Showing 9001 words to 12000 words out of 35867 words

Chapter 4 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt

29 Jan 2025

1676

da inada hali bazasu sako musu zakiba, shi zan tura" murmushi tae mata


"Lawuri aike ta dabance, koma wani zakin ya zab'a semu mayar wannan" Murmushi tae daya mugun k'arawa fuskar ta kyau ta tab'e baki had'e da d'age kirarta d'aya


"Muje" tafad'a bayan ta juya tana takun k'asaita babu ko takalmi a k'afarta kafatanin garin ma bame takalmi harshi kanshi sarkin, harsun juya ta kuma waigowa ta kalli jakar su dake wurin tacewa d'aya


"D'akkomun abinda ke jakar cen nacikin irin wancen seki bar musu abunsu agun" dubawa tae bame fari seme baqi haka ta d'akko coke d'in d'aya tabar jakar anan, bayan sun gama maganganun dasuke suka ruf'e qofar cake d'in bayan da suka sako musu wani qaton zaki wanda ya sanya Abu sufyan sakin fitsari a wando ya koma bayan tawayen shi, se ihu mutanen garin keyi ganin yanda suka rud'e anata zabgawa zakin kirari, lokaci d'aya ya soma rura yana zagayen su, yayinda su kuma suka had'e gu d'aya suna adu'a had'e da kukan zuci haukace suke dukkansu.




Wurin Abu huraira yae gadan gadan, shi kuwa yae maza yana k'araso jikinshi ya kwanta k'asa ya dakarwa zakin ciki ya hankad'ashi bayan shi seda ya mulmula, tasowa zakin yae ya karkad'e jikinsa ya k'arayi kansa, nan ya soma adu'a dakiran sunan Allah ya k'ara kaimasa naushi ajikin wuya inda ya kuma zubewa, koda zakin ya d'ago sega idanshi yakoma ja kaman jini jikinsa ya koma kalar baki qirin, atake suka fahimci zakin na tsafine


"Ku d'auki ayar Allah Dawood wlhy ba zakin asali bane ba" haka suka had'a baki suna rero ayatul kursiyu da duk wata adu'a da karatun alk'ur ani me girma dayazo bakin su, hakan ce ta sanya zakin ya gagara dogon motsi ya zube agun yana zabga rura, daganan ya soma shure shure, itaciya d'aya Abu huraira ya zaro daga cikin wanda aka kafe akai cage dashi yace


"Allahu Akhbar!!" Ya dab'a mai aciki take agun zakin ya mace beko shura ba, mik'ewa tsaye sarki yae ya kallu k'uruwa yace


"Bala'i ya samemu ance me tarwatsa garin nan shine me kashe zaki, wannan akashesa da ruwan jikin zakin shine kad'ai maganin sa" Itad'inma rikicewa tae tace


"Hakane, daya tarwatsa garinmu gwara mu kashe sa, tunda susu ukune akashe makashin Lamme" haka suka d'auki kuka gaba d'aya garin ana wak'a aka kwashesu suda gawar zagin akai cikin gari dasu, a hanya sukejin labarin za'a jiqa Lamme (zakin suke kira haka), seya kwana ajik'e se'a baiwa wanda ya kashe zakin ruwan yasha shima ya mutu idan ba haka ba, garin ze kama da wuta danme tarwatsa gari ya karkashe su ne yazo idan be mutuba su zasu mutu...... Dawuda dakejin wannan yaren ya sanar dasu me ake cewa suka hau adu'a, yanzun ma a cage d'aya aka ajiyesu akaje domin aje a jik'a gawar lamme akashe Abu huraira.


*Littafina na kud'ine idan kinsan baki biyaba karki karanta dan Allah, idan har kinaso ki siya akan farashin 200 kacal ki nemi wannan lambar 07084161619*


*********
Da sassafe sauya agogon hannunsu sukai da sufyan da zobe harma da rigarsu dayake dama ba kala d'aya bace ba, suka shirya idan an kawo yayi bismillah so 21 shi yasha sun kula tsafine kawai Allah ne kawai ze kub'utar dasu.........


Lawuri duk yanda taso tayi bacci abun ya gagareta, abinda taji suna karantawa da k'arfi shine yake mata amsa kuwa acikin kunnuwanta, ko shakka babu so takeyi ta k'ara sauraren wannan abun, bazata iya bacci basam so take ta rik'aji sunayi koda mutum d'aya ne yana mata, mesa takeson ta saurari wannan abun? Mesa ma takeson yanda wannan yake kallonta? So take taje ita yama k'ura mata idanshi, kodan sabida ba'a saba kallonta bane ba takejin hakan? Tana tsananin son taga idanshi a nata, Kalmar sa ta karshe itace tafi kowacce yi mata yawo sabida yawon datake mata harta haddace "Allahu Akhbar!!", matsafane ko shakka batayi wannan ruwan datasha sun mata wani stafin ne aciki amma bari tabi daren nan taje gunsu ya mata wannan karatun dayake koma su duka su mata.


********
Shirinta tsaf tayi taje inda aka ajiyesu a sace, akwai masu gadinsu a wurin amma setayi magana akan zata gansu ne, suka bata hanya tashiga bukkar, tunkan ta k'arisa gun kage d'insu take kiyo sautin muryoyinsu suna wannan abin irin na d'axu, zama tayi batare data k'arisa inda suke ba tafi 3 hours seda taji shiru sannan tabar wurin, jikinta yana mata wani nauyi mesa bataso suka dena ba? Mesa batajin bacci, ya akayi acikin muryoyin nasu take gane muryan me kallonta ido cikin ido? Mesa ya tsaya mata arai, tsafi ko? Ta ayyana a ranta idan hakane zata gwada cin ubansa tun kafin dare yae mata.


*************
Washe gari dabino sukaci da cookie's da lemo roba d'aya kowa ya kurb'a, gwara sui manage kafin k'aryarsu ta k'are, sunaji ajikinsu cewar tabbas da yardar Allah zasu kub'uta.
Da shirinta tsaf tazo gunsu, itada muqarabanta, fitowa dasu akasa tayi dukda ya sauya kaya kallo d'aya sukawa juna ta gane cewar shine, dariya sosai tayi kafin tace amayar da sauran shi abarshi, sosai suka tsorata naba gaira ba dalili, suna mamakin yanda ta gano lagonsu da wuri haka, kodai wani yaga sanda suke sauya kaya ne? Kai tsafine dai danba wanda ya gansu.


Kallon juna suke ko k'iftawa basayi daga shi har ita, seda ta gaji ta janye idanta, hannunta takai inda gefen k'irjinta na hagu naji yanda wurin ke harbawa sauri sauri kaman ze faso k'irjinta ya fito da sauri tace a mayar dashi...lallai tsafine, so yakeyi ya kasheta, me kenan haka takeji a k'irjin ta?




********
"Bana tunanin baza'a gane wannan shirin namu ba, ina tsoron azo asamu matsala gaskia, kar su cutar dakai Abu sufyan, tun jiyan nan seda na sanar dakai banso wannan shirin ba, dan Allah ku taimaka na mayar da komai nawa, idanfa mutuwar ce k'addarata anan tabbas sena mutu kome sabarar ku, dan Allah ku sauya tunani" Dawud ne ya karb'e zancen da cewa


"Nasan tsafine shisa nace kuyi hakan, idan tsafinsu akan wanda ya kashe zakin ne kaga baze kama Sufyan ba, tunda muka fito gida muke had'uwa da hatsarin rayuwa iri iri, kuma adu'a ce take bamu kyakyawar kariya ko yanzu adu'ar zamuyi" haka suka zauna suka dinga zuba adu'a kaman ba gobe kafin a kawo Jiqaqqen ruwan zaki.




*kark karantamun littafi idan baka biya ba, idan ka karanta kuma toh.....idan kanason ka siya ka kira wannan number 07084161619*
Mom Nu'aiym.


[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*Lillatfina na kud'ine idan baki biyaba karki karanta dan Allah idan kin karanta kuma toh, masu son su siya ga number dazaku tuntub'a 07084161619*


06


Kwana d'aya sukayi kafin su tarar da inda motarsu Abu Huraira take ajiye, ganin motar ya tabbatar musu da cewar lallai nan suka bi, amma suna ina? Shine tambayar da suka gagara baiwa kansu ansa, barde ne ya jagoranci ci gaban tafiyar sabida ya tabbatar akwai dalilin su na ajiye motar, kuma amaimakon baya gaba sukayi, dankuwa ko yanzu bayan aka tsinci motar.


***********
Shirye shirye kurun akeyi na yanda za'a gabatar da bikin sadaukar war da za'ayi nanda kwanaki hud'u masu zuwa, yayinda aka jiqa gawar Lamme (zaki) ana so yacika lokacin da akeso a baiwa Abu Hurairah, Lawuri dukda jikinta a mace yake hkan be hanata murna ba, za'ayi maganin wanda ya Rainata, yacika son stoma idanshi acikin nata,tunda take kuwa babu namijin daya tab'a kallon k'wayar idanta seshi, agarin tagwaye so d'aya aka haifa 'ya'yan albarka ake musu suma maza ne kowa yanaji dasu amma suma basu tab'a kallonta haka ba, yanzu ta fahimci irinsu d'aya da wad'ancen bak'in, shirinta tsaf tayi tayi kwalliyar daidai yanda ta saba, taja layi itada masu take mata baya zuwa filin daza'a shayar da Abu huraira ruwan, burinta kawai taga da kanta tana tsaye yasha ruwan harya mutu agabanta taga yanda idan na raini ze kalleta.......


Duk yawan yalwar iskar safiyar dake kad'awa hakan be hanawa Abu sufyan had'a gumi ba, baze iya kallo akashe masa d'an uwansa ba amma tabbas a tsorace yake, shi kanshu Huraira baya cikin nutsuwar sa ko kad'an, banda adu'a babu abinda suke aransu dawud ma haka ba wanda zuciyar sa bata tsere wurin dukawa amma hakan be dakatar dasu daga ambaton Allah daneman kariyar shiba.


**********
Mom yaukan tafi ko yaushe rikicewa, kwanaki nawa suka shud'e? Lokaci yanata kwaranya ba daddy babu kuma labarin shi dama 2 weeks zeyi ga wannan mutanen kusan sati da tafiya amma shiru, bata samun wayan kowa acikin su, ta kasa gane meke faruwa, Cyama dake zaune kusa da ita itama cikin damuwa ta kalleta tace


"Mom please yaran nan inaga da adu'a kika dage kina musu daze fi musu amfani akan wannan damuwar, mom wai kinga yanda kika rame kuwa mom? Dan Allah niki rufamun asiri ki tashi muje k'asa kici abinci semu zauna mu musu adu'a"
A raunane ta kalli yarinyar


"Cyama wazan gaywa kukana dacen banda Allah?, kowane lokaci kika ganni a damuwa shi nake gayawa, ko yanzu shina duk'ufa nake gayawa ina yin adu'a na tabbatar Allah ze amsa mini sabida shi maji roqon bayin sane" Rik'o hannun mom d'in tae


"Tunda kinsan hakan mom seki rage damuwa, kinyi imani da Allah tokuwa tabbas zakiga ribar imanin, dan Allah kici abinci, ban isa ince karki shiga damuwa ba dankoni ma ina cikin damuwar amma baxanji dad'i ba ace bakyacin binci" Jinjina kanta tae


"Shikenan Cyama muje, inshaa Allah zanna rik'aci Allah ya miki albarka" .


**********
A filin aka ajiye Abu sufyan shishi kad'ai su Abu huraira kamma suna cen gefe an ajiye su, ruwan aka kawo inda sarki k'uru yae bayani akan yanason ya cikawa 'yarshi Lawuri burinta, ta shayar da ruwan ga mugun da kanta, take agun aka yarda da hakan manyan garin sukace shine daidai hakan.


Kallonsa takeyi sosai amma shi sam yaqi ya had'a idanshi da nata, a yanayin data kula dashi ma kaman tsorace yake, batajin fad'uwar gaba, kazalika batajin wannan idan daya gagara had'a ido da ita mamallakin gangar jikin ne ya gagara had'a idanshi da nata, mesa takejin daban? Ya akayi takeji cewan ba wannan bame makashin zakin? Idan hakane kenan sanjiya sukai? Kenan so suke su juyar musu dakai, tajima tana tsaye amma kanshi a k'asa duk yanda taso ya d'ago ya kalleta amma abun yaci tura, waigawa tae ta kalli Babbar yarinyarta hadimarta me suna Linta tace


"Kicewa aakam ya kawo d'ayan yaron me kamada wannan" sunkuyawa tae ta amsa sannan ta juya cikin sassarfa, bata dawo ba se tare da Abu Hurairah jerasu akai gu d'aya tabisu da ido bata ko k'iftawa, kafeta da ido shina Abu Hurairah yae cikeda tsana, kallo d'aya ta masa tagano Abu sufyan bashi bane ainahin me kisan Lamme, bashi bane me sanya zuciyarta na harbawa so dubu saba'in acikin daqiqa d'aya ba, idan hakane mezai faru idan da an baiwa wannan ruwan? Amma ita sam bazata iya tonawa wannan me kallon nacin asiri ba, bazata iya furtawa da bakinta tace shi bane ba wannan me kamadashi ba


"Ku mayar dashi" shine abinda ta furta jikinta ba k'wari cikin murya me tsananin rauni, batasan wane kalan tsafi yae akanta ba, wannan waiko aljanai ne? Ta tambayi kanta, da kanta tayi tsaye seda taga yasha ruwan adadin yawan da ake buk'ata tana mamakin wace kalma ce yake furtawa kafin yasha ruwan menene yake furtawa haka?.....


Ihu suka hau yi ganin yagama shanye adadin copunan da akeso yasha, jira kurun suke suga macewar shi, amma shiru shiru har akafi tsawon mintuna talatin!! Ganin hakanya sanya barade soma dukanshi kaman ba gobe da manya manyan itatuwa, tun yana iya kaiwa kanshi kariya da hannunshi harya galabaita ya durqushe, Dawud da Abu Huraira se ihu suke suna k'ok'arin k'wacewa amma an rirriqesu, duka aka masa bana wasa ba, harseda ya dena numfashi, haka suka d'aukesi akan wani abu me kaman dogon baro amma wannan shanaye suke turawa sukai ta zaga garin dashi daga k'arshe sukai bayan gari dashi.


************
Duk yanda Dawud yaso ya basu hak'uri akan su basu koda gawar Sufyan ce abin yaci tura, acewar su sun jefar dashi ma acikin jejin da naman jeji ze cinyeshi, kuma ma tunda yasha wannan ruwan narkewa zeyi.


Abu huraira kuka wannan ma ya gagareshi, idanshi ya weqashe duk shi ya janyowa d'an uwanshi mutuwa,daya sani dashi yaje yasha, duk sa'in daya tuna da yanayin dukan da akamai akanshi seyaji hankalin shi ya tashi, yana jiyo amon sautin muryarshi yana furta
"Huraira ka taimakeni, huraira zasu kasheni" runtse idanshi yae sosai ya k'udurta aranshi seya nemo d'an uwanshi, jikinshi be bashi cewan ya mutu ba kuma a wannan daren ze fita.
********
Littafina na kud'ine kada ka karantamun idan har baka biya ba, idan ka karanta kuma tam. Me buqatar siya ya tuntub'i wannan lambar 07084161619


**********
Dare yana rabawa kuwa Huraira beko tashi Dawud ba ya bige bukar dasuke ciki ya fito, yayi sa'ar babu wanda ya ganshi ya lallab'a yabi sawun d'an uwanshi dukda yake besan inane aka kaishi ba takamaimai........ Acikin duhuwar daren yake haska fitilar k'aramar wayarshi dake daf da d'aukewa duka sabida rashin cajin ta, tafiya sad'af sad'af cikin tsoro yana me fatan had'uwa da d'an uwan sa koda amacene kuwa, baze so yayi mutuwar wulak'anci hakaba, ko kad'an! Motsin dayaji ne ya bashi dama tsayawa k'yam ya waigo domin ganin ko miye, abinda ya haskane ya firgitar dashi ya kusan suma awurin..


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*Littafina na kud'ine idan ka karanta baka biya ba kuma tam.meson ya siya ya tuntub'i wannan lambar 07084161619.*


07


Sauke abinda ke kanshi yae yace


"Karka tsorata Hurairah Dawud ne, dama ina bayanka, na rufe fuskatane na sace kayan jikin d'aya daga cikin masu gadin mu, shiyasa kamun nisa ma, naga suma haka suke yawon dare da ganye akai shine na d'ora" Ajiyan zuciya me nauyi sosai Abu Huraira ya sauke yace


"Kayi hakuri Dawud, banda nutsuwar zama acen nabar d'an uwana a uk'uba koda hakan ce sun kasheshi gwara amai salla Dawud, basusan darajar mutane ba" Rik'o hannunsa Dawud yae


"Kashe fitilan wayar nan muyi adu'a kar wani ya hango haske, mutafi inaga nanne hanyan bayan gari, sabida nan sukace sun kaishi sun wurgar kuma akwai naman jeji inaga fa" shiru yae baya ya kashe suka rik'e hannun juna sannan sukai gaba cikin sand'a, seda sukaji sun dena yawo ajikin bishiyoyin sannan suka kunna fitilar wayar su, lokacin har gari ya soma wayewa, sunyi nisa sosai harsun k'araso wurin ruwan suka hangoshi yashe ko motsi bayayi, da sauri sukai kanshi, d'an uwanshi ya tallafo kanshi sosai ya d'aura asaman cinyar sa yana zubar da k'walla, ganin yanda duk kanshi ya kukkunbura harma da jikin sa sabida azabar duka, kwantar da kanshi yae jikin k'irjinsa yaji yana zuciyar sa na bugawa amma cen maqale, hannunsa ya d'aga ya rik'e ta wutsiyar da kan yatsunsa yaji purse nashi ma ba laifi sedai a hankali sosai komai yayi law sosai


"Dawud yanada ranshi duba mana jirgi mubar nan gun dashi kawai" D'aga kai Dawud yae amma ba alamar jigin k'asa ko d'aya, wannan alamace ta cewar wancen jirgin ma da sani aka turashi gun hanyar ba wacce ake yawan bi bace ba, kai ba'a ma bi ruwan yayi yawan da bazasu iya tsallakawa ta hanyar aiki da jikin suba


"Abu Huraira babu jirgi anan, sedai da ace a farke yake zamu iya amfani da manyan icen cen kowa ya rik'e d'aya mubar nan jejin tun muna shaida juna" ruwa ya ebo a hannunsa ya wankewa Sufyan Fuska dashi, seda yae kusan so uku sannan ya farfad'o sedai ba k'arfi, suka tashesa a zaune yana buqatar ruwa ba abin shansu, haka suka dinga ebowa da hannu suna bashi harya k'oshi, Shiru sukayi dan sunga garin ya soma washewa sosai, tabbas kuwa se anbi bayansu, dan zuwa yanzu dole ansan basa nan


"Ka bari na sanya Al-hasan a bayana mu tafi, biyo sahu zasuyi kuma tabbas sesun tarar sun fimu sanin hanya" Tashi tsaye sukayi ya sanya Abu Sufyan a bayan shi suka kama hanya cikin sassafarwa, agefen ruwan dabasuda tabbacin zasuga k'arshen sa. Basufi 30mns suna tafiya ba aka zageyesu, cikin takaici Abu Huraira ya k'walla k'ara ya sauke Abu sufyan a k'asa yabi k'artin da kallo, matsowa Lawuri tae sosai suka had'a ido da Abu Huraira kallon dayake mata kawai ya isa ya nuna tsantsar tsanar dayake mata a k'wayar idansa, hannunta takai ta rik'e masa hannu, yanayin rik'on datamai bega alamar na fad'a bane wanan ya sanya yae sororo yana kallonta, jira yake kurun yaga me take nufi da wannan salon iskancin kuma, Abu sufyan ta nuna da yatsanta tace


"Ku bashi yasha" Da sauri gardawan sukai kanshi suka tashshi zaune suka d'ago kanshi suna shirin qyanqyama mai ruwan, kallon Dawud tae tace


"Dashine ya kashe lamme (zaki) da tuni ya mutu, nasan wannan ne me hanani nutsuwa ya kashe sa, shisa na kawo masa magani inba hakaba shima dafin ruwan a hankali a hankali ze zagaye jikinsa harya mutu" kallon Abu Huraira yae cikin sauri yace


"Barshi yasha Abu Hurairah magani ne, ta gano bashi bane ya kashe wancen zakin kaine" bece komai ba se kallon cikin k'wayar idanta dayakeyi, Abu sufyan yana shaye ruwan ya singa aman jini ya jima sosai yanayi kafin ya tsagaita, ruwa tasa aka bashi yasha sekuma gashi ya mik'e asaman k'afafuwanshi, kallon muk'arabanta tae maza da mata, babu wanda yasan tafito tasan bayanta zasu biyu musamman dayake baqi ma sun gudu, koda yake seda ta sumar da masu gadin su, hannun Abu huraira taja


"Kujagirancemu mu rakasu hanyar barin gari me sauki, wacce muke bi da sarki" Zaro ido wani daga cikin su yae kanshi a k'asa ya soma bata hakuri akan ta dubawa Danginta da mahaifinta tabar biyu su tafi amma d'ayan na sacrifice a barshi ya koma" kallonsa tae tace


"Naji muje semu dawo da d'ayan, ainima bazanyi hakan ba" haka suka kama hanya cikin sauri harsu har ita, koda yake duka ya lankwashe Sufyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login