Showing 3001 words to 6000 words out of 34150 words
Chapter 2 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt
koyon son mata. A nan ake cusa musu ra’ayin su kara aure, ba za su tashi dawowa gida ba sai matar ta yi bacci, yaransa sun yi bacci. Kai wani ma saboda tsabar kwarewa da yawon majalisa yaransa ba su gama sanin waye shi ba, wani fannin in matar ba ta samu damar yin bacci ba, daga ta yi musu sannu da zuwa a ciki za su amsa suna faman cika da batsewa, wai kada ta raina su, za su baka abinci idan ba masu ci a waje ba ne, da zarar sun dirka a ciki sai kwanciya, sai dai ka ji yana jan minshari, shi ke nan ke an mayar da ke dutse kin zamo mai zaman ‘ya’yanki.
“Ammina ta kasa gane inda na dosa ita dai kullum na fitar da mijin aure, ba zan taba biye mata ba. Mijin da zan yi rayuwa da shi dan gaske ne, wanda zai ba ni hakkina a duk lokacin da na buqata. Ai ni da na ga mijin da zai iya ina ganewa, har yanzu ban ganshi ba”.
Tana matuqar son namiji wanda ya kai qololuwa gurin haduwa, kyawun, suffa da na aljihu, shahararren mai kudi shi ne burinta, don haka a kullum ta ke mafarkin kasancewa da Ahmad Deedat. Tana ji a ranta kamar shi din ajiyarta ne.
Kiraye-kirayen sallah ne ya katse mata tunani. Mikewa ta yi hade da kashe kayan kallon ta nufi dakin Ammi, wadda da alamun kiran sallar bai ratsa ta ba. Ta shiga dukan filon da Ammin ke kwance a kai.
A firgice ta bude ido, tana tunanin ta makara. Jin alamun za a tada sallar a masallaci ta yi, da sauri ta miqe har tana ture Aazeen.
“Haba Ammi, ki bi a hankali mana, ba fa ce miki aka yi tashin alkiyama za a yi ba”.
Ba ta bi ta kanta ba ta fice abinta.
Aazeen ta koma bedroom dinta ta mike a gado, tuni bacci ya yi awon gaba da ita.
karfe goma da rabi sun hallara a dinning room, Alhaji Usman ya dubi Hajiya Rahma, “Ya dai?”
“Me ka gani?”
“Na ga kamar kina da damuwa”.
Ta kada kai, “Ko daya”.
Nurat ko littafi ne a hannunta tana dubawa.
“Nurat ki aje littafin nan ki ja abinci duk kin daga hankali, in dai ba kya cin abinci zan fa hana ki”.
Ta ajiye alqur’anin a gefe tana cin abincin. Tana leka surar da ke a bude.
Aazeen ce ta fito cikin kayan bacci manne da waya a kunne. Da alama waya ta ke amsawa, gaba daya ita suke bi da kallo.
Bathroom ta nufa.
“Ran gida me ya samu bathroom dinki?”
“Ina ganin kamar rariyar ce ta toshe”.
“Ok”.
Ta shige bathroom din. Mintina biyar ta diba a ciki ta fito da kayanta a jike sharkaf! Wai nan alwala ta daura.
Ammi ta cika fal da takaici, kokarin zama ta ke a dinning.
“Kin ga ki fara sitirta jikinki, idan ki ka yi sallah sai ki yi break ”.
“Tab! Ammi, sallah ba zai yiwu cikin wannan yanayin ba, kin ga kuwa yadda nake jin yunwa?”
Kokarin zuba dankali ta ke a plate.
“Magana fa nake yi”. In ji Ammi.
“Oh my Mom, please ki kyale ni”.
“Haba Rahma ke kuwa ki kyale ta mana, ai shi ci shi ne gaba da komai”.
Dole ta yi shiru tana jin zuciyarta duk a jagule. Ta sani tun farko shi ne masomin rusa tarbiyyar Aazeen, yadda yake yi din ne ya sanya ta ke tuhumarsa da abubuwa iri-iri. Ta sani wannan ba shi ne so ba, me ya sa ita Nurat bai ba ta irin wannan tarbiyyar ba? Shin a cikinsu waye ya fi so kenan? Yana nuna ma Aazeen duk wata gata da soyayya, ba ya son bacin ranta. Ita kuma Nurat tsangwama, da kyara. Yana shigowa gida sai ya fara tambayar ta yi sallah? Ta je islamiyya da ire-iren wadannan tambayoyin. Shin wa ke nan yake kauna?
“Dankali kawai na gani, ban ga farfesun da na ce ladidi ta yi min ba?”
“Kira ta, kila karasawa ne ba ta yi ba, ai babu wanda zai ketare umarninki Rangida”.
Ta bude murya baki daya cikin kwala mata kira.
A sukwane ta karaso tare da durkusawa a gabanta. Ta watsa mata harara.
“Ina kayan karyawata?”
“Yanzun nan na hattama, bari na kawo miki”.
Da sauri ta yi waje, sai ga ta da kayan karyawar ta jere a gabanta.
Janye plate din Ammi ta yi a gabanta.
“Kada ki taba komai a nan ba tare da kin je kin sauya kayan jikinki ba”.
“Haba Ammi, kashe ni za ki yi? Na ce da ke yunwa nake ji. Ni kam gaskiya a’a”.
Ai kuwa ta shiga yi mata fada, takaici kamar Aazeen za ta mutu. Baqin cikinta wai Ammi ta yi mata fada a gaban mai aiki. Juyin duniyar nan ba ta mike ba, ta bude farfesun a qufule, cikin neman wanda za ta huce a kansa. Ta dubi Ladidi.
“Cewa na yi ki saka min curry? Uban waye ya sa ki? Kawai ba ki yi shawara da ni ba kin yi abin da ki ke so ko?”
A sanyaye, “Ki yi haquri, na ga ai kullum ina yi miki amfani da shi”.
“Shut up! Ina magana kina yi?”
Gaba xaya ta dauki plate din farfesun ta watsa mata a fuska. Wata gigitacciyar qara Ladidi ta saka. Da gudu Nurat ta mike tare da rungume ta a jiki. Ladidi na ta ihu tamkar wadda ake kokarin zare mata rai. Da taimakon Nurat suka nufi famfo.
“Man kana ganin abin da Aazeen ta aikata ko?” Hajiya Rahma ta fada tana kallon Alhaji Usman.
“Ita ta ja ma kanta. Ya kamata ta dinga kiyaye matakan aikinta, tunda ba kyauta ta ke aikin ba”.
“Dad, ina son gaya maka. su Zee fa na tafe”. Aazeen ta fada ba tare da ta nuna nadama a abin da ta aikata ba. Gaba daya ma sun mance da ita Hajiya Rahmar, hirarsu suka shiga na yadda za su sauki bakin nata.
Miqewa ta yi cike da takaici, har lokacin tana jin ihun kukan Ladidi, Nurat na faman ba ta haquri.
A can shashin masu aiki, Ladidi ta yi matashi da cinyar Nurat ta dage sai bushe mata idanu ta ke faman yi, hankalinta a tashe, yadda idanun suka kumbure sun yi jajir da kyar ta ke motsa su. Hawaye sai faman tsinkowa suke daga idanun. Cikin muryar kuka.
“Ladidi sannu, za ki warke. Yana yi miki zafi? Sannu”.
Ta rude matuqa, jikinta sai bari yake, zuciyarta fal haushin Aazeen. Karin bakin cikinta shi ne na halin ko’inkular da akai wa Ladidi akalla ya kamata su zo su duba halin da Ladidi ke ciki, yanzu ya za ta yi idan Ladidin ta makance?
“Nurat ina son dora girki”.
Cikin tausayawa, “Haba ta ya ya za ki iya wani girki? Ki bari ni zan yi kokari in ga na yi”.
“A’a Nurat, ki rufa min asiri”.
“Kada ki damu babu wanda zai fahimci haka. Ina zuwa… amma dai akwai duk abin da zan bukata ko?”
Ladidi ta jinjina kai.
“Ok, yanzu ki kwanta ki huta kafin ki tashi na gama kin ji”.
“Na gode Nurat”.
Ta bi Nurat da kallo tana jin qaunarta a ranta. Halayyarta daban da na iyayenta, kamar yadda ta lura kowa na gidan bai damu da damuwar wani ba, sun dauki rayuwarsu tamkar na turawa, musamman Aazeen wadda duka dabi’unta irin na ubanta ne. Ita kam Hajiya Rahma babu wanda ya fahimci inda ta sa gaba, ba za a dai a kira ta mara kirki ba, kodayake ba lallai a fahimci wace ita ba, saboda ba ta cika shiga shirgin mutane ba, sabanin Nurat wadda ba ta wuce shekaru sha bakwai ba, yarinya mai mutumci da shiga rai, wadda ba ta xauki kanta da zafi ba, ba ta da wahalar sha’ani, kunyarta shi ke kara mata daraja a idanun jama’a, don hakan ya zame mata tamkar wani ado.
Tazarar da ke tsakanin kicin da dakunan da ke gidan ya sanya babu wanda ya lura da kai-komonta. Wanke-wanke ta fara yi, ta ci uwar damara. Bayan ta gama ta shiga dogon tunanin abin da za ta dafa wanda ba zai ba ta wahala ba. taliya ta ayyana a ranta, amma ta ya ya za ta sarrafa kayan miya? Ita ba ta taba kwatanta shiga kicin don sarrafa wani girki ba.
Komawa ta yi dakin Ladidi, don ta gaya mata yadda za ta yi. Bacci ta ke yi lakadan, har da su minshari. Murmushi ta yi ta koma ta shiga tunanin yadda za ta yi. Tunawa ta yi da tana da littafin girki, da sauri ta nufi ma’ajiyar littattafanta. KADARAR KITCHEN wanda Bilkisu Salisu Funtua ta rubuta ta nemi guri ta zauna, tare da dubo abin da ta ke son dafawa. Ta mayar da littafin ma’ajiyarsa, ta koma kicin ta debo kayan miya ta wanke, ta soma yanka albasa.
Ji ta yi wuqa ta shige hannunta, ta kwalla kara tare da sakin wukar yadda ta ga jini na zuba ne ya sanya ta rudewa.
A sukwane Zaruk ya dano kicin din ya kai hannu zai riko hannunta. Da sauri ta maida hannun baya cikin tsananin tsoro.
“Ki bari in gani, ba ki ga jini ne ke zuba ba?”
Ta yi saurin maida hawayen da ke qoqarin silalo mata.
“Kada ka damu, kawai jinin ne, amma ai babu zafi”.
“Oh God! Wai ke me ma ya kawo ki kicin? Wa ya aike ki?”
Ta fara in’ina, ya daure fuska.
“Na ce da ke waye ya aiko ki kicin?”
Za ta yi magana ya mike a fusace zai fita.
“Don Allah ka yi haquri, zan gaya maka. Ka dawo don Allah Yaya Zaruk”.
Ya koma ya zauna cikin kafe ta da idanunshi.
“Ke nake ji”.
“Ladidi ba ta da lafiya shi ne nake taya ta”.
Ya sake xaure fuska.
“Ita din ce ta ce ki taya ta?”
Cikin rawar murya, “A’a, to gaya min”.
Dole ta zabi ta ba shi labarin yadda abin ya faru. Ya ja tsaki ya janyo mata kujera.
“Maza zauna”.
Ba ta da zabi dole ta bi umarninsa. Komawa ta yi ta zauna, nade hannun rigarsa ya yi ya shiga aiki tukuru. Ta dinga kunshe dariya a ciki, ga mamakinta Zaruk ya iya komi.
Ya dube ta a sakarce, “Nurat, fito ki yi dariyarki a bayyane”.
Ta dabarbarce, “Da gaske Yaya Zaruk ba dariya nake yi ba”.
Jalof din taliya ya yi, sai plaintain da ya soya farfesun kifi. Ya diba a cokali ya mika mata. Ya yi mata alama da ta yi testing.
Ta karba tana dandanawa. Ya kafe ta da ido.
“Ya ki ka ji?”
“Yaya Zaruk, ashe ka iya girki?”
Ya harare ta, “je ki yi maza ki shirya dinning ko?”
“An gama Yayana”.
Da sauri ta yi abin da ya ce. Bayan ta gama shirya komai ya ce da ita, zai je ya siya ma Ladidi magani. Yana fita ta shiga wanka.
Zaruk ta hango da Hajiya Rahma zaune suna cin abinci, ta sakar masa murmushi. Karasawa ta yi ta zauna. Ba a jima ba Alhaji Usman suka shigo da Aazeen rike da ledoji a hannu, su ma joining suka yi zaman cin abincin.
“Yau Rangida babu korafi, da alama abincin ya yi dadi”.
Nurat ta dubi Zaruk ya sakar mata murmushi.
“No Dad, kawai dai ina jin yunwa ne”.
“Da ma ai ke ba a taba iya miki”. Hajiya Rahma ta ce da ita.
“Ladidi ta cancanci tukwici kenan?” In ji Zaruk yana kallon Nurat, ya faki idonsu a hankali ya dinga motsa baki yana nufin zai fada.
Ta yi saurin kada kai tana rokonsa. Mikewa ya yi tsaye.
“Ni zan wuce Ammi, a yi wa kuku godiya sosai”. Ya fada yana murmushi.
ABUJA
“Ummi ya kamata ki saba, na yi tafiya zuwa qasashen waje bila’adadin, na zaga duniya komai bai same ni ba, nan zuwa Kano tafiyar mintina ne, da zarar jirginmu ya sauka shi kenan an wuce gurin. Ko kina tsoro ne kada jirgi ya fado da dan lelenki?”
Deedat ya fada yana kokarin tallafo kuncinta da hannayensa biyu. Ta sauke ajiyar zuciya cikin damuwa.
“Ba haka ba ne, kawai dai ina tsintar kaina cikin rudu duk lokacin da ka ambata cewar za ka Kano. Bana samun nutsuwa, ban san me ya sa haka ba”.
Ya yi murmushi cikin kokarin kwarara mata gwiwa.
“No, Ummina kada ki mance kirarina, in ka san ni ni ne, in ba ka sanni ba, ba ni ba ne. Ummina. Kowa ya san ba ni ba ne, kin ji sam ba ni ba ne babu wanda ya san ni, kuma ma ban da ke da abinki addu’arki fa na tare da ni, ba zan mutu YAUTAR ZUCIYA PAGE 2 3 4
NA BILKISU H MUHD
Ban taba ganin mutum irinsa ba, ina da tambayoyin da zan yi masa bila adadin, ban san me ye ribarsa na tuna in boye kansa ba”.
“Rangida na fi tunanin asalinsa talaka ne, kai ni gani nake ma kamar babu shi, kawai ana son yawo da hankalin mutane”.
“No Dad, na ji a majiya mai qarfi akwai shi, duba ka ga yadda yake sakar wa Malaman addini miliyoyin kudi duk wata, sauka ko musabaqar alqur’ani da za a yi sai ya kashe miliyoyi. Na fi tunanin qila aljani ne. In ba aljani ba, waye zai yi abin da yake yi? Duk wani mai kudii yana so idan ya yi abin bajinta a san ya yi. Yana son duk inda ya sanya qafarsa ana girmama shi”.
“Dad su ma wadan da suke program din nan ba su sanshi ba kenan?” Nurat ta tambaya.
“Haka na ji ana cewa”.
Aazeen ta ce, “To me ye amfanin abin da suke yi?”
“Saboda suna son ya san taimakon da yake yi, saqo na isa gare su”.
“Mtsew! Ji wani shashanci”.
Alhaji Usman ya ci gaba da fadin, “Wannan da zai fito ya zama dan siyasa ba zai wani sha wuya ba, don abin ma da yake yi zai zamo kamar kamfen ne”.
“Dad bana ji an ce ba shi da aure ba, kuma mara aure ba ya tsayawa takarar neman gwamna?”
“Wannan ai mai sauqi ne, daga ya amice cikin lokaci qanqani zai iya yin aurensa”.
“Dad idan na kwanta ina mafarkin ya zama mijina. Dad ina ma zan ganshi ko da sau daya ne?”
“To Dad ta yaya taimakonsa ke isa hannun mutane?” Nurat ta sake tambaya.
“Ya kan kintaci duk lokacin da yake da buqata ya je inda yake buqata, bayan kiran assalatu yake isar da zakkarsa ko sadaka, sai dai ka ji an dan qwanqwasa maka qofa. Kana budewa za ka ci karo da abin da yake rabonka, duk nacinka ba za ka ga kowa ba. Da yawa an sha yin dako sai kun gama hada target da inda za ku ganshi, sai kawai ya sauya yanayin lokutan rabon babu zato babu tsammani ka ke ganin kayan arziqi, kama buhun shinkafa, taliya, kudi, sutura da sauransu. Ba qananan kudi yake badawa ba, kudi ne wanda zai ishe ka ka ja jari, wanda in ka yi dace ka yi sallama da talauci. Dadin dadawa yana da asibitoci, makarantu wadanda an gina su ne kawai saboda talakawa”.
“Tab! Ka ce shi kawai don taimako aka halicce shi?” Aazeen ta fada.
“kila ma na sanshi”.
Alhaji Usman ya yi dariya, “Babu mamaki don an ce yana nan yana mu’amala da mutane ba tare da sun sanshi din ba ne”.
“Gaskiya wannan batan basira ne, shi ke nan ya dauki kansa kamar kowa, ba ya son idan ya shiga guri a dinga nuna shi ana b shi girma? Shi sam bai damu da ya yi suna ba Dad? Wadannan abubuwan fa su ne jin dadin, kamar ni in na shiga guri za ka ga yadda ake girmama ni, ina taka duk wanda na so”.
“Yaya Aazeen wannan riya kenan fa, kuma duk mutumin da yake riya ladansa iya nan kawai za ta tsaya. Sai dai mutane su yabe shi. Shi ya ji dadi gurin Ubangiji komai fanko yake”.
Ta ja tsaki, “Ai kin ji irinta. Dad shi ya sa na qi amincewa da makarantun nan, islamiyya tahfiz, makarantar magriba ko yaushe ba ta da hutu tana zuwa ana zura mata al’adun mutan da. Ta sauke abin da aka ce an fi buqata, wato alqur’ani mai girma, amma har yanzu ta qi ta haqura”.
“Ke ma da a ce kina zuwa duk za ki watsar da wadannan shirmen da ki ke yi”. Hajiya Rahma ta fada.
“Hum Ammi kenan, da girmana da komai kawai sai na je na zauna ana koyar da ni salon kowa ya raina ni? Ita dai da ta ga za ta iya sai ta je ta qara ta”.
“Da Allah malama rufa mana baki”. Ammi ta ce da ita.
A take ta ji haushi, Alhaji Usman ya dubi hajiya Rahma.
“Ba kya kyautawa”.
“To yanzu me na yi ne?”
Bai ce da ita komai ba ya miqe ya rufa wa Aazeen baya.
A lokacin da kowa ke bacci, a lokacin ta ke sake sabon zama a gindin akwatun talabijin, a nan ne ta ke cashe mata kallon. Qarfe goma sha biyu tana zaune a sitroom dinta ta dora qafa daya kan daya, lokaci-lokaci ta kan dauki tea ta kurba. Rimot ta dauka tana canza tashoshi. Ta ji dadin film din da ta ga ana yi. Ta ajiye rimote gaba daya hankalinta ya karkata daidai lokacin da aka nuno jarumin da budurwarsa rungume da juna suna yi wa juna wani irin wasa, yadda jarumin yake ba ta wani hot kisses tare da sake rungume ta tsam-tsam cikin wani irin salo, ji ta yi gaba daya hankalinta na neman fita a jikinta.
“Wayyo! Tana son wannan rayuwa, su kam Turawa sune suka zo duniya a sa’a, sukan yi duk abin da suka so a gaban kowa ba su da shamaki da duk wata rayuwa da holewa.
Ta lumshe ido tare da kwantar da kai a allon kujera tana saukar da numfshi, ina ma a Turan aka halicce ta? Ba za ta iya jurewa ba. ta zaro waya ta shiga lalubar wata lamba.
Ringin daya aka dauka daga dayan bangaren aka ce, “Ya na ji muryarki haka? Me ke faruwa?”
“Komi ma ya faru. Ya za a yi ka zo gare ni?”
“Ke ba ki da hankali? Idan na zo in ce me? Ba ki ga dare ya yi ba? ki lallaba zuwa gobe, amman gaya min duk me ya janyo hakan”.
Ta ja tsaki hade da katse wayar. Ta yi lamo cikin wani irin shauqi, shi ne kawai yake dan kwantanta yadda ta ke so, shi ne yake fahimtar feeling dinta, shi ma din tana tunanin don ya yi karatu a Turai ne.
“Mtsew!” haka ake ta faman son ta yi aure, to ta auri me? Babu abin da auren bahaushe ke haifarwa sai bacin