Showing 1 words to 3000 words out of 35867 words
Chapter 1 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt
[11/20, 2:59 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Littafina na siyarwa ne, idan kinsan baki biyaba dan Allah karki karanta, bazan miki Allah ya isaba koban fad'a ba dama Allah ishashene kowa sani, dan haka idan kinga daidaine seki karanta*
0
Dukda nasarar shigewar da Abu huraira yae hakan be hanawa murfin motar dakar k'afarshi ba, da sauri ya rufe motar suka soma zarar ido suna bin halittar datayi burki tana kallonsu harshe a waje, bazasu iya gano ko wace halitta bace ba amma tabbas bazaki bane ba, hasken dake nan na farin wata baze basu damar ganin abun da kyau ba, sedai koma miye muguwar halittace kuma taso cutar dasu, haka tafi 1 hour tana zagayen su su kuwa se had'a gumi sukeyi dukkansu acikin mugun tashin hankali suke mara misaltuwa, daga bisani dabbar ta wuce abunta kuma, dukda haka sun kasa sakin jikinsu gashi k'afar ta Abu Huraira tana masa zogi, Allah ne ya taimakeshi amma ya bugu da kyau, Tawayen sane yaja masa qafar gaba man zafi haka sukai masa luddan gaske suka rage glass na motar sabida ventilation ya shigo sosai.
*************
Yau daikam baccin ma babu wanda yayi shi acikinsu, da asuba haka suka daure suka cire tsoro suka sakko sukai alwala sukai salla, sun jima suna adu'o'i har gari ya waye sannan suka k'urawa inda suke ido, kowa hankalinsa atashe yake
"Abu Huraira ni wlhy tsoro nakeji, nagaji kuma inaso inje gun Mom ma" dama yasan halin rikicin d'an uwansa shi arayuwa bayason takura ko rayuwan wahala sam
"Haba Twin? Kayi hakuri mana, ya zaka sako zancen gajiya agun dababu alamun mutane ma bare musamu maceci? Wannan wurin abu d'aya zan sanar daku ku saka aranku cewan Allah ne kawai ze fitar damu a wannan jejin, so acire zancen zuwa gida yanzu, Allah dai ya rufa mana asirin mu ya nuna mana hanyar barin wannan gun acikin sauqi" Kallonsa kurin yae amma bece qala ba, hankalinsa atashe yake dan shima ya hango abin, ga basuda mai isashe danko rabin tanki basu dashi....
***********
"Haj na sanar dake yaran nan suna lafiya, mesa kike hakane wai?, ni kinga yau zanje ghana tafiyar nan ta aikice ba fashi, bazanji dad'i ba ace wai na barki a wannan halin, ki kwantar da hankali, na tura su barde mota biyu da sojoji tare dashi mukaje kaita wancen lokacin yasan k'auyen inyaso su duba idan sun baro ne se aduba ko ina, bana tunanin komai amma an sanar dani wai wataqil sun saki hanyane, dan inka shiga jejin rud'u ne dashi amma babu namun jeji sosai a wurin dan haka kiyita adu'a, kinji" Nisawa tae yanzu kam
"To hakan ma yayi Allah ya tsare munkai su kuma ya bayyanar dasu cikin qoshin lafiya" murmushi yae ya shafi gefen fuskarta
"Ayita adu'a hajiyan general, Allah ya bayyanar mana dasu" Murmushi ta rakashi dashi kurun harya bar gidan.
******'''''''******'''''''*******
Tafiyar nan dai anyita babu ji ba gani, amma ba alamun gari agaba ko kuma abayansu abu huraira, basuda wata torchlight seta waya, gabaki d'ayan hankulansu sun tashi, tuni man motarsu ya k'are qaf, gasu a tsakiyar jeji ba hanyan gaba babu na baya, suna gudun su taka konan dacen ne azo kuma idan anga abun tsoro ba wurin b'uta, acikin k'ank'anin lokaci duksun rame sun zagbe
"Bana tunanin shawarace me kya barin gun motar nan da yamman nan, kurun mu kwana kaman yanda muka saba, inyaso da safe semu soma cin kasar" jinjina kai Dawud yae cikin gamsuwa da bayanin Abu sufyan
"Hakan yayi, mu kwana amma fa idan muka cinye cake da wancen bushashen donut ko shakka banayi se yunwa ta hallakar damu idan bamu b'ulle tafiyar jejin nanba gobe, sabida bamuda sauran wata madafa" Girgiza kai Abu hurairah yae
"Allah yasoma acikin k'aramar jakar cen ta baya akwai cookies me yawa da cyama ta mana, bamuko tab'a shiba, idan zaku tafi mu kwashe bread da Baba ladi ta bari dukda ya soma sandarewa" Babu wanda yae magana yammakam acikin bayan motar suka kwana dukansu a takure rayuka ba dad'i.
***********
Sallan Asuba kurun suka idar suka kama hanyar dasuke tunanin itace me b'ullewa, badan zukatan su sunyi na'am da bin hanyar ba sedan basuda wani zab'in daya wuce wannan.
***********
Zaman shiru ne ya ratsa wurin na kusan dak'ik'u sama da hamsin kasamcewar hanyar dasuke tunanin itace har sukai tattakin binta ta b'acewa ganin su, mamakin ganin agaban wannan babban Tekun sukeyi tunda yake sun sandai mota bata tsallaka ruwa, kuma su sam basu bi wannan hanyar ba, agogo Abu sufyan ya kalla dake d'aure a wutsiyar hannunsa k'arfe biyar da rabi na yammaci, tun asuba suka kamo hanya da k'afa kasamcewar motarsu ba mai, gasu d'auke da kayan abinci na flour da ruwan sha, ga daddumar sallah, sun gaji iya gajiya idan ba wannan hanyar bace ba ana nufi juyawa zasuyi su koma baya kenan? Subar jejin yaushe? Koda yake har suka iso nan babu wara dabba dasuka had'u da ita idan ba tsuntsaye da k'adan garu ba,se kulb'a dasuka gani so d'aya jal! Shiru kowa da abinda yake sak'awa aranshi secen Abu Huraira yace
"Ku tashi mu mik'i hanya muga ko zamu kai k'arshen kogin nan, bana tunanin ma a Nigeria muke yanzu kam watak'il tunda kukaga ruwa idan muka tsallaka zamu samu hanyan b'ullewa mu fita daga cikin wannan doguwar hanyar mara hanyoyin b'ullewa danni fa a gaskia na sare ma da rayuwar gabaki d'ayanta" Nannauyar ajiyar zuciya Dawud ya sauke
"Hakane mu zagaye mugani, tunda akwai ruwa da ikon Allah zamu akwai gari a kusa" Haka suka mik'i hanyar zagayen babban ruwan dabashida iyaka dan basako hango k'arshen sa takowane kwana.
Sunyi kusan awa d'aya babu labarin k'arshen ruwa ga magrib tayi duhu ya sauka sallah suka tsaya sukayi, da ruwan sukai alwala bayan sun idar suka karanci alkur'ani me girma sannan suka suka zauna suka jira zuwan isha suna idarwa suka kunna torchlight ta wayan Dawud dama irin me hasken nan ce ga wayar tana baiwa wata wayar charge ma suka qarayi gaba, basa so su kwana abakin teku, so suke suga wuri me yalwar fili sabida tsaro.
**************
Hankalin sarkin atashe yake sabida yau saura kwana bakwai ayi sacrifice da rayuwar wani me tsautsayin tsallakar tekun ya shigo garin su, gashi har yanzu shiru, wani daga garin be tsallaka ba gashi wani daga wani garin be fito ba, idan har sati ya zago batare da ansamu wanda za'a sadaukar ba shi za'a yanka, kuma a k'ona iyalanshi da ransu, shekararsa ashirin da uku kan mulki wannan ne karon farko dayazo saura kwanaki bakwai batare da ansamo me tsautsayin daya tsallako ba koya fita ba, sun tura jirgi yakai bakwai amma shiru kakeji kanshibya matuk'ar d'aure....se zagaye yake a d'akin shishi kad'ai yana zare idanshi, batun yauba yaso ya kashe wannan bak'ar al'adar amma be samu dama ba har yanzu, duk yanda yaso bokan garin baya barin sa, shikad'aine sarkin dayae shekaru masu yawa ma, sauran duk basa wuce uku biyar zuwa bakwai, cikin damuwa matarsa ta kallesa da yaren dabaka gane wane iri ne tace dashi
"Nayi mafarki wani zezo ko saura kwana d'aya ne, kayi hak'uri k'uru" kallonta yae cikin damuwa
"K'uruwa, idan kuma ba haka bane fa, rayuwar mu duk k'arewa zatayi "
"Shekaru da yawa kanayi, kaine me tarihi kayi shekaru da yawa kanayi, ko yanzu zakayi" zama yae kusa da ita
"K'uruwa idan yakai saura kwana d'aya bezoba zamu gudu da dare, nasan hanyoyi da yawa bani bari akashe mu" Cikin damuwa tace
"Ze mazo kaji?" Shiru dukkansu sukayi ba wanda ya k'ara cewa komai, Lawuri dake kwance tana jin me suke cewa ta share k'wallan daya zubo mata, ita tasan mutuwa ma zasuyi ko basu gudu ba ita zata gudu gobe gobe ma, bazata bari a kashe ta a banza ba........
******
Littafina na kud'ine, dan Allah idan baki biyaba karki karanta mun, idan kinaso kinsiya ki tuntub'i wannan lambar...07084161619.
**********
Wannan daren a zaune suka kwana dukkansu, babu wani wanda ya iya runtsawa acikin su, ga mamakin su safiyar Allah suna tashi sega jirgin ruwa abakin teku, basuga wanda ya kawo ba, kurun dai suna tunanin cewar daga wata gab'a yazo nan koda yake ba kusa da tekun suka kwanta ba, sunga yana hawowa idan yazo da gudu watak'il wasune suka ajiye in hakane su ara kawai su tsallaka ruwan, a gurguje sukayi sallah, sunyi mintuna goma suna adu'a kafin su shiga jirgin suka d'auki falankan da ake turawa dake shinfid'e acikin jirgin suka somayi kamar yanda suke gani anayi a film.....
********
Lawuri kuwa ta gama shirinta tsaf acikin dare taje bakin tekun, tana jiran zuwan saurayinta Mik'aru, shine ze taimaka mata subar garin sabida a tsorace suke, sun gano kashe sarki za'ayi lokacin mutuwar sa yayi, kuma idan har aka kashe sa to kuwa tabbas ita mazajen garin zasuta amfani amfani da ita layi layi harseta mutu, kasancewarta mace kuma 'yar fari, sauran 'yan gidan kuma za'a qonasu, idan akayi amfani da ita so 100 bata mutu ba to da ranta za'a binne ta, acewar su tun daga ka kanin ka kanni idan sarki ya gagara kawo wanda za'a sadaukar idan ba'a kashesa da iyalansa ba wani mugun abu ze faru a garin wanda ze iya kashe kowa da kowa ma.
Mom Nu'aiym 03
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
01.
Ko kad'an bazaka ce ya tab'ayin dariya bama idan ka kalli fuskar sa yayi wani kici kicin da fuskar nan sekace wanda aka aikowa da manzon ranar mutuwar sa, cikin tsare gida mahaifin sa ke kallon sa
"Yaya zakace bazaka ba? Ni kakeso naje kokuma so kakeyi ka mayar dani sa'anka sarai ka sani bana sauya hukuncina, baiwar Allah nan tayi shekaru masu yawa bataje gidansu ba, sabida haka kai da kuma Abu huraira kune zakuje ku kaita idan yaso ku dawo city ku jirata daga nan baya ta kammala adadin kwanakin data gaya muku zatayi seku koma ku d'akko ta tunda yake tafiyar akwai nisa daga nan DOGUWAR HANYA ce zakubi" Be isa ya k'arayin gaddama dan haka cikin girmamawa yace
"Kayi Hak'uri dad, dama ban fahimci manufar kaba ne se yanzu, yaushe zamu tafi to?" Kallon sa uban yae
"Kuje ranar Juma'a da safe" iyakar abinda General ya fad'a kenan ya mik'e cikin isa dajin mulki ya haura saman sa ransa ad'an b'ace, besan meyake sa Abu Sufyan yake da kafiya ba akan al'amura wataqil kuma halin sane daya gada yakeso ya masa fintinkau akan halin.
Abu sufyan yana mik'ewa hanyar waje ya nufa, sojoji se k'ame masa sukeyi kkallon su beyi ba yau ran maza ya b'aci, kurun shi dad baze saurari uzurin mutum ba seya wani kafe akan seyayi abu, yana da hidimomin gabansa yazece seyaje har wannan garin abin haushin ma acikin k'auye irin wannan tafiyar wahala ce zasuyi yasani tabbas dan kuwa akwai direbobi masu tulin yawa agidan, sesuje da ita mana amma dan wani neman rigima dad har yace ita zata fad'i adadin kwanakin datakeso su duk uzurinsu ya zamto na banza kenan? Haba dad sam baya adalci wasu lokutan wlhy, figar motar yae ya soma gudun fanfalaqi akan titin na birnin Tarayya ranshi a b'ace.
***********
Amma General kana ganin hakan ya dace kuwa, yaran nan dukan su sunada uzuri ni samma se nakeji ajikina tafiyar ba alkhairi bace ba sam" Harara ya wurga mata
"Se uzurin su yafi aiken dana musu? Sesuke had'e kai sunawa mutane shashan ci da girmansu da komai shekarunsu nawa yanzu? Haba Haj Adama, mesa newai ke har yanzu kike biyewa shirmen yaran nan da yawo suke so suje inane bazasu jeba dan Allah? Wlhy bazan janye maganar tafiyar nan tasu ba jibi jibi, dole ne sukai mun uwata har garin su su kuma jirata tayi adadin kwanakin datakeso tayi sannan su dawo da ita, mutunci d'aya zan musu shine su koma cikin gari su kama hotel su kwana kafin ta kammala sesu koma k'auyen su d'akkota su dawo" Nisawa tae
"Shikenan tunda haka kace, ina musu fatan Alheri Allah ya kaisu lapiya ya kuma dawo dasu lapia"
"Ameen" itace kurun kalmar da general ya furta ya mik'e yabar d'akin, yana fitowa motoci suka jeru burjik da sojoji se sare masa akeyi shi kuwa dama fara'a bawai damun sa tae ba ya wani sha mur bako alamun rahama a fuskar sa.
************
"Dude kana ina?" Ya tambaya bayan tawayen nasa ya d'aga wayar sa
"Ina Green tea" tsaki yae ya juya akalar motarsa zuwa cen batare dayace masa komai, cikin mintunan dabasu wuce sha biyar ba se gashi a wurin, k'arisawa yae ya baiwa Abu huraira hannu shida wani abokin shi suka gaisa yace
"Kai Musty shine zaka gudo ka barni da Dad kaga wani had'a rai da yae yanata mun masifa sekace wani abu" Murmushi yae dayake shi dama be cika shariya irin na Abu Sufyan ba shi bama shida yawan surutu
"Bansan mezan ce masa bane ba, kuma kaima nace karkace masa haka ka hak'ura da bikin kawai tunda ba dole, amma ka kafe aika jaraba, halin dad ka manta kaima kasani wlhy baze tab'a bari mu tsaya biki mubar aikensaba kona waye" Tsaki Abu sufyan yae
"Amma bro aikasan ana iya d'age lokacin tafiyar nan, dama Allah ya taimakemu zamu samu wannan program na mata wanda za'ayi thursday night kaga Bashir bazeji zafinmu sosai ba" Kishin gid'a yae ajikin kujerar dayake kai cikin takaici
"Allah ya mana jagora, ni gabaki d'aya tafiyar se idan na tunata k'irjina yake bugawa wlhy, Doguwar hanya ce zamu bi fa" murmushi yae
"Nan zuwa garin aiba nisa karka wasu 'yan damu inshaa Allah zamuje lapia mu dawo lapia, kuma zamuji dad'in tafiyar nan" murmushi kurun yae yana tunanin tafiyar, dole yaje Shops nasu yaga tafiyar al'amuran yau tunda yake gobe thursday tafiya kuma friday ne, ranshi a jagule ya mik'e
"Abu Huraira zanje Building materials shop, sekaje tile making company ka had'a abubuwan nan, sauran kuma Cyama taje, tunda yake tana gari" jinjina masa kai Abu huraira yae yayinda ya mik'e ya musu sallama shida Friend d'inshi Dawud ya wuce.
***********
Hanifa kam tayi kici kicin da fuskarnan se rigima take masa akan tafiyar nan
"Amma yaa abu huraira da gasken wai tafiya zakayi, tayaya kakeso naci bikin nan baka nan" murmushi ya sake mata
"Hanny kiyi hak'uri banida wani zab'in daya wuce nabi umarnin dad,indai baso kike ya fasamun kai da gun ba toki dena wannan rigimar" Turo baki tae
"To naji amma karku wuce 2days plss" murmushi ya sakar mata
"Inshaa Allah my hanny karki damu kinji" Langwab'ar da kanta tae
"Ban maka alqawarin cewan baran damu ba, amma zan kwatanta" Murmushin dake fuskarsa ya fad'ad'a
"To my hanny barinzo in wuce yanxu dai, kinga gobe da sassafe zamu cira kuma ga gajiyan biki yau, Abu sufyan yanata kirana a waya ma" Fuskar ta sam ba dad'i tace
"Ina maka fatan Alheri Yaa Huraira kace ina gayar da yaa sufyan, zan muku waya so 20 akowace rana amma zancen motar fa?" Murmushi yae
"Tana waje ai, habu ya kawo tuni, yanzu zanje na daukeshi kese ki shigo da ita, and plss karki mun wasa da motana, kar kuma na dawo na tarar tayi datti ko wani scratch ajikinta" murmushi yanzu kam tae
"Yaa Abu kacika rigima indai akan motane, inshaa Allah ma biki kurun zanje dashi sena dawo na ajiye" murmushi yae
"Nizan wuce muje gate seki karb'a ko?" Haka ta tako shiyaja motarsa har xuwa gate suka rabu zuciyoyin su ba dad'i, itadai haka nan hankalinta be kwanta da tafiyar nan ba ajikinta setage ka tamkar akwai wani abu daze faru da yayyunta abinda bazata iya d'auka ba kenan har abada, jikinta amace ta k'arisa cikin gidan, kallonta Baba saude tae
"Hanifer na yada fuska haka ne? Naga duk kinyi wata kalar tausayi" kwanciya tae ta kwantar da kanta asaman cinyar Baba
"Baba hakanan hankalina ne kwanta da tafiyar su yaa Abu ba, ni tunda nake banji tafiyan dabe kwantamun ba kaman wannan" murmushi irin na manya Baba saude tae, dukkuwa da yake cewan itama tafiyan ba wani yi mata yae ba sam, jitakeyi tamkar tawa General magana akan a fasa tafiyar da yaran a bata kud'in mota aitasan hanya inyaso seta tafi abunta, batayi tsufan daza'ace bazata iya tafiya da kanta ba amma Tarasa meke damu General yacika kafiyan tsiya yanzu koda cewa tae zata mai magana ma baji zeyiba ranta ne kurun ze b'aci
"Hanifer a sanya alkhairi acikin zuciya, a k'ullawa zuciya salama, adu'a itace abun buk'atar su yanzu, Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya kurun zakice kinji" murmushi tae
"To Baba, ni ki sosamun kaina yana mun k'aik'ayi" sosa mata kan tahauyi batayi magana ba, tana tunanin yanda yafiyar nan ta yara zasu kasance, kosu sunce basason tafiyar, mahaifiyarsu ma haka mesa General ze kafe ne? Tana musu fatan alheri aduk inda suke"
**********
Dukkaninsu suna durk'ushe agaban mahaifiyar su sunyi shiru suna sauraraenta amma shiru batace dasu komai ba, yanayin shigarsu ya karb'esu sosai shadda ce brown me duhu da hula brown amma light sunsha d'inkin zamani d'an cakwai yayi cas ajikinsu, komai nasu iri d'aya ne banda abu d'aya shine agogon hannunsu wannan nashi fatar kalar baqi ce wuluk yayin da d'ayan ke sanye da kalar fari k'al, wanda wannan shine kad'ai abinda zesanya ka banbanta su sabida tsananin kamanin dasukeyi, ko iyayensu idan ba ta wurin idanunsu ba basa banbance su se abu d'aya na halayya koda yake dukkaninsu basuda yawan magana bare kace ka gane su sedai kurun d'ayan yanada hak'uri sosai yayinda d'ayan sam bashida hak'uri komai k'ank'antar laifi abin masifa ne a gunshi, amma yafi wancen sauk'in kai sabida baya rik'ewa mintuna k'alilan sun wadace shi ya manta da abu komai b'acin ran daya sakashi
"Kyautar Allah inaso aduk inda kuke kuji tsoron Allah, ku sani dukkkanin abinda kuke aikatawa Allah yana ji yana kuma ganinku, bakuda abinda shaku shamakance Lillahi daga ganin ku a komai dakukeyi, karkuga kaman kunyi nisa da gidan kuce zaku aikata abinda bashi bane halayyar ku ta asali, karkuyi abu koku bari danni kuyi dan Allah ku kuma bari dominshi, shikad'ai yasan ladan daze baku, kuna k'ok'ari sosai kuma ina