Showing 15001 words to 18000 words out of 19982 words

Chapter 6 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf

zo da wadansu takardu warka biyu na Alkur’ani
ya ba ni in karanta domin shaida. Kowa fa sai ya ja ya yi shiru, aka kasa kunne kawai, ni kuma na
fara karatu. Na karance takardun nan sarai, babu ko dan garma-garma. Da na gama sai duka
wurin aka dauka Alhamdu Lillahi. Aka yi mini addu'a, sa’an nan aka shiga rabon abinci.

Bayan na sake sauke Alkur’ani da kwana kadan sai maigidana Abdulkarim ya kawo wadansu
littattafan ilmi ya ba ni, game da wadansu kuma na addu’o’i da na magunguna. Na karba na tafi
da su wurin Shaihu Mas’ud. Yayin da na kai masa ya karba ya zuba bisa shimfidarsa, ya dauko
daya ciki wai shi Ashmawi ya ba ni, ya ce da shi zan fara, domin kuwa shi ne littafi na farko
wanda ya ke koya wa mutum batun addini sosai. Na Shiga wannan littafi, kafin a ce me na rigaya
na sauke. Kafin 'yan shekaru kadan sai na zama kusan na biyu bayan Shaihu Mas’ud a Birnin Ber
Kufa. Daga nan fa sai mutane suka fara kirana Shaihu Umar. Mutane da yawa daga biranen
Masar suna zuwa su ziyarce ni. In sun zo sai su yi mamaki cewa ga ni Baki, amma Allah ya ba ni
basira da fahimta mayawaita. Ana cikin haka sai Shaihu Mas’ud ya rasu, ba wata tantama sai aka
sa ni a matsayinsa na limanci, dukan almajiransa kuma ya zama ni na na ke ba su karatu.

Gyatumata Ta Tafi Nemana

AMMA a can kasarmu gyatumata tun da aka ba ta labarin an sace ni hankalinta bai kwanta ba da
kome na duniya. Yayin da duk ta zauna ita daya sai ta rika fadi a cikin ranta cewa in Allah ya
yarda garin da duk na ke sai ta je. Tun da muka rabu ba ta ci abinci ya zauna mata ba. Ta kare, ta

39

rame ta zama fara sol kamar fatalwa, duk ta fita haibarta. Makau ya yi mata abu da yawa domin
ta manta da tunanina, amma babu dama, har dai ya gaji ya daina.

Ran nan fa bayan na rabu da ita kamar shekara daya, sai ta tashi ta ce wa Makau ya ba ta izni ta
je duk inda na ke cikin duniyan nan ta dubo ni. Da farko Makau bai yarda ba, amma da ta
tsananta ya yarda. Ya kawo kudi da tufafi masu yawa ya ba ta, ta tashi ta tafi Kano. Da isowarta
birni, sai ta tambayi gidan Gumuzu, aka kai ta ta sauka. Ta tambaye shi labarin inda na ke ya
gaya mata, bai boye mata kome ba. Ya gaya mata sunan kasar da na ke ciki, da garin, da sunan
maigidana. Da ta ji wannan labari ta ajiye zuciya, ta yi hamdala, sa'an nan ta tambaye shi yadda
za ta yi ta tafi can inda na ke.

Gumuzu ya amsa mata cewa, “Lalle kin zo cikin sa'a, domin wadansu ayari za su tashi zuwa can
kafin kwana uku. Amma fa ayarin kashi biyu ne, daya za su tafi Murzuk, daya kuwa inda danki ya
ke."

Bayan sun yi wannan magana da kwana biyu, sai ta tashi ta tafi kasuwa tana tambayar inda ayari
masu tashi gobe su ke. Aka nuna mata wajen ayarin masu zuwa Murzuk. To, a cikin ayarin kuwa
akwai wani attajiri na Birnin Kano wanda zai tafi can wai shi Ado. Da zuwanta wajen da ayarin
nan ya ke, sai ta tafi gabansa ta durkusa, tana tambayarsa zancen tashi. Shi kuma ya gaya mata
gobe, sa'an nan ya tambaye ta, “Ke ma za ki shiga cikin tafiyar ne ?"

Ta amsa masa, “I, ina so ne inje in sami dana wanda ya ke a wani gari wai shi Ber Kufa cikin kasar
Masar."

Da Ado ya ji wannan, sai ya kulla a ransa ya cuci gyatumata su tafi tare, ya mayar da ita Kamar
matarsa, a cikin matarsa kuwa kuyangarsa. Ya ce mata, “To, ai wannan daidai ne, sai ki je gida ki
debo kayanki. Amma dai Allah ya yi maki sa'a tun da ya ke kin samu ina cikin wannan tafiya. Sai
ki zo ki zauna tare da ni, har sa'ad da Allah ya kai mu can, gama ta garin da kika fadi ta nan ne za
mu bi."

40

Da uwata ta ji wannan magana sai ta koma masaukinta, ta debo 'yan kayanta ta danka masa a
hannu da cewa ta zama amanarsa da ya ke Allah ya hada su haka. Bayan ta kawo masa kaya da
yamma, da asussuba suka tashi. Suka yi ta tafiya, su kwana wannan gari yau, gobe su tashi, da
haka har suka isa Ghat. A wurin fa suka yi niyyar kwanaki da dama sabili da ciniki. Har yanzu
uwata ba ta san abin da Ado ya ke nufi da ita ba. Sauran mutane kuwa da suka gan ta tare da shi
suka zaci mata tasa ce, domin kuwa sun ga a kan hanya yana nuna alamar yana kishinta.

Ana kamar gobe za su tashi, ran nan Ado ya tafi kasuwa domin ya sayo wadansu kayan guzuri,
sai uwata ta sami wata Bakanuwa baiwar wani Balarabe. Suka zauna suna tadi sai ta tambayi
uwata dalilin fitarta daga gida, ta gaya mata, kana sai waccan ta buga kirji ta ce mata, “Wayyo
Allah ! Ai wannan mutum ya batad da ke. Kun bar hanyar Masar tun daga birni."

Uwata ta yi kurum kawai ta rasa abin da za ta fadi. Zuwa can ta ce, “Kaico ! Ni wance yaya zan yi
? Ga shi mun yi tafiya mai nisa, babu damar in koma. Kudin da na fito da su daga gida ma sun
kare.”

Waccan ta ce, “ln kin ji shawarata kada ki nuna masa kin gane dabararsa, sai ran da Allah ya sa
kuka isa Murzuk, sa'an nan ki yi kararsa."

Sun lsa Murzuk

Ado ya dawo kasuwa wajen la'asar, da almuru ta yi sai suka tashi. Suka yi ta tafiya kwana da
kwanaki har ran nan Allah ya kai su Murzuk. Su Larabawan da ke cikin ayari kowa ya tafi gidansa,
Ado kuma ashe yana da gida a garin, sai ya dauki uwata da kayansa suka tafi can suka sauka.
Bayan sun kwana biyu sai Ado ya ce wa uwata, “Kada ki yi tsammani ba zan tafi da ke Ber Kufa
ba. Ina so ne in na gama ciko mu bi ta can sa'an nan mu koma gida tare.”

Ya yi ta magana, ita kuwa ba ta ce masa ko ci kanka ba, har ya kare ya yi shiru. Ta bar shi kurum,
sai da duk ta ga ya shirya komawa gida. kana ta ce, “Zan kai kararka wajen Alkali.”

41

Ado ya ce, “To, je ki wurin Alkalin mana, in gani ko ya iya kwace ki daga gare ni !“

Sai Ado ya fita abinsa, bai zame ba sai gidan Alkali, ya ce masa, “Wata baiwa ce na zo da ita daga
Kasar Hausa, amma na ga hankalinta ya tashi, in zan koma lalle ba za ta bi ni ba, gama ta ce za ta
yi kara ta gare ka."

Alkali ya ce, “To, na ji, Allah ya kawo ta.”

Ado na komawa gida, sai ta fita ta yi kararsa gidan Alkali. Alkali ya tambaye ta abin da ya kawo
ta. Ta ce, “lna karar wani mutum ne wai shi Ado, tun daga Kano ya ce in biyo shi zai kai ni wajen
dana, ga shi kuwa mun dade a hanya ban ga alamar zai kai ni ba. Ni kuwa ban san kowa a nan ba
wanda zai nuna mini hanya."

Alkali ya tambaye ta, “Wane gari danki ya ke ?”

Ta ce, “A Ber Kufa cikin Kasar Masar.”

Da Alkali ya ji haka, ya gane lalle ba ta da wayo, sai ya ce, “In don wannan ne abu ne mai sauki !
Sai ki zauna a gidana har in sami mai tafiya."

Da yamma ta yi Alkali ya aika aka kira Ado, ya kawo ’yan kudi ya ba shi ya ce, “Shi ke nan, koma
gida, magana ta kare. Ka sauka lafiya.”

Uwata tana nan gidan Alkali sai wani mutumin Tarabulus sunansa Ahmad ya gan ta, ya ce wa
Alkali yana so ya fanshe ta ya tafi da ita. Suka yi ciniki ya biya Alkali.

42

Alkali ya kira ta ya ce mata, “Ga shi na sami mutum wanda zai tafi da ke Ber Kufa zan hada ku da
shi ya kai ki inda danki ya ke.” Sai ta yi ta murna da farin ciki, ta yi masa godiya.

Kashegari suka tashi suka yi ta tafiya har ran nan Allah ya kai su Tarabulus da magariba. Shi
mutumin kuwa bai zame ko ina ba sai gidansa. Da gari ya waye ya kira babbar baiwarsa ya ce
mata, “Ga wata ’yar’uwa na samo miki, kome a ke yi ku yi tare.”

Da uwata ta ji haka, ta ce, “A‘a ! Maigida, kai da Alkalin Murzuk ya hado mu ka kai ni wurin dana,
sa’an nan ka ce ni baiwarka ce ?"

Ya ce, “Da dai ba haka ba ne, ni sayo ki na yi daga hannun Alkalin Murzuk.”

Sai ta ce, “Haka ne." Ta koma tana cewa, “Ni dai, Wance wahalar duniya ta same ni, saura Allah
ya kyauta.”

Ta yi zamanta, ba ta nuna kamar abin ya yi mata ciwo ba, har dai ta ga an saki jiki da ita sarai.
Ran nan aka aike ta kasuwa, sai ta zarce gidan Alkali ta yi kara. Alkali ya sa aka kirawo Ahmad. Da
ya zo ta mai da jawabi. Shi kuwa ya ce, “Karya ta ke yi, na sayo ta ne a hannun Alkalin Murzuk."

Alkali ya ce, “Shi ke nan, ki koma gidansa ki zauna. Zan yi takarda wurin Alkalin Murzuk, duk abin
da ya fadi idan amsa ta komo zan neme ku."

Da suka tashi Alkali ya rubuta takarda ya aika wa Alkalin Murzuk. Ana nan ana nan amsa ta
komo, Alkali ya sa aka kiran su, ya ce mata, “Na sami amsa daga Alkalin Murzuk, ya ce karya ki
ke yi ya sayar masa da ke ne. Sai ki tafi ki zauna, ki yi ta bauta.”

Ta ce wa Alkali, “Na ji,saura Allah ya isa tsakanimmu.” Ahmad ya yi sallama, ya tashi da
kuyangarsa.

43


Da suka koma gida ya ce mata, “Tun da ya ke kin nuna mini wannan hali, ba zan bar ki a sake ba,
zan daure ki har lokacin da kika sake halinki.” Ya sa aka buga mata mari. Dukan aikin gida mafi
tsanani, ita ta ke yi, abinci ma ba ya ba ta sai lokaci lokaci. lta kuma sabo da bakin ciki da zullumi
duk ta rame ta fita kamarta, in ta gama aiki sai ta yi zugum tana ta kuka. "

Da ya ga haka a ransa ya ce, “Wannan baiwa ta cika shegantaka, maganinta sai duka.” Kullum
kullum sai ya buge ta, amma duk da haka ba ta bar halinta ba. Haka ya yi ta yi mata azaba
misalin shekara daya. Amma ita dai duk wuyar da ta sha ba ta dame ta ba, kullum abin da ta ke
tunawa a ranta shi ne rashin saduwa da danta, har ta kare ta kasa aiki, sai yawan koke-koke.

Ubangijinta ya rasa abin da zai yi da ita ya ce, “Lalle in na bi ta wannan baiwar banza zan kashe
ta in yi hasarar kudina.” Ya kwance ta, amma duk da haka ranta ya ki kwanciya, sai dada
lalacewa ta ke yi.

Na Yi Mugun Mafarki

LOKACIN da ina tsakiya jin dadina a Ber Kufa, babu wani abin da ya sha min kai, na manta da
kome na kasar Hausa, sai wata rana bayan lisha na tashi na yi alwala, na dauko Alkur’ani ina
dubawa kamar al’adata ta kullum, sai barci ya share ni. Ban yi nisa cikin barci nan ba, sai na yi
mafarki, ga ni a kan dutse mai tsawo a bakin wani babban kogo. A cikin kogon akwai zakanya da
’yarta. Da ma muna tare da wadansu maharba ne masu farautar zaki. Kafin a jima kuwa da na
waiwaya sai na ga babu kowa a kan dutsen, sai ni daya da zakanya da ’yarta. Sai ga ta ta fito
daga kogon za ta tafi cikin daji ta yiwo farautar abinci. Bayan da ta tafi kadan, sai na ga ta dawo
ta shiga kogon. Da shigarta sai ta juyo a guje, tana raratu da gurnani, ashe ba ta ga ’yarta ba. Ta
yi ta zaga dutsen tana kuka, amma ba ta same ta ba. Kai, na yi dai ta ganin abubuwa barkatai. Da
na yi kusan farkawa, sai na ga gyatumata a bakin kogon zakanyar tana kiran sunana.

Da ganin wannan sai na firgita, na tashi a dimauce na gigice cikin tunanina. Na yi ta tuna wannan
mafarki a cikin raina, na dade ban bayyana wa kowa ba. Sai na kasa daurewa dai na tafi na gaya
wa maigidana Abdulkarim. Na ce masa, “Yau raina ya baci. Abin da na fi kawowa cikin zuciyata

44

dai shi ne uwata tana nemana kuma na ga duk hankalina ya koma cikin kasarmu, amma ban ga
yadda zan yi in gan ta ba har abada.”

Sai Abdulkarim ya ce, “Ni ma ina cikin tunanin yadda zan sami ikon komawa Kasar Hausa, domin
abin nan da mu ke rainawa ya gawurta, kasar Sudan duk ta lalace, jama’ar Mahdi sun rinjayi
Kasar, ban ga alamar Masar za ta sake samun iko a kansu ba. Ga shi kuwa duk kayan da na shirya
na sayarwa a can suna nan a ajiye a banza. Amma jiya na sami labari daga wani dan’uwana
wanda ya tafi ciniki a Tarabulus cewa ta can ayari su ke bi zuwa kasar Hausa, ita ma babbar
hanya ce, tafi wadda muka biyo da kyau. Domin haka abin da na yi shawara, in tafi bakin teku in
shiga jirgi zuwa Tarabulus, daga nan in sami ayari zuwa kasar Hausa. To, in Allah ya yarda zan
tafi da kai, kuma zan kai ka har garin da gyatumarka ta ke. Amma fa ina da sharadi daya wanda
za mu yi. Ina so ka yi mini alkawari cewa in mun tafi za mu dawo tare. In kuwa ka san in mun je
kasarku za ka yi mini halin ’yan duniya ne, ka gaya mini tun da wuri in sani. Ina so kuma ka
tabbata a cikin ranka, ko ka ce mini in ka je ba za ka dawo ba, shi ke nan, ba zaa matsa maka ba.
Domin ka sani na maishe ka dana, kuma kai ne na zuba wa ido."

Na kasa kunne kawai har Abdulkarim ya kare magana tasa, sa’an nan na ce masa, “Yau a
duniyan nan na sani ba ni da wani uba sai kai, a hannunka na girma, kai ka sa ni cikin mutane to,
ina ka ga hanyar da zan guje ka?Ai yanzu ka sani koda ya ke dai wani akan yi masa rana shi kuwa
ya kan yi dare ai ba irina ba ne. In na yi maka haka ai Allah ya tambaye ni."

Muka zauna muka yi ta tadi da Abdulkarim har kusan azahar, sa'an nan ya ce in tafi gida, domin
almajiraina sun fara taruwa. Da na tafi na sami masu daukar karatu sun taru da yawa a gindin
itaciyar kofar gidana, kowa ya bude littafinsa yana yin bita. Sai na shiga gida na yi wanka, sa‘an
nan na fito na ba su karatu. Bayan na gama ba da karatu sai muka tashi, kowa ya yi alwala, na
wuce gaba muka yi salla. Da muka idar sai na ba su labari cewa a cikin wannan wata da mu ke
Abdulkarim ya ce za mu tafi in dubu gida cikin yardar Allah. Da na fadi wannan ban ga sun yi
farin ciki ba. har na tambaye su dalili. Suka ce wai abin da su ke tsoro ko in na tafi gida ba zan
dawo ba. Na shaida musu wannan ba haka ba ko kadan.

Cikin watan azumin tsofaffi da kwana tara muka kare shiri muka tashi. Muka shiga jirgi, muka bi
igiyar kogi har muka kai Birnin Masar. Daga nan sai lskandariya, inda muka sami babban jirgi.
'Yan kwanaki kadan sai ga mu a Tarabulus.

45


Da muka sauka daga jirgi sai Abdulkarim ya tambayi wani mutum ya ce yana so ya fada masa ko
akwai wani a garin wanda ya saba ta'ammali da kasar Hausa.

Ya ce masa, “A garin nan dai babu wani mashahuri sai Ahmad.“ Ya tafi da mu gidansa. Ahmad ya
yi mana maraba, ya saukad da mu ya yi mana karimci mai yawa.

Bayan mun huta ran nan sai Abdulkarim ya zo suna tadi yana tambayarsa labarin hanya, Ahmad
ya gaya masa iyakar abin da ya sani. Abdulkarim ya ce, “ln Allah ya kai mu gobe zan tashi."

Sa'an nan Ahmad ya ce masa, “Ina da wata baiwa mutumiyar Hausa, wadda na sayo ta daga
Murzuk bara, amma ta cika mugun hali, tun ran da na sayo ta ba ta yi mini wani amfani ba sai
dada lalacewa ta ke yi sabo da tunanin kasarsu, in ba na rabu da ita yanzu ba sai in yi hasarar
kudina. Kai kuwa da ya ke cinikinka ne, ga shi kuma kana jin harshensu, watakila ka san
maganinta, ni dai in rabu da ita."

Abdulkarim ya ce, “Ina ta ke ?"

Ahmad ya shiga ya yi kiranta ta fito. Da ta fito sai Abdulkarim ya ce, "Sannunki !"

Da ta ji ya yi mata magana da harshenta, sai ta fadi gabansa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login