Showing 6001 words to 9000 words out of 19982 words
Chapter 3 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf
iyalinsa su zo.
Tanimu ya ce, “Daidai ne, wannan shi ne muhimmi, gama dattijo kamarka bai kamata ya zauna
babu iyali ba. Ni ma ina da wani yaro mutumin Kagara sunansa Isa, in ba ka da wanda za ka aika
sai shi ya tafi."
Da aka kwana biyu sai Makau ya shirya tafiyar Isa. Ya sayi riga wurin Tanimu ’yar madaka
kankararriya, ya kunshe ta cikin tsumma ya ba Isa, ya ce ya kai wa Sarkin Kagara. Kuma ya kawo
wadansu ’yan tsaraba na Zazzau, ya ce a kai wa wadansu abokansa a can. Kuma ya ba shi
marfiyu biyu, daya ya ba Sarkin Zagi, daya Sintili. Ya kawo ’yan kudi ya ba shi, ya ce ya rika saya
wa mata abinci kafin su iso. Kuma ya ce masa, “A cikin matana akwai wata yarinya mutumiyar
Fatika, da zan taso ta tambaye ni iznin ta je ta dubo iyayenta. To, in ka je ka samu ta tafi, ka bar
mata sako cewa ta yi maza ta same ni tare da 'yan'uwanta a nan. Kuma in tana zuwa ta zo da
danta maraya. Shi ke nan, Allah ya dawo da kai lafiya."
Ran da ya isa, bai zame ko ina ba sai fada. Ya tafi ya ba Sarki kyautar Makau, ya gaya masa abin
da ya ke bukata na zancen iyalinsa.
18
Sarki ya ce, “To, madalla, a kai shi gidan Makau ya sauka har kafin ran da iyalinsa suka shirya,
sa’an nan su tashi.“
Isa ya je ya sauka. Da la'asar ta yi sai ya aika wa Sarkin Zagi da Sintili da huhunan da Makau ya
aiko musu, ya kuma ba da sauran tsaraba ga mutanen da Makau ya aiko shi gare su, suka yi ta
murna. Bayan da Isa ya gama rabon wadannan kaya, sai ya shiga wajen iyalin Makau ya gaya
musu dalilin zuwansa gare su. Suka yi ta farin ciki sai ka ce wadanda suka fada cikin ruwan
Alkausara.
Sa'an nan Isa ya tambaye su, “Ina yarinyan nan mutumiyar Fatika, ko ta tafi ne ko ?“
Matan suka ce, “A’a, ga ta, da ma tana jiran aikensa ne."
Isa ya ce mata, “Makau ya ce ki tafi, amma ki hanzarta ki same shi a can. Kuma yayin da za ki tafi
sai ki je tare da danki.”
Ta ce wa Isa, “To, daidai ne, Allah ya sa muna da rai, da kuma rabon ganawa."
Iyalan Makau suka yi kwana hudu suna kintsawa, sa'an nan rana ta biyar Isa ya tafi ya yi sallama
da Sarki, kashegari suka tashi. Aka bam mu, ni da uwata, a Kagara. Bayan iyalan Makau sun
tashi, sai kuma gyatumata ta yi shirin tafiya Fatika. Ana gobe za ta tashi, sai ta danka ni ga wani
basakkwace sunansa Buhari, wanda ya ke makwabtaka da ubana mahaifi.
Tun da rana sai na ga uwata tana ta yawo a cikin gidaje, a ran nan ban yi tsammani ko bakin
ruwa ma ta sha sosai ba, domin ba ta zauna ba ko kadan a wuri daya, sai dawainiya ta ke yi
tsakanin gidajen kawayenta har dare ya yi. Bayan da ta gama yawace-yawacenta, sai ta dawo
19
gidan Buhari ta yi kwance tana ta kuka. Ni a lokacin nan babu abin da ya miskile ni ko kadan, sai
farin ciki na ke yi, domin a gidan na sami yara 'yan‘uwana wadanda mu ke wasa tare.
An Kai Umar Riko
Bayan da dare ya yi, gari ya yi shiru, sai uwata ta tashi ta tafi wurin daya daga cikin matan
Buhari, sunanta Amina wadda na ke dakinta, ta ce mata, “Amina, ina so mu yi ban kwana da ke
yanzu, domin ina so zan tashi tun kafin a kira salla. To, sai fa ki dauki hankuri, kin san halin
yaron, kullum abin da ya ke so ya yi in ba a bar shi ba sai ya yi kuka, amma idan ana barinsa ya yi
abin da ya so a gaba ba zai ji dadi ba. Ya kamata ki rika kwabonsa ko yaushe, kada kuwa ki kula
da cewa ai wannan yaro ba nawa ba ne, wallahi da ni da ke duk daya ne, tun da ya ke Allah ya
hada mu, kuma a kan amana mu ke zaune."
Amina ta ce,' “Lalle dukan abin da kika fadi daidai ne, kuma ina fata Allah ya ba ni wuyan
dauka.” Bayan wannan suka zauna suka yi ta tadi har mu yaran da ke dakinta muka yi barci.
Da suka jima kadan suna tadi, sai barci ya fara kama su, uwata ta tashi ta tafi ta kwanta, amma
ko runtsawa ba ta yi ba domin tsananin tunanin abubuwan da su ke kan hanya kafin ta isa gida,
da kuma tsoron da ta ke ji na wajen barina a garin da ya ke ba ni da dangin uwa balle na uba.
Tana cikin tunanin nan sai ta ji carar zakara, ta tashi ta dauki kayanta ta kama hanya. Ashe
kaddara ta riga fata. Ban sake ganinta ba sai bayan shekaru da yawa !
Wani Ya Sace Ni
DUKAN abin nan da ya auku ba ni da labari, ba kuwa ba ni da labari ba ne, don a sa’an nan ina da
wajen shekara hudu ne kawai. Tunda uwata ta tashi daga Kagara ban ga wani abin da ya sake ba
daga gare ni. Ina ci ina sha sosai, ga kuma yara wadanda mu ke wasa da su kullum. Ita Amina
kuwa, matar Buhari wacce na ke gare ta, ba ta taba nuna mini wani mugun hali ba. Kullum abin
da na yi duka daidai ne. In wani laifi na yi mata babba, yayin da ta zo za ta doke ni, in ta daga
hannu sai ta fasa, ta ce, “Allah Sarki, yaro wawa !” Ba ta son in rabu da ita ko kadan, kullum tana
20
son mu zauna tare. Kuma yayin da na yi wani wawan kiwo nan da nan sai hankalinta ya tashi. Ta
fita ta tafi gidajen yara wadanda ta san ina wasa da su, ta jawo ni.
Ran nan fa mun taru da yawa a kofar gidammu muna wasa, mu wajen yara tara, sai muka ga
wani mutum mai babbar riga da babban aljihu yana zuwa ta ind mu ke. Dukammu muka bar
wasa, muka zuba masa ido muna ta kallonsa har ya kawo gare mu.
Da ya iso wurimmu sai muka gaishe shi, "Sannu baba."
Shi kuma ya ce "Mai gidan na ciki ne "
Wani yaro daga cikimmu mai dan dama sai ya ce, "A'a, ya tafi bayan gari, amma zai dawo gobe."
Mutumin nan ya tsaya, ya yi ta kallommu muna Wasa, kana bayan zamani guda sai ya tambaye
mu sunayemmu. Dukammu kowa ya fadi sunansa. Da ya ji sunana sai na ga ya tsaya kawai, ya
kafa mini ido. To, duk daga cikin yaran kuwa ni ne karami. Ba a jima ba sai ya kira ni ya ce,
"Sannu Umar, yanzu ka san ni dai ? Ina uwarka ta ke, ina ku ma babanka ? Zo mu je in kai ka
wajen babanka, ka ji."
Na ce, "To."
Nan da nan sai na ga ya sa hannu a cikin wata 'yar jaka tasa, ya fid da soyayyen nama game da
kudi biyu ya bani. Ka san al'amarin yaro, sai na karba ina tsalle. Ya kama hannuna muka yi ta
tafiya, wai zai kai ni inda uwata da ubana su ke. Ni kuwa na yi ta binsa da kudina da namana a
hannu, ina fincika. Muka yi ta tafiya yana kame da hannuna har dai muka fita bayan gari. Da
muka isa bayan gari sai na ga ya ja ni mun shiga kwarin ganuwa. Muka yi ta tafiya har na gaji, Sai
na yi kamar zan yi kuka, sai ya dauke ni a kafada ya dada mini nana.
21
Muka yi ta tafiya ina kan kafadarsa tun wajen azahar har goshin magariba. Su sauran yara
wadanda mu ke wasa da su da ba su gan ni ba, sai suka fara yin kuka. Daga nan mutanen
gidammu suka ji sai suka aiko wata kuyanga ta zo ta ga dalili. Da ta fito ta tambayi yara dalilin da
su ke kuka, suka amsa mata wai Umar ne ya bata ba su gan shi ba. Suka ce kuma yayin da su ke
wasa da rana, sun ga wani mutum mai babban aljihu ya zo ya dauke ni a kan wai zai kai ni wurin
uwata da babana. Da kuyangar ta ji wannan sai ta yi salati ta sanad da Ubangji, ta shiga cikin
gida wajen iyali don ta gaya musu abin da ya auku.
Da Amina ta ji sai ta fashe da kuka tana cewa, "Wannan abu ya kai gargara, lalle wani dan sane
ya dauke Umar. Ni Amina wallahi yaya zan yi da raina ? In uwarsa ta dawo ba ta same shi ba, me
zan ce ?" Sai ta fadi ta yi birgima tana kuka tana kururuwa har duk gari suka ji. Nan da nan sai
aka buga gangami, kafin lisha ta yi duk daukacin namiji da ke garin yana bayan gari wajen
nemana.
Amma ni da mutumin da ya dauke ni ba mu san abin da a ke ciki ba. Da dai ya ga dare ya yi, sai
ya sauke ni daga kafadarsa, ya zaunad da ni a cikin wani dan kogon dutse, sa'an nan ya shiga. Ya
fitad da nama da nakiya daga cikin jaka tasa ya ba ni, ya kawo ruwa ya ba ni na sha. Muka zauna
a cikin kogon, a sa'an nan kuwa ban kula da kome ba, domin cikina ya riga ya cika. Shi kuwa
nufinsa in huta kadan sa'an nan mu tashi.
Ina zaune, yana cin abinci, sai na ga ya tsame hannu daga abinci ya bar taunar wanda ke bakinsa,
ya tsaya kawai kamar doki yayin da ya ji motsin wani abu. Ya dade cikin wannan hali sa'an nan
ya tashi da sanda, ya durkusa a kan guyawunsa, ya leka waje. Ba a jima ba sai na fara jin
maganar mutane arewa da mu. Da jin wannan sai na ga ya sa hannu a cikin jaka tasa ya dauko
wata laya ya buge ni da ita a ka. Bayan wannan ya kwanto wuka daga cikin ratayensa, ya ce mini,
"Ka ga wadan nan mutane sun fito yawo ne a cikin daji domin su kama yara su cinye. Watakila za
ka ga wanda ka sani a cikinsu, amma fa kada ka yarda ko ya kira sunanka ka amsa, in kuwa ka
amsa lalle ka tabbata zan yanke wuyanka da wannan wuka." Sai ya zaro ta ya nuna mini. Da na
duba sai na ga tana walkiya walwal a farin wata, duk jikina ya dauki bari, nan da nan sai na
tsunke da zawo.
Da masu nemana suka kusato kogon inda mu ke, sai wani daga cikinsu ya ce, "Kada mu wuce
wannan wuri, domin da na sani a wajajen nan akwai wani kogo inda wata rana da muka fito
22
gudummuwa muka kama wani dan sane da ya sato yarinya. Sai mu je mu duba nan tukuna, in
babu kome mu wuce." Duk abin da su ke fadi muna ji. Sai mutumin nan ya dauko wuka tasa ya
aza mini a wuya, ya ce in na yi magana ko dan motsi ma lalle zai yanka ni.
An Yi Nema Ba A Gan Ni Ba
Mutanen nan suna zuwa suna tadi har dai suka zo bakin kogon da mu ke. Da zuwansu sai daya
daga cikinsu ya kira sunana, "Umaru dan Makau !" (Domin shi ne sunan da Amina ta ke kirana da
shi). Ya yi ta kira, ni kuwa ina ji, amma babu dama in amsa sabo da tsoron kaifi. Suka yi ta kira
har suka gaji, babu wanda ya amsa musu, su kuwa ba wanda ya leka kogon balle ma ya shiga.
Daga nan suka koma gida. Sauran mutane kuwa suka gauraye dajin, ko alamata ba su gani ba.
Da suka gaji su ma suka kama hanyar gida. Suna tafiya suna cewa hakika uwar yaron nan in ta ji
wannan lalle za ta yi hauka ko ta mutu.
Mutanen nan da suka isa gida sai suka gaya wa Amina, ba su same ni ba. Sai ta fashe da kuka,
dukan mutane suka kewaye ta suna ba ta hakuri, cewa haka Allah ya kaddaro. Sai ta share
hawaye ta shiga cikin dakinta. Amma da ta duba akushin tuwona d ta ajiye mini, da kuma inda
na ke kwanciya, duk duniya ta zama baki sitik a wurinta. Sai ta fada a kan gado ta yi ta kuka ita
kadai. Tun ran da na bace ba ta sami kwanciyar rai ba sai da ta hadu da uwata a Fatika.
Kura Ta Cinye Barawo na
LOKACIN da masu nemana suka koma tsakar dare ta yi. Da mutumin da ya sace ni ya ji daji ya yi
shiru, sai ya ce da ni, "Yanzu mun huta ko ? Mu tashi mu tafi. " Sai ya dauke ni a wuya ya yi ta
tafiya da ni a cikin daji har muka kawo wani dan gidan gona. Sa'ad da muka zo wurin asuba ta yi,
sai ya sauko da ni daga wuyansa, ya ce ya gaji! Sai mu shiga cikin gidan nan domin ya yi rurumi.
Ya ja ni, muka shiga tare muka kwanta, ba a jima ba sai barci ya share shi. Amma ni ba ni jin
barci, domin na rigaya na yi yayin da na ke kan wuyansa. Da ma fara barcinsa ke da wuya, sai ya
fara gwarti wanda har ya razana ni. Da ya saka ni a bayansa yayin da zai kwanta amma da ya fara
gwartin nan tsoro ya kama ni, na tashi na shiga cikin wani kwando wanda masu gonar suka bari
a dakin na yi zamana.
23
Ba a jima ba sai na fara jin gurnanin wani abu mai ban tsoro a bayan daki. Ashe gurnanin kura
ce, da ta fito farauta ba ta samo kome ba har asuba, za ta koma kogonta, sai ta ji gwartin
maigidana ta zago ta gani. Ka san yadda dakin gona ya ke, babu wani sayi mai aminci, ko
tufaniya ma babu a kofar dakin da mu ke. Da kura ta zo kofar dakin sai ta tsaya, tana shawara ko
ta shiga ne ko ta koma. Gari kuwa ya kusa wayewa.
Sai ta yi kuru ta kurma kai ta shiga, ta sami mutumnin a bakin kofa, ta tsaya a kansa tana jin ta
inda numfashinsa ya ke fita. Sai na ga ta kafa masa hakori a makogwaro, ba wani jinkiri ko
wahala, sai na ga ta raba kansa da jikinsa, misali kamar mutum ya sami almakashi mai kaifi ya
datse ganye sabon toho.
Duk abin nan da kura ta yi mutumin bai farka ba. Ka san mutuwa yadda ta ke, kowane irin mai
rai yayin da zai mutu sai an dandana masa zafi. Sabo da haka yayin da iska ta bugo mutumin nan
dan ta wajen yankan nan, sai na ga ya fara shure-shure, kura kuwa tana jira. Da ya gama shure-
shure sarai, ta tabbata ransa ya fita, sai ta suri uwar jikin ta saba a baya, ta nufi kogonta, ta bar
kan a a cikin dakin tare da ni.
Gari ya waye, rana ta fito sai na tashi na fita waje. Na je gindin wata dorawa a cikin gonar, na
zauna ina ta wasa da tsakuwa. Da hantsi ya dubi ludayi, sai na fara kuka, ina kira, "Baba, baba."
Ba wanda ya amsa mini. Bayan da na dade ina kuka, sai na hango wadansu mutane suna zuwa,
ashe masu gonan ne. Sai na dada kuka ban bari ba sai da suka iso gare ni. Yayin da suka zo suka
gan ni yaro ne karami. Suka tambaye ni abin da ya same ni. Na gaya musu kaman nan, domin a
lokacin ban san yadda za a ba da labari ba. Na ce, " Baba kula ci daji jiya a daddale, kansa cikin
daki."
Bayan na fadi wannan magana saí wata mace daga cikinsu ta ce, "Ayya! Yana nufin wai ya ce ne
jiya da daddare kura ta cinye babansa, ta bar kan a cikin daki."
Sauran suka ce, "Ai wannan kuwa ya zama gaskiya. Kai yaro, ina ubanka ?"
24
Sai na nuna dakin da na kwana. Nan da nan sai suka nufi wurin. Da dai zuwansu kofar dakin sai
suka fara ganin jini a bango, sai ka ce saniya ce aka yanka.
Mijin Ya Zo
Muna cikin haka, sai ga mijin matan nan da mu ke tare da su ya zo ya same mu muna tsaye a
kofar daki matan suna ta salati irin nasu. Da zuwansa sai suka habarta masa duka abin da ya
auku, ya yi salati, ya dauki kan nan da kura ta bari, ya je bakin gona ya turbude. Bayan wannan
sai ya ga tufafin mutumin ya shiga binciken abin da ke akwai. Da bude rigar mataccen sai ga
wata babbar zabira, ba kome a ciki sai soyayyen nama, da dandakwarya, da garin soye, da wani
dan koko. Kuma ya duba yar ciki sai ya ga wadansu layu guda biyu, daya an mata rufi da fatar
goshin damisa da sasari a hancinta. Dayar kuwa da fatar minjirya aka rufe, aka dinke da jijiyar
biri. Ita layan nan ta biyu kuwa a cikin wani yankin tsumman saki aka kunshe ta. A nan kuma ya
sa kitsen mutum wanda ya ke milke ta da shi. Kuma tana hade da idon jinjiri.
In gajarta maka magana dai, da ya dudduba kayan mataccen nan sarai sai ya ajiye zuciya ya ce,
"Lalle wannan mutum ba uban yaron nan ba ne, ba shakka ya sato shi ne daga wani wuri, domin