Showing 3001 words to 6000 words out of 35867 words
Chapter 2 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt
matuk'ar jin dad'i ina kuma yabawa sosai akan hakan, sedai ku k'ara, kuma ku rik'e adu'a ku yawaita yin adu'a, musamman idan zaku fita da kuma duk wani abun k'i daya tinkaro ku kubishi da ambaton Lillahi inshaa Allahu zakuga haske komai yawan duhun daya taso muku, kuci gaba dason juna tafiya ce ta sati d'aya nake ga, dukda koni a raina banson tafiyar amma babu yanda zamuyi, awurin Allah sati ai kaman yau ne zakuga kun dawo, fatan kuje ku kuma dawo lafiya" A tare suka had'a bakinsu wurin cewa
"Mungode sosai Mom, Allah ya saka da alkhairi, kuma inshaa Allahu zamu kiyaye" Dafa kan Abu hurairah tayi ta masa adu'a sannan ta sake ta dafa kan Abu sufyan ta masa sannan sukai mata sallama suka fita" A waje suka tadda general ya murtuke fuskar nan tamkar be tab'a dariya ba, k'arisawa Abu sufyan yae kusa dashi yace
"Dad yanzu zamu tafi" kallonshi yae kanya kai kallonshi zuwaga zoben hannunshi sabida yanaso ya gano ko waye, shi kanshi idan bada zoben nan ba to baya tab'a banbantasu, shisa tun suna yara suna k'ara girma yana sanyawa ana musu zobuna masu sunayensu d'aya me d'igon bak'i d'aya kuma me d'igon fari, agogon hannunsu kuwa sune dan kansu suke sakawa sabida abokanan su da sauran mutane
"Abu sufyan?, kun fito kenan ina Baba ladin?" Sadda kanshi yae a k'asa
"Tanawa mom sallama ne, yanzunnan zata fito" Jinjina kanshi yae
"Zaku d'auki *DOGUWAR HANYA* k'auyen kuma babu gari irin haka akusa dashi sam se jeji tako ina, shekarun bayan nida kaina na kaita amma ita da kanta ta dawo, nasan yanda hanyar take seku dinga adu'a akoda yaushe" godiya dukkansu sukayi sannan suka juya wa kotocin Abu Huraira shine ya zauna gefen direba se Abokinsa Dawud dayace seya bisu yawo, se Abu sufyan daya zauna abaya sekuma Baba ladi a gefenshi motace suka d'auka k'irar hilux fara qal sabida yanayin hanyar, da adu'a d'auke a bakunan su suka hau *Doguwar Hanyar* se d'aga musu hannu Cyama keyi yarinyar dake tsananin kamanni dasu, agidan nasu bazaka iya cewa game kama daban ba kowama kama yake da d'an uwansa Baran ma hasan da Usaini (Abu sufyan da Abu Huraira) suda bakama iya banbancesu aduk duniya mahaifiyarsu ce kurin kallo d'aya take gane waye wannan acikin su.
*************
Yanayin shirun da motar ta d'auka kurun zaka kalla ka gano babu mejin dad'in tafiyar, jefi jefi Baba Ladi kan wurgo zance dayike ita macece me tsananin son raha kuma Abu sufyan shine yake yawan biye mata wannan dalilin ke sanya tana saurin ganesu itakam kota hanyar gaisuwar suma, ga mamakkinta yau koshi tsit yake sedai idan tayi maganar ze bata amsa cikin sakin Fuska, haka suka naushi hanyar har suka isa babban garin, Tsayawa Abu Huraira yae lokacin k'arfe sha biyu ta gota yaceda sauran
"Abu Mage bana tunanin zamu iya nausar hanyar garin nan a wannan daren, so kawai inaga mu nemi k'aramin hotel mu kwana gobe muje mu kaita da asuba haka semu dawo kaga man motar ma yaje down baze mana kyau ba mu naushi jeji a haka gaskia" Murmushi yae jin sunan daya kirashi dashi yace
"Abu takobi zancen ka dutse ne, hakan shine shawara me kyau, yanzu wane hotel zamu sauka?" Kallon agogon hannunsa ya qarayi kan ya yamutsa fuska
"Bawani sanin garin mukayi ba, inaga mu tambaya semuje takusa sosai,inyaso ma mu ajiye kayanmu anan mu semu tafi muna dawowa munsan inda muka sauka"
Da tambaya suka isa wani hotel me kyau da tsari, ya had'u ainun, d'aki me suit suka kama susu uku se Baba ladi da suka kamawa k'aramin d'aki ita kad'ai, sun siya kayan abinci suka k'araci sannan sukayi sallan isha suka hau hirar duniya sosai da sosai se dariyarsu kakeji a wannan daren kam sun rabashine suna hirarrakin duniya.
*Washe gari*
K'arfe bakwai na safe suka fito, inda suka tarar Baba azumi harta rigasu bakin motar, sunyi breakfast awurin inda suka biya wani wurin suka kwashi kayan snacks musamman cake dai suna sanshi sosai babba d'aya suka siya da qananu se donuts da sauransu, Baba Ladi kam har bread tasa aka siya mata kusan k'waya 4 da kayan shayi akan idan taje tariqa yin kalacin safe, komai sun tanadarwa kansu, daidai da ruwa sun nemi carton na faro me 24 aciki, drink ma haka, daga nan gidan mai suka nufa sukayi wa motarsu full tank, hadda siyan wani a jarka, dukda kuwa Abu sufyan yana ganin had'arin d'aukar fetur a hanyan dabasu san yama take ba, haka Abu huraira yace dashi basusan nisan wurin ba, ya tsani short na mai a mota, kuma sun samu anwa jarkar d'aurin kazar kuku an d'aure sosai, beside bama boot bane ba irin haka ai a bud'e bayan yake kayan Babane kurun da en tsarabe tsarabenta se suka rufe da k'yalle sabida k'ura....da adu'o'in tsari d'auke abakunansu suka d'auki hanyar k'auyen na b'ingirau dake cikin jeji me nisan gaske.
************
Sosai suka gajiya da nisan hanyar dasukebi, gashi dai garin maman ba cikin wannan nahiyar ba, ace tafiya tun bakwai na safe sukeyi har yanzu k'arfe biyu da rabi ta gota, sukam yaushe suka ajiyeta har suka juyo zuwa masauki, Tsaki kuwa Abu sufyan yayi yafi so hamsin, har ita Baba ladi da kanta ta kula da k'osawar da yae, ita da kanta taso General ya barta ta hau motan kasuwa amma ya kafe, sassanyan ajiyan zuciya ta sauke ganin sunzo hanyar dazasu yanki jejin daze sadasu da K'auyen na B'ingirau, da hannu ta nuna musu suka kuma karkata akalar motarsu zwaga wannan b'angaren Abu huraira ya juye baki da harshen turanci yace da Abu sufyan
"Abu Takobi kaga wannan jejin kuwa, kasan wai jikina ya soma mutuwa, a gaskiya dazaran mun ajiyeta mu juyo sabida ina jiye mana yin dare a wannan muguwar hanyar" Kawar da kanshi yae gefe d'aya ya kaiwa agogon hannunshi kallo
"Dama munsan hakane aida yaseen a motan haya zamu d'urota, yanzu fa uku saura mintuna biyar kacal, dama mun juyo ne mu soma timing amma wannan masifar har ina?" Dawud ne ya karb'e zancen da cewa
"Ba masifa bane ba kadena kira mana ita, idn dai kan wannan hanyar ne ai inaga zamu juyo dare be mana ba" shiru dukkansu sukai, zuwa hud'u saura kwata sun k'arisa garin, mafiya yawancin mazauna garin fulani ne kamar Baba ladi, harkokin su suke gudanarwa cikeda aminci, sun gaggaisa da mutane kansu tsaye suka nemi yin salla azahar da la'asar kansu ce zasu koma, duk yanda akaso suci abinci sun gagara tsayawa se wuraren biyar da rabi ma sukai shirun tahowa duk saurin dasukayi...wani mutum ne me tsananin kamanni da Baba ladi yazo ya kalli Abu sufyan daya karb'i tuk'in motar ganin kamar Abu mage ya gaji yace dashi
"Yaro dazaku bi shawarata dakun hak'ura da tafiyar nan zuwa asubahi, komu damuke da garin nan bama yi masa fitar yamma, koba komai kuna baqi seku saki hanya ai" kallon Abu Sufyan yae cikeda takaici yace
"Kamana adu'a lafiya lau zamu fita mun gama haddace hanyar inshaa Allah" jinjina kanshi yae alamun gamsuwa yace
"Idan kuka miqi hanya zuwa gabashin nan, karku neki ko washe hanya sheta kudu, kunayin kudu kuka raba jejin masarau biyu seku yamma kuyi arewa se titi kuma, kushkure d'aya jal je sanya ku shaki hanya, kuma shakin hanya a wannan daren baze muku da kyau ba, ina muku fatan alheri kaji ko" jinjina kanshi yae yana sakaya murmushin yak'e kansu d'aga musu hannu subi hanyar daya dace...
**************
Shiru dukkansu sukayi kowa da abinda yake sak'awa aranshi, jin kafewar tayar motarsu ne ya sanya suka kalli juna shida Dawud dake gaba yayinda Abu Huraira ke kwance abaya yayi matashin kai da wani trow pillow daya zame masa abun yawo duk inda zashi, shi d'inma d'gowabyae yace yadai?" Cikin sanyin jiki yace
"Ga duhu ya soma sauka, ji nake fa kaman laka ne muka mak'ale aciki, amma ai d'axu bamu bi wata hanya me laka haka ba ko?" Wasu yawu Masu d'acin gaske ya had'iya kanyace
"Ko kusa bamu wani shiga laka ba gaskia, amma kaja da kyau mana" Iyakar dagewar shi yaja ya taka totor amma sam motar taqi ta motsa, kashewa yae suka fito dukkansu, babu wanda jikinshi be b'aci ba, lakar ce kuwa tsaki Abu Sufyan yaja ya koma cikin mota sukuwa suka ja baya suna me karkad'e k'afansu daya lalace da tab'o, giya ya sauya zuwa me iya fitar da motar daga wurin, dama Allah ya imakesu Hilux ce seta fito daga cikin Lakar lafiya, duhu ya soma sauka wannan ya sanya dawud ya ciro wata k'atuwar waya a aljihunsa ya kunna torchlight dake jikinta me hasken gaske, kai tsaye ta mamaye lakar da haske arziqi ma sukayi irin me zurfin gasken nan ce, cikin damuwa Abu Sufyan yace
"Dawud anya bamu sake hanya ba kuwa? Nifa sam babu wannan lakar a inda muka biyo ni gaskia na tsorata" Dafe kai sukayi dukkansu kansu d'akko ruwan faro dasukai guzurinshi su wanka k'afansu dashi sannan su koma kotar, sunyi adu'a kafin su d'auki hanyar dasuke tsammanin ita zata fitar dasu kan titin dabeda maraba da babu....
K'arfe takwas ta gota sanda Dawud cikin damuwa yace
"Abu sufyan ka kwatanta ka gani, uku saura mintuna biyar muka yanki jejin nan d'azu, kuma koda hud'u saura kwata tayi fa mun isa qauyen kaga tafiyar 45 mns ta kaimu, yanzu kuwa tun biyar da rabi muke zagayar jejin nan, ko shakka banayi wlhy b'atan hanya mukayi" wani dogon burki yaja ganin k'aton maciji agabansa gudun karya taka shi, bakinsa har rawa yake ganin macijin ma yaja burki ya d'ago kai yana kallon haske fitilar motar sekace yana ganinsu
"Abu Huraira maciji" Lek'owa shima yae shida Dawud, lokaci d'aya suka shiga ambaton mahalicci, basuko matsaba kuwa kaman yanda basu d'aga da motar ba konan dacen ganin yanda macijin kr kallon su kaman wani mutum.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: 🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*
*Billy Galadanchi*
*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*
*Littafina na kud'ine dan Allah idan baki biyaba karki karanta, idan kinaso ki biya kudi ki riqa samu a kud'inki*
02
Adu'ar tsari dukkansu ke karantawa har suka ga macijin ya wuce abunshi batare dayayi ta kansu ba, dukda Ac dake kunne a motan hakan be hanawa dukkansu tsiyayar da zufaba
"Abu sufyan ina wannan kalan macijinne ke had'iye mutum?" Wasu yawun wahala ya had'iya kafin yace
"Ni gaba d'aya na rikice ma, jikina yae sanyi sosai da tafiyar nan, ina roqon Allah ya mana shamaki daduk wani abun k'i" cikin damuwa Abu huraira yace
"Yanada girma amma da wannan macijinne aida motar gaba d'aya xe had'iya sedai fa aganina mu juya gwara mana kwana a k'auyen nan da mu lula acikin wannan jejin, ko shakka banayi mun sake hanya sosai" Nisawa Abu sufyan yae
"Bazan iya tuk'in nan ba, mu juya kawai kaikaja" cikin damuwa Dawud yace
"Kai yanzu seka sauka ku juya, kana ganin wannan mucijin, idan kuma be tafi bafa, kaidai ka juya kurun" haka ya juya akalar motar sa sukaci gaba da tafiya........
**********
"Bana samun number yaran nan koyaya na gwada, rabon danayi wayama dasu tun da rana dasukaje ajiye Baba ladi, ga garinsu babarma ba Ntwrk inaga dan wayanta itama a rufe" Kallonta General yae cikin takaici
"Ko? Toki musu adu'a inshaa Allah suna nan lafiya lau, maybe basu juya da wuri bayan sun ajiyeta inaga basuda caji, kuma k'aninta ya sanarmun sun ajiyeta harsun juya tun yamma, Glo kurun ke aiki a k'auyen, kinga mtn take using soba lallai ki samu ba" Ajiyan zuciya ta sauke hankalinta sam baya jikinta amma batace dashi komai ba se kwantawan datayi jiki a mace.
*********
Duk yanda taso tayi bacci abun ya gagareta, bazata iya hak'ura da rashin jin yayyun nataba, shak'uwace me tsanani a tsakaninsu, Fuskar wayarta ta kalla da sunayen su a k'alla ko wanne ta kira wayanshi yafi so hamsin amma baya tafiya, duk iyakan k'ok'arinta not reachable ake cewa da ita to ina suka shiga? Wannan itace tambayar da takewa kanta amma bata samu amsaba har wannan lokacin.
***********
Wayanshi ya danna gefen key haske ya bayyana, agogon wayan ya nuna k'arfe goma da rabi hadda mintuna uku na dare gumi ya sharce dan a zahirin gaskia a tsorace sosai yake, yawun bakinsa ma ya k'afe sam bayada wani abu dayae saura daze had'iya a bakin
"Abu Sufyan nashiga dana sani fa, dana sanin hanyar nan damuka d'akko cikin wannan daren damun sani damun kwana a k'auyen, gwara zazzab'in cizon sauro da wannan tashi hankalin damuke ciki, idan dai har daidai muka biyo hanyarnan tokuwa da tuni munzo wurin lakar damuka fad'a ciki d'azu, amma gashi yanzu shiru kusan sa'o'i biyu da matasan mintuna sun shud'e amma shiru kakeji, ina fatan ba wata hanyar muka k'ara cafka ba mara b'ullewa" Cikin damuwa Dawud yace
"Wannan kam tabbas wata *Doguwar hanya* ce muka d'akko me matuk'ar wahalar b'ullewa"
"Tuk'in nan danake tafiya ne kurun nakeyi amma wlhy bana gane kan hanyoyin nan, ban magana bane dankar na tsoratar daku amma hanyar seta rik'amun iri d'aya duk inda zanbi, ya dace musan abinyi gaskia" Yawun wahala Dawud ya had'iya ya tuna maganar mahaifuyarshi sanda ze fito gida
"Yanzu kai me zaka cewa kabeer? Kaine babban abokinsa amma akan ka tsaya hidimarsa kafiso kaje gantale, su sunada hujja dan ubansu ne ya aikesu kai kuma kanada wata hujjar ne, haba Dawud? Ya dace kawa kanka fad'a gaskia" Nisawa yae tunawa da ansan daya bata
"Umma ki gane tafiyan nan tunda Twins zasuyita nima dolene inje, bazan ganewa komai ba idan basa nan bikin ba wani dad'i zemu mn ba, nidai kimun kurun ita nake buk'ata" Adu'ar tamasa ya juya abunsa kuwa yabar gidan.
"Afu sufyan kasan me, Nemi wuri med'an fili kayi parkin motar nan kurun, mu kasheta mu sauke glass ko yayane, ka kunna mana karatun alqurani me girma, idan gari ya soma wayewa semu kama hanya, dan kar mui nisa inda bazamu ganeba koda akwai yalwar haske" Kallon juna sukai shida twin d'inshi ya kad'a masa kanshi akan hakan shawarace me kyau, cikin sanyin jiki yaja gefe yae parking adaidai wata bishiyar tare da janyo wayarshi ya kunna karatun alk'urani me girma a hankaki ya zuge glass na gaba duka biyu na baya d'aya kawai kwanciya yae jikin sit na kujerar ya lumshe idanshi tare da soma rero duk wata adu'ar datazo bakin sa ta tsari, haka suma sukeyi a hankali....
***********
Hasken Rana shine abinda ya farkar da Abu Sufyan dayan daga nannauyan baccin daya d'auke dukansu batare dasun shirya zuwan saba, wayarsa kuwa har cahrge ya d'auke sabida ya da take kunne, karon sa na farko kenan tun bayan daya girma da wani abu me kamada yin salla asuba ba'a cikin lokaci ba ya same shi, kallon Dawud yae dake gefenshi,baccin sa shima yake cikin nutsuwa sedai badan dad'i ba kod'an da yake a zaune yakene oho, ko shakka ba yayi sun kai nisa 5 kafin baccin ya sacesu dabadan hakan ba ba abinda ze hanawa d'ayansu farkawa adaidai lokacin daya saba tashi sallan asuba, hannu yakai yad'an bubbugi kafad'ar Dawud inda a hankali ya bud'e idanshi d'auke da salatin annabi a bakin sa, Abu Huraira ma farkawa yae suka kalli juna cikin mamakin baccin dasukayi, kan su sakko daga motar dukkansu su soma shirin d'aura alwala da d'an ruwan dasuka zo dashi na Faro.... Se bayan da suka sallaci sallolin dabasu samu sunyiba data asuba sannan suka yi addu'ar neman yafiya kan daga bisani su mik'e suna ninke carpet dake hannun su wanda dama anxo dashi, Abu Huraira ne yawa wurin kallon tsafta sosai kan daga bisani ya nisa yace
"Ko kunsan cewan kwata kwata ba alamun sawun mutane nabi nan hanyar ko zancen wata mota kaiko babur da keke banaji suna bi" Jikin motar Abu Sufyan ya jingine cikeda damuwa yace
"Abinda ya kamacemu shine mu qarawa motar nan mai mu kama gabanmu yanzu Alhamdulillah safiyane inshaa Allah zamu gano hanyar" kallon tausayin kansu Abu huraira ya mai kanyace
"Abu Sufyan kasan Allah, wlhy a madifar tsorace nake, dabadan da Hilux mukazo ba da ba abinda ze hanamu shan bak'ar wahala tun daren jiya, yanzu kuma tsorona Allah banga inda zamu biba, ko ina yakoma mun iri d'aya" Mamaki ne sosainya bayyana a idon Dawud
"Kaima ka kula kenan? Na zata d'emuwane ya kamani ai" Hannunsa ya zura a lajihunsa d'aya jal
"Nikaina ban fahimci komai ba, kasan me dana farka senaga kaman jiya banan na ajiye kan motar ba" shiru ne ya ratsa wurin na wuccin gadi kafin daga bisani Abu sufyan yace
"Allah ya gani iyayen mu mukewa biyayya mukazo wanan jejin, da yardar Allah da qarfin adu'ar su bazamu tab'e ba, kuzo mui lalube inshaa Allah zamu b'ulle" cikin damuwa suka d'akko man fetur suka zube ajikin motar sannan suka koma ciki suna tashe tax wannan karon Dawud ne ya karb'i Tuk'in, Abu sufyan yana baya ya kwanta yana me lumshe idansa, yunwa yakeji ma sosai dan haka ya janyo musu cake da drinks ya baiwa kowa yanka suna tafi sunaci badan dad'i ba, gabaki d'ayansu hankulansu a tashe suke kasancewar basu tab'a tsintar kansu a jeji ba se wannan karon........
********
Yajima tsaye a kanta yana nazarin yanayinta, samsamsam ya kasa gane kan Haj Adama,tunda aka gagara samun lambobin wayoyin yaran nan jiya ko abinci tak'i taci, zama yae kusa da ita ya rik'o hannun ta
"Haba hajiyar general mesa kike hakane? Ai duk yayinda kikaji shiru tokuwa da yardar lillahi lafiya ce take kawo hakan, nifa inaga yarannan dan kurin sunyi tafiyar nan ne basaso suka kama suka rufe wayoyinsu, suna kan fushi har yanzu, amma zasu bud'e ne" d'ago idanta tae dasu kae ja ta kalleshi, cikin takaici tace
"Bana tunanin na d'aura kyautar Allah akan wata turba masiffanciyar wannan, da kansu bazasuyi fushi da iyayen suba akan abinda yafi wanan ma bare wannan abin dabe taka kara ya karya ba, girman nak'uda yawane dashi koda bazaka yarda dani ba kasani koyaya matsala take kad'an tokuwa tabbas itace ta hanasu bud'e wayoyinsu kokuma a samesu" Sauke nannauyar ajiyan zuciya yae
"Bamuda wani zab'i daya wuce mu musu adu'a arayuwa, da damuwar nan tana maganin wani abu data miki Haj, ina baki shawara kurun ki musu adu'a zatafi saurin isa garesu akan wannan damuwar dakika sanyawa kanki, kici abinci ki miqawa