Showing 6001 words to 9000 words out of 35867 words

Chapter 3 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt

29 Jan 2025

1681

Allah lamuranki inshaa Allah zakiga haske" Batace masa komai ba harya mik'e yabar mata d'akin.


*********
Duk yanda sukaso su gano kan hanyar abun yaci tura, sunyi zagaye sunyi kwana har sun gaji amma sam basu gano komai ba, zuwa yanzu man motar tasuma yayi qasa sosai ga yamma tayi cake kurin sukeci se sallah dasuke idan time yayi, alwala ma se sun riqe sabida ruwan su saura roba bakwai kurin, kansu ya kunce ainun.


Tunda magrib tae musu a wannan jejin suka sare da fita aciki a wannan ranar, to save there remaining fuel kurin sukae parking sukai sallah skaci cake se dabino suka sha lemo sa ruwa suka hau karatun alqur'ani me girma, sun jima sunayi har suka kintaci lokacin sallan isha suka tashi sukayi sannan suka shinfid'a qatuwar dadduma ajikin bayan motar su, suka koma suka kwanta acen cikin budadd'en booth d'in dasuka shinfid'a dandumar, sama dukkansu ke kallo bayan sunyi pillow da trow pillows dake cikin motar farin wata ya haske sararin samaniya bakajin sautin komai se bugawar zuciyoyin su dakuma sautin kukan tsuntsayen dake tashi lokaci zuwa lokaci, Abu sufyan ne ya kai hannunshi ya rik'o hannun Abu Huraira cikin muryan damuwa ya furta


"Brother am really scared please pray for us" Matse hannun nashi danashi cikin tausayi yace


"Keep reciting Ayatul kursiy brother, everything will be alright ok?" Yafad'a yana me duban face d'inshi acikin d'an hasken na farin wata, dawud ma a hankali ya soma adu'a ba k'akk'autawa........ Kuka suka soma jiyo tamkar na zaki, a tare suka miqe a zaune dukansu, se zare ido sukeyi yayinda kukan ke qara kusan tar inda suke, da gudu suka sakko suka bud'e motar, amma ina kafin sukai ga shigewa har abun ya qarado inda suke.....


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


04


Sojojin basu isa garin nasu Baba ladi ba se bayan 2 days,haka suka wuni a garin bayan an tabbatar musu sun juya, amma wannan karon tare da Baba ladi suka juyo, sabida ta kaisu wannan Hotel dasuka sauka aji kosun koma, ga mamakin su basu koma ba tun ranar, ga kayansu ma dasuka bari anan kuma kud'in sati suka biya gashi yanzu kusan 6days babusu babu labarin su sam, sojojin hankalinsu ya tashi, anan sukawa kansu masauki washe gari suka juya k'auyen nasu Baba ladi da guzurin man fetur me yawa kaman yanda sukeyi idan zasuje jeji aiki.


K'anin Baba Ladi yae gyaran murya yace da Oga Shamsu


"Ranka ya dad'e kamar dai yanda ka sani wannan yankin namu muna boader da k'ashashe kusan uku, kuma idan ka lura da kyau zakaga cewar bama kusa da mutane sam, mun yanko jeji sosai munbar gari da nisa, itama sanadi ne ya fitar da ita daga garin nan dabadan haka ba bana tunanin akwai wamda ya taso ba'a nan ba, Hanyoyine muke dasu masu rikitarwa sosai anan jejin, dagazaran ka saki hanya da kuskure d'aya tokuwa tabbas zaka yanki wata uwar *Doguwar Hanya* ne dabakasan sanda zaku rabu da itaba, acewar kakan ninmu, hanyoyin kana isa zasu koma maka iri d'aya kuma da gabas da yamma da kudu da arewa duk zasu zame maka alqibla d'aya ne, sa'n nan kuma bazaka gane inda ka dosa ba, duk inda ka duba zaka ga kamar nan kafito, seka bi seta dulmiyar dakai, acewar su ko namun jeji basa zama a jejin duk wani naman daji daka gani agun tokuwa tabbas aljanine dansu kad'aine ke iyawa da gun" Wani tashin hankaline ya ziyarci Oga shamsu ya kalleshi cikin takaici yace


"Yanzu kenan bamuda ikon shiga jejin neman su?"


"To nidai bazance bakuda ikon shiga ba, ikon shiga kam aikowabyanada shi, ikon fitowa ne babu kaga anan zab'i nakune,tunda mutane suke shiga jejin ana zuwa nemansu, Barde ne ke zuwa kafin a haifeshi kakanshi keyi, yazo Baban shi nayi yanzu shiya gada jikan sarkin malamai ne anan garin, babu wanda aka tab'a samu da ranshi ajejin, kowanne zaka tarar gawa aka tsinta kokuma alamun yaje jejin, baka tab'a samun tarihin wanda yaje ya fito, idan ma ansamo mutum tokuwa zakaga dawani ciwon ze dawo, to idan ma mutum yakai gab'ar kogin ko Barde baya shiga wannan ruwan zaka hau su bakada tabbacin sauka kuma idanma ka saukan baza'a k'ara samun labarin kaba, mahaifin Barde ma daya tsallaka haryau shiru kaga akwai matsala kenan?" Hular kansa ya zare cikin mutuwar jiki yace


"Lallai wannan doguwar hanya ce, to amma shi barden baya zuwa tare da wasu ne? Kaman yanzu yajagoran cemu?" Murmushi yae


"Yakanje tare da mutane matsalan shine ko kabishi ba amfanin ka bishi dan ba'a kagana a jejin, kana yi kana dulmiyewa, bafa k'aramin mugun abu bane a wannan wurin, koda kuna tare kanshi kurun yake iya baiwa kariya sabida haka gwara karkuje, ku koma ku bashi aiki ya muku acikin kwana uku yake dawowa da bayanin wanda yaje nema, ko rai ko babu idan ma mutum beje ba ze gane, idan yaje kuma ze gane meya sameshi koda ya tsallaka kogi ne kuwa, matsalan d'aya ne baya wa kowa aiki seya bashi damin hatsi 20, na dawa 20 na masara ma haka, sannan ga tsaban kud'i jaka talatin" Kallon shi oga yae


"Nawane jaka talatin?"


"Dubu shida fa, shiyasa wasu idan d'an uwansu sun tafi basa iya biyan barde wlhy" murmushi yae


"Ba kud'in bane abinji mu zamu ma qara masa ninkin ba ninkin, mu cetosu mukeso yayi, gashi kuma kace baya iya baiwa wani kariya, yazeyi to idan ya gansu?" Murmushi yae


"Yasan yanda zeyi ai, masu rabon fitowar sukan fito tare dashi, wannan aikin sane, ku bari muje gunsa inyaso kunga semui magana dashi idan ze iya jagoran tarku ko?" Hakan kuwa akayi sedai ya sanar dasu shi sam se laraba yake zuwa jejin dan haka tunda yake yau alhamis sedai su jira nanda kwanaki shida, yakuma musu alqawarin inshaa Allah zeje tare dasu indai zasu biyashi kud'in aikin nasu... Ba b'ata lokaci sukai na'am da wannan sabida basuda yanda suka iya haka dole suka juya zuwa gida domin sanarwa da mahaifiyar yaron bisa jagorancin wani d'an k'auyen gudun kar hanya ta k'ara saka subi doguwar hanya mara b'ullewa.


***********
Ruwan yanda ya taso da k'arfi sekace had'iyesu zeyi, idan ana zancen tsorata sam baza'a kawota anan dan abinda sukeji azukatansu a wannan lokacin yafi k'arfin tsoro, dukkaninsu sun sare da rayuwa se Abu sufyan ne kurun ya soma adu'a cikin muryar sa me dad'i, ilahirinsu d'auka sukayi babu wanda abakinshi ba adu'a yake ba, jirgin se tangal tangal yakeyi dasu kaman ze kife, suda sukeda niyyan tsallakawa seya juyar da akalan jirgin zuwa mik'ewa ata tsakiyan ruwan tsaye, duk yanda sukaso su juyo abin ya faskara, da k'arfin adu'a cikin iyawar Allah suka samu suka daidaita kan jirgin zuwa tsallakawa, hakan ce ta basu damar samun yar nutsuwa a hankali suka ci gaba da tuk'a jirgin har zuwa sanda sukazo gab'ar Tekun suka gangara suka ajiye shi suka sakko daga kai suna me zaunawa, ilahirin jikinsu ruwa ta gama jiqashi gashi kala d'aid'aya dama suka zaro daga kayansu gudun kota kwana, wannan najikinsun tun ranar dasuka zo yake, gyara jikinsu sukayi suka shirya dukkansu cikin qananun kayan sannan suka ninke wancen suka mayar a qatuwar jakar bayan dasuke juyawa daga wannan zuwa wancen.


Tafiya suka somayi suna mamakin ikon Allah azukatansu, wannan shine Allah d'aya amma gari banban, ka kalli nisan dabe wuce sa'o'i uku ba daga shigarsu jirgin su tsallako wannan wurin har sunga sauyin yanayi, babu wani gari dasuka hanga amma tabbas wurin ya k'ayatar, sabida ga 'ya'yan itatuwa nan burjik se kalan wanda bakaso dogayen itatuwa sunwa wurin k'awanya wurin ya burgesu sosai dukda zukatansu ba dad'i hakan be hanasu yada zango anwurin ba suyi sallah azahar harma da la'asar kasancewar su matafiya an halatta musu aikata hakan, bayan sun idar sukaci dabino da lemo harma da korawa da ruwan robar dabe wuce musu saura roba uku ba yanzu suka kama hanya bayan sunji cikinsu ya musu nauyi suka naushi hanyar suna tafe suna bin karatun alqur'ani me girma dake tashi daga k'aramar wayar Abu Huraira, yayinda suke tsintar lemon zak'i dakuma Tufa da suka taradda itaciyar kowannen burjin agun suna wurgawa a jakarsu wasu kuma a hannayensu.....


Ganin su da yarinyar tae ne yabata damar k'ara fitowa daga jikin itacen data bu'ya ta k'ura musu ido, shigar jikinsu kurun take kallo tana mamakin wad'an nan wane irin muta nene haka? Tun tashinta tana k'arama duk shekara se k'addara ta kad'o wani garin nasu amma wannan ne karanta na farko dataga masu irin wannan shigar kuma ga alama mazane ma, Dawud ne ya fara ganinta seda yaja baya ya rik'o hannun Abu Huraira


" Abu Huraira kalli wata aba!" Ya furta cikeda tsoro dan harga Allah shi kallon aljana yake mata, Atare suka d'aga suka kalleta kowa yae turus yana kallon ta ita d'inma su take kallo bata ko k'iftawa amma tafi nacewa kallon Abu Huraira da tawayensa kasancewar tana musu kallon aljanai gasu iri d'aya komai nasu iri d'aya tosu waye? Ta tambayi kanta


"Dawud mugodewa Allah mun had'u da mutum, wannan mutanene masu rayuwa jeji bakaga yanayin shigartaba?" Sauke ajiyar zuciya yae


"Toni naganta kaman daga sama kuma ta wani tsaya ta kafemu da ido ko k'iftawa batayi" Murmushi Abu sufyan yae yace


"Muda muke tare da tsarewar Allah, kai banda ikon Allah ka isa kazo nan wurin da ranka, koma aljanar ce magana zam mata niba ruwa na" takawa yae har zuwa inda take seda ya k'are mata kallo sannan yace


"Baiwar Allah dan Allah nand'in inane? B'ata mukayi wlhy muba en nan nahiyar bane" kallon sheqeqe ta masa sarautar da mulkin suka motsa dan dama ita ba'a kallonta a garin kwata kwata, baka isa ka kalli 'yar sarki ba, k'wak'ulemaka ido d'aya akeyi musamman mazan garin, cikin yaransu dabayaji ta sanya hannu ta tankad'a shi yae baya yaje taga taga ze fad'i seda Abu Huraira ya rik'eshi sannan tace


"Kai waye dazaka kalleni ido cikin ido? Zan saka a kashe ka fa" kallon juna sukai da tawayen nashi, shi Abu huraira ya fahimci sam batajin yaransu suma kuma bawai gane komai sukayi dangane da yaran nasu ba, hard'e hannaye Dawud yae ya langwab'ar da kanshi gefe d'aya ba tsinta dukaba, amma tabbas magana takeyi akan kisa dakuma fad'an yana kallonta, ko shakka bayayi yarbanci takeyi sedai banbancin kalamai da wurin furtasu daya kula akwai da yaren shida yakeyi, matsawa yae kusa da ita ya juye yaran bakinsa, cikin harshen na yarbanci ya soma bata amsa


"Kiyi Hakuri baze k'araba kinji" kallonsa su Twins suka tsaya yi sun gano yarbanci tae sedai suma natan ya musu wani iri, dukda yake sunsan abokin nasu Mahaifanshi duka yarbawa ne zama acikin hausawa yasa suka riqa, gasu musulmai ne kuma sosai tun kakaninsu shisa har komai nasu ya juye zuwa al'adun hausawa sedai kam sukanyi yarbanci sosai agidan nasu.
Kallanshi tae ya sauke k'wayar idanshi k'asa da sauri yanaso ya gane idan ya fahimceta sosai kallon natane ba'ayi, murmushi tae


"Wane magana yake haka? Bana ganewa?" Ta tambayi Dawud kanshi a k'asa yace


"Yaren sa kenan" Murmushi ta k'arayi


"Bayan yamura yarenmu sekuwa yamura kawal susu kad'aine yaruka biyu aduniya kuma duk na iya, ya akayi nashi bako d'aya aciki" D'an kallonta kad'an yae ya fahimci sosai bata san annabi ya faku ba, ko yanayin shigar tama ya nuna rayuwar dabbobi suke a jeji


"Akwai yaru kan dabaki saniba ne ai, duniyan yanada fad'i sosai yaruka sunfi a irga" Wata dariya ta kwashe dashi, sannan tace


"Ni babu inda ban saniba aduk fad'in duniyar nan, ko ina nasani kuma ina zuwa ko ina ma, Sarki k'uru shine mahaifina tare muke zaga duniya dashi" JINJINA kanshi yae bece qalaba, kafin wani yae magana acikinsu har wasu qartin mazaje sun zagaye su sun shiga d'aurinsu da igiyoyi, mamakine ya hanasu magana haka aka jasu tabi bayansu tana murmushi, dukda saurayinta ya b'ata mata rai, amma hakan be hanata murmushi ba, idan sukabar garin sama ina zasuje? Yanzu kam an samu na sadaukar wa ta huta....




Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins💕❤: *🏇🏇DOGUWAR HANYA....🏇🏇*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*Littafina na siyarwane idan kinason ki karanta kibiya kud'i, ida kika karanta baki biyaba kuma toh...idan kinaso ki siya ki nemi wannan number 07084161619.


05


Acikin sojojin nan Barde da mutane bakwai ya tafi jejin nan, a mota suka tafi dukda yake yace shi baya shiga jejin a mota, amma suka lallab'ashi ya amince musu.


***********
Hankalin su Dawud a tashe yake musamman shi Dawud dayakan tsinci abinda suke fad'a acikin wak'ar dasuke rerawa da harshen su me kamada yarbanci, dukda yake ya kula akwai banbanci sosai acikin yaren nasu, ko shakka baya yi wannan wani ikone na Allah amma yarbancinne dai, tunda har ya iya yin magana da ita,gashi kuma yakan gane abinda suke nufi, se turasu sukeyi sekace sun kamo bayi


"Abu sufyan wlhy zancen Sacrifice sukeyi fa, kanajin abinda suke cewa a wannan wak'ar dasuke inajin wani abun kaman yarbanci suke, mun shiga uku munzo garin matsafa" cikin tashin hankali Abu Huraira yace


"Dena gayamun mun shiga Uku Dawud, inshaa Allah bamu shiga komai ba se Alheri, sunada k'arfin tsafi munada k'arfin ikon Allah, kaci gaba da addu'a da karatun alqur'ani inshaa Allah zamu kub'uta" shikamma Abu sufyan ya dena gane komai, gaba ki d'aya ya gagara furta wata kalma banda gumi babu abinda yake had'awa haka aka tankad'a k'eyar su har zuwa wani babban fili me zubin yashi kawai ba itatuwa, a tsakiyar yashin aka ajiyesu aka d'auresu kowa baya fuskantar d'anuwansa dan a had'e aka d'auresu sedai bayansu dake gugar juna,a nan aka barsu har rana ta fito ta fad'i bako ruwa gashi an k'wace musu jankunkuna an ajiye angefensu har wannan lokacin kuwa wayar Dawud tana rero karatun alk'urani seda k'yar ya janyota a aljihunsa ya kashe sabida gudun k'arewar caji.


*********
Yamma lik'is mutanen garin suka firfito aka zo aka ajiye kujera koda a k'auyen dake dokar jeji ne kana gani zaka hango cewan harkan saraki ne, haka aka jere kujeru sassak'ar katako sunkai k'waya bakwai mutanen gari suka zo sukazo suka jeru bame wata sutura se kayan fata da kuma wasu ganye sun rufe iya farjinsu maza da mata, matayen kuwa zuwa k'irjinsu ma arufe yake da kayan fata, zuwa akayi aka zagayesu da wani abu kaman cage amma na kara, kaman k'ananun ramukan dake gun dama jira suke dankuwa acikinsu kurun ake kafe abun ana zagayewa har aka kammala


Wani wanda ko ba'a gaya musu ba sunsan sarkine da ahalainsa suka iso gun an d'akkosu acikin wani cage na itace shima k'arti sun d'akko ko wanne susu hud'u d'auke dashi Kowa sujuda yae harseda sarkin da ahalinsa suka zauna sannan suka mik'e tsaye dukansu, gasunan da tsofaffi da kowa, wani ne yafito da jawabinsa na cewan Er sarki Lawuri itace ta kamo mutanen da zasu ceci babanta da danginta batare data tsallaka ruwan ba anan aka d'auki tafi da sowa saurayinta sr murmushi yake yayinda ko kallonsa batayi ba sabida taji haushin yanda bezo ba, Cikin takunta na k'asaita ta k'arasa cikon hilin tare da rakiyar muqarabanta mata masu kula kula da ita. Kunce mata su akai duk aka mik'ar dasu tsaye, lokaci d'aya Abu Sufyan ya nemi zubewa k'asa sabida azabar kishirwa da kuma wuni a dunk'ule gu d'aya, da sauri Abu huraira ya rik'oshi


"Sannu Sufyan, menene?" Ya furta cikeda tashin hakali


"Ruwa nakeso Huraira, kuma k'afana baya iya d'aukana" jakarsu ya janyo da sauri ya zaro roban ruwa, wurin kowa yayi tsit ana kallon su har Lawuri ma, bud'ewa yae ya jonama mai robar a abaki, sosai yakeshan ruwan jiyake kaman ze iya had'iye kogi ma akan tsabar kishin dayakeji, hannu Lawuri ta saka ta karb'e roban ruwa ta tuttular da sauran a k'asa sannan ta wankawa Abu Huraira mari ta turw sufyan a k'asa


" kai waye dazaka mana k'aud'i, ka isa kaciyar dashine?" Dafe kuncin sa yae cikin mamaki ya bita da ido beyi aune ba yaji dirar k'asa a idan sa


"Ni wannan abun ze kalla ido cikin ido? Kai d'an iskan inane dazaka kalleni ido cikin ido? Tabbas inaga kaine zamu yankawa Raminus a wannan shekarar" murza idanshi ya hauyi ga k'asar ya shiga masa sosai haka ya dinga murzawa ya rasa inama ze sanya rayuwar sa, Abu sufyan ne ya rik'oshi ya soma hure masa idan sa, haka yae ta masa kowa yae tsit daga k'arshe ya janyo roba daga jakars ya bashi ya wanke masa fuakarsa da idansa seda yaga ya samu nutsuwa sannan ya rik'e hannunshi yaja yayan shi bayan shi ya had'e hannayensa gu d'aya alamar rok'o kan cewar suyi hak'uri, wata mahaukaciyar dariya ta kwashe da ita sannan ta sanya hannu ta d'auki robar ruwan daya ajiye takai bakinta ta k'wankwada, wani iri taji daban kaman an sanyawa ruwan rake lumshe idanta tae ta shanye duka sannan ta kalli Dawud, tace dashi cikin yaren data fahimci yana ganewa


"Ruwan meye wannan?" D'agowa yae ya kalleta amma be bari sun had'a idoba yace


"Ruwan shane" atak'aice. Murmushi tae masa


"Amma ba irin namu bane, ina ku kuka samo?" shid'inma kafirar k'ishi yakeji seda ya hadi'yi bushashen yawunsa sannan yace


"Dashi mukazo daga garinmu, ku taimaka kubarmu mu koma gida, badasan ranmu mukazo nan ba, hanya ce ta b'ace mana" Hannun ta takai taja gashin gemunsa seda yae k'ara sannan tace


"Wannan zan saka a soma askewa, kaf garin nan babu wanda yakeda daman ajiye wannan se Sarki k'uru naka yayi yawa" Bece komai ba se jakar shima daya janyo ya zari robar rowan da itace ta k'arshe ya kwankwad'a sosai yakusa shanyewa ma kanya ajiye, warcewa tae ta k'ara shanyewa kamar wata mahaukaciyar zakanya. Matsawa tae kusada Abu Huraira ya k'ura mata ido, Dawud dayaga kowa baya iya kallonta sosai ya fahimci ba'a kallonta seya sanya hannu ya rufe masa ido, hannun nasa Abu Huraira ya bige ya sake sanya idanshi a nata, matsawa sosai tae kusa dashi tace da macen dake gefenta


"Wannan nakeso abayar wannan shekarar, banason yanda yake kallona, na tsaneshi sosai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login