gani sukayi safwan na motsi,gamida tari
Da sauri aka karasa dashi dakin da yadace,wanda tunkan ashiga ya bude idonshi yana kallon sanaya hawaye nabin idonshi.
Daddy komawa gefe yayi yana kallon sarautar Allah,danshi ko a film betaba ganin so irin wannan ba,se ayau ya yarda babu me rayuwa cikinsu in ya rasa dan uwansa,sosai ya gamsu da son da sukewa juna.
Sanaya fafur taki daukar yaran bare ta gansu wai acewarta se safwan ya miko mata da hannunsa atare zasu gani
Muje zuwa anjima.
Surbajo for life.
May 9 at 11:44am · Public
*SANADIN KIDNAPPING*
*ZAHRA SURBAJO*
*Allah abin godiya masoya abun alfahari,kamar yau na bude group dina na facebook segashi yanzu kimanin mutane dubu dari da daya da dori ne aciki,ina alfahari daku ahlin group dina na facebook mazan ku da matanku,da zan iya lussafoku da ba abinda ze hanani yin hakan,daukacinku masu hankaline aciki,bakwa fada ko fadin bakar mgn wlh na shaideku,Allah yazaunar da masu auran cikinku lfy agidajensu,samari Allah ya kawo mace tagari,yanmata Allah ya kawo miji na gari,zawarawa kui hkr kui addua ga azuminan ya gabato,ku roki Allah duk damuwa ze yaye Allah ya aurar daku ga mazajen da suka san darajarku,maza abar ruwan ido mata adena jan aji(wulakanci),dan so nake kamun babbar sallah duk na aurar daku na huta ,Allah ya hadamu a aljanna cikin aminci,*
Facebook@zahra muhammad surbajo
Instergram@zahra_surbajo1
*Note:bana chartting inbox a facebook dan ko yanzu sakwannin dake jiran na karantasu sunfi dubu biyu,akwai wanda tunda na fara rubutu suka rubuto amman har yanzu Allah be bani ikon isa gurin ba,amin afuwa don Allah,wlh idona har ciwo yake in na fara dubawa,nafi yin chartting instergram,ko whatsapp,,taku har kullum surbajo*
*Dedicated to Fatima Abubakar Radda*
*41-42*
Haka sukai jugum jugum suna jiran fitowar likita,
Ba a basu damar ganisa ba seda ya warware tas,sedan abinda baa rasa ba sannan likita ya amince su ganshi.
Sanaya ce agaba,suna shiga suka ganshi andan jingina masa filo abaya yadan kwanta,shigowarsu ce tasa ya zabura da sauri ya diro daga kan gadon ya nufi sanaya dake dingishi ta nufoshi,
Da sauri ya karaso gurinta,ya duka agabanta,inda yasa hannu yadan daga zanin dake jikinta dan yaga me yasa sanayarsa dingishi,bega komaiba dan haka dago kai yayi yana dubanta,itama shi take kallo yayinda kowa na gurin su suke kallo.
Idonshi ne ya sauka kan cikinta inda yaga babu komaiazabure ya mike yana fadin.
"No!!!!No!!!!!!,"
Rungumota yayi jikinshi da karfi yana fadin.
"Ina babyn mu yake sinaya,?me ya sameshi ko shiyasa rahama ta dauka kin mutu ne,?tell me,"
Rungumeshi tayi itama tana murmushi gamida hawaye tace.
"hubby babynka be mutu ba,be salwanta ba,ammade badan taimakon Allah ta silar daddy ba da dagani har su mun zama yan gari a lahira"...
Jan hannunshi tayi zasu fara tafiya,dukawa yayi ya dauketa cak dan baze juri ganin tana dinshi ba,
Adaidai kofar fita suka ci karo da daddy dake tsaye yana kallonsu,safwan kallonshi yake cike da mamakin ganinshi agurin.
Ahaka suka wuceshi,zuwa dakin da jariran suke.
Sanda safwan yay arba da yayan sa kadan ya rage ya suntuma sanaya da kasa dan ya kosa ya isa garesu.
Wayyo dadi,rasa inda zesa kanshi yayi dan farinciki dukawa yayi ya kwasosu gaba daya jikinshi,yana kuka,yaran ko sunyi kuri suna binshi da ido,mikawa sanaya yayi su yana fadin.
"sinaya bantaba son abun kwatankwacin son da nake mikikeda yaran nan ba,inkika cire iyayena da rahama,sinaya babu abinda nakeso sama dake,"
Rungume juna sukayi suna kukan murna rungume da yaransu.
Rahamace ta karaso gurin ta rungumesi itama tana fadin.
"Allah mungode maka daka turo mahaifin sanaya ya ceci rayuwar sainnan family dayanzu wannan farincikin bamu ganshi ba".
Waigowa safwan yayi yace.
"bani labari mana rahama me yafarune?"
Ba bata lokaci ta kwashe komai ta fada masa duk yadda akayi.
Wasu hawayene kebin fuskarshi,bin yaran yake da kallo cike da danasani,wai jinin wanda ya tsana fiye da kowa yau shine ya gauraya dana yayansa,wanda da taimakon hakanne yasa suke araye yanzu,wani kukanne yasake kwace masa.
Mikewa yayi ya nufi kofar fita inda ya nufi gurin da daddy yake tsaye.
Yana zuwa zubewa yayi akan guiwowinsa yana kuka,yakasa mgn.
Daddy binshi yayi da ido yayinda cikin zuciyarshi godiya yakewa Allah da ya bashi siriki kamar safwan,
Sunfi minti talatin ahaka safwan bedena kukaba kuma yaki mgn,shima daddy haka.
Daddy yagaza jure ganinsa yana kuka besan sanda ya mika hannu ya dagoshi ba da sauri safwan ya shige jikinshi yana kuka.
Rungume juna sukai shima daddy harda kwalla seda ya fitar.
Su sanaya da suka fito ganin abinda ke faruwa sosai sukaji dadi,
Safwan zeyi mgn daddy ya rugashi da cewa.
"komai ya wuce,kayafeni nine ummul abaisin faruwar komai,don Allah ka yafemin"
"tsakanin uba da da babu neman gafara daddy komai kayi akaina daidaine"cewar safwan cike da kulawa.
Ranar de kowa bakinshi yaki rufuwa,dan murna,.
Ba abunda yaba kowa mamaki se sanda safwan ya gama yin huduba wa yaran,aka tambayeshi sunansu.
Yace
"dukansu sunan daddy na sa musu,dan shine sunan da yafi dacewa dasu su duka sabida muhimmiyar rawar da ya taka arayuwarsu,"
Daddy murmushi yayi,najin dadi.
Aranar aka sallami love birds daga asibitin.
Kai tsaye gidan su sanaya aka nufa da ita,dan mummy tace se anmata wankan jego.
Safwan be musa ba,haka aka tafi da ita,can din harda shi da rahama.
sanaya farincikinta be faduwa yau gata ta dawo gidansu bayan lokaci me tsayi.
Sosai mummy ke kulawa da sanaya har akayi suna na gani na fada,safwan raguna hudu yayi kokarin yankawa yaran nasa da duka albashinshi.
Babu yadda daddy beyi dashi ya bari ba amman fafur yaki.
Haka akayi taro aka watse.
Da yake safwan anbashi hutu gurin ayki hakan ya bashi damar wuni gidan daddy gurin sanyin idanuwansa.
Se dare yake komawa gida.
.
Shaheed da,hisham ake kiran yaran,wanda kullum suke gurin daddy matukar yana gida.
Daddy yayi yayi da safwan akan ya koma gidan da yabashi amman fafur yaki yace da kanshi yakeso ya gina gida.
duk wata gudummawa in daddy yayi yunkurin yimasa amman fafur yaki amincewa.
ganin baze amince bane yasa daddy batare da sanin safwan dinba,yasa aka kara masa girma sosai agurin ayki inda yake daukar albashin daya tasarma milyan guda.
Saɗwan sosai yayi murna dan shi ya aza kwazanshine yasa aka dagashi
Tuni yasai fili,dan haka ko batun komawar sanaya gida beyi,dan so yake se yagama ginin su tare agida.
Sanaya tuni tayi arbain,bame ganinta yace tayi aurema bare akai ga batun haihuwa
Sosai mummy ta gyarata,haka munaya ma baa barta abaya ba gurin kulawa da sanayar
Tuni safwan ya koma bakin ayki sede waya kullum suna makale awaya shida babynsa.
Yau watanni hudu kenan da haihuwar sinaya,tuni ginin safwan ya kammala,har saukar al'qurani anyima gidan,furnitures kawai ya rage azuba shima yafiso suje shida sanaya ta zaba.
Yau da kewar sinaya ya tashi dan haka tun safe ya shirya ya rubuta pass da yake babbane ba bata lokaci aka bashi.
Da azahar ya iso kaduna acikin motarshi,range rover wacce aka bashi sanda ya samu karin girma.
Sanda ya iso gidan ba kowa daga masu ayki se sinaya,dan har yaran suna gidan munaya ta turo an kwashesu,mummy kuma taje taro abuja,daddy bayanan yana office.
A falo ya sameta,da gudu ta nufoshi ta rugumeshi,dagata yayi cak yana shinshinata.
Kukan shagwaba ta farayi masa.
"oh baby ya akayi kuma,bakisan kin girma bane yanzu,kefa mamace"
Turo baki tayi gaba gamida fara dukanshi abaya tana fadin.
"shine tunda akayi kwana Ashirin da haihuwa baka zoba se yau wata hudu,wallahi mun bata ni saikeni"
da gudu ya haura sama da ita inda dakinta yake.
Kan gado ya dorata sannan yabi bayanta shima yadan kwanta ajikinta yace.
"to me zanzo nayi,kullum daddy se ya kirani video call ya nunamin su twins,ke kuma muna waya dama de innazo zan dan samu abun tabawane to danazo,to kedince tunda kika haihu se leeking kike,sekace damuna"yakarasa maganar cikin tsokana yana mata dry.
Kuka tasa mishi tana tureshi.
da sauri ya hade bakinsu guri guda ya shiga mika mata sako.
Wayyo abunka da anjima baa haduba.
Yi suke kamar zasu cinye junansu.tuni sun jima da rabuwa da suturarsu.
seda suka samu biyan bukatar juna sannan hankalinsu ya kwanta,kwance suke sanaya ta dora kanta jankirjinshi,se ajiyar numfashi sukeyi
dago fuskarta safwan yayi yana murmushi yace.
"komai naki ya sauya baby wlh har kinfi da dadi,meye sirrin,"
runtse ido sanaya tayi tana dariya tace.
"jego"
"Ayko inde jegone ke kawo hakan zan dage wajen ganin jego beyi nusa dake da yakai shekaru biyu ba"
Duka takaimishi tana dariya.
wanka suka shiga tare,inda sosai ya nuna mata kulawa.
Bayan sun fito suka shirya,safwan da kanshi yamata kwalliya,sannan ya jata suka fice daga gidan,
ba kadan sukai kyauba,abun burgewa.
gurin saida kayan furnirures yakaita ta zabi komai aka hada guri guda,akasa a mota,yabasu key din gidan,yace suje su shirya musu kamin dare.
daganan gurin kayan abinci ya nufa yasiya komai shima
Ya biya yasa suka kai masa gida.
sannan suka nufi gidan munaya,tana ganinsu tace cikin zolaya.
"marasa kunya wato kun biyo yayanku ko?"
Dariya safwan yayi yace"haka yake yayarmu ta minti biyar"
Dariya dukansu sukayi.
Sundan jima gidanta sannan suka kwashi yaransu zuwa yawon shan iska.
Sosai sukaji dadin fitar safwan manne da sanayarsa.
Da magrib,suka isa tsohon gidansu gurin rahama wanda tuni safwan yayiwa gidan kwaskwarima babu me cewa shine na da
Sosai rahama taji dadin ganinsu su twins se nan nan take dasu.
Basu jimaba,aka kirashi awaya cewa komai ya kammala na gidan,dan haka mukewa yayi yasa rahama ta dauki abinda takeso,suka rankaya gidan.
wayyo aljannar duniya,komai na gidan ya hadu,ba abinda yafi basu shaawa irin dakin su twins yadda aka kawatashi da kayan wasanni.
Rahama harda kukanta sanda taga duniyar da Allah ya sauya musu.
Tuni yasa aka kawo kayan abinci,dan haka sanaya da rahama kitchen suka fada suka hada abinci me rai da lafiya.
Can gidan su sanaya ko jin shurune yasa daddy kiran safwan anan ya shaida mushi aysufa sun tare agidansu sosai abun yaba daddy dariya,fatan alkahairi yay musu.
Rayuwar tayi dadi duk kunci ya yaye Allah kenan me yanzu yanzu.
*.Alhamdulillahi rabbil alamin*
Anan sanadin kidnapping yazo karshe ,duk inda nai kuskure Allah kayafemin inda nai daidai Allah kabanu ladan.
Semun hadu cikin sabon littafina me suna
*TAMBAYA*
Bayan sallah da yardar Allah.
taku har kullum zahra muhammad mahmoud wacce kukafi sani da surbajo.