Showing 27001 words to 30000 words out of 35867 words

Chapter 10 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt

29 Jan 2025

1674

na Baban ka kuma?" Cikin raha yace


"Auu hakane yarenki mom sorry, ni inaso su shiga hasken musulunci wlhy, gashi narigada na had'a alk'awarin aure da Cyama dabadan hakan ba daba abinda ze hanani aurarta in musuluntar da ita" kallon mamaki tae masa


"Amma wasa kake ko? Ina haukane dazan barka ka auri er jeji, beside kai waye dazaka b'ata mu'amalan gidan nan dana gidan General? Cyama duk halaccin datama?" Sadda kanshi yae a k'asa cikin damuwa


"Mom nifa bance haka bafa, nace daze yiyu kawai ko?" Harara ta wurga masa


"To baze yiyu ba kaji na gayan maka, har abada wlhy, kamazo da salon raini" bece komai yasan halin mom, akan Cyama seya nemi d'aga masa hankalinsa gwara yae shiru kurun.


************
Yau tun 12:noon ya tashi daga office, beko lek'a ofishin Cyama ba ya wuce kanshi tsaye gidansu, yasan yanzu har mom tana gun aiki bakowa agidan nasu, A parlor gidan ya zauna sunata kwasar hira shida Lawuri, taji dad'in ganinsa har take masa bayanin Abu Huraira ya kaita wurin koyon hausa, kuma tana ganewa sosai ba kad'an ba, dan yanzu hartasan gaisuwa ma da wasu abubuwan yaren ba wahala sedai rubutu ne bata iyaba ko kad'an, anan take gaya mai rayuwar su akwai dad'i ba'a wahala kaman su, itafa noma take dukda zamanta 'yar sarki amma anan bataga gona bama, to ina suke samo abinci da nama, tunda bataga suna fita farauta ba" Dariya sosai yae har yana rik'e ciki, nan take ya mata bayanin komai dangane da rayuwar birni an dad'e sosai da barin wannan yamayi mamaki da ace duk wayewa bata kai musu ba har yanzu, aranshi yace watak'il hakan baya rasa nasaba da tsafin su waze iya zuwa garin... Sunsha hira sosai se raha suke


Da sallama Cyama ta shigo gidan tayi mamakin ganin Dawood da Lawuri a parlor suna hira da dariya haka har basusan da zuwan taba, matsawa tae kusa dasu tace


"D inata sallama fa" yanayin zaburar dayae kurun ya isa ya nuna mata cewan tabbas bashida gaskia, tasha mamakin wannan abin lokaci d'aya ya soma kallon agogon hannunsa, agogon dake manne a bangon parlor ta kalla cikin mamaki itama k'arfe biyu ta kwata ta mayar da dubanta zuwa gareshi


"D lafiya dai? Ko bakai tsammanin ganina yanzu bane ba" wayancewa yae


"Damafa ke nake jira, nayi mamakin yanda lokaci yae saurin gudu ne har haka" Rausayar da kanta tae


"Amma shine kuma bakaje guna ba office, bayan secretary naka ya sanar dani tun 12:noon kabar office" sosa kanshi yae


"Gida nakeso na ganki shisa nazo, aikin jaridancin zaki faramun ko?" Shiru tae ta harari Lawuri,taga alamar yarinyar nan seta mata saiti tukunna, D betab'a zuwa office beshiga sun gaisaba, shisa ma idan taga ya wuce time daya saba zuwa be zoba takan je da kanta dukda babu tsarin hakan akanta


"Sannu de zuwa anty Cya" harararta tae


"Yauwa sannu Laure" ta fad'a dan wancen sunan sun soma dena ambatar sa baso suke ba" Mik'ewa yae


"Zanje nae sallah time ya tafi" da mamaki ta kalleshi


"Auu sallan azahar ne kuma D bakai ba ka zauna wannan arniyar tana maka tatsuniyar gizo, har biyu ta gota" B'ata fuska yae sosai


"Meye haka Cyama? Yaya zaki kalli mutum agabansa kice dashi arne? Daidaine hakan kike gani?"


"To k'arya nai ita ba arniyar bace? Ko tana sallan ne? Idan da tanayi aida bazata zaunar dakai ba ayi sallah tun fin awa kana zaune" Shiru yae ya tsaya yana kallonta hartaja tsaki tae sama cikin fushi, girgiza kanshi yae yace da Lawuri zeje masallaci, itama saman ta haura gun Cyama, har k'asa ta tsuguna cikin fuskan tausayi tace


"Anty Hakuri" Batako kalleta ba, wani azababben kishi takeji game da yarinyar ance bayarbiya ce yada kyau haka? Sewani haske take k'arayi, ko shakka babu seta rabata da gidansu da rayuwarsu gaba d'aya, take taken Dawood nuna mata yake cewan son yarinyar yake tun kwanakin baya ta kula da hakan, ta tsani yarinyar, tunda take dashi yace rana ta farko dayaje office harya fita be nemesu ba, a k'ark'ashin company d'in dad yake aiki yanxu itama kuma acen take.


Da hannu ta mata alama akan ta tashi ta bata wuri haka ta mik'e jiki ba k'wari, ko shakka batayi tasan fad'a sukeyi kuma akanta ne, tarasa wannan mugun bak'in jinin dake bibiyar ta, tanason tasan ma'anar kalmar Arniya! So tari idan ana magana da fad'a akanta takanji ana yawan ambatarta da wannan kalmar, me wannan kalmar take nufi? Dama yau zataje gun d'aukar karatu da yamma seta tambayi Anty Risi akan hakan......


*Se mun had'u a shafin yamma inshaa Allah*


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*please book nawa na siyarwa ne, idan kinaso ki karanta ki biya kud'in ki a sakaki a group, 07084161619*


15


K'uru zirga zirga yakeyi cikin tsananin tashin hankali, duk tsafin daya dace ya sanya ayi ya saka anyi amma har yanzun Lawurin sa bata dawo gida ba, anje garin kusa dasu ma amma shiru kakeji, tunda yae sa'a wani acikin bayinsa ya tsallaka ruwa ya samu sacrifice yake cikin murna sedai tashin hankalin rashin Lawuri, dole seya nemota amma besan akwai wata duniya ba bayan tasu data mutanen dake tsallako ruwa suzo, mutanen daya gani da wannan abun kashe mutum abun ya tsorata shi, ga K'uruwa ma ta dena cin abinci kullum zancen kenan Lawuri.


"So nakeyi aje nemanta har waccen duniyar dabansan ya ake zuwa ba, ina buk'atar yarinyar nan ta dawo ko anaso ko ba'aso" Kallonsa Barden garin yar


"Zamuje mu nemota, koda xamu mutu ne K'uru sarkin adalci ka kwanta kayi bacci dole zata dawo" haka suka shirya sunkai su 20 aka soma nausar jeji.


*************


Rik'e take da book a hannunta ta k'urawa rubutun ido kurun amma sam bata gane komai, bazata iya rubutu ba ko karatu tasani har abada amma hausar dai tanaso ta koya, so take ta iya yaren Aboo Wurairai (In Lawuri's voice), ta rik'ayin hira dashi kafin ta koma garin su, kife littafin tae ta mik'e zuwa cikin gidan sabida tanaso tasha ruwa, zuwa yanzu tasoma sabawa da d'and'anon ruwansu me sanyaya zuciya, kai tsaye ciki tashiga bayan tayi sallama ba kowa a parlor d'in, kitchen ta wuce ta bud'a fridge ta d'akko robar ruwa d'aya ta shiga dudduba kofi, sedaga cen ta samu tana fitowa sukai karo da Hanifer cup d'in ya sub'uce mata dama na glass ne lokaci d'aya ya tarwatse, cikin tsoro taja da baya bata tab'a tsammanin abun yana tarwatsewa har haka ba


"Hanty Anny hakuri kinji?" Ta furta muryanta yana rawa, tsaki hanifer tae


"Dama mana Arniyar jeji, yaya zaki yi abu cikin nutsuwa wama ya baki damar d'akko cup na daddy kizo harki fasa? Wlhy yau keda mommy ne, zuwa zan na fad'a mata abinda kikayi idan akwai wanda kika tab'a ganin ya d'akko cup d'in daddy yana amfani dashi" ta gano masifar takeyi dukda bajin me takecewa duka take ba,jin ta ambaci momy ma ya k'ara firgitar da ita tasani kashinta ya bushe, kuka ta hauyi tana rok'onta amma da gudu ta juya saman, segata sun dawo tare da mom har lokacin kuwa Lawuri tana nan tsaye tana sharar k'walla, salati mom ta hauyi tana tafa hannu


"Hanifer d'akkomun dorinan danake zane su Nu'aiym shida Khabbab kizo ki sameni a garden tare da ita zakizo" haka Ta wuce garden Hanifer kuwa ta wuce saman ta d'akko dorina ta kuma zo taja hannun Lawuri garin tsallakawa qatoton glass ya cake ta, k'ara ta kwalla yayinda hanifer ta tizgeta zuwa garden d'in cikeda fushi, d'ingishi ta somayi tana kuka amma ko kallonta hanifer batayi ba taci gaba da janta har garden, mom zama tae akan kujera hanifer ma haka


"Hanifer tashi ki nuna mata yanda zatayi kneeldown" mik'ewa tae tayi kneel down agabanta tana nuna mata da hannu akan itama tayi, ba musu tayi harda d'age hannayenta sama yanda hanny tae, tana ganin tayi ta mike itama ta mik'e wanka mata mari hanny tae


"Danla ki koma wayace ki mik'e?" Bata gane abinda take nufi ba ga glass a qafanta se kuka take tana ambatar kalmar ki Akuri da k'yar, duka sosai mom ta mata da dorina ta kira Dawood a waya


"Ga wannan mejin yarbancin Arniyar yarinyar dakuka kawomun agida na, ka sanar mata glass cup data d'auka tasha ruwa harta fasa na daddy ne nxt time idan taga abu ta rink'a bincikawa danni ba lamuni zan mata ba" tana kaiwa nan ta kara wayar a kunnen Lawuri daga cen yayi Lawurin bayani akan shine ga abinda akace tayi ta rik'a kiyaye, tana kuka ta ansashi da ta dena zata nasu hak'uri amma a mayar da ita garin su


"Zamuyi magana idan nazo Lawuri kinji, yanzu kiyi hak'uri" godiya ta masa sannan suka karb'i wayar dukai hanyar ciki ita duka barta nan


"Allah Hanifer banajin dad'in yanda nakewa yarinyar nan, kurun dai na tsane ta ne so nake wuya tasa tabar gidan ba komai ba" jinjina kai hanifer tae


"To mom harga Allah aibaki da laifi, tunda laifi tae kika hukuntata" Jinjina kai mom tae alamar gamsu kafin tace


"Amma naga kaman Glass yashiga k'afanta kidubata da kanki" Jinjina kai Hanifer tae


"To mom zan duba ta inshaa Allah" Barbo ce ta tattare kwalban ita kuwa hanifer tunda ta shiga hidimar girkin daza'aci na dare bata k'ara tunawa da wata Lawuri ba...


**************
Tunda ta sanya kiran wayansa agaba be d'aga ba take cikin yamutsi, ta cab'a ado iya ado sedai babu walwalar zuci, mesa ne ita Pure heart yake mata haka? Meta masa ina laifin masoyinka? Shirin zuwa gun k'awarta tafito da amma se kurun ta karkata akalar motarta zuwa Tile making company nasu ta tabbatar yana cen yanzu.


Kai tsaye office nashi ta nufa, akai mata iso ta shiga, fuskar nan babu walwala ya tarbeta


"Me kika zo kimun anan?" Kallon sa tae har idanta sun sauya sunyi ja


"Meye laifi na sufyan? Mena maka hakane wai? Na dinga kiranka kenan a waya baka d'agawa? Sannan kuma baka kirana, baka zuwa inda nake ni idan nazo seya zama laifi? Yaya kakeso nayi da rayuwata ne wai?" Hannunshi ya ssanya ya shafi sumar kansa


"Na sanar dake ai banaso kike yawaita kirana a waya ko? Nakuma sanar dake ba girmanki bane ba ace kina kawomun ziyara da kanki" cikin damuwa ta furta


"Amma idan nakira baka d'auka bafa? Kokuma idan na kira baka kirani back ba fa? Idan inaso na ganka amma bakazo bafa ya zanyi ehm Abu sufyan?" Ta k'arashe maganar cikin tausayawa kanta har tana zubar da hawaye, tausayi sosai ta bashi ya tashi daga kan kujerar da take yazo ya zauna kujerar dake fuskantar nata, cikin sanyin murya yace


"Kiyi hakuri my Ayusher kinji? Ni abunda banaso missd col ya wuce 1, idan da kin kira so d'aya ban d'aukaba idan kika jirani zan kiraki back ne, zancen ziyara kuma naji, yanzu so nawa kikeso ki ganni a sati?" Share hawayen ta tae


"Nagode sosai pure heart ni idan da wannan kalaman masu dad'i kurin ka barni zan gode maka" Murmushi yae


"Gayamun mana so nawa kikeso ki ganni a sati?"


"Niko sa d'aya ne ma kaji" murmushi yae


"Nacire kwana uku kacal a sati, zaki ganni so 4, inshaa Allah muddin ina garin nan, kira waya kuma zanna riqa kiranki kullum safe da dare wannan fa ta miki?" Ya k'arashe maganar cikin sakin fuska sosai


"Nagode pure heart" murmushi yae


"Da driver kikazo?"


"Da kaina nazo" mik'ewa yae


"Muje gidan mom nayi wanka semuje yawon yamma" murmushi tae itama ta mik'e


"Zaka sanya mom tace bana zuwar mata se idan kai ka kawoni ko" mirmushi yae


"Idan bazakiba sena tafi abuna" Rike baki tai tana murmushi


"Nina isa nace bazani ba? Aiban isaba ko pure heart?" Murmushi yae suka fita.


Aqilu ya wurgawa key na motar Ayusher ya cafe yace


"Ka kai motar gidan Su Ayusher ka baiwa gate man na gidan kace injita ya ajiye agunsa harta dawo" cikin girmamawa yace


"To yallab'ai" Takardar dubu d'aya ya zaro ya mik'a masa


"Kayi tranport zuwa gida daga nan" nanma godiya yae ya juya.


**********
A b'angaren Lawuri kuwa yau duk kuka ta wuni yi, ta samu Barbo ta cire mata glass d'in amma sun duba a garden d'in babu wani ganye daze iya tsayar da jinin da k'afar keyi,wajen gidan Barbo taje ta duba ko akwai ganyaye irin na garinsu....... Zaman dirshan tae a bakin gate d'in tana jiran isowar Barbo sabida yanda jinin ke zuba, ga yau banda masu gadin gidan duka sojojin sun kama gabansu,Shigowar barbo yayi daidai da dosowar motar Abu sufyan gidan, parking yae ya fito daga motar ya bita da kallon mamaki kafin ya k'ara wurinta cikin azama, durqusawa yae ya tallafi k'afar ba laifi tasha faso da kirci na rayuwar jeji


"Meya samu k'afar haka ne?" Amaimakon ta bashi ansa se kurun ta shiga rera masa kuka wiwi..... Nuni ya mata da hannu alamun ta mik'e a hankali ta tashi ta doma d'ingisawa tabi bayanshi zuwa ciki, Hanifer ya soma k'wallawa kira yama manta da wata Ayusher dasuka zo tare, da sauri ta sakko daga saman


"Zoki treating wound na yarinyar nan, bansan meya same taba" tab'e baki tae


"Yaa sufyan kofin dad ta d'akko na shan ruwa, shine kuma ta fasa shi garin gidadanci ta taka glass nisam nama manta mom tace na duba mata gun" Haukace mata yae da masifa, ita kuwa Ayusher tayi sororo tana jiyo su, haka ya dinga masifa har sanda ta shiga taitayinta, ya haura saman mom itama


"Mom yanzu daidai ne dan Allah, yarin yarnan fa mom mutum ce fa? Amma ace kun barta da miki haka tun safe kuma akan glass cup ace hadda duka, Hanny ta gayamun kin dake ta kuma nima na gani duk jikinta ya fashe" Mik'e wa tae daga zaman datake


"To ubana seka daken ai, nace seka daken, ni yanzu Sufyan ni kakewa magana irin haka acen wancen banzar, yaushe ta juyar mun da kanka har haka? Yaushe ma kai ka isa ka gayamun abinda ya dace ya wanda be dace ba?" Saukar da kanshi yae k'asa


"Mom kiyi hakuri kurun naga an qyale tane acikin jini tun safe shiyasa" tsaki taja tafice daga d'akin gaba daya.


Seda aka bata anti tetanus sannan akae dressing na gun se kuka take, lokacin ne barbo ta tallafeta zuwa d'akin su.


Sun baiwa Ayusher tausayi sosai bako na wasa ba, bataso taga ana cutar da mutane ita kam,amma haka ta gaisa da mutane gidan ta zauna a darare har ya kimtsa suka fita, fitar ba dadi sabida fuskar babu wata walwala haka suka yishi.


*********
Ana sallan isha Lawuri da Barbo suka sakko daga saman, sa'an dasukaci ba kowa ya basu daman zarcewa har gate, me gadin sun sansu dan haka babu wanda ya hanasu fita haka suka fice da zummar suda gidan har abada, Lawuri gida takeso taje dan haka ta nemi hanyar datafi mata sauk'i kawai, ta kula wannan mutanen kasheta zasuyi idan tayi wasa.....


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*Littafina na siyarwane, idan kinaso ki siya, karki karanta idan baki biyaba 07084161619*


16


Tunda suka fito duk titin dazasu tsallaka sesunji jiki, sunsha bak'ar wahala kafin subar unguwar ma, tafiya dukayi ta kusan sa'o'i uku, sun jigata sosai, ga ciwon dake k'afar Lawuri, yanxu kam so suke su tsallaka babban titi sui ta kansu amma sunfi 30mns agun suna k'ok'arin tsallakar titin sedai kuma basu iyaba, sesunkai tsakiyar titin se kuma su dawo da gudun fanfalak'i, a garin hakan ne mota ta musu d'ebar karan mahaukaciya taje ta watsar gefen titi, matashiyar budurwa ma mallakiyar motar tayi azamab fitowa da saurinta bayan tayi parking inda ya dace tayi, Takalminta me d'an uban tudu tana tafiya cikeda yanga, bazaka ita cewa ga kalar taba ka kad'e mutane har biyu kuma kana tafiyar son rai? Sedai kumafa kallo d'aya zaka mata ka tabbatar tashiga tashin hankali, a rud'e take sosai, ga alama iyakar saurin ta kenan a yanayin tafiyar ta, mutamen dabasu suka kad'e sunba har sun rigata isa gunsu, itama cikin azama ta k'arasa yanxu kam, abinda ta gani ya matuk'ar rikitar da ita sabida d'ayar gabaki d'aya fuskarta jinine ga k'afa ma haka she's unconscious ma, d'ayar ce ke ihu tana magana cikin yaren daba kowa ke ganewa ba, dafe goshi tae lokaci d'aya wani ya taimaka mata aka sanya daya a motarsa daya a motar ta duka lula asibiti mafi kusa dasu.


Lawuri tafi Barbo shan azaban dan ita batako san wake kanta ba, Barbo kuwa ta k'arye a k'afa, ita Lawuri ba'a san iyakan ciwukan datajiba har yanzu, matashiyar budurwar data kad'esu se kuka take tana mamakin sanda sukazo gabanta batai auneba, kamar aljanu? Gidansu ta kira waya lokaci d'aya asibitin ta cika fam da mutanen gidansu.


***********
Hanifer ta kula yaran basa d'akin su da dare amma tana mamakin ina sukaje? Taso ta ankarar da mutan gidan amma setayi tunanin suna garden, tunda k'auyawane ko tsakiyar dare saje garden ai, wannan ya sanya tana kammala ayyukanta tae shirin kwanciya, tana sakaran ta koma gidansu ma nanda 2days.......Cyama ma tayi mamakin rashin ganinsu amma hakan be sanya ta wani damuba dan itama tunani d'aya tae suna garden suna hira cox haka sukeyi dukda basu saba kai dare ba, da wannan ta watsar da tunaninsu tae shirin kwanciya abunta kamar yadda Hanny tae.


***********
Duk mutan gidan sun hallara dining kasancewar General ya dawo, k'a'idane idan yana gari ko bakaso se dole ka fito cin abincin safe a dining dake babban parlor na gidan, sun shirya sosai abinci kala kala, ita kamma mom bata ko damu da rashin suba tama manta dasu, seda aka nutsu ana cin abincin kowa yayi tsit sannan General ya kalli Adama


"Ina bak'in gidan ne ko kunya suke?" D'ago idanta tae ta kalleshi had'e da tab'e baki


"Oho, ni yau duk ban gansu ba" Cyama ce tace


"Dad jiya da dare ma basu zo d'aki da wuri ba, nazata ko suna garden sabida cenne gun zamansu shisa banyi magana ba har bacci ya kwasheni, yanzu mun wayi gari basa d'akin na tambayi hanifer ma tace bata gansu ba" Duka ya kaiwa table d'in da k'arfi


"What?!!!! Kuna haukane shine bazaku sanar da wuri ba? Bama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login