Showing 30001 words to 33000 words out of 34150 words

Chapter 11 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt

14 Jan 2025

3059

Kai ma ka ne ka xora ma kanka,. Babbar soyayyata ita ce in gan ni da kuxi. Duk lokacin da na ga account xina ya soma qasa a nan za ka ga tashin hankalina”.
“ba za ki gane ba, yanzu dai ya za a yi ki iya turo min ita?”
“Korata ka ke son yi kenan ko? Shi kenan bari na turo maka ita”.
Ta miqe ta yi waje.
“Wai ke ba dubiya ki ka zo ba ne, kin wani kime a nan?”
Ta xaure fuska, har kullum gani ta ke duk lokacin da suka kevance da Zaruk xin abin da ta gani shi ne suke yi.
“Tare za mu shiga da Ammina”.
“Tashi ki shiga, ga ni nan”.
Ta miqe cike da damuwa, ko kaxan ba ta son ganin fuskarsa, kullum qara tsanarsa ta ke.
Ta daxe tsaye a bakin qofar, sai da ta ji motsi kamar za a taho ta yi saurin ture qofar ta shiga haxe da sallama.
Yana kwance dafe da gurin ciwonsa, a daidai wannan lokacin zogin ciwon ya addabe shi. Kasa qarasawa ta yi ta tsaya a xan nesa da shi, ko son kallonsa ba ta yi.
Yunqurawa ya yi ya miqe zaune cikin dubanta.
“Qanwata ga kujera ki zauna mana”.
Ta yi yadda ya ce kanta a qasa.
“Sannu, ina wuni? Ya jiki?” Duk ta faxa a lokaci xaya.
“Sai ki ka ji mummunan labari ko?”
Qala ba ta ce masa ba.
“Yau babu makaranta? Ammi tana sitroom?”
Haka ya yi ta soki burutsunsa ya qosa da yanayinta, ya kafe ta da ido.
“Qanwata kin canza, gaya min me ya sa ki yin shiru?”
Nan ma babu amsa, tilas ya tsuke baki cike da tunani barkatai. Ya zai yi ta fahimci yana sonta? Ya zai yi ta fahimci ita ce farin cikinsa?
Zumbur ya ga ta miqe, kasa magana ya yi kawai ya bi ta da ido. Me ya sa ta daina sakin jiki da shi a daidai lokacin da ya fi buqatar haka? Me yake faruwa haka?
“Ya Allah ka nuna mini hanyar da za ta fahimci ita kaxai nake so”. Ya ayyana a zuciyarsa.
“Nurat tafiya za ki yi?”
“Sallah zan yi”.
Ba ta jira jin me zai sake cewa ba ta yi saurin ficewa.
Bayan ta idar da sallah tana sani ta miqe a kan doguwar kujera da faxin kanta ne ke ciwo.
Ba su bar gidan ba, sai bayan sallar magriba.


*** *** ***
Alhaji Usman ya shigo gidan cike da farin ciki.
“Daddy ta samu kenan?”
“Rangida ina cike da farin ciki, burina kullum zumuncinmu ya xore da Alhaji Aminu. Yanzu kam za mu zama xaya, don ko har zuri’a za mu haxa, kin ga kenan zai sake sakin jiki, babu maganar qyashi a tsakaninmu”.
Hankalin Ammi ya tattara a kansa, tana son jin inda ya dosa.
“Daddy ka vatar da ni, sam ban gane ba”.
Ya numfasa, “Ina Nurat?”
“Tunda muka dawo ta ke kwance”. Aazeen ta faxa.
“To lafiya kuwa?”
“Kanta ne ke ciwo, amma ta sha magani tun a gidan su Zaruk”.
“Ok, to shi ke nan Allah ya sauwaqe”.
“Dad ina jinka”.
“Mutuminki Zaruk ashe duk wannan abin wai Nurat yake so?”
Aazeen ta yi tsalle ta dire, har tana guxa.
“Dad dole ka yi farin ciki”.
“Allah dai ya sa Nurat ta amince da shi”. Ammi ta faxa tana kawar da kai.
“Duk wani abu da na tsara a gidan nan ke ce ke rusawa, an gaya miki ina son jin ra’ayinta ne? to bari ki ji, ko tana so ko ba ta so Zaruk shi ne mijinta. Ni ne na haifi Nurat ba ita ta haife ni ba, ina da ikon ba ta duk wanda na yi ra’ayi kin gane?”
Ya tashi ya shige sashensa ransa a matuqar vace.
Duk jikinta ya yi sanyi, ta yi da ta sanin ba ta yi magana ba.
“Ammi, Daddy yana da gaskiya fa. Ai ita Nurat ba ta da wani ra’ayi, kawai ki sanya masa ido, don ni ban ga aibun Yaya Zaruk ba, sai dai in ke xin ce ba kya son ta aure shi’.
Ita ma ficewa ta yi ta barta zaune a gurin qiqam kamar an dasa ta.
Tun daga farko har qarshe Nurat ta ji hirar tasu. Kifa kai ta yi a filo tana faman gursheqen kuka. A haka Ammi ta riske ta, zama ta yi a gefenta, ta ma rasa ta ina za ta fara. Ita kanta ba ta so hakan ba, ba wai don ba ta qaunar aurensu ba, sai dai tana ganin nawa Nurat xin ta ke da za a yi zancen aurar da ita yanzu? Ban da ma ta fara makaranta da wuri bai fi a ce tana J.S 3 ba.
Hannu ta sa tana shafa bayanta.
“Me ye na kuka Nurat? Fata za mu yi Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi. Shi xin mutumin kirki ne, Yaya yake a gare ki”.
Ta xago kai idanunta na tsiyayar da qwalla.
“Ammi ki taimake ni, wallahi bana son auren nan. Ammi, Dad har ya gaji da ni ne da zai aurar da ni? Me ya sa ba za a yi wa Yaya Aazeen ba? ta fi ni girma, ta gama karatu. Ta fi ni cancanta, don Allah ki taimake ni ki fahimtar da shi”.
Ta kai hannu tana share mata qwallan.
“Shi ke nan, zan yi hakan. Amma sai na ga kin cire damuwa a ranki kin ji. Yanzu tashi ki je ki yi wanka ki ci abinci”.
Ta miqe ta yi waje, Ammi ta bi ta da kallo, gaba xaya tausayinta ta ke ji.
Babu kunya ya saka wa Abbansa rigimar ba zai iya jira zuwa wani lokaci ba.
Alhaji Aminu mamakin Zaruk yake yi.
“Ka shaida mini tun tana qanqanuwarta ka ke sonta, ka duba ka ga shekarun da ka xiba, don ka jira shekara xaya ai ba zai cutar da kai da komai ba…”
“Abbana ba zan iya ba. ina sonta kamar raina, ba zan iya ba. Ji nake kamar zan mace, Dad ina son na yi rayuwa da ita kafin in mutu. Don Allah ka saka baki na sani muddin ka ce ba ka amince ta qarasa karatunta a gidansu ba zai amince. Abba kai ne fa komai nasa, da taimakonka yake samun komai’.
Xaga masa hannu ya yi.
“Kada in sake jin makamancin wannan zancen a bakinka”.
“To Dad na ji, ba zan sake ba. amma ka duba, na amince ta qarasa karatun a gidana”.
“Oh God, shin Zaruk ba ka san a gaban wa ka ke magana ba? ina kunyarka ta ke ne? ni ba zan yi musu dole ba, idan auren ka matsu da shi ka nemi wata cikin sati biyu zan aura maka ita. Amma ba za ka sanya ni in takura bayin Allah a kan son ranka ba”.
Ya miqe a fusace ya yi waje.
Zaruk ya miqe ya shiga sintiri, wani irin son Nurat na ratsa dukkan sassan jikinsa. Fuu! Ya yi waje da nufin ya koma gurin Abban nasa ya sanya masa kuka, qila ya gane abin da yake ji.
Sai dai yana sa kai ya ji tashin motarsa, ya juya a zabure zai koma ciki suka yi arba da Ummansa. Kallonsa ta ke a tsorace.
“Ciwon ne ya motsa?”
“Umma, Abba ne, ba ya son farin cikina”.
Kamo hannunshi ta yi, ba su zame ko’ina ba sai sitroom,. Ta zaunar da shi a kan kujera, ta soma magana cikin kafe shi da ido.
“Tunda ka furta kana son Nurat, ba ta da miji sai kai. Me ya sa ba za ka kwantar da hankalinka ba?”
“Oh Umma, me ya sa ba kwa ganewa? Nurat mace ce, kuma mai matuqar kyau. Tana da xabi’u masu kyau, a yanzu haka tana da masu sonta da yawa, wataran za su hure mata kunne, za ta juya min baya… Umma ta ma fara yanzu haka Nurat ta daina kula ni, ba ta son ganina. Ina ganin qiyayyata kwance a fuskarta…”
“Ka ga Zaruk, kai ma ka riga ka sani aurenka da ita tilas ne, ko da tana so ko ba ta so. Na sani mahaifinka ya fi ka son wannan auren shi ya sa nake son ka nutsu”.
“Zan yi haka, amman sai dai ta dawo gidan nan, inyaso ni sai na dinga kai ta makaranta”.
“Haba Zaruk, ina ka tava ganin an yi haka? Gaskiya ba zai yiwu ba”.
Ya miqe a fusace.
“Umma, ke ma ba za ki fahimce ni ba ko? Shi ke nan”. Ya juya ya koma ciki.
Aazeen tunda ake wannan abu ba ta xora ido a kan Nurat ba, kwana uku kenan ba ta zama a gida saboda binciken inda za ta samu Ahmad Deedat. Kuxi ta ke ta faman kashewa har da masu bincike a yanar gizo, wasu ma qarya suke yi mata da cewar sun sanshi don kawai su karvi kuxi. Duk kuxin kuma da ta ke kashewa ko a jikinta, kullum gani ta ke yi wataran za ta fanshe, ba ta fidda tsammanin cewar shi xin zai zamo nata ba.
Yau qarfe huxu ta dawo gida, kai tsaye ta faxa bathroom ta yi wanka, riga da wando ta saka marasa nauyi, ta miqe a kan gado, ta janyo waya. Wasu rubutukan batsa ta ke karantawa, lokaci xaya ta ji kewar Zaruk, tunda ya qwallafa rikicin son Nurat ba shi da lokacinta, ita xin in ba shi ba ba ta tava ganewa, ya xora ta a kan salon da ba ta iya haqurcewa da shi, dole ne ta yi wani abu a kan lamarin nan ko don ya samu nutsuwa. Za ta je ta samu Nurat, za ta yi mata wayo.
Ta shigo xakin, a bakin gado ta same ta a zaune tana ta fushi. Ta zo ta zauna a kusa da ita ta sa hannu ta kamo nata, ta kira sunanta. Ba ta amsa ba sai ma kawar da fuska da ta yi, ta soma magana.
“Qanwata kin ba ni kunya, anya kuwa Nurat xina ce kuwa? Ni dai na san tawa Nurat xin mai biyayya ba ta tsallake abin da family xinta suka gindaya mata, amma yanzu duk ta sauya, me ya sa?”
Ta saki hannun nata ta kamo havarta.
“Gaya min ko akwai wani a cikin zuciyarki?”
Da sauri Nurat ta kaxa kai, da ido taf qwalla.
“Kullum kina yi min wa’azi ta ya ya mai dokar bacci zai vuge da gyangyaxi? Kin ga ke fa saukakkiya ce ga hadda a kanki, duk wasu littattafan addini suna kanki, kin kuma san hukuncin mutumin da bai bi iyayenshi ba, kin san irinku Allah ya fi kama ku da hujja”.
Wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta, lallai wannan ‘yar rainin hankali ce. Ta faxa a ranta.
“Ni bana sonsa. Ban tava sonsa ba”.
Ta kai hannu fuskarta tana share mata qwalla.
“Kin ga in dai wannan ne ta zo gidan sauqi. Ke da ma ba ki san me ye so ba? Babu kowa a zuciyarki, zai koya miki yadda za ki so shi kin ji”.
Ta kama kumatunta ta ja.
“Yauwa qanwata, small”.
Maimakon murmushin sai ta rushe da wani sabon kukan, cikin shesshekar kuka, “Yaya Aazeen ai kin fi ni buqatar aure, amma ni me na yi wa Dad da yake son xauke ni a gidan nan? Ni ba zan iya ba”.
“Ni ma ina son ki yi aure ba Dad kaxai ba Nurat, ina qaunarki, ina tsoro kada ki riski kanki a rayuwa irin wadda nake ciki. Yadda Ammi ta ba ki tarbiyya ina son ki xora duk inda ki ka shiga a yi alfahari da ke…”
“Yaya shi xin ai ba na gari ba ne”.
Ta katse ta da faxin haka.
“Wa ya gaya miki?” Ta tambaya cikin faxuwar gaba.
Shiru Nurat ta yi.
“Ni kam ban ga aibunsa ba, Zaruk xan asali, ga shi mai kyau. Za ki yi alfahari da shi”.
Zumbur ta miqe tsaye.
“Da an yi magana ki ce kyau, shi kyau ba abu ne mai xorewa ba, ai ba a tava gama wa xan Adam halitta har sai ya koma ga Ubangijinsa. Halayyar Yaya Zaruk nan gaba zai iya tsintarsa a kowane yanayi, ina da yaqini Allah ba zai xora qaddarar aurensa ba domin an tsarkake kaina”.
Ya dace a ce Aazeen ta gano inda Nurat ta dosa a maganganunta, sai dai ba ta gane komai ba. Miqewa ta yi.
“Shi ke nan, ni ma idan ki ka amince da Zaruk zai auri wannan Adamun zan yi duk yadda ki ke so, me ki ka ce? Ba kin ce kin yi masa alqawari ba?”
A hankali ta jinjina kai.
“Zauna, kirawo min shi, ina son ya zo in ganshi”.
Ta dube ta don gaskata abin da ta ke faxi.
“Yayata da gaske ki ke yi?”
“Mamaki zan ba ki. Zan yi komai don xorar da farin cikin qanwata”.
Take suka shiga kiran layinsa, sai dai an yi rashin sa’a wayar tasa na kashe. Daxi ne ya kama Nurat, a tunaninta wayo za ta yi wa Aazeen, ta sani in ta ganshi za ta iya sonsa, yayin da ita ma Aazeen ke murmushin mugunta, tana jin cewar dabararta ta yi.
Sun tsayar cewar duk lokacin da ya kunna wayarsa za su kira shi.
Hankalin Alhaji Usman ya kai qololuwa gurin tashi a kan abin da Alhaji Aminu ya zo masa da shi a kan Nurat, ya sani rashin amincewarsa zai iya haifar da komai, yana tausayin Nurat, ya sani kawai son rai zai nuna, bai dace a ce ya aurar da ita nan kusa ba.
Alhaji Aminu yana da kirki, ya taka rawar gani a rayuwarsa, shi ne ya koya mishi yadda zai dinga juya kuxi, shi ya fito da shi a idon duniya har aka sanshi.
Alhaji Aminu ya fi qarfin komai a gurinsa, akwai kunya in har ya juya wa buqatarsa baya, ya yi masa halacci da yawa. Yanzu ne lokacin da ya kamata ya rama masa, don haka ya qudiri niyar kyautatawa Nurat ko don ya shawo kanta, don haka yau bai dawo gida ba sai da ya yi mata siyayyar kayan kwalliya, kayan sawa har da sabuwar waya.
Lokacin da Hajiya Rahma ta shigo xakin, ya lura da yadda ta rame, tausayinta ya kama shi. Ya kai hannu ya janyo ta jikinsa, yana son Rahma tamkar ransa, in ban da fitina irin ta zamani mutumin da yake da kamar Rahma ya gama samun arziqin duniya, sautari in yana baqanta mata rai ya kan ji ya tsani kansa. Ta nuna mishi qololuwar so, ta rabu da komai da kowa saboda shi. Me ya sa shaixan ke hilatarsa haka?
Sakin baki ta yi tana dubansa, ya xan numfasa, idanunsa a kanta.
“Kin tsane ni ko?”
Da sauri ta kaxa kai.
“Me ya sa zan tsani mijina uban yarana?”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Na sani ban kyauta muku ba ke da Nurat, ni kaina na shiga tsaka mai wuya ne, babu abin da Alhaji Usman zai iya nema in hana shi, idan na juya mishi baya ma duniya za ta zage ni, danginsa za su yi mishi dariya. Kuma ni ban ga aibun shi Zaruk xin ba”.
Idanunta fal qwalla.
“Ai ni ban ce komai ba, Nurat ‘yarka ce, ka fi kowa iko da ita. Ina fatan Allah ya sa haka ne ya fi alheri”.
Ya sake shiga jikinta yana zargin kansa da abubuwa da dama.
“Yauwa Rahmar Allah, haka nake so. Yanzu ki turo min ita”.
Ta miqe jiki a sanyaye, yadda ta samu suna hira da Aazeen har da dariya ya sanya ta xan ji sanyi a ranta.
“Alhaji na kiranki”. Ta ce da ita.
Tunda ta zauna yake ta rarrashi, amma zuciyar nan tamkar rodi, musamman da ta fahimci yadda yake qoqarin sai ya cusa mata son Zaruk ta qarfin tsiya. Ta yadda yake ta faman yabon Zaruk, yana kururuta dacen da ta yi, da faxin jaruntarsa, son mutanensa ga addini da taimakon marasa qarfi.
Ya xora da cewar, “Ki fidda ni kunya, ban tava neman abu a gurinki ba Nurat, yau na zo da qoqon barata, kada ki zubar min da mutuncina, ki rufa min asiri”.
Ba ta ji daxin yadda Dad ke roqonta ba, tamkar zai yi kuka.
“Dad na amince, na yarda Dad. Ka daina roqona, kai mahaifina ne, za ka iya yin duk yadda ka so da ni. Zan aure shi ka bada aurena a duk lokacin da ka so, ba zan musa ba”.
Daxi ya kama shi, ya sani an wuce gurin, ya gama sanin ‘yarsa kaifi xaya ce ba ta magana biyu, yadda ka san babbar mace.
Yaqe ta ke yi yadda ta ga mahaifin nata na ta rawar jiki, yadda ya nuna farin cikinsa idanunta ke qoqarin zubda qwalla. Cikin dabara ta goge su ta sani zai iya tilasta mata ta aure shi, amma ba za a tilasta mata ta so shi ba. shi kenan ba ita babu wani farin ciki a duniyar nan?
Ta katse tunaninta a daidai lokacin da ya nuna mata kayayyakin da ya siya mata. Ya xauko waya ya miqa mata, da cajinta full har ma an xora layi a kai. Yadda ya santa da son waya tun tana qaramarta, ya yi zaton za ta nuna farin ciki, karva kawai ta yi kamar ba ta so, haka ne ya tabbatar masa cewar ba ta son Zaruk.
“Na saka miki lambata da ta Amminku, ki tashi ki je, Allah ya yi miki albarka”.
Ta kwashi kayan ta yi waje.


*** *** ***
Rashin ganin Ummita a bakin get ya sanya gabanshi bugawa. Ba ta qin tsayawa tarbarsa, duk lokacin da zai dawo daga tafiya sai in har ya yi mata laifi ko da ba ta da lafiya yana ce mata ga shi nan ya kusa qarasowa ta ke cin dako a bakin get, duk ruwa duk sanyi, duk iska.
Maigadi ya yi saurin buxe mishi murfin mota.
‘Sannu da dawowa yallavai”.
“Yauwa Adamu, yau kuma lafiya ban ga Ummina ba?”
“Lafiya qalau”.
Mamai ya qara kama shi.
“Adamu gaya min gaskiya”.
“Da gaske nake Yallavai, yanzu haka daga cikin gida nake”.
“Ok”. Ya ce.
Buxe mishi but ya yi ya tafi ya barshi a gurin yana fara jidar kaya.
Ko da ya isa ciki bai ga alamar an shirya zuwansa ba, savanin da da ya shigo zai dinga jin qamshin girkin tarbarsa, an cika teburi da kayan abinci kala-kala, yau ga shi wayam! Jikinsa ya yi sanyi, cikin rashin kuzari ya nufi xakinta.
Tana zaune a kujerar roba, da asuwaki a hannu, fuskar nan a kirne. Ya zauna a sanyaye.
“Ummita, yunwa nake ji, ban ga kin shirya min komai ba, bayan kin riga kin sani duk lokacin da zan dawo gida bana iya karyawa a ko’ina”.
Ta ajiye asuwakin cikin sake xaure fuska.
“Daga yanzu na daina, kuma kai nake jira yau zan bar gidan nan”.
Bai san lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login