Showing 33001 words to 34150 words out of 34150 words
Chapter 12 - KYAUTAR ZUCIYA Book Complete By Bilkisu H. Muhd.txt
da ya dire gwiwoyinsa a gabanta ba, ya lura babu alamar wasa a maganarta.
“Ummita me na yi? Gaya min, ba zan jure fushinki ba. Kada ki yi min haka”.
“Da gaske nake yi, yau zan bar maka gida, ai ni ban san haka kuxi ke sanya izza ba, ban san haka kuxi ke sanyawa a daina girmama na gaba ba”.
“Wayyo Ummita, ya isa haka. Yi sauri ki gaya min abin da ki ke so na yi, in gaggauta yi”.
“Ka fi kowa sanin abin da nake so’.
“Ummita a tunanina ina yin duk abin da ki ke so, ki ka umarce ni tun ina qarami. Kin tarbiyyantar da ni, kin nuna min yadda zan kyautata wa marasa qarfi, rayuwata gaba xaya ta tafi ne a taimakon miskinai. Na kan ajiye buqatata na yi tasu Ummita, arziqina gaba xaya ya zamo ba nawa ba, na gina asibitoci saboda talaka ya ji sauqi. Na gina makarantu saboda su. Na gina rayuwar mutane da dama duk domin su ma su ji cewar mutane ne, kin ce in voye kaina saboda kada yabon jama’a ya haifar min da girman kai duka na yi. Yanzu me ye ya rage? Me ye ban yi ba?”
Ya qarasa maganar a raunane.
“Duka ka zubar da ladarka. Auren Nabila shi ne ya fiye min dukkan komai, wallahi idan Nabila ta mutu ta sanadiyyarka iyayenta da ni ba za mu yafe maka ba”.
A ruxe ya ce, “Tana ina? Me ke faruwa da ita?”
“Tana asibiti babu yadda ta ke. Wallahi kai kam Babana ba ka da imani, me ye laifin Nabila?”
Ya kamo hannunta ya riqe.
“Ki yi haquri komai zai yi daidai, bari in je asibitin idan na dawo za mu yi magana”.
“Ka ga na gaji da qarairayinka babu abin da zan ji daga gare ka, na gaya maka ba za ka same ni ba”.
“No kada ki yi min haka, na yi miki alqawari za mu sasanta ki ba ni lokaci in dawo ko kuma in zauna mu gama magana sai in tafi”.
“Shi ke nan, je ka zan jirayi dawowarka”.
Receiption xin cike dangin Nabila ganinsa ya sanya kowa miqewa, don nuna girmamawa a gare shi. Haka ya dinga miqa hannu ga masu qoqarin durqusa masa. Wani abin takaici har da tsoffi, arziqi kan sanya rashin gane masoyin qwarai.
Abdul babban yayanta yana nan zaune sai faman cika da batsewa yake, yana kallon Babansu na zungurinsa a kan ya je ya kwashi gaisuwa da kansa ya qarasa ya miqa masa hannu. Da qyar Abdul ya miqa nasa, nuna masa xakin da ta ke suka yi.
Likitoci biyu tsaye a kanta, xaya na qoqarin xora mata drip. Ganinsa ya sa su ma suka gaggauwa abin da suke yi, bayan sun gaisa duka suka yi waje, da alamar ba ta ji shigowarsa ba, qamshin turarensa ta shaqa. Ba ta tava jin irin wannan qamshin a jikin kowa ba in ba shi ba.
Tana qoqarin juyowa muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ji ta yi tamkar a mafarki, qoqarin miqewa ta yi.
“No Nabila, ki bi a hankali, kin ga ba ki da lafiya, kin ji?”
Wani irin daxi ya kama ta, ta dinga jin kamar ta rungume shi.
“Yaya Deedat ka dawo?”
Ya jinjina kai, tausayinta ya dinga shigarshi ganin yadda ta rame, idanunta sun faxa loko.
“Qanwata me ke damunki haka?”
Idanunta fal qwalla ta ji kamar ya yi mata fami.
“Yaya Abdul ya ce na haqura da kai ba aurena za ka yi ba, ba ka sona, da gaske yake yi kai ka ce da shi ba ka sona?”
“In ji wa ya ce miki bana sonki? Kin tava jin mutum ya qi qanwarsa?”
“Yayana na gode, kuma ina sonka. Ban taba son wani abu kamarka ba. Ina matuqar sonka, yanzu ka dawo ne mu yi aure ko?”
Ta tambaya cikin tsira mishi ido.
“Yaya Deedat ba haka ba ne?” Ta faxa daidai lokacin da ta xora hannunta a kan nashi.
“Kin ga ki bari ki qara samun sauqi sai mu yi maganar, kin ji?”
“Ba zan warke ba, ba zan tava warkewa ba in har Allah zai nuna min ranar da za ka qi aurena gwara ya xauki raina, ba zan jure ganinka alhalin ba ka zamo nawa ba”.
Cikin dabara ya zare hannunsa daga cikin nata. Ta sani qoqarin ficewa yake yi.
Ta yi saurin zare drip xin da ke hannunta, sai ga jini. Ya yi gaggawar gutsuro auduga ya danne gurin jinin ba tare da ya xauke hannun nasa ba. Haka ya fi komai yi mata daxi, sai ta ji ina ma su dauwama a haka? Tsananin kallon da ta ke yi masa, har ya qufula ba ya son mace mara kunya. Duk macen da ke tsura wa namiji ido haka, yana yi mata kallon mara kamun kai.
Lokaci xaya ya ji yana jin haushinta, daga vangarenta ji ta ke yi tana qara sonsa. Tana jin ya fi kowa idan ta tuno da shi ko da ba ya nan nishaxi ta ke ji. Ko kallonta ya yi sai tsigar jikinta ta tashi.
“Yaya Deedat bana son wannan shirun, don Allah ka ce wani abu”.
Ganin jinin hannunta ya tsagaita ya sanya shi xauke hannunsa.
“Tafiya zan yi Nabila, zan dawo kin ji”.
“Ba za ka tafi ba, ka gaya mini yaushe ne za a yi auren nan, ka ga kowa fushi yake yi da kai. Kowa haushinka ya ke ji, Ummita, Yaya Abdul, Ummata da kowa”.
Ya yi saurin katse ta.
“Ba zan tsallake lokacina ba, duk kun mance da cewar shi aure lokaci ne, da zarar Allah ya kawo lokacin komai sai ya zamo labari”.
Kalamansa sun fusatata, ta dinga jin kamar ya gama raina mata hankali. Idanunta suka juya.
“Da haka ka ke fakewa”.
Cikin xaga murya ta dinga magana, ta ci gaba da faxin, “Komai sai ka ce Allah, ni na gaji! Na gaji da wannan qarairayin naka”.
Yana son yin magana ta qi ba shi dama.
‘Ba zan saurare ka ba, komai ya zo qarshe, ka fita ka je, na haqura, inyaso in mutu’.
Tausayinta ya sake mamaye zuciyarsa, yana cikin yanayin da ta ke ciki. Yadda yake ji ya ninka nata, inda zai iya da ya haqura da ita, sai dai halayyarta ya sanya shi yake qyamarta, ya so ya aure ta duk da cewar bai tava jin sonta ba, amma gurvataccen halinta ba su barshi ba. yana son ya yi aure, ya hayayyafa yana son yaransa su kasance a qarqashin uwa ta gari. Auren Nabila zai rusa masa dukkan mafarkinsa, yana da burin auren mace xaya, muddin ya auri Nabila yana da tabbacin tilas nan gaba sai ya sake aure. Zai auri Nabila ne alhalin ya auri wata, zai aure ta ne da sharaxin ba zai haihu da ita ba, abin da ya san ko a mafarki ba zai yiwu ba.
TURQASHI!
Mu je ga littafi na biyu don jin yadda wannan gumurun za ta kasance. Yanzu aka soma labarin ma.
*_wanan shine karshan littafi na daya Kuma karshan free page duk Mai son cigaban shi zata iya tu tubata a Kan number da nabada da Kuma account din da suke sama karku manta kudin karatu 300 ce kacal_*
Taku har kullum.
Bilkisu H. Muhd.