Showing 24001 words to 27000 words out of 34150 words

Chapter 9 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt

14 Jan 2025

2676

a ba ka sona xin”.
Kalamanta sun karyar masa da zuciya. Duk sai ta ba shi tausayi.
“Nabila ban ce bana sonki ba, xabi’unki kawai za ki sauya”.
“To ka gaya min, me ye aibuna? Me nake yi wanda ba daidai ba?”
Ya ja wani xan qaramin tsaki, matsalarta kenan ba ta amince da ba ta yin daidai, xabi’unta tana xaukarsu abin burgewa.
“To shi kenan, tunda kina ganin komai daidai ne babu matsala, yanzu ki gaya ma su Papa, wata biyu na xiba”.
Ta yi sororo.
“Yaya Deedat, wata biyu ba ma sati biyu ba?”
Ya ce, “Akwai tafiyar da zan yi, zan kai kusan hakan idan na dawo sai a yi bikin. Ni zan wuce”.
Ta matso kusa da shi, matsalarsa kenan, sam bai iya soyayya ba, yadda ka san mutumin da.
“Yaya Deedat shin ba ka xokina ne? Ya kamata a yi bikin nan kafin ka tafi inyaso sai mu tafi tare, please”.
“Ba zai yiwu ba, idan hakan bai yi miki ba kin iya neman wani”.
‘Uhm Yaya Deedat, ka sani ba ni da mijin da ya wuce ka. Ina son ka sani ko da za ka kai shekaru goma ina nan daram babu inda zan xaga, kawai dai ka sa a ranka duk bala’i ba ka da matar da ta wuce ni”.
Ya yi wani murmushi mai ciwo.
“Allah ko? To sai ki ci gaba da jira”.
Murmushi ta yi, ta sani gaba xaya Deedat ba ya sonta, bai tsara rayuwarsa da ita ba, kuma dole ne ya aure ta, ba za ta bari wata shegiya ta rave shi ba, ba ta fatan ganinshi da wata ko da ba shi da komai, ballantana hamshaqi kamarsa, ko za ta mutu babu aure za ta jira shi. Ta sani haramtaccen abu ne ya yi aure ba tare da ya aure ta ba. Ta sani dama yake nema da zarar ta ji haushi ta ce za ta auri wani zai auri wadda yake so, don haka za ta jira shi.
Ta qarasa gabanshi inda suke iya jin hucin juna.
‘Zan jira ka ko da hakan zai kai mu da tsofewa, na yi alqawari ba ni da miji face kai, in ka je ka yi shekara ba ka dawo ba Mr. Man”.
Ta yi murmushi, a gurin ta barshi.
Takaici kamar zai rufe ta da duka.
“Dole ne fa ka yi yadda iyayenka ke so, kai ma ka sani tuntuni ita xin zamanka ta ke yi, ba ka da hujjar da za ka guje mata”.
“Mtss! Salim ka sani bai tava sonta ba, ta ya ya zaman aure ya yiwu a haka?”
“Nawa aka yi Yaya? Iyayenmu na da suka yi ba su tava zaven mace a kan kansu ba, kai wasu ma ba za su tava sanin wace matarsu ba sai ranar da suka tare”.
‘Ok, na ji wannan, amma kuma ba ka tunanin ita xin Nabila wace ce ita ba?”
“Wannan ba hujja ba ce, a koyaushe xan Adam na iya sauyawa, ballantana Nabila wadda da zarar ka aure ta soyayyarka na iya sauya ta, in fa ka aure ta za ku kasance ne tare, in ma ba ku kasance tare ba kana datse ta a gida zama za ta yi”.
Deedat ya furzar da wani huci mai zafi, kalaman Salim ba su zame masa hujja ba. ya sani babu wanda zai iya fahimtarsa, babu wanda zai hangi abin da shi yake hange.
“Kawai ka lallava ku rabu da Ummi lafiya”. Salim ya katse shi da faxin haka.
Bai dai ce masa komai ba, ya soko wata maganar, ba ya son ci gaba da maganar Nabila.
Gaba xaya rayuwar gidan ta sauya, gida ya koma tamkar ba na musulmi ba, kixe-kixe da raye-raye shi ne abin yi. A kullum cikin kawo maza suke, da Hajiya Rahma ta yi magana sai Aazeen ta ce abokansu ne daga ofis xinta, tana tsoro, don haka kusan kullum ta ke nemar wa Nurat inda za ta tura ta ta wuni. Tana jin tsoron kada idanunta su dinga ganin irin waxannan abubuwan.
Haka a wannan lokacin ta qara qaimi gurin kai kukanta ga Ubangiji a kan Aazeen, babu abin da ba ta ayyanawa a kan Aazeen. Tuni ta gama sallama cewar ita xin tana bin maza ne, don haka ma babu aure a gabanta. Yau kam ta gama kai wa qololuwa, ko qawayenta ko ita ba za ta ci gaba da zama da su ba alhalin ba su da niyyar komawa, sun ma miqe qafa, don haka ko da ya dawo ba ta doshi turakarsa ba, ba ta kuma kai mishi abinci ba.
Ya dinga kiranta a waya ta yi biris! Ya turo text nan ma babu amsa. Ya qulu sosai har wani huci ya dinga yi. A zafafe ya miqe ya nufi shashinta, ya afka ciki. Tana zaune a kan sallaya yana huci.
“Ban san sa’adda raini ya shiga tsakanina da ke ba, ina so ki sani ba zan xauki wannan wulaqancin ba, ba zan tava ba. In ban da rashin mutunci ta ya za a yi in dawo ban tarar da abinci ba, in kira wayarki ki qi xauka, wannan ai iskanci ne”.
Har ta shafa addu’a ta cire hijabi tare da ninke darduma ta ajiye a gefe, ta koma bakin gado ta zauna ba tare da ta tanka mishi ba, hakan ya sake qular da shi, hannu ya xaga ya kifa mata mari.
Dafe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla.
*💖💕KYAUTAR ZUCIYA💖💞*



*NA*




*BILKISU H.MUHAMMAD*
_(Matar Auwalu By fos zage)_










*Free page 14*








*_Wanan littafin na kudine akan 300 kacal in kinsan zaki biya don ki fitarmin dashi Dan Allah ki barmin kayana yar uwa_*




*Ga jerin sunayan litattafai na da zaku samu a kasuwa*


*1. IZZATU*
*2. MULKIN MALLAKA*
*3. KAUNA CE*
*4. DACEWA*
*5. RASHIN RABO*
*6.TARAIRAYA*
*7. JINI BIYU*
*8. AKWAI BAMBANCI*
*9. TSALAR KAUNA*
*10. YA YI SAKE*
*11. ILLAR SABO*
*12. SO DA SANKARA*
*13. RASHIN RABO*
*14. WATA RAYUWA*
*15. HUBBAN SHADIDAN*
*16. BAKIN K'AZAFI*
*17. MATSALAR KAUNA*
*18. KYAN KUSKURE*
*19. WA YAFI SONTA?*
*20. GABA DA SO*




_NOW_
*KYAUTA ZUCIYA*


```Duka wanan litattafan sunanan akasuwa zaku sameso a shagunan sai da litattafai inasha Allah```




*_Wanan littafin na kudi ne, Mai bukata karanta shi zai turo 300 ta wanan account number din_*
*_2277439558 UBA Bank_*
Bilkisu H Muhammad_* *_idan an turo sai a turawa wanan number alter 08031307884 domin tabbatar da an turo din idan kuma VTU za'ayi ita dai number za'ai da ita ko katin MTN na 300 din sai in saki a group paid insha Allah_*




*_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*








*D* afe da kunci ta dube shi da ido fal qwalla.
“A kan me za ka mare ni?”
Ya sake xaga hannu zai qara mata, ta yi saurin kaucewa ta dube shi a tsakiyar ido, yayin da qwalla ta gama lulluve mata ido.
“Akwai Allah”.
Ya bi ta ya shaqo ta.
“Ki gaya min abin da ki ke nufi”.
‘Ni ka cika ni na ce”.
Ta daddage ta qwaci kanta da qyar tana haki.
“Wallahi muddin waxannan yaran ba su bar gidan nan ba, ba za mu tava zama lafiya ba”.
‘Zancen banza, an gaya miki su irinki ne? su xin suna da gurin zuwa, ke kam idan na kora ki ba ki da gurin zuwa, su da gatansu, ke ko fa? Ba ki da gatan, ke xin korarriya ce, mujiya ce wadda ki ke da danvareren tabo har a gurin Allah, ke xin…”
“Ya isa! Ya ishe ka haka! Ka fara tunanin makomarka kafin ka hangi tawa. Wannan fuffukar da ka ke yi a da kenan, yanzu kar nake kallonka, na san ta yadda zan bi in wanke kaina. Na san yadda zan yi shari’a ta xaure ka, ita xin kanta na san yadda zan bi ta dinga ganin baqinka saboda ni ce mahaifiyarta. Sanin kanka ne uwa ta fi uba soyuwa a gurin zuciyar yaransu”.
Ya saki wata dariyar takaici.
“Ni a gurina Aazeen na yi nisa! Yadda nake da Aazeen ko cewa na yi ta kashe ki na yi imanin za ta bi umarnina, kuma wallahi idan ba ki bi a sannu ba sai kin yi kuka da idanunki, sai kin zamo qasqantacciya a gurin yaranki. Sai na yi miki lambar da za ki zame musu tamkar java, mara mutuncin banza. Qarqari kuma ki ce ba za ki ba ni abin da nake so daga gare ki ba, ki je ki riqe, kawai ina zuwa ne saboda in fita haqqinki, abin naki da kike rowarsa ba ya qara ta da komai, kawai maleji nake”.
Ya yi waje, ya rufe qofar da qarfi har sai da ta firgita.
“Wayyo Allah, na shiga uku!”
Ta zube a qasa tana wani irin kuka.
‘Ni na ja wa kaina, kaico! Na sani hakan za ta faru. Usman tuntuni na gama sanin waye kai, sai dai soyayyarka ce ta makantar da ni. Usman ban tava ganin mara imani irinka ba, Ubangiji ka kashe ni in har mutuwa ta za ta zamo alheri a gare ni”.
Wunin ranar ba ta iya fita ko da sitroom ba. A haka Aazeen ta riske ta, hankalinta ya yi matuqar tashi, duk shaixancinta tana son mahaifiyarta, ba ta son abin da zai xaga mata hankali. Da gudu ta tsugunna a gabanta.
“Ammina, waye ya tava ki? Ammi kalli yadda ki ka komo wuni xaya, gaya min, Dad ne ko?”
Ta kaxa kai.
“To me ke damunki? Don Allah ki faxa min kin ji”.
“Na ce da ke babu komai, kawai kaina ne ke yi min ciwo”.
“No Ammi, ban amince ba, tunda qawayena suka zo ki ka kasa sukuni. Za su tafi, zan sallame su, ko kuma na maida su hotel, hakan ya yi miki?”
Ba ta kula ta ba, kawai binta ta ke yi da ido har ta gama surutunta ta fice, tsananin tausayinta ta ke ji.
Ta gama ba su labarin abin da ta fahimta ga Amminta.
“Tab! Lallai Ammi tana da matsala”. In ji Tina.
“To ai shi ke nan, sai ki yi irin rayuwar da ta ke so xin, saboda na ga kamar kin shiga damuwa”.
Zee ta karvi zancen, “Yanzu ke hakan ne zai sauya ki? Kin ga Hajiyata kawai injoy your life”.
Mima ta ce, “Ita wannan Ammin a haka kamar wayayyiya. Duk ta maida kanta wata ‘yarqauye, ba ta da aiki sai riqe carbi, ga kyakkyawar qanwarki na qoqarin kwaikwayarta, qauyancinta ya sanya an kasa gane ita xin mai kyau ce. Wai shin ma idan ba ki more rayuwarki a lokacin quruciya ba, yaushe ake son ki more shi? Sai lokaci da ta zamo yagwalgwal?” In ji Zee.
Gaba xaya suka xau shewa.
“Kun ga ku daina wannan zancen kuna kada min da gaba, babu abin da na tsana irin in ji an ambaci tsufa, a hakan ma nauyin shekaruna na ke ji, don haka nake roqon in mutu kafin tsufa”.
“Shi ne aminiyas, kawai ki huta”. Minal ta ce da ita.
“Amman da har Ammi na son karya min zuciya, na ji tausayinta yau”.
“Okey, shi kenan sai ki koma zumbula hijbi, riqe carbi, zama a kan darduma takura kai”.
Suka sake kwashewa da dariya.
“A duk lokacin da ta sanya karatun alqur’ani na kan ji duk na takura”. Tina ta faxa, “Ban sakewa wallahi. Ki yi mata magana”.
‘No Tina, don’t cross your limit. Ki rufe bakinki haka kada ki wuce gona da iri”. Minal ta katse ta da faxin haka.
Tuni ta shiga taitayinta.


*** *** ***
“Ba aiki ya kamata ki yi ba, hutawa za ki yi, ki bar ni da wannan uwar qwiyar”.
“Babu komai Anty, kin ga idan na saka hannu sai mu fi saurin gamawa”.
“Okey, shi ke nan tunda kin dage. Ga kaya can na xauko miki ki saka, kada ki vata na jikinki”.
“To Anti”. Nurat ta faxa.
Ta koma xaki ta sauya kaya. Kayan sun yi mata xas tamkar nata. Ba ta xaura xankwali ba, ta gyara tufkar gashinta ta fito. Kicin ta nufa inda ta samu Anti Aisha da qanwarta Yusra.
Anti Aisha ta bi ta da kallo, ba ta tava ganin Nurat ba sai yau, amma jinta ta ke yi kamar wadda suka shekara da ita. Wani irin qaunarta ce ta xarsu a zuciyarta. Ta sauke ajiyar zuciya.
“Kawai ki tafi da kayan, da ma ban tava saka su ba, tunani nake yi kamar sun yi min kaxan shi ya sa tuntuni na qi sakawa”.
Yusra ta ce, “Wallahi kin yi kyau”.
“Yanzu ki ci gaba da aikin, zan je na yi wanka, na san suna hanya kada su zo ban shirya ba. Oga ya yi min kashedin in yi kyau sosai, kada Ogansa ya raina shi”.
“Wai Yaya Aisha waye wannan xin?”
Yusra ta tambaya tana kallonta.
‘Shi xin na musamman ne. Takensa shi ne, in k sanshi shi ne, idan ba ka sanshi ba, to ba shi ba ne”.
“Okey, to me hakan ke nufi?”
“Ni kaina ban sani ba, a bakin Ogana nake jin wannan kirarin, na dai san mutum ne mai kirki. Da bazarsa muke rawa, ban tava ganin mutum irinsa ba, ya fi kowa kirki…”
Ringin xin wayarta ne ya katse ta. Ta zaro ido.
“Kada dai sun iso?”
Jiki na rawa ta xaga wayar.
“Da fatan kun gama shirya komai?” Deeni ya tambaya ta xaya vangaren.
Ta ce, “Sauran qiris”.
‘Okey, shi ke nan. Mu ma ga mu nan mun nufo gidan, abu mafi muhimmnci ki bar su Yusra su qarasa aikin ki je ki yi wanka”.
“An gama ranka ya daxe”.
Da gudu ta fice ta nufi bathroom.
“Tunda ki ka ga Yayata na wannan rawar qafar ba qaramin kuxi za ta shaqa ba, Deeni yana da son abin duniya, na tabbata ba qaramin samu yake a gindin wannan baqon ba. shi fa mijin Yaya idan ya raina ma qura ko kallo ba ka ishe shi ba. Yana da girman kai, ya fi mu’amala da manyan mutane…”
“Kin ga Yusra ki bar wannan gulmar mu yi qoqarin gama aikin nan tukunna’.
Sun gama komai, suna jidar kayan abincin zuwa dinning room, Aisha na can xaki tana shirya kanta, Nurat ta xauko jug na glass ta nufi dinning room. Ita kuma Yusra na moping xin kicin. Nurat ta duqufa tana shirya dinning table suka kutso kai. Sallama suka yi gaba xaya su ukun idanunsu a kanta, ba su tava ganin kyakkyawar halitta irinta ba.
Zo ka ga kunya da tashin hankali, qam! Ta qame a gurin.
“Subhanallahi! Ya Allah, na shiga uku, ta ya ya zan iya ficewa?”
Ba ta iya amsa sallamarsu ba.
Shi kam Deedat gabansa ne ya shiga bugawa.
“Ba kya jin ana sallama?” Deeni ya faxa.
“Amin”. Ta ce a taqaice. Da qyar ta ke xaga qafafunta ko gabanta ba ta gani saboda kunya. Juyawar da ta yi Salim da Deedat suka dubi juna. Da sauri ya voye kansa da wani irin sonta da ya shiga naso a dukkan sassan jikinsa. Ita xin ma duk da ba ta waye da ko su waye ba, ai hijabinta kawai ta xauka ta yi waje ba tare da ta yi sallama da su Yusra ba.
Aisha ta fita daga xaki cikin qayatacciyar shigar da ta sanya ma Deeni nutsuwa. Bayan sun zazzauna, Deeni ya dube ta.
‘Waccan baquwar muka yi?”
“Ni ma yau na fara ganinta, qawar Yusra ce. Yarinyar kirki ba ruwanta, komai nata abin burgewa ne”.
‘Yaya ban ga Nurat ba fa, ina ta shiga?” Yusra da ke qoqarin shigowa ta tambaya.
“Ki duba”.
Ta ce, “Ba ta nan, daga can nake”.
“To ina ta yi?” In ji Aisha.
“Shi ya sa ban so ta fio diining ba, ba ta son mutane. Ina zuwa”. Aisha ta ce.
Xaki ta koma, inda ta tarar da kayan ta zube a kan gado ta dawo gurinsu.
“Wallahi ko tafiya ta yi, hijabinta kurum ta xauka ko kayan nata ba ta canza ba”.
Yusra ta yi murmushi, “Da alamar kacivus ku ka yi da ita cikin rashin sani kuma babu hijabi a jikinta ko?”
Da sauri deeni ya kaxa kai.
“Tab! Yaya ai ko ke da ganin Nurat Usman a gidanki za ki rina, ita xin wata iri ce, kunyarta ta yi mata yawa, ai wannan xin ustaziyya ce, ni fa na yi mamakin da ta amince ta sanya wannan riga da wandon, Nana ta ce min, ko a gidansu ba ta zama babu hijabi, idan ma ba a yi sa’a ba ko gidansu Nanan ba za ta koma ba, qarshenta ma tana can tana kuka”.
“To ke ba ki san gidansu ba?”
“Ina zan sani, ni da ba ‘yar gari ba? Ni ma yau darajar Nanar ba ta nan ne ya sa ta shigo gidanmu. Ni kuma na rakito ta nan”.
Salim kam hankalinsa gaba xaya ya dawo kan Deedat, tsantsar sonta ya dinga hange a idanunsa. Tabbas wannan xin ce ta dace da rayuwar Deedat, ita ce macen da yake mafarkin mallaka. Da alamun an tada mishi mikin da ke kwance a zuciyarsa.
Gaisuwar Aisha ce ta katse masa tunani. Hira suka shiga yi tsakaninsu ban da Deedat, ba su wani damu da hakan ba sanin cewar shi xin ba mai son magana ba ne. Tashin hankalinsu xaya, ya qi cin abinci sai lemo kawai da ya sha. Qarshe ma miqewa ya yi.
Suka bi shi da kallo.
“Sai ina?” Deeni ya tambaya.
“Ku ba ni minti goma zan dawo”.
Bai jira amsarsu ba ya yi waje.
Duk inda yake tunanin zai ganta ya duba babu alamarta, dole ya koma gidan duk hankalinsa a tashe. Yana son zama da Yusra domin tambayar inda ta ke, to amman yana jin wani irin nauyi, ba zai iya tsayawa yana taxin budurwa da ita ba, yana jin hakan bai dace ba, ko ba ma haka ba, hakan ba girmansa ba ne.
Sai bayan magriba suka bar gidan, inda Salim ya ajiye ma Aisha dubu xari biyu gen-gen, ya bai wa Yusra dubu hamsin. Farin ciki a gurinsu tamkar za su shixe.
Bayan fitarsu Yusra ta dubi Aisha.
“Kin ga Nurat ta yi ma kanta, da tuni ta samu kuxaxen nan”.
“Amma dai ko ‘yar dubu goma kin ba ta?”
“Tab! Wai ma, wa ya ce ta tafi? Ko sisi ba zan ba ta ba”.
“Shi ke nan zan ba ki dubu goma ki ba ta”.
“Wannan kam in ki ka ba ni zan ba ta”.
Aisha ta kai mata duka.
“Mara mutunci”.


*** *** ***
Ta rungume shi ta baya, “Daddy kana sona da yawa, ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login