Showing 12001 words to 15000 words out of 15499 words
da sauri suka cusata kasan pillow kowa ya kama gabansa dariya ta tuntsere da ita sae da tayi Mae isarta kana ta tsagaita tace" matsoratan banza gaba dayan bakwa tsoron Allah"
Chaaaaa sukayi kanta suna masifa akan ta katse musu kallo da sauri ta zauna kan gadon tace"dama dazun bana gani da kyau yanzu kuma dole gani fa Hafeesha Zan zauna"
Kowa ya fara wlh sadixy Baki isa ba kawae kowa ya koma gurin daya zauna.
Hade fuska tayi tace"wlh sae dae a gas kallon Nan Dan yanzu sae na Kae Kara gurin mama principal"
Hafeesha tace"abun bae Kae chan ba nikam Dan Allah ku zauna mu karasa kawae"
Bosa tace"aikin banza ki Kae Kara din wlh sae dae asirin kowa ya tonu sbd kema ae kinzo da waya"
Dariya tayi tace"da ake cewa bakida wayo ban taba sani ba sae yau a tunanin ki Dan kinje kin fada shi zae saka ache na fito da wayar besides bama yarda da mgnrki akeyi ba ko kin fada kinyi a banza yarinya Dan Allah Kama hanya ki tafi yanzu sauri sauri me Kika tsaya jira kuma"
Hafeesha tace" Kinga sadixy nikam ya wuce Dan Allah ku zauna mu karasa inaso idan aka kawo wuta Zan saka chargy"
Ba yanda suka iya sae dae suka zauna a hakan har aka gama kallon Dan sun san halin sadixy rass basae an fada musu ba.
_____________★
Yau ta kama visiting gaba daya makarantar ta kicime da hayaniya ko Ina kaje wannan Karan Hafeez bae samu yazo ma Ma'u visiting ba sbd ya tafi service sae dae ya bada sakonta Dana Raj.
A lokacin ne kuma ake gayawa su Raj basa nan za'ayi aure wata cousin sister dinsu Rasheeda abun bae damesu ba Dan ba shiri suke sosae ba.
*R* ayuwa sae tafiya take dan yanzu students suna Fara shirye shiryen Fara exams Amma Banda ss3 sbd su zasuyi mock ne kafin suyi jamb........
*Inshallah book din ya kusa zuwa karshe*
Sorry sisters it seems like nayi repeating part 14 say biyo sorry pls mistake nayi
Comments
Vote
Share
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
http://ayshartou.blogspot.com
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
17
........Yau ta kama Monday kuma yaune zasu fara exams bayan an gama assembly kowa ya Shiga yana jiran invigilator yazo Bayan Kamar 30mins aka fara raba papers English...
Ss3 kuma suna hostel kowa da abunda suna sharholiyarsu wasu na bacci wasu kuma shara wasu kuma fira. Kowa dae da abunda yakeyi.
Malama shafa ce tashigo ta fara korasu class sae turo baki suke suna aika Mata da zagi. Bosa Kam kwance take ragajab tana bacci sae saukar duka taji a cinyarta a firgice ta tashi tana missika Ido malama shafa tace"dallah tashi ballagaza kawae kin kwanta kin wani saki jiki gaki kwatuwa"
Turo baki tayi tace" yoo Naga ai malama ba exams zamuyi ba meye kuma na tadamu"
Maka ta Kae Mata ta kauce tace"Dan ubanki class zaku je wannan zaman banzan baza kuyi shi ba sae kace ba exams zakuyi ba"
Tashi tayi tana turo baki dukansu suka fita sae class suna zuwa kuwa suka kulleshi ta ciki Dan basa so ko wane teacher ya shigo blanket suka shifida Nan f fira ta barke sae tsif suke abunsu duk malamin da yazo yayi knocking basa budewa"
_______★
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya watarana suje class wani lkc kuma suna hostel sauran students kuma ana Shirin tafiya gda.
Yau Friday hostel duk ya kitsime yayi dirty sbd masu tafiya gda gobe. Raj tace"Ni wlh yunwa nake ji kamar Zan mutu"
Aaj tace"Bari na Mana socking indomie"
Ushe tace"Bari zanyi kawae"
Koda ta duba dakin ba ruwa sae ta wuce dakin dake kusa da nasu kasan bonk ta fara dubawa ko zata samu ruwa dayake magrib ta gabato kuma duhu ya fara sauka sae kawae ta karkata kan bucket din ta diba kuma direct cikin indomie Dan already ta zuba a roba tana neman ruwane kawae.
Rufewa tayi ta mike ta koma daki sae gashi an zo korarsu sallah hakan yasa ta ajiye akan idan sun dawo sae suci kana tayi.
Bayan an gama sallah suka dawo kowa da yunwarsa Koda sadixy ta kunna torch light dinta ta haska sae kawae gani sukayi ruwan wanki ne gashi indomie din ya jika kuwa kowa tsaki ya fara wasu kuwa dariya suka saka Raj Kam ae kuka ta saki Dan wata irin yunwa takeji kamar me..
Sadixy ce ta fita da sauri sae gata ta dawo da golden morn a hannun ta mikawa Raj da sauri ta karba ta fara sha Kamar Bata taba cin abinci ba.
Washe gari aka fara kwasar students ranar ne kuma za'ayi ma su Raj visiting ae kuwa duk anzo musu sae wadan da iyayen su keda uzuri.
Zaune take gaban mama tana"mama Ni wlh bana son irin wanna sardine din Allah Kamar zarni yakeyi"
Mama tace"to ku barshi Mana idan na koma sae na bama yayanku ya Kae a chanza wanne kuke so"
Aaj tace"Titus Dan yafi dadi"
Tace"toh shikenan fatan dae ba wani matsala"
Suka ce aa Raj tace" wae Ina ya Bg?"
Mama tace"ta tafi argungu last week maybe ma ta dawo Monday"
Tace" Dan Allah mama idan ta dawo kice tazo"
Mama tace "to Zan gaya Mata"
Haka suka cigaba da firar su har lkcn tashi yayi suka watse.
Bayan sun koma hostel suka gyara duk abunda zasu gyara suka shirya komae.
Daya daga cikin metron dinsu ce ta shigo suna kiranta da baba sa'a tace" ku tashi ku gyara hostel din Nan ko Ina yayai dirty"
Chaaa sukayi Kanta suna su bazasu yi ba tunda Basu suka Bata ba.
Dole ta hkr ta koma suka nema masuyi...
*EXTENSION*
💃💃💃💃💃💃💃
Comments
Vote
Share
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
http://ayshartou.blogspot.com
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
18
.......Zaman extension suke cikin jin dadi dan yanzu ba wani malamin da ke takura musu duk abunda suka ga dama shi skueyi. Waya kuma sun dae na boyewa fito da kayansu suke masu sneaking kuma sunayi kuma ikon Allah har yau ba'a kamasu ba.
__________★
A gidan su Raj twins sister din mom dinta ba lpy sosae mma Hassana kariya ta samu a kafa kuma har India akaje gyara bayan sun dawo alhmdllh kafar tayi sauki saw dae tana yawo da sandar dake taimaka mata.
Macece Mae matukar son mutane kowa natane gaba daya tundaga siblings dinta har y'ay'ansu sun mai data kakarsu sbd yanda suke wasa da dariya kuma hakan baesa raini ya Shiva tsakani ba duk wani Mae matsala toh mama yake gayawa a duk cikin gdansu kowa ya tashi Neman shawara toh mama yake nema.
Tunda ta karye lpy ta mata karanchi bata kwana biyu bata kwanata ciwo ba yau lpy gobe ciwo hardae abun ya kae ga kwantar da ita hospital din Sokoto kuma.
Ba wani chanji da aka samu a tattare da ciwon ita kadae tadan abunda take ji a jikinta. Su yaya BG ne suka shigo dawowarta kenan daga abuja shima dan an gaya musu anyi admitting mama ne. Tunda taga condition dinda mama ke ciki hankalinta ya tashi itama sae kawae taji zazzabi na Neman rufeta har dare suna asibitin sae da Dr yazo yace ya kamata su tafi yanzu Dan basa bari a kwana da patient.
Was he gari haka suka kara dunguma sukayi asibiti sae dae ba'a bari a shiga gurinta haka sukaci zama har kusan 6pm Dr S. Jegah ne ya fito gaba daya hankalinsa a tashe da Sauri yabar gurin ganin haka yada aunty fareedah (step sister) din Raj bin bayansa dan tasan tunda taga mijinta haka tasan ba lpy ba a bakin mota ta same sa tsaye ya jingina Kansa a jikin motar dafasa tayi ya jiyo yana share hawayen da suka zubo masa Jiki a sanyaye tace"my dr lpy?"
Hawaye na zuba yace"fareedah mamah gaba daya komae ya tsaya oxygen dinma ya daena bazata bazata wuce 10mins ba yanzu haka"
Zama tayi dabas a gurin tana inna... Wasu hawayene suka zubo mata sae kuka ya barke kokarin yake ya danne NASA ya rarrasheta amma ina gaba daya tq burgaye sae kuka takeyi cikin tsananin tashin hankali.
A gurin su BG kuma ganin Dr ya fito ya wuce yasa ta mike tana tafiya a hankali sbd gaba daya bata da wani karfin jiki yanzu ita kadae tasan yanda take ji. A hankali ta tura kofar dakin ta shiga a kujerar dake bakin gadon ta zauna ta daura kanta a kan gadon kana ta kama hannun mama cikin nata hawaye na zuba non stop haka Drs biyu suka shigo Dr Aysha ta kama ta suka fito waje Dr Jabeer kuma ya dubata cikin tashin hankali ya fito sbd ganin gaba daya komae ya daena aiki Neman taimakon wani Dr yake nan ya hadu da dr Yusuf suka shiga tare shima gaba daya ya kideme a hankali ya kulle mata ido kana yaja zani ya rufe mata fuska gaba daya ya sun kada fitowa waje sbd basu San ya zasu gayama wnn a halin rasuwar baewar Allahn nan ba.
Sun kusa 30mins kafin dr Yusuf yayi ta maza ya fito da sauri uncle murry ya karaso yana tambayar dr halinda ake ciki dafa shoulder dinshi yayi hawaye na zubo masa yace"sae dae muyi hkr..."
Bae karasa ba ya wuce dan bazae Iya tsayawa ya masa bayani ba a duk zamansa hospital din nan bae taba jin mutuwar data ratsada kamar wnn ba.
BG nan take ta sulale saka sume gaba daya hankalin yan gidan ya tashi maman Raj ma sae da ta fadi dan wani irin sone suke ma junansu abun gwanin tausayi nurses ne suka zo suka tafi dasu aka basu taimako.
Tsaywa fada muku tashin hankalin da wnn family din suka shiga bata lkc ne.
Sae dare su BG suka farka a time din ana shirye shiryen tafiya da gawar mama duk da dare yayi haka suka dunguma cikin high speed zuwa jega uncle murry daya dakko gawa dakyar yake tafiya dan harda kaucewa titi yake sae karfe 1am suka isa Hajiya kam gaba daya kukama yaki zuwa mata idonta yayi jajir sosae sun kafe hmmm tashin hankali dae sun shigesa haka aka zauna zaman gaisuwa gaba daya BG ta zabje kamar wacce ta shekara tana ciwo.
______________★
Gaba daya Raj ta sauya ta kamar ba ita ba haka ma Aaj sadixy ma ganin frnds din Nata cikin wani hali yasa itama duk sae ta koma so silent.
Sannu a hankali ciwo ha fara cin Raj amma daure sosae haka dae suke zaman extension din Nash cikin wani yanayi.
Bayan sati daya ciwo ya rufe Raj sosae ganin haka yasa aka mai data gda koda taje su mama har sun Dawo daga jegah data ji lbrn mutuwar mama Hassana ba karamin tashin hankali ta shiga ba tayi kuka harta gaji a haka har mutuwar ta same masu jiki Raj taji sauki aka maedata skl da Aaj taji itama ta shiga tashin hankali sosae haka suka cigaba da zaman Nasu.
*Hi amazing souls #wattpadians your vote is very low pls bazae yiyu ace more than 1k mutane suna karanta book din nan ba amma vote ya gagara shi yasa kwana biyu banyi typing ba Allah idan kun gyara zan cigaba and for my WhatsApp people am very sorry Ku zan dinga muku posting inshallah*
Comments
Vote
Share
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
http://ayshartou.blogspot.com
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
19
........ 2 days later.
Zaman su kam yanzu ya chanja sosae suke sheke ayarsu a hostel da kuma suka fara jamb registration aka fara kwasar students zuwa gda yayinda wasu kuma a skl zasu dan sunyi nesa sosae.
Zaune suke a hostel sun gama lunch sallamar sadixy ne yasa suka mike da gudu sukayi hugging dinta Jakarta ta ajiye tana"wash Allah wlh banso dawowa ba yau"
Faty tace"shegiya da kinyi zamanki ai dan wlh ni if to say naje gda to sae an gama jamb zan dawo"
Dariya sukayi Raj tace"INA sako na?"
"Ohh karki cinyeni daga dawowa zaki dameni"
Raj tace"atoh aiyafi waya gaya miki ana wasa da sakon masoyi"
Dariya suka sheke da ita Aaj tace"wato Ruqayyah green sneka ce "
"Ba wani green snake bazaki gane bane baby dazun bakiji yanda ya kasheni da romantic words dinsa bane oh my gosh am dying"
Daka mata duka Sadixy tayi tace"saeki gaya mana waye bashida soulmate din da zaki zo kina cika mana ears da zancen ki"
Dariya tayi irinta shakiyanci tace"ko baba da babansa in gaya miki Hafeez yayi ma Shuraim zarra kama kanki"
"Ahh wlh kinfi karfina yarinyar nan haka Hafeez ya lalataki ban Sani ba"
"Hhhh sae kiyi baby"
Kiran sallar asr ne yasa suka tashi gaba days xasuje masjid suna tafe suna fira abunsu dan basuda wani yawa sbd ba gaba daya suka Dawo ba
Alwala sukayi kana suka wuce cikin masallacin suka dasa wata fira ganin har 4:45 ba'a tada sallah ba yasa suka mike Aaj taja su sallah suna cikin 3rd raka'a ne Malam yashigo tsaye yayi Kansu yace"kae Ku katse sallar nan tunda nazo"
Banza suka mishi suka dago daga rukuu na last raka'a a tsawace yace"bada Ku nake mgn bane?"
Ina sallah suka cigaba dayi yana tsaye Kansu har suka idar ya cika yayi fam kamar xae fashe. Kallon Aaj yayi yace"ke shugaban marasa kunya Dawo nan kiyi kneeling "
Kallonsa tayi tana smiling kana ta mike tayi hanyar waje fizgo hijab dinta Malam Shafa tayi tace"ke Mara kunya rashin kunyar taki har ta kai kiyima Malam sbd bakida tarbiyya gidanku ba'a Baku tarbiyyar girmama na gaba da kuba toh ni xan baku
Fixge hijab dinta tayi tace"nikam malama inada tarbiyya ban Sani ba dae ko da wancen bangon kike yi"
Rike baki tayi tace"ahhhh lallai yau zaki ci ubanki a makarantar nan sae kin San yau kinzo GGC heeee bari na kira daddy wlh yau sae kinyi aiki kamar jaka"
"Nikam Malama ba jaka bace kuma wlh sae dae muci urban juna dan bana tunanin a wannan era din akwae malamin da ya isa ya dake ni na barsa"
Mari ta kae mata Aaj ta kauce kafin Malama Shafa tayi wani yunkuri ta zube kasa aljanunta sun tashi gaba daya yan masallacin kanta sukayi ganin tayi wata irin zabura ta mikene kamar snake yasa suka tsaya cak fa gudu tayi hanyar waje Malam yayi saurin tareta ta kai masa maka a fuska sae da hakorinsa daya ya fita Ashanty da zata shigo kenan sukaci karo Jan hannunta tayi da gudun masifa ihu Ahsnaty ta dingayi kamar ranta zae fita dan ita kadae tasan mafisar data hango dan wani irin gudune Aaj keyi kamar zasu tashi sama gaba daya yan masallaci hankalinsu ya tashi Raj da idonta ya kawo hawaye sbd tausayin Yar uwarat dan tasan halin aljanunta idan suka tashi ba sauki kallon sadixy datayi tsaye tayi tace"wayyo ban San ya zanyi ba wlh" shrr sae kuka itama sadixy hawayene suke sintiri .
Sae da tayi nisa sosae ta kusa gate kana ta saki Ashanty ta fadi kanta ya saki wani dutse sae suma.......
*Hello dearest abunda yasa kuka jini shiru kwana biyu rashin vote dinku ne a gaskiya abun na bata min rae sumtyms sae na zauna zanyi typing kuma sae naji haushin wasting tym dina da zan zauna nayi sbd bakwa voting kuma kun San shine karfin gwiwar mu more than 1k mutane ke karanta book din nan amma fisabilillahi ace vote 100+ ne kawae haba gsky Ku gyara if not all my book da zanyi yanzu zan mayar dasu na kudi kuma harda Wanda kuke karantawa Take Note*
Comments
Vote
Share
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
http://dry
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
20
Da kyar securities din bakin gaye suka samu damar kamata haka suka dakko ta duk ta sankare sae faman fisgewa take tanaso ta gudu amma saboda rikon da suka mata bana wasa bane yasa ta kasa kwacewa.
Malam kuwa tunda yaga an nufo masjid da Aysha ya kama hanyar gabansa ya gudu sae dae aka samu aka kunna mata karatun alqur'an kana tayi lakau ta koma ajiyar zuciya da haka har wani nannauyan bacci ya tafi da ita.
Bayan kwana biyu
Zaune suke a common room din red house kowacce da abunda yake yi su raj sae fira suke kasancewar Saturday ne yau students suka fara dawowa hakan yasa hostel din ya fara hargitsewa da hayaniya kowa sae murnan jin dadin ganin frnd dinshi yake da haka har sauran students din suka gama dawowa aka cigaba da skl life.
Bayan dawowar students da sati ss3 suka fara waec haka suke exams din cikin jin dadi Dan answer ake basu shi yasa ko karatu basayi sae dae zaman banza a hostel da hayaniya haka dae suka cigaba har suka gama kullum sae anyi fama dasu tunda sukaga barin makarantar zasuyi yasa suka fara bannar cin rae ba wacca bata rubuta sunan ta ba a jikin bangon skl ko ina saeda suka maka sunan su acewarsu sun bar record. White board dinsu ma sae da suka saka compass suka rubuta sunan su.
Daddy 504 ne yazo wucewa yaga an rubuta *Platonic yan aljannah* yasan ba aikin kowa bane sae ss3 Dan haka yasa aka Tara masa su sae da ya gama kallonsu kaf kana yace "Platonic yan aljannah" kallon kallo akayi tsakanin Raj da su sadixy banza suka mishi sae da ya koma maemaetawa kana sadixy ta daga hannu Raj ma haka da Aaj yace"oya pack one side so ss3 u guys are trying to prove to us dat u are stubborn you went on writing your names everywhere listen and listen attentively wlh non of you will ho out of dis skl har sae kun kawo mana one one bucket of milk paint and one one white board then back to u Platonic I don't want to see dat name were I saw it use your tongue and wipe it before the sun set am I clear" suka amsa da yes sir kana ya kara gaba dariya suka sanya Hanifa ta fito tana Mae Maeta abunda ya fada cikin shakiyanci suka koma saka dariya kana suka watse
Sorry guys I know I don't have mouth to apologize but am sorry plsss
*YAN BOARDING*
(🅻ᴀʙᴀʀɪɴ 🆁ᴜǫᴀʏʏᴀʜ)
Na
*ᎪYᏚᎻᎪᎡᎢᎾᏌ*
Wattpad @Neeshejay
http://ayshartou.blogspot.com
ғᴏʀ ᴍʏ
*Ruqayyah Ahmad Jega*
(ᴍʏ ᴅᴀʀʟɪɴɢ ʀᴏᴏᴋᴇʏ❤)
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su Raj sae fama da exams sukeyi amma duk da haka basu daena shakiyancunsu ba Saema abunda ya karu malamansu sae dae hkr kawae sukeyi dash.
Yau Wednesday da dare sun fita night prep shima Dan an korosu ne da bazasu fito