Showing 1 words to 3000 words out of 15499 words
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʟᴀʙʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
all rιgнт reѕerved. no parт oғ тнιѕ вooĸ мay вe rewrιтe or тranѕмιттed ιn any ғorм or вy any мeanѕ wιтнoυт a wrιттen perмιѕѕιon ιғ тнe aυтнor wнo ιѕ тнe copyrιgнт owner
ᎷY ᏔᎾNᎠᎬᎡFᏌᏞ FᎪᎷᏆᏞY ᏞᏆKᎬ NᎾ ᎾᎢᎻᎬᎡ ᎢᎻᏆᏚ ᏴᎾᎾK ᏆᏚ YᎾᏌᎡᏚ ᎷY ᏞᏆFᎬ *ᎢᎻᎬ ᎻᎪᏴᏆᏴᏚ* YᎾᏌ ᎪᎡᎬ ᎪᏞᏔᎪYᏚ ᏆN ᎷY ᎻᎬᎪᎡᎢ ᏞᎾᏙᎬ YᎾᏌ ᏚᎾ ᏙᎬᎡY ᎷᏌᏟᎻ ❤🔐
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqqayah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
1
Katafariyar makarantace dake mabera cikin garin sokoto wato *Government Girls College* GGC.
Students kowa da abunda yake yi saka makon yau weekend ba class fitowar sukenan daga hostel an gama inspection kowa ta kama harkar gabanta sae himarsu sukeyi
Yan mata ne guda uku zaune a cikin kwanar suna fira hankali kwance waccen ke kan up bonk ta leko tace"sadixy wlhi na gaji da saka uniform da hostel wears ni yanzu burina kawae murubuta exams ace munyi candy"
Wacce aka kira da sadixy ta kalleta tace " kae uwar kwana baki da dama kice ke uniform din ma ke damun ki"
😄 Dariya tayi btace ba kedae wlhi abun ba'a mgn wae nikam yau me su farcy sukayi ne na gansu gurin mama principal tana musu fada"
Sadixy tace wlhi ban sani ba
Aaj ta bata yi mgn ba tunda suke firar su sae yanzu tace "wae marin wata Junior tayi shine takae karar ta"
Sadixy tace " wlhi matar nan na jamana raini hmm ni bari na daki wata taga mae min mgn"
Dariya sukayi gaba daya Raj tace kae diyar kwana shiyasa kike burgeni
Aaj tace ba wnn ba kun manta on monda muna da test din mai nika biology kuma gashi wnn matar mal Aysha Adila zata karba assignment din chemistry din ta
Raj tace kae ku bari sae gobe ko anjima wlhi duk na gaji da wnn inspection din na yau
Sadixy ta gyara kwanciya tace hmm ni bari na danyi bacci kafin ayi sallah"
Har ta kwanta ta mike ta fita wasu juniors ta gani tace" kar gaba dayan ku ku zo nan"
Da gudu suka nufi kofar dakin suka tsaya sae da ta gama kallon su gaba daya kana ta zabi yara biyu tace sauran ku tafi.
Juyawa tayi ta koma daki sae bayan ta kwanta tace ku min fitara har nayi bacci
Nan yaran suka duka suna yi mata fitara sae da suka tabbatar da tayi bacci kana suka fita
********★
Da dare bayan sun gama dinner gaba daya students din suka koma hostel wasu students ne yan jss3 suka taru a kwanar daya daga cikin yan class din su suna fira can sukaji ance *all j3 class* da gudu suka fita suna zuwa bakin kofar dakin suka hau layi wata yarin yace a karshe dan haka ita aka zaba.
Wannan dabi'ar bosa kenan idan tana bukatat wani zata tara gaba daya class dinda ta ga dama na hostel din duk wanda yazo a karahe to fah shi zaeyi duka aikin
Bayan sauran sun tafi tace yauwa so nake ki gyara min gadona kuma ki share dakin nan so goma bayan kin gama ki debo min ruwa a bucket" tana gama fadar haka ta juya tayi gaba
Nan yarin yar ta hau gyaran gado gashi gaba daya duk gadon kayane haka ta linkesu ta gyara gado tayi shara kamr yanda akace ta debo ruwa ta tsaya jira dawowar bosa dan tasan halin ta idan ta tafi toh ko jaki sae yafita jin dadi
Zama tayi tana tunanin test din da garesu on monday gashi ko karati batayi ba kuma teacher din mugu ne baya bada simlpe questions kuma idan kayi failing ya zane ka hade kanta tayi da gwiwa tana tunani can sae ga bosa da sautan yan dakin su sun dawo tare da wata junior tana ganin su ta mike tsaya ita bosa gaba daya ta manta da ita sae da taga gadon kana ta kalla yarinyar tace "sau nawa kika yi shara"
Yarinyar tace "sau goma"
Bosa tace "ina ruwan da na aikeki debowa"
Tace "gasu can"
Sae da ta zauna ta kalla Junior dinda suka zo tare tace " ke kneel down kuma ki sani a haka zaki kwana"
Hawaye yarinyat ta goge tayi yanda akace tayi
Bosa kuma ta kalli dayar tace jeki ta fita tana tunanin waccen da akace a haka zata kwana gashima js1 take abun tausayi Allah ya isa ta dinga jerawa acikin ranta har ta kae daki.......
Vote
Comments
&
Share
#ayshartou
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
2
.....Yau sunday gaba daya students din sun fita sanitation kowa an bashi portion dinda zae gyara basu gama ba sae kusan 12 kowa kuma ya kama harkar gaban sa masu wanki nayi masu kitso ma haka wasubkuma karatu aukeyi wasu ko assignment wasu kuma zaman banza gaba dayavkowa na rayuwar sa.
Bosa ce ta kira yarin yar da suka shigobdaki tarw jiya tace ga uniform dinta ta wanke su tas idan suka bushe ta kawo yarin yabkaram ba yanda ta iyavdan tasan halin bosa sarae duk acikin seniors dinsu tafi kowa mugunta da cin amana.
Raj sadixy da Aaj zaune suke a dakin su rabash suna fira gaba dayan su Aaj na ma zee kamaila kitso mar kuma na musu kwadon cornflakes da sardine bayan ta gama suka zauna sukaci bayan sun gama Rasheedo ta ska aka kira mata dika dikan yan mata na ss1 ta tarkato gaba daya kayan wankinta ta bada harda sabuku da kiln ta hada musu suka kwasaa tafi Rag ta aika aka kira mata skl dota dinta Asma'u santali ko da ka je sae akaga tana wanki hakan yasa aka dawo aka sanar ma Ruqayyah asma'u na wanki kuma senior bosa ce ta bata tace idan ta gama zata zo
Da sauri sadixy da Raj suka tashi suka fita a tare Aaj tace ke sadixyvina ruwanki wlh kidae na siyan fada
Tsakibkawae tayi taja hannun Raj suka fita basu tsaya ko ina ba sae gurin bosa sadixy tace ke bosa mae haka yanzu ki rasa duk cin yan matan dake skl din nan wa zaki saka ya wanke miki kayanki sae wnn jaririyar yarinyar dako kashi bata isa gama wanke ma kanta ba toh wlh idan kika kara sae mun saka kafar wando daya dake ke kin sanni na sanki ta juya ta kalli asma'u tace ke kuma ajiye kayan nan ki tashi mu tafi tunda bana uwarki bane jiki a sanyaye ta mike ta buya a bayan Raj
Bosa da ranta ua gama baci tace wkh sadicu ki fita daga idona oh su sauran yaran da akae sakawa aiki ba mutane bane
Saidicu tave oho wnn kuma ke kika sano amma wlh kika kara saka wnn yar gold in aiki haduwar mu baza tayi kyu ba
Gaba daya yan sauran dakin su bosa suka taso da fada dama su kowa yasan basu mkuma duk student sunfi tsoronsu akan kowa sadixy tace dan gin mahaukata zuri'ar mugaye yan uwan azzalumai wlh kuji tsoron Allah kuna tunanin addu'ar da yaran nn keyi muku baza ta kama ku wlhi sae daya daga cikin ku ta rubuta ecams taga flat f9 baku saka komae gaba ba sae cinzali da iskanci gaba dayan ku da za'a kara muku interview inada tabbacin da primary kalar brain dinku ya dace
Tana kae nan t suka wuce abunsu sauran kuma suka rakasu da zagi.
*ASALIN RUQAYYAH RAJ*
Sunan ta Ruqayyah Ahmad Jega zuwanta skl ne aka mae da mata da suna _RAJ_ sadixy kuma tana kiranta da uwar kwana
Ya ce ga babban lawyer mae zaman kasan wato Barrister Ahmad Y. Jega aslin babanta dan garin jega ne amma gaba dayan su suna zama a sokoto ne gaba daya rayuwar au a sokoto suka santa matan shi biyu hjy Rabi wacce auke kira damamar birnin kebbi sbd ita a can ta koma da zama yanzu kuma itace uwar gida tana da yara 7 sae hjy Hassana wato amary kuma maman Ruqayyah tana da yara 8 itama amma shida ne kadae a raye Aunty sha itace first born sa ya kabeer sae aunty hafsa sae ya zainab sae Ruqayyah sae sumayyah sae wta ameena amma allah ya mata rasuwa sae autansu abdulnaseer
Suna zama na mutunci gaba daya basa fada dansu basu dauki wani abu wae shi kishi a zaman su sae dae son barka
Mama sokoto da babansi auren zumunta ne auren dangi
Maman sokoto sun kasan ce sune first born a gdan su ita da yar uwarta ya'ya ga late musa Habeeb kuma asalin su ba yan nan bane kakan mamansu wato Habeeb ya dawo jega da zamane sanadiyyar wani fada da akayi a chan wata kasa guraren sudan su uku ne a gurin iyayen su toh sanadiyyar wnn gusun ne yasa dukan su suka rabu sae daga baya habeeb ya gane dan uwanshi dake zama a zamfara amma shi na ukun har yau ba wanda yasan shi sunyi nema har sun gaji suka barwa Allah.
Matarlate musa ita hjy Hadeeza mata mai mutunci da karamci yaranta 8 hudu mata hudu maza hasana da husaina ne farko sae Ameen sae Basheer sae zainab murtala Mukhtar Asma'u gaba dayan su sun taso cikin gata da so da kauna har Allah ua dauka ran baban su basu raba kansu ba ko a tsakanin yaransu baka gane waye dan wnn kona wnn sbd kansu a hade yake komae basa yi sae da shawarar junan su.
Itama Ruqayya ta taso cikin tsantsan so da kauna daga gurin mamanta da babanta bata da hayaniya ko kadan kuma ba ruwanta she is so silent baka taba jin bakinta idan ana fira kuma kyakykyawa ce ajin karahe though bata da tsowo amma kuma baza ka saka ta a jerin guntaye ba black beauty ce sosae ga gashi ga ilimi Allah ya bata shi yasa iayayenta ke sonta ko acikin yan uwanta gaba daya halayyar mamatr ta ta dakko ta cika sanyi bata son fada shiyasa mutane ke ganin kamar dan bata da karfi ne shi yasa amma sam ba haka bame Allah dae bae yita da haya niya bane gaba daya.
Aaj sunanta Aysha Ahmad Jega kanwar Ruqyyah ce amma few months ne kawae a tsakani Aysha tafi Ruqayya tsawo sosae kuma kansu a hade yake ko kayan sawa basa yi sae iri dayabharta da underweara dinsu iri dayane shi yasa wasu ke ce masu yan vmbuyu duk da basa kama ko kada........
Vote
Comments
&
Share
#ayshartou
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
3
.......Ruqayyah suna ss1 aka maida su GGC sabodan son boarding school da takeyi ita da yar uwar ta anan ne suka hadu da sadixy ita kuma real name dinta Khadeeja Abdullahi Gobir farkon zuwanta skl din ba mae shiga harkar ta gaba daya yan class din basa kula ta ganin haka yasa itama ta kama kanta bata shiga harkar kowa kuma gata da kokari da maida hankali akan karatu.
Ganin haka yasa Raj ta fara janta ajiki acewarta bae kamata ba abunda yan class dinsu keyi da haka suka saba sosae kuma itama yar skt ce babanta babban mai kudine abunda yasa take skl din ma yanzu sbd mamanta bata gdan baban kuma gasu da yara da yawa kowa da mamanshi suka dae yaran wani katon part ya ware musu iya su da masu musu aiki set by set wani shi kadae ne bashi dan uwa wasu kuma su biyu haka dae ba wanda ya damu da tarbiyyar su hakan yasa maman sadixy ta maidata boarding bayan tayi aure.
Acikin su uku din Raj ce bata da fada ita data ga an fara ma kuke take saka musu idan kuma fadan da ita akeyi toh su zasu siya sae daga baya kuma suyita mata masifa wae ita wawiua ce ta cika tsoro sae dae taji su kawae ta share...
Wannan kenan
*MONDAY*
Hmm ranar da kowa ne mutum ke tsoro tindaga masu zuwa skl har masu zuwa aili kuwa.
Assembly aka bayan an gama kowa ya koma class dinshi ss3B mai nika ne a class dinsu wato biology teacher (haka suke kiranshi da) kamar yanda ya fada test zae musu hakan kuma ba'a fasa ba yana shigo yace morning all submit ur books b4 i count 3
Da gudu kika ga suna submintting dinshi a kan desk sbd sun san halin sa baya wasa bayan sun gama ya zaro paper daga cikin envelope ya fara rabawa abunda basu ta tsammani ba suka gani gaba daya kowa da kalar questions dinsa kafin kisamu mai irin naki sae kin kirga mutum biyar wadan da basuyi karatu ba duk suka sha jinin jikinsu bayan ya gama yace u can start now and u give i only 15mins
Kowa na iya kokarinsa yaga ya gama wadan da are not seriois kuma in banda kallon sama ba abunda suke yi sae cin marfin pen
Wata student gaya tana kallonshi yace ye look at me wel wel maybe u find the answer in my face will u write something my frnd kasa tayi da kae tacigaba da abunta
Hmmm maryam (em jamil) ya gani tana bacci hankalinta kwance paper ya samu ya tura mata a hanvi da sauri ta mike tana hafa hancinta ganin shi yasa ta gyara zamanta tana hamma tace sir i dont kniw what to wirte cn i just give u ur paper kallonta yyi yace ehhh see ur nose like shortnika if i trash u here ko baki san komae ba sae bacci everyday u will be sleeping in d class sleeping master just ask ur papa ya miki aure cause he is just waisting his money ne baban gwaza big for nothing ba yan class ba ko readers sae da sukayi dariya 😆
Ruqayyah ta fara submitting sae class captain kana sadixy da AAJ ma sukayi
Yana fita malam Aysha Adil ta shiga dama sun san policy dinta idan ta bada assignment kafin ta shiga class toh kowa ya tabbatar yyi submitting idan ba haka ba toh na kowa baza karba ba kuma zatace shine test dinku over 40 shi yasa kowa ke bayar wa kafin ta shigo.
Bayan sun tashi hostel suka koma bayan sallah daga can suka wuce dining da bayan sun gama kowa ya fada kan gado dan sun san halin manyan nasu.
Basu tashi ba sae da aka fara kiran sallah daya daga cikin yan ss2 ana kiranta da rumeey ta daura abincin kan stove tana jin alamun ss3 ta dauki duka stove din da tukunyar ta saka acikin locker dinta ta fita sae da akayibsallah kana kowa ya shiga class gurin evening prep.
Su Raj da wasu yan class dinsu kuma suka zo satar ruwa suka ga dakin su rumeey na hayaki da gudu suka fita suna ihun gobara.......
Vote
Comments
&
Share
#ayshartou
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
4
...... Da sauri staffs dinda ke quaters suka fito mama principal ranta gaba daya ya baci bayan an kashe wutar ta tara duka students din emergency Assembly fada ta musu sosae ta dora da fadin wlh baza ku kara cooking ba gaba da na hana zuwa da wani kayan abinci fatan kunji me na fada kuma wadan da hostel dinsu ya kone suyi squatting a hostel din yan uwansu
Bayan assembly kowa ya koma class nan fa aka samu topic of discussion duk inda ka kutsa magnar akeyi hmmm abunka da boarding harda kari
Da dare bayan sun dawi daga night prep nan fa wadan da hostel dinsu ya kone suka fara neman gurin kwana da kyar kowa ya samu ya kwanta har zuwa gari ya waye
Washe gari bayan sunje class yan ss3A babban R ne yashiga class dinsu wato mathematics teacher dinsu bayan sun gaida shi suka zauna malamin ba ruwanshi ya cika sakin fuska sosae ya juya ya kalli board ya fara rubutu *MEASURATION* ya juya kalli students din yace our today's lesson is measuration with full confidence Bosa tace but sir u wrote *MENSTRUATION* dariya aka saka duka class din hakan ya bata mishi rae ya hade fuska yace am not here for joke i know u were thought this topic in ur ss1 or 2 mine is just to revise so ols concentrate dariyar suja tsagaita ya cigaba da da musu explaining sae bayan ya gama lesson din gaba daya farcy tace excuse me sir juyowa yayi yace yes how can i help you tace sir i dont understand yace where tace from the beginning wani kallo ya watsa mata kana yace u mean all di time i wasted u re saying u dont understand sha dat is ur own cuo of tea i have done wat i can dat y i like ss3A they don't play with their studies but u dis class gaba daya an hada masu fish brain a guri daya tsaki yyi ya fita abunshi nan suka dinga zaginshi suna tsine mishi
*SS2A*
Biology teacher dinsu ne a ciki Nawaaz explanation yake musu akan *EVOLUATION* abinka da students kuma masu tashen balagar tsuntsaye sae dariya suke yi dama tunda suka fara hormones shikenan yaran suka maida abun dariya da anyi abu daya sae wnn ta kalli wannan sae kaga sunyi dariya hakan yasa malamin daure fuska.
*Breakfast*
Bayan an fita break daddy 501 (haka suke kiranshi) mugune sosae shi acewar shi ma cinzalibakwae dadi shike yanka portion idan kayi laifi.
Wasu students jss3 sukayi laifi wani uban katon portion ya yanka musu koni abun ya bani tsoro dan wlh ko maza aka saka sae sunsha wuya kagin su gama kuka suka fara suna rokonshi shiko mugu sae faman dariya yake ba yanda suka iya dole suyi gashi suna da test din B/tech.
Bayan an koma class malam Aysha Adil ta shiga ss3B bayan ta gama lession ta basu assignment dan ita kullum