Showing 18001 words to 19982 words out of 19982 words

Chapter 7 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf

tana kuka. Ya tambaye ta, “Me ya
same ki ? Ke kuwa mutumiyar wane gari ce ?"

Ta ce, “Ni mutumiyar Fatika ce, mijina yana can a wani gari ana ce masa Makarfi, can na bar shi."

Ya ce “Yaya aka yi kika zo nan ?"

46

Sai ta shiga ba shi labarin yadda ta fito garin neman danta, da yadda aka yi mata wayo aka sayad
da ita, har zuwanta wannan gida. Da ta gama ya ce mata, “Yanzu me ki ke so ?”

Sai ta ce, “Ai ba abin da na ke so kamar in cika abin da ya fito da ni daga gida, in samu in ga dana
sa'an nan in na so in mutu."

Da ya ji haka sai ya yi mamaki karfin halinta ya ce, “Kin san sunan garin da danki ya ke ?"

Ta ce, “I, domin an gaya mini wani mutum ne ya tafi da shi garinsu a kasar Masar sunan garin
kuwa Ber Kufa."

Ya ce, “Ber Kufa ! Ina sunan maigidansa ?"

Ta ce, “Wai sunansa Abdulkarim."

Ya ce, “Abdulkarim ! Ina sunan yaron ?"

Ta ce, “Umar.”

Da ya ji haka, ya ce, “Allahu Akbar ! Allah mai yin yadda ya so ! Ki yi murna, Allah ya dube ki, yau
wahalarki ta kare."

Sai ya juya wajen Ahmad ya ce masa “Nawa zan ba ka in fanshe ta ?"

Ya ce, “Kome ka ba ni, shi ke nan."

47


Ya tafi ya kawo kudi ya ba shi. Sa’an nan ya kira ni, ya ce mata, “Ga wanda ki ke nema. Kuma ni
ne Abdulkarim."

Mahaifiyata Ta Gan Ni

Sai ta dube ni ta ce, “Umar ! Kai ne ?" Sai ta fashe da kuka. Ni dai ina tsaye ina mamaki, sai na ji
jikina ya yi sanyi. Na tambayi Abdulkarim, “Wace ce wannan ? Ina dalilin da ta ke kuka ?"

Sai uwata ta amsa ta ce, “Ni ce mahaifiyarka, shekarun nan da yawa ina nemanka, sai yau Allah
ya hada mu.” Ta yi wuf ta rungume ni, ni dai na kasa magana.

Sai Abdulkarim ya ce mu tafi masauki. Da muka tafi hankalinta ya komo, ta yi ta ba ni labarin
abin da ya same ta duka. Ni kuma na gaya mata nawa.

Sa'an nan na ce, “Yanzu dai sai na kai ki gida, in Allah ya yarda."

Sai ta ce, “Kayya ! Na rabke. Na sani ba zan koma gida ba, amma tun dai da na gan ka ya ishe ni.
Kai dai Allah ya kai ka gida, ka ga sauran danginka."

Na ce, “Kada ki ce haka, Allah ya Sawwaka."

Ashe karfinta ya rigaya ya kare, sabo da wahalar da ta sha, ga kuma murnar ganina ta yi mata
yawa. Daga nan ba ta kara tashi ba. Ashe Allah ne ya sa muna da rabon ganawa. Bayan kwana
kadan sai ta rasu. Muka yi mata sutura. Da ta yi bakwai muka mika. Ni dai tafe na ke kawai,
amma zuciyata tana cike da tunanin abin da ya auku a gare ni. Kwanci tashi, ba abin da ya same
mu a hanya har muka kai Murzuk.

48


Da muka sauka a Murzuk, ba mu sami ayari masu wucewa ba, sai muka zauna nan watanni,
sa’an nan muka sami wadansu muka wuce.

Mun Ci Gaba Da Tafiya

DA muka tashi daga Murzuk muka yi ta tafiya kamar wata uku, har Allah ya kai mu wani dan
kauye wai shi Muhtad. Da saukarmu sai muka fantsamu muna tambayar labarin hanyar da za
mu bi. Kowa muka tambaya kuwa sai mu ji wai hanya ta baci, babu abin da a ke yi sai fashi da
yakoki tsakanin kabilu. Da muka ji haka sai manyan tafiyarmu suka taru domin su yi shawara a
kan abin da za a yi. A wurin fa, sai bakinsu ya saba. Wadansu suka ce a koma, wadansu suka ce a
ci gaba. Kai, a cikin shawarwarin nan ne na ga inda a ke son dukiya. Dukansu kowa sai duban
ribar da zai ci kawai ya ke.

Da wadanda suka ce a ci gaba suka rinjaya sai kowa kuma ya yarda, aka yi ta shiri domin mun yi
niyyar tashin dare ne.

Da gama cin abincimmu sai aka buga kuge, muka tashi. Muka sake hanya sabo da tsoron
mayaka, muka ratse cikin hamada. Wannan sakin hanya fa ya zama babbar hasara a gare mu.
Tun da muka tashi daga Muhtad muna tafiya a cikin dare ba mu gamu da kowa ba, ba mu kuwa
ji motsin kome ba, har gari ya waye mana a kusa da wadansu manyan tuddan yashi wadanda
iska ta tara. Da muka kai wurinsu nan rana ta bullo sai madugu ya ce a huta har rana ta yi sanyi
kana a tashi. Muka sauka, kowa ya debe wa rakuminsa sirdi. Muka yi kwance bayan da muka sha
ruwa muka ci abincimmu. Muka zauna a wurin, masu yawo suka tafi, masu barci suka yi, masu
karatun Alkur'ani suna yi, masu tadin duniya kuma suna yi. Kowa dai daga cikimmu yana aikata
abin da ya ke bukata har rana ta take tsaka cur.

Yayin da kowa yana cikin hidimarsa, an sake sarai, sai muka ji kuwwa daga wajen 'yan'uwammu
da suka tafi yawo, muka hango su a guje ridididi kamar garken Uda. Mu duba haka wajen gabas
sai muka ga wani abu can baki kirin kamar hadari, daga kasa ya tokare da samaniya, ya nufo inda
mu ke. Ni kam ban san ko mene ne ba, amma sauran mutane da mu ke tare da su sai na ga kowa

49

ya fara tara kayansa yana kuka. Ni kuwa sai na tsaya kawai ina ta kallo, ban san abin da a ke yi
ba. Zuwa can in daga kai dai, sai na ga abin nan a gabana kamar hadari. Ashe ba hadari ba ne.
Iska ce kawai ta girma ta zama haka. A cikin iskar kuwa ba kome sai yashi. Yayin da iskar ta kawo
wajen da mu ke nan da nan sai na ga duk wurin ya hargitse, ba ni iya ganin kome balle in san
inda yan ’uwana su ke. Sai na dame, na rasa abin da na ke ciki.

Ni Kadai Na Tsira Bayan Hadari

Kada dai in kai ka da nisa, iskar ba ta tashi yin sauki ba sai bayan lokaci mai tsawo, kana ta d'an
kwanta. Da idona ya waye na duba cikin sarari sai na ga babu kowa sai ni daya. Kuma tuddan
nan na yashi da muka sauka gindinsu ban ga alamar ko daya ba. Sai tsoro ya kama ni, a raina na
ce lalle halakata ta zo. Sai kuma na tuna da maigidana da sauran jama'ar da mu ke tare dasu,
gama zuciyata ta saka mini cewa lalle yashi ne ya rufe su duka. Na yi ta zagawa ina kiran
Abdulkarim, ban ji amsa ba ko motsi, har na gaji. Sai na zauna, na fashe da kuka; lna cikin haka
har gari ya rufa. Nan na kwana a sararin Allah, ko barci na kasa yi.

Da gari ya waye na tashi na sake zazzagawa ko na ga wani mai rai. Ban ga ko alama ba. Na yi ta
yawo kawai ban san inda na ke nufa ba. Kwana uku ina haka, dan ruwan da na ke da shi cikin
butata ya kare. Kishirwa ta kama ni, ga zafin rana, wurin fakewa ma babu. Sai na kasa ko
tsayawa balle tafiya. Na yi kwance kawai, ina jiran mutuwa.

Rana ta hudu wajen la’asar ina kwance sai na ji kuka kamar na rakumi, gabana ya fadi, na daga
kai, sai na hango wani rakumi daga nesa da labtu ya nufo inda na ke. Na ce, “Hakika Allah shi ne
mai iko !" Ina zuba ido kawai har ya iso gare ni, yana sansane-sansane. Ya tsaya, na dube shi,
ashe rakumina ne, sai na ga ya durkusa a gabana, na ja jiki na kai gare shi, na rarumi salkar ruwa,
na sha. Hankalina ya komo, na debo dan abinci na ci, na yi godiya ga Allah. Na kwana a nan tare
da rakumi.

Da gari ya waye na ji karfi, na kintsa kaya na hau, rakumi ya mike a tsaye. Ina zullumin ta inda
zan bi, sai na ga rakumina ya kama wata hanya da kansa. Ni kuma da na ga haka ban yi wani
zumudi ba sai na bar shi ya yi ta tafiya, har ran nan sai na fara hangen wadansu bishiyoyi na

50

dabinai daga nesa. Da muka iso wajen da itatuwan nan su ke sai na ga babban gari ne. Rakumina
ya yi ta tafiya har ya kawo ni bakin wata rijiya, ya ja ya tsaya. Na sauka daga bayansa na debo
ruwa na ba shi, ni kuma na je gindin wata itaciya, na zauna a kusa da wadansu ayari. Na same,
su suna tadi, na ji suna cewa wai rana ya ta yau war haka, in Allah ya so, suna Birnin Kuka cikin
kasar Barno. Suna ta tadinsu, ni kuma ina ta murna a cikin zuciyata na sami masu zuwa kasarmu.

Muna zaune a gindin wannan bishiya muna tsakiyar tadi ke nan sai muka ji an yi ihu daga cikin
gari. Nan da nan sai muka ga mutane suna ta fitowa a guje. Ba a dai jima ba sai muka ga duk
garin ya fashe, kuma muka hango wuta ta kama gida. Mu muna zaune, ba mu san abin da ya
auku ba, sai dai hankalimmu ya ba mu cewa lalle ba lafiya. Duka sai muka tashi, kowa ya yi shiri.
Muka hau rakumammu, muka yi tsaye a kan kayammu.

Ba mu jima ba da gama shiri sai muka ga rundunar wadansu mutane da bindigogi. Da ganinsu
muka watse, kowa ya kama hanyar da ya ga za ta fisshe shi. Muka yi ta gudu. Yawancimmu da
suka tashi gudu sai suka nufi ta inda suka fito, watau cikin hamada. Ni kuwa da dai na ruga a
guje bisa kan rakumina sai na nufi wajen da masu bindigogin nan su ke. Na zo na wuce su a guje.
Na yi ta gudu har na kawo zuwa wani gari babba mai yawan itatuwan kuka. Na zo wani gida na
sauka daga kan rakumina, duk hankalina ya fita daga jikina.

Mai gidan ya fito, ya ce mini, “Yanzu daga ina ka ke ?"

"Na ce masa, “Daga wani gari ne wadansu 'yan yaki suka koro mu."

Shi kuwa ya ce, “Lalle wadansu daga cikin mutanen Rabe ne wadanda suka barko bayan da
Faransai suka kama shi suka kashe."

Yadda Na Iso Rauta
A garin nan fa ban sami tashi ba saboda rashin lafiyar rakumina. Da na kwana shida a wurin sai
ya mutu. Bayan mutuwarsa da kwana biyu sai na tashi zuwa kasarmu a kasa. Kwanci tashi, har
Allah ya kawo ni wannan gari naku Rauta. A nan na ji labarin Makau ya mutu. Ba ni da sauran

51

dangi wadanda zan tafi in dubo, sai na yi zamana a nan ina karantarwa. Ka ji dalilin zuwana
kasarku ke nan.
Alhamdu lillahi Allah kai ne abin godiya. Ina rokon Ubangiji ya gafarce mu bisa kan abin da muka
aikata da kuma abin da za mu aikata zuwa gaba. Allah Ubangiji ka kore mana huznu da hassadar
magabta, ka kubutad da mu daga sharrin duniya da na lahira, amin.

52

SHIRYAWA

(c) 2017 Bukar Mada
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Facebook: @bukarmada
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Za a kuma iya samun wasu littafan a shafin Taskar Bukar Mada:
http://bukarmada.blogspot.com

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login