Showing 30001 words to 33000 words out of 35867 words

Chapter 11 - Doguwar Hanya Complete 1 Book by Billy Galadanci .txt

29 Jan 2025

1678

wannan ba da ban tambaya da bazaku sanar ba kenan" tsoro ya kama su Hanny tace


"Dad na gayawa mom tinda na idar da sallan asuba, setace badai inda zasu waiko a garden suka kwana tunda sun saba kwanan jeji" Wani kallo ya wurgawa adama daya sanya ta sadda kanta k'asa ba shiri sannan ya kalli twins


"Kai Huraira jeka ka duba mun lungu da sak'o na gidan ina yaran mutane suka shiga" A tare suka mik'e da sufyan dukkaninsu cikin tashin hankali mara misaltuwa, neman duniya sunyi agidan basu gansu ba, sedaga baya suka tambayi securities na gidan anan sukejin wai tun jiya da kusan isha suka fita babu kuma wanda yaga dawowar su gidan, hankalinsu ya tashi suka koma ciki suka sanar, mom dai ko gezau su hanny ma ganin dad a wani yanayin duk se ya rikitar dasu suka shiga taitayin su


"Mesa nida gidana bazan kawo ajiyar abinda nake so a kular dashi ba? Shisa Captain yace zeje dasu gun matarsa bayarbiya na hana, yanzu a matsayin ki na uwa me kenan kikai? Kin burge kenan? Kin cinye kike gani? Yaran mutane dasuka fice dalilin masifar wlhy tlahi na baki awa ashirin da hud'u duk inda sukaje ki nemosu inba hakaba kinsan sauran" Mik'ewa tae cikin b'acin rai


"Haba Muhammad, se yaushe zan girma ne a wurinka wai? Nina koresu? Koni nace su bar gidan? Banko san sun tafi tayaya zan nemosu? Idan har kace akan yaran nan zaka mun haka wlhy sena bar maka gidan, kaida ka kawosu sekaje cen ka nemesu danni babu ruwana" Kallonta yae cikin b'acin rai


"Yanzu dama kafin na fita nakeso na duba CCTV nawa, an sanar mun har dukanta kikae a dining, suma securities sesunsha wuya a hannuna, yanda zasu bari su fita ba tare da sanin kowa ba, dan sunga shamsu baya nan" Juyawa tae rai a b'ace ta haura sama tana mejin zafin abinda ya mata agaban yara.


***********
Lawuri unconcious take har washe garin, anma rasa gane meke damunta, dole yanzu ct scan za'a mata tunda yake ta samu rauni aka.... Yarinyar data kad'esu duk a rikice take tarasa nutsuwarta dukda kasancewar ta likita hakan be hanata shiga tsananin rud'u ba, musamman ganin wannan kamar zata mutu ma.


Neman duniya anyiwa su Lawuri ba labarin su, Abu sufyan daren ranar bekoyi baccin kirki ba, yayinda Abu Huraira ya gagarayin baccin ma kwata kwata, hankalinsa ya tashi sabida yasani tabbas hanyar gidansu zata nema kuma bawai tasan hanyar bane ba, sedai ya kula tanada basira tabbas inda suka biyo tanan zata nemi komawa, sedai ta yaya? Tunda yake jirgi suka hau daga babban garin dasuka sauka zuwa nan garin Abuja, yashiga rud'ani sosai ya rasa tudun dafawa hankalinsa in yayi dubu to tabbas a tashe yake kuwa.


************

Banida zab'in daya fi in koma garin su Lawuri, banida zab'in dayafi inje garin nasu in binciketa inji kota gane hanya tazo, ai taji ana anbatar sunan garin dasuka hau jirgi sukazo wato OGUN state in hakane mota zata hau, taje cen sekuma ta nemi hawa wannan motar dasuka hau suka tafi wannan k'auyen na fulani, duk yanda akayi gida zataje amma bari ya bada sati d'aya idan ba'a samu labarin suba dole yaje garin koyaya ne kuwa!!!.




*****Bayan sati d'aya*


Har akayi sati d'aya babu neman dabasu musuba amma shiru kakeji, bame hotonsu bare su saka a media, general yayi bk'in cikin wannan abun, yanaso yarinyar ta karb'i musulunci yana so ya nuna mata cikar musulunci abun arziqi amma anzo an tilastata guduwa tabar gida sabida wani ra'ayin banza, damuwar sa d'aya ma besan hannun dazasu fad'a ba, nagari ko mugu?, yama rasa tudun dafawa!


*********
Hankalin Twins baya jikinsu, Abu Hurairah be fahimci tsananin so da illar dason ya masa ba se yanzu, hankalinsa ya matuk'ar tashi ainun, har 'yar rama, wannan wace irin masifa ce wai? Yana cikin dubun tashin hankali akan wannan abun, sabida ya shirya sosai akan yanda ze shawo kan iyayensa ya musuluntar da ita ya aureta, amma shine za'a wani ce ta gudu? Lallai wajibine ya koma wannan *Doguwar hanyar* yasan abunyi akan Lawuri idan ma batacen duk inda tashiga aduniya seya nemota yaga cewar sun sake had'uwa itace farin cikin sa, itace komai na rayuwar sa yakeji dai........


A b'angaren Abu sufyan kuwa shisam bama shida lafiya, wani ciwo ne ya sameshi me wuyar magani, ya tabbatar rashin ganin Lawuri a rayuwarsa abu ne me shirin kasheshi har abada ba shiri, mesa yarinyar nan ta masa katutu a zuci ne wai? Meke damunsa game da ita? Ne kodai haukacewa yake shirin yine be shirya hakan ba? Duk iyakar tunaninsa ya rasa abinyi.


Dawood yaji zafin wannan abin sosai
Sedai shi bekaisu damuwa ba kasancewar ba wani d'ad'ashi da k'asa tayi ba, shidai kawai yana mata kwad'ayin musulunci ne, bayaga haka kuma yaso ya aureta ya sanyata a rigar musuluncin gaba daya, abu mafi damunsa shine besan hannun dazasu fad'a ba, sun shigo garine kurin batare dasun san waye mutanen birnin ba? Yana musu fatan alheri.


*********
Duk wani shiri daya kamata huraira yae yayi abunshi na zuwa garin su Lawuri, babu wanda ya gayawa, se Sufyan daya kula tamkar da abinda yake b'oye masa yamasa shiru ne kurin yaga iya gudun ruwan sa.


Ranar da ya fita aiki kuwa bekoma waiwayen gida ba ya Lula *Doguwar Hanya* wacce besan wane tanadi tae masa ba yanzu..........


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


*Assalamu Alaikum masoya, litattafai namu masu suna kamar haka na kud'ine.*
*Sultan merah*
*Kamar da wasa*
*Doguwar Hanya*
*Zafin rana*
*Sanadiyya*
*muna roqon duk wani me tsoron Allah da idan be biyaba karya karanta mana book koda marasa tsoron Allah sun fitar kuwa, yin hakan ganganci dan gashi munyi bayanin kanmu, idan kayi hakan kaida Allah mahalicci, munyi garab'asa gaduk meson duka biyar ya biya N500 kacal,meson 1 N200 kacal, me buqatar siya ya nemi wannan lambar 07084161619 kokuma 08030811300*




******** 17


Abu Hurairah bebi ta k'auyen su Baba ladi ba, ya kula hanyace me rikitar wa mara b'ullewa, jejin tamkar aljanaine aciki, da wannan ya samu isa OGUN STATE da yamma sakaliya, yayiwa wayoyinsa kisan gilla dan karma wani ya sameshi, shidai burinsa d'ayane shine ya samu Lawuri, rashin ganin babban tashin hankali ne agaresa, koda yake b'angarora da dama na zuciyar sa suna sanar masa tsabagen wowtar da yae na tunanin komawa wannan masifar, har wata zuciyar sa tana sanar masa tunda harshi ya kawo kansa tokuwa tabbas babu abinda ze sanya idan yae adu'a Allah ya amsa masa, sedai kuma a wani b'angarn yanaji ajikinsa cewar tabbas Allah ze nuna masa hanyar b'ullewa, dan kuwa bayaga soyayyar data janyoshi akwai kwad'ayin ya janyo musulunci a garin, abu d'ayane yamai tsaye arayuwar shi shine yarensu da bayaji? Yaya zeyi huld'a dasu, yaya zeyi communicating dasu? Ta ina ma ze fara? Daga wane b'angaren ze soma ? .......


**********
Ayusher yarinyace me matuk'ar tausayi tunda abin nan ya faru da yarinyar nan kullum setayi kuka ga yarinya a ICU dukta fita hayyacinta gashi batasan ina zataga iyayenta ba batasan inda ya dace ta dosa ba gun nemansu, kodai zasu d'auki hoton tane sukai sanarwa gidan tv da kuma sauran media flatform taga ko za'a dace? Da wannan shawarar yau ta kira Sufyan, yana d'agawa suka gaisa yace


"Ayusher tunda kikai accident d'in nan ko nemana bakyayi duk kin nemi d'aga hankalinki a banza" murmushi tayi sannan tace


"Kayi bak'uri nutsuwarce tamun k'aranci wlhy ina cikin tsananin damuwar rashin sanin iyayen wanda na kad'e" Nisawa yae


"Haba Ayusher kema dai kunyi sakaci mezai hana kanki tsaye mana ki kai agidan tv na dad d'inku, a duk fad'in abuja wane gidan TV ne yafishi suna? Zakiga an dace ai" Nisawa tae


"Shawara dana yanke kenan amma nace sena kira pure heart, barin gayawa mom kawai, yanxu kana ina" Nisawa yae


"Ina OGUN STATE fa" wara ido tayi


"Yinme pure heart?" Murmushi yae


"Zan gaya miki daga baya kinji yanzu dai kiyi yanda nace d'in" sallama sukai sannan yaci gaba da tuk'insa.


**********
Tsoro ya baiwa Abu hurairah sanda ya ganshi akan kwanar da ake d'aukewa aje wannan k'auyen na fulani, bashida dabarar dayafi ya gangara ya tsaya danya tabbatar yanda ya ganshi shima ya ganshi ido cikin ido, fitowa yae dama shi a tsaye suka kalli juna ido cikin ido, a hankali ya tako yazo ha rik'e hannun d'an uwansa cikin sanyin jiki yace


"Al-hussain" amma seya gagara furta komai bayaga wannan kalmar, har wannan lokacin idonsu yana cikin na juna, Abu Hurairah yau duk dauriyarsa seda yae kuka besan sanda ya rungume d'an uwan saba yace cikin muryan kuka


"Wlhy ina santa Al-hussain, rashin ta baze barni acikin sukuni ba, soyayyar ta tagama zagaye ilahirin jikina, dan Allah karkace zaka hanani zuwa nemanta kaji" murmushin takaici yae ya kula da wannan tunba yanzu ba shisa ya k'udirta a ransa koda soyayyar yarinyar zata hallakar dashi toze sadaukar da rayuwarshi akan d'an uwansa yaji dad'i, dukda shima yana shan wahala amma yasani beyi sabo da ita yansa za'ace baze iya barwa d'an uwansa ita ba


"Nasani Al-hassan amma wannan baze barni in barka kabar wannan duniyar tamu zuwa wata duniyar ba me cikeda abun tsoro kala kala gakuma doguwar hanya me rikitarwa, iya kar wacce mukasha ta wadatar Al-hassan, sabida haka zuwa zakayi mu koma Abuja, idan nemanta kakeso aje semuje da soja yanda Dad amma kafito bakako nemi adu'ar iyaye ba ka ganta yaya? Ka gane ta aya? Shin kanada tabbacin taje garin nasu ne, karka manta Lawuri fa ko nan garin bata san sunan saba, kai koda ta sani ma tayaya zata zo nan? Ya zata iso har nan garin? Kay8 tunani mana, kokai aka bari kazonan da k'afa ta ina zaka fara? Karfa ka bari soyayya ta rufe maka ido, tasha makance ka daga ganin gaskia me amfaninka, ka nutsu kayi adu'a ka kuma nemeta a garin abuja da kewaye amma sam bata wannan Doguwar hanyar ba, nasan kalar tunaninka wannan ne ya sanya na biyoka tanan hanyar, agarin na kwana senawa nan hanyar sakkon asubahi, ina me fatar ganin ka dikda na kula sam ka manta da tracker dake jikin motarka dakuma agogon hannunka daka iya sanya nasan location naka aduk inda kake, hotel d'inma ban nem bane dana iso sabida gajiya" Nisawa Abu huraira yae


"To yanzu Al-Hussain kana ganin zamu sameta a gari?" Murmushi yae


"Nama alk'arin zanyi amfani da ilimina da basirata dakuma k'arfin ikon danake dashi wurin ganin na nemota, idan har kaga ban nemotaba Allah ya yanke had'uwa tsakaninmu da ita ne na har abada" Sauke nannauyan ajiyan zuciya yae


"Yanzu gida zamu koma?" Murmushi Sufyan yae


"Da jirgi ba,dama na mana booking akwai wani inyamuri abokina ne, ana garin yake zamu bar masa motocin nan, zanje inji nawa zamu bashi ya kawo mana su abuja"


"Baka gudun ya gudu dasu?" Murmushi yae


"Daze gudu dasu da bazan bashiba ai, yanada motocin jigila ne yana jarkar mota kuma ya siya ya aikama duk garin da kake, yanada qwararrun direbobi zasu kai mana ne mu biyasu" murmushi shima yae


"Kasanni da mota subi a hankali ko gogewa tae bazan k'ara hawanta ba ka sani" Girgiza kai Abu sufyan yae


Zaka rantse da Allah huraira me sauk'in kai ne amma komai nashi na gayu ne se high taste yafi kula da mota akan jikin sama, Abu huraira ze iya maka komai amma banda aron mota sam shi ko wankin mota yakai seya kasa ya tsare, tsaftar sa kuwa har takaici take baiwa sufyan wani zubin dukda shima ba baya bane gun tsaftar.


*********
Abun sam bewa mahaifiyar su dad'i ba tun faruwar abun take cikin fushi da general, shikuwa yayi biris da ita har gashi yau kwana 8,abin mamaki Kyautar Allah duk basu kwana a gidaba, to ina sukaje? Hakan ba sabon su bane ba, me sukayi hakan kenan? Ina sukaje? Yanzu k'arfe d'aya na rana? .....sallamar sune ya katse mata tunaninta gaba d'aya ta d'ago a hargitse tana kallonsu, dukkaninsu tashin hankali suka shiga sunsan halin mom, zuwa sukai kusa da ita suka gayar da ita ta ansa cikin sakin fuska abinda ya masu mamaki kenan, batako tambayi inda sukaje ba, ta mik'e tabar wurin, kallon juna sukayi kafin suma su mik'e gwiwa a sace zuwa cikin gidan a b'angaren su.


************
Tun jiya ake zuba sanarwa amma har yau babu wanda yace yasan fuskokin mutane biyu, Ayusher dukta shiga damuwa, wayan Sufyan ta kuma kira, bayan sun gaisa tace cikin sanyin jiki


"Pure heart beyi working ba wlhy, har yanzu fa shiru babu wanda yace ya sansu ma" nisawa yae ya kalli Abu huraira dayake kwance ya lumshe idansa kamar me bacci amma a zahiri ba baccin yake ba yace


"Ina kince d'ayar karaya ce kawai, a baki ake karaya ne? Tayi magana mana" Nisawa tae


"Yare takeyi kamar yarbanci kamar kuma wani abu daban" zabura yae ya kalli Abu huraira yaga bashi yake kallo ba yace


"Kina ina yanzu?"


"Ina asibitin mu" ta bashi amsa a tak'aice kashe wayar yae ya fice daga d'akin cikin hanzari, huraira yana wata duniyar dabemasan wainar da ake toyawa ba tukunna....


Kallon patient d'in yae cikin nutsuwa hankalinsa duk se ya tashi yace yana kallon Ayusher


"Ayush baki gane wannan yarinyar ba wai?" Kallon mamaki ta masa


"Ni ina zan santa bare na gane ta?" Shafar sumar kansa yae


"Yarinyar dakika tarar agidan mu ta taka glass d'innan, danakewa hanifer masifa akanta" waro ido tae


"Are you serious?"


"Wlhy itace Ayush, kwana nawa muna nemanta, ni banmasan yanda akai ban gane ba tun sanda kika gayan" nisawa tae


"Alhamdulillah yaa Allah, hankalina a tashe yake tun faruwar al'amarin, bansan madafa ba" yafita shiga farin ciki me yawa, daga bisani kuma ya shiga fargabar sanarwa Abu Huraira, ko shakka babu yanawa Lawuri Son so, duk kalaman daya fad'a dad'in baki ne kurin wa d'an uwansa bayaji ze iya sadaukar masa da soyayyar dayakewa Lawuri koda dawowa tayi arayuwar su kowa ya fanshi kansa agunta kawai, da wannan ya yanke shawarar barin hakan sirri na sanin makomarta.


"Ayusher akwai taimakon danakeso kimun" kallon sa tae cikin mamaki


"Name pure heart"


Murmushi yae


"Zanje da kaina nawa mom mgana akan yaran, muso muke su karb'i musulunci amma mom bataso ta barsu agidan mu, koda zata taimaka idan sunji sauk'i sesu xauna gunku, yaran danake gaya miki ne fa munzo dasu a hatsarin damuka shiga,kuma wannan ta taimakemu sosai, and please karta gayawa mom suna gunku" Nisawa tae


"Pure heart dan wannan sekaje gun mom, karka damu bazan mace mata su bane, kurin zan dakatar da sanarwar kuma inshaa Allah zan nuna bamu samu iyayen suba zan rik'esu zuwa time daya dace kake kuma buk'atar su" godiya yae mata sukai sallama ya yafi.


A hanya se murna yake akan ya samu Lawuri, ya k'udirta kuwa baze tab'a gayawa Abu huraira inda suke na.


************
*Bayan kwana biyar*


D'awai niya sosai yake dasu har lokacin Lawuri se adu'a amma jiyan anyi nasara ta farfad'o, Dr. jalal shine mutum na farko datayi karo dashi tun bayan data farfad'o d'in, iyakar bincikensa akanta kuwa ya gano ta samu total lost of memory!!!!! Wanda tayi matuk'ar bashi tausayi duba da yanayin shekarunta.


Yarinyar ta tsaya masa arai so yake ya taimaketa ta dawo daidai amma waze taimakeshi aikata hakan? Irin wannan fa dole se akwai wanda ya sanka cen baya, wacce suke tare ma tana samun sauk'i amma magana da ita ma wahala ne, shi kuwa da kanshi yakeso ya taimaketa, da kanshi yakeso ya daidaita tunanin ta zuwa duniyar ta ta baya, taji jiki ainun, da wannan yanemi Ayusher.


Mom Nu'aiym.
[11/20, 3:01 PM] Maamah twins๐Ÿ’•โค: *๐Ÿ‡๐Ÿ‡DOGUWAR HANYA....๐Ÿ‡๐Ÿ‡*


*Billy Galadanchi*


*Haske writer's Association(home of expert and perfect writer's)*


Litattafan mu ba free bane, na kud'ine dan Allah idan baki siyaba karki karanta,idan kuma kina buqatar daya daga ciki ki nemi wannan lambar 07084161619.


Kamar da wasa (ummie Aisha)
Sultan merah (fatima zarah)
Doguwar hanya (Billy galadanchi)
Zafin Rana (Ayusher muhammad)
Sanadiyya (Maman khadyy).


18
Jinjina kai Sufyan yae bayan ya gama jin bayanin Dr jalal


"Duk zan iya likita nidai fatana ta dawo cikin hankalinta kawai komai nata ya zama normal"


"Idan akayi hakan zamu samu sassauci kaga tana samun difficulties wurin magana so dole semun d'auki mataki wannan ciwon maya buk'atar magani sedai ayita kulawa dasu ana koyar dasu abubuwa masu yawa" Sosai sufyan yae godiya kafin su rabu.


***********
Murna awurin sufyan ba'a magana yana fatar karma memory d'in nata ya dawo sabida yanaso tasoshi shishi kad'ai batare da wani ba, yanaso ta manta da wani Abu Hurairah tun a wancen garin ya kula cewar tanason huraira shikuma baya fatan taso waninsa.


Zama yae da kanshi yake bata abinci abaki, se murmushi yake zuba mata yana mata magana da hannu, kallonsa kurin takeyi bata fahim tarsa sam, language data iya shibawai ya iya bane ba ruwa ya bata tasha sannan yace


"Lawuri?" Kallonsa takeyi sam bata gane ko waye bama tunaninta ya tsaya cak ta gagara tunanin komai ita kam


"Sannu" shine abinda ya furta yana murmushi, ta gane kalmar tasan ta amma bata tunano komai ba, TV ya kunna ya zauna yana kallo yana nazarin kalmomin yarbanci daya soma koya a wurin Dawood da takarda da biro a hannun sa, so yake yariqa yin magana da ita shishi kad'ai, ya iya yaren su sabida kota kwana idan ma memory d'inta ya dawo shine abu huraira shi takejin yarensa kawai.....


"Al-Hussain ina cikin tashin hankali, yaran nanfa hakk'in su yana kanmu, mune fa mukazo dasu wannan Doguwar hanyar batare da munyi wani dogon tunaniba, yanzu kana ganin daidai ne ace mu k'yalesu? Kana ganin daidaine mu fita sha'anin su bamusan hannun wa suka fad'a ba? Bamusan inda suke ba bayan ni dakai munada tabbacin cewar yaran nan basusan hanyar garin suba, ni inaga bamuwa kanmu adalci ba bakuma mu musuba" Nisawa yae yana me kallon yayan nasa


"Twin ya kakeso muyi? Neman mutum a fad'in Nigeria nan ba abu bane daze mana sauk'i, munyi iyakar yinmu mesa newai kake k'ok'arin jefa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login