Showing 1 words to 3000 words out of 19982 words

Chapter 1 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf

1

Shaihu Umar

Na

Sir. Abubakar Tafawa Balewa



Shiryawa
Bukar Mada

2


Shaihu Umar

ALLAH shi ne Sarki mafi ɗaukaka daga dukan Sarakuna, shi ne mafi tsarki daga dukan abubuwa,
shi ne kuma Sarki wanda ba shi da makamanci. A kusa da Birnin Bauchi akwai wani ɗan gari ana
kiransa Rauta. A cikin wannan ɗan gari, ya kasance akwai wani malami ma'abucin hankali,
masanin taurari da Alƙur'ani da littattafai, kuma mariƙin addini. Shi malamin nan yana cikin
mutane na duniya waɗanda Allah ya yi musu baiwa ta wajen fahintar abubuwa. Sunansa Shaihu
Umar. Saboda tsananin saninsa da kuma hankalinsa, har labarinsa ya, isa ƙasashe masu nisa
daga inda ya ke. Mutane suka yi ta fitowa daga ƙasashe, suna ta tahowa gare shi domin neman
sani. Kafin a jima kaɗan sai ya zama mutane da su ke zuwa gare shi suka taru suka yi yawa, har
suka rasa wajen yin gidaje, Saboda haka ya zama tilas ga waɗansu su nemi gidaje a cikin 'yan
ƙananan ƙauyuka na kusa da Rauta.

Duk waɗanda su ke ɗaukar karatu a wajen Shaihu Umar ba su taɓa ganin wani tashin hankali
game da shi ba, kuma ba su taɓa jin ranar da suka zo karatu ya ce musu ya gaji ba, sai ko in ba
shi da lafiya. Ko rashin lafiya ne ya same shi, in ba mai tsanani ba, Ialle zai zo ya ba da karatu. Shi
Shaihu Umar mutum ne wanda ya yi nisa, ba za a sami kamarsa ba. Kowane irin mugun abu ne
ya same shi sai ya kan ce, “Allah shi ne mai sawwaƙewa." Bai taɓa fushi ba, kullum fuska tasa a
sake ta ke, bai taɓa shiga magana wacce ba ta gamo da shi ba, ba ya gardama da kowa balle
wata ‘yar tankiya ta tashi game da shi. Kai, don wannan hali nasa, har ya zama duk ƙasar babu
wanda ya ke haye masa, kuma mutane da yawa sai suka fara cewa, “Lalle mutumin nan ba kawai
ba, waliyi ne".

Wata rana wajen goshin la'asar bayan Shaihu Umar ya ba da karatu ga almajiransa, suna zaune
suna taɗin duniya, sai wani almajirinsa ya tambaye shi cewa, “Ya mu'allim ni dai ina so in yi
maka wata 'yar ƙaramar tambaya, amma ina shakka a raina kada ka yi zaton wai ko raini ne ya sa
haka."

3

Shaihu Umar ya amsa masa, "Ai hankali bai taɓa cika ba sai game da tambaya, mutum kuma ba
duka ya ke zamowa ya san kome ba. Saboda haka tambayi dukan abin da kake bukata, kada
kuwa ka yi shakkar kome a cikin ranka. Ni kuwa Allah ya sa na san abin nan da za ka tambaye ni."

Matambayin nan ya ce, "Gafarta malam, abin da na ke buƙata in ji game da kai abu biyu ne. Na
ɗaya dai, ka gaya mini inda ka fito, ka kuma bayyana mini Iabarin ƙasarku. Yadda ka ke ɗin nan
duk mutanen ƙasarku haka su ke ? Don ni dai Lalle kana ba ni mamaki da yawa. Ba kuma ni kaɗai
ba, dukan wanda ya san ka zai yi mamakinka. Na biyu, ina buƙata ka faɗa mini asalinka, domin
na ga kai ba ka yi kama da mutanen ƙasarmu ba. Ga shi dai kana da sani da lafazi irin na
Larabawa, amma na ga ba ka kai kanka can ba."

Umar ya amsa masa, “Haƙiƙa kuwa ka yi mini tambayoyi masu ma‘ana, waɗanda zan iya ba ka
amsarsu ba da tantama ba. Kuma lalle ka tambayi labari mai tsawo, mai ban mamaki da tausayi
ga dukan wanda ya ji. Yanzu zan yi ƙoƙari in ba ka labarin ƙasarmu da asalina, kuma da na
yawace-yawace waɗanda na yi, da wahalar da na sha kafin in iso nan garinku.”

Ni Mutumin Kagara Ne

DA can ni mutumin ƙasar nan ne, in ji Shaihu Umar, amma ko da ya ke haka ban girma na yi
wayo a ƙasan nan ba. A can ƙasar Larabawa na girma. Ni dai tun fil azal mutumin wata ƙasa ce
kusa da Bida. Sunan garimmu Kagara. Ubana kuwa wani mutum ne dogo, fari sana’arsa dukanci.
Uwata mutumiyar Fatika ce. Yayin da a ke da cikina, ubana ya rasu, ya bar mini gadon shanu
shida, da tumaki uku, da goɗiya tasa wacce ya ke hawa, sa’an nan kuma ita goɗiyan nan tana da
ciki. Su waɗannan abubuwa duka sai aka danƙa su a hannun gyatumata, aka ce mata ta riƙe
waɗannan sai sa'ad da Allah ya sa ta haihu, domin kayan ɗanta ne, kuma shi mijin nan nata ba
shi da waɗansu dangi da za su ci gadonsa.

Ana nan ana nan, ran nan sai aka haife ni, na ksasance namiji. Da lokacin suna ya yi, sai uwata ta
sa aka kama mata ɗaya daga cikin ragunan nan nawa, aka yanka, aka raɗa mini suna Umar.
Muna nan dai, yayin da na zama ɗan shekara biyu, watau lokacin yaye, sai kakata ta wajen uba

4

ta karɓe ni domin ta yaye ni. Muka zauna tare da ita har ya zuwa lokacin da uwata ta yi buƙatan
yin aure.

Sai uwata ta ce wa kakata, “To, kin ga ba ni da wani ɗanuwa a nan gari, daga ke sai wannan
yaro, yanzu ina son aure, ga shi kuwa masu nemana da aure da yawa sun zaburo, sun ce lalle sai
a ɗaura aure da wanda na fi so. Na kawo miki shawara, wane da wane su ne su ke nemana,
amma fa har yanzu ban fid da gwani ba, ina so in ji abin da kika ce tukuna. A cikinsu kuwa akwai
wani bafade na kusa da Sarki ainun wai shi Makau."

Da dai kakata ta ji sunan Makau a cikin maneman nan sai ta ce, “Ke, ’yan nan, ai Allah ya yi miki
gyaɗar dogo ! Ga mai gani sarai, ki auri makaho? Ni dai in a shawarata ce babu wanda za ki aura
sai Makau. Na san shi mutum ne mai kunya wanda ba shi da ƙaranta ko kaɗan. Shi kam lalle in
kin aure shi gidanki lafiya".

Uwata sai ta yarda da wannan shawara, kashegari aka ɗaura aure, aka kuma ba da ranar da za ta
tare. Da lokaci ya zo sai uwata ta tare ɗakinta, ni kuma ina tare da kakata. Muna cikin jin daɗin
zama da kakata, sai ran nan ciwon ajali ya kama ta. Da dai ta ga ciwo babu dama sai ta aika aka
kirawo gyatumata ta yi mata kashedi cewa, "Kin ga dai ban yi tsammani zan tashi daga wannan
ciwo ba. Saboda haka ina so ki ɗauki wannan yaro, ki tafi da shi wurinki, domin ba ni son in gan
shi yana kuka ko kaɗan, raina ya kan ɓaci da yawa a kan haka"

Gyatumata ta ce, “To”.

Bayan ta fita kaɗan sai kakata ta cika, mutane suka taru da yawa, aka yi mata salla, aka kai ta
kushewarta.

Bayan wannan ya ƙare, muna zaune cikin kyakkyawan hali tare da uwata a gidan Makau, sai ran
nan Sarki ya sa aka yi kiran dukan fadawansa. Da suka taru ya ce musu, “Ba wani abu ne ya sa na
kira ku ba, abin da na ke so game da ku shi ne ku yi shiri ku tafi ku yiwo mini hari a Ƙasar Gwari.

5

Ina da wata babbar buƙata ne, saboda haka ina son ku yi shiri maza ku tafi domin ku komo da
hanzari".

Da fadawan nan suka ji wannan magana ta Sarki duka sai suka zama kamar mahaukata sabili da
farin ciki, suka yi ta murna suna cewa, “Da ma mai neman kuka, balle an jefe shi da kashin awaki
!" Dalilin farin cikinsu kuwa shi ne don ka sani a wajen harin nan za su yi samu da yawa na
dabbobi har zuwa bayi. Kuma in sun dawo Sarki zai sam musu rubu'i daga cikin abin da suka
samo. Ko wataƙila im mutum ya kama bayi uku ne, sai Sarki ya ɗauki biyu daga ciki, shi kuma
abar shi da ɗaya.

Wannan hari kuwa da Sarki ya shirya, dalilinsa wai don yana son ya sami waɗansu bayi ne
waɗanda zai gama da nasa ya aika da su Kano, domin a sayo masa tufafi da kayan doki, waɗansu
kuwa ya aika da su Bida domin a sayo masa bindigogi

A cikin baraden nan waɗanda Sarki ya zaɓa zuwa hari akwai Makau. Da lokacin tashinsu ya zo,
bayan Sarki ya nema musu sa'a wurin wani malami sai Makau ya shigo cikin gida ya tara iyalinsa
duka, ya ce musu, “To, yanzu kun ga zan tafi hari a Ƙasar Gwari ban san sa'ad da zan dawo ba.
Ko a kashe ni a can Allahu a'alamu. Saboda haka ina so mu yi ban kwana, ku yafe ni abin da na yi
muku duka, domin mutum na duniya duka in kana tare da shi, lalle wata rana za ka baƙanta
masa zuciya"

lyalinsa duka sai suka amsa gaba ɗaya suka ce, "Wallahi tallahi, mu dai babu abin da ka yi mana
na ɓacin rai. Muna fata ka tafi lafiya, ka dawo lafiya." Dukammu muka fashe da kuka, babu mai
jin na ɗan'uwansa.

Dukan masu zuwa harin nan suka yi ta shiri, asubar fari suka fita suka mika zuwa cikin Kasar
Gwari. Suka yi ta tafiya har suka isa wani dan kauye na Arna a wata kwaifar dutse cikin kurmi. Da
isarsu wurin duk suka sauka daga kan dawakansu, suka yi kwance a gindin itatuwa masu duhu,
inda babu wanda zai iya ganinsu. A lokacin nan kuwa ruwan sama ya fara sauka, dukan manoma
za su yi ta gyaran gonakinsu. Su kuwa arnan nan babu yadda za su yi su shuka wani amfani
wanda zai ishe su ci har shekara, saboda haka sai su fito daga cikin garuruwansu, su sauko kasa

6

su shimfida gonaki a sarari. Amma duk da haka ba su da damar su yi aikin gonaki sosai ba
saboda tsoron ‘yan hari.

Yayin da 'yan hari suka isa kauyen nan sai suka buya a bakin gonaki. Da sassafe wajen goshin
asalatu, sai arna suka fara fitowa daga kauyukansu, suna zuwa gonakinsu. 'Yan hari kuwa suna
kwance kurum, suna ganin dukan abin da su ke yi. Suka bari har dukan mutane suka fito. Bayan
sun sake sosai suna ta aiki, suna tsammani babu wani abin da zai faru gare su, 'yan hari suka
fada musu gaba daya, suka kama mata da maza har da kananan yara. Kafin arnan su ankara 'yan
hari sun riga sun yi musu ta'adi. Nan da nan sai arnan suka fara fitowa da shirin yaki domin su
kwaci 'yan'uwansu da aka kame. Af ! Kafin su shirya maharan sun yi nisa. Suka yi ta binsu, amma
babu dama su same su, na gaba ya yi gaba, na baya sai labari.

An Bata Tsakanin Sarki Da Makau

YAYIN da maharan suka ga sun kubuta, sai suka kama hanya sosai, domin an sani ba za su bi
hanya ba don kada Arna su iske su. Da dai suka fada hanya sosai, sai suka yi ta hanzari, kowa
yana ce wa dan'uwansa, "Sai ka zo." Suna ta tafiya har Allah ya sa suka iso gida lafiya. Da suka
shigo cikin gari sai kowa ya kama hanyar zuwa fada, tare da abin da ya samo daga wajen hari.
Dukansu daga mai bayi biyu sai mai uku har ma akwai mai hudu. Kowa daga cikinsu ya gabatar
wa Sarki da abin da ya samu. Sai Makau kadai. Shi Makau da ya dawo bai bi ta fada ba, sai ya
nufi gidansa. Amma wannan ba da nufin wani abu ba ne.

Da dukan mutane suka hallara, kowa ya ba da abin da ya kawo, sai Sarki ya ce, “Kai, ina Makau ?
Ko an kashe shi ne a can ku ke boye mini?"

Jama'a duka suka amsa, “A’ a ! Ranka ya dade, ai ka san halin mntanen duniya. Mu da ma mun yi
shiru ne kawai tun da farko da muka ga ka dauke shi, mu ga yadda za ku kare. Domin mun sani
duk wanda aka ba shi amana ya ci lalle Allah yana kama shi, balle ma kamar kai da Makau wanda
ya ke ka yarje masa kome naka. Bari dai mu fede maka biri har wutsiya, a cikin garin nan ba ka
taba samun wanda ya ke cin amanarka kamarsa ba. Ai Makau ne ya ke fallasa ka a wajan
talakawa da ka ke ganin suna girman kan nan yanzu. Kuma babu asirin da za ka yi da shi

7

wadansu ba su ji ba. Ka gani tun da muka fita zuwa harin nan har muka dawo bawan Allah nan
bai bar zaginka ba, a kan haka ma har Sarkin Zagi ya yi hushi ya zare takobi zai yanke kansa, sai
da barde ya ba shi hakuri. Yanzu ma abin da ya sa ba ka gan shi ba a nan, ya bi ta gidansa ne
domin ya boye wadansu daga cikin bayin da ya samo, gama dai bawa hudu ya kama, mata biyu
duka yara, da kuma yara maza biyu, amma dayan ya isa misali. Amma dai ba mu sani ba, ma ga
abin da zai kawo."

Da Sarkin ya ji wadannan maganganu sai ya ce, "Daidai, amma Makau ya kyauta."

Bayan jimawa kadan, sai Makau ya tinkaro da 'yan bayinsa guda biyu wadanda ya kamo. Yana
zuwa kawai da holokon ciki, bai san abin' da 'yan'uwansa fadawa suka kulla masa ba. Bayin nan
kuwa da ya zo da su guda biyu su ne da ma abin da ya samu tun asali, cewa ya kamo bayi hudu
karyar magabta ce. Da Makau ya kusanci kofar fada sai ya hango Sarki yana zaune a waje, ana ta
fadanci. Da dai fadawa suka gan shi, sai suka fara cewa, “Ai ga Makau can yana zuwa da bayi
biyu kawai, watau ya boye biyun ne ?" Da Makau ya iso wurin da Sarki ya ke ya fadi ya yi
gaisuwa, amma Sarki bai amsa ba. Duk jama'ar wurin babu wanda ya ce masa ci kanka. Kowa dai
sai kallonsa kawai ya ke yi, mahassadansa suna ta murna sai ka ce wadanda aka ba su gashin
tozo.

Da aka jima kadan Sarki ya ce, "Makau, sai yanzu ka iso?"

Sai ya amsa ya ce, “A’a ranka ya dade, na bi ta gida ne domin in daure doki, in kuma sake shiga,
sa'an nan in iso gare ka."

Sa'an nan Sarki ya ce, "To, bayi nawa ka samu ?"

Makau ya ce, “Biyu.”

8

Sarki ya ce, "Haka ne. Lalle ne bayi biyu ka samu kadai? Ka yarda in na yi bincike na iske ba bayi
biyu ka samu ba, in yi maka abin da na so duka ?"

Makau ya ce, "Wallahi na yarda."

Da suka gama wannan magana, sai Sarki ya kira Sarkin Zagi, ya tambaye shi cewa, “Bayi nawa ne
Makau ya samo daga wurin hari ?”

Sarkin Zagi da ma yana Allah Allah wannan abu ya auku. sai ya ce, "Bayi hudu, amma da biyu ya
iso cikin garin nan domin ya sayad da biyun a hanya ga wani ayari na Kanawa wadanda za su tafi
daukar daddawa a kasar Bauci. "

Sarki ya ce, “To, ka ji, Makau".

Shi kuma ya amsa, "Ranka ya dade, yanzu ni ai ba ni da ta cewa, domin wadannan mutane sun
riga sun yamutsa magana, babu sauran abin da zan shaida maka ka yarda da shi."

An Washe Gidan Makau

Sai Sarki ya fusata, ya ta da fadawa ya ba su izni su je su washe gidan Makau, kada su bar masa
kome ko da tabarma. Fadawan suka tafi, suka washe gidan kaf, hatta ciyawar da aka yi jinkar
dakuna da ita sai da aka yaye. Kuma yana da wadansu 'yan shanu a wani dan kauye na kusa da
gari, nan da nan sai aka sa wani ya je ya zo da su. Da aka tafi za a zo da shanun nan na Makau,
sai aka hado da nawa wadanda ubana ya bar mini gado, duk da tumakina, da godiyata, da danta.
Bayan an gama washe-washen nan duka, sai aka hada kayan aka kawo wurin Sarki.

Da aka kawo sai Makau ya tashi ya ce wa Sarki, “Ranka ya dade, ina rokon a cikin kayan nan,
akwai wadansu wadanda su ke ba nawa ba, kamar godiyan nan da danta, da tumaki, da kuma

9

wadansu daga cikin shanun. Su wadannan na wani yaro ne maraya wanda na auro uwa tasa.
Abin da na ke roko a fid da kayan marayan nan a mayar masa."

Da jin haka sai fadawa suka dauka gaba daya, "Mhm, kun ji ya fara irin karyan nan tasa ! Ina ka
ga wata dukiyar maraya har daza ka ce tana wurinka? Allah ya dade da Sarki, karya ya ke yi. Ita
dukiyar marayan da ya ke fadi ba wurinsa ta ke ba, tana wajen uwar yaro, ita ta san inda ta kai
abinta.” (A lokacin ina dan yaro karami babu wayo, balle in san abin da a ke yi. Ni dai kawai sa'ad
da a ke washe gidammu, na ga iyayena suna kuka).

Nan da nan ba a yi ma ko da wani dam bincike ba, sai Sarki ya yarda da maganan nan da
fadawansa suka gaya masa. Bayan wannan ta kare, sai ya ce wa Makau, “To, ka gani wannan shi
ne sakamako wanda ka samu daga Allah, domin cin amanata da ka ke yi bayan na amince da kai.
Kuma ni yanzu ba zan ce maka wani abu ba, abin nan da aka yi maka ma ya isa. Bayan wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login