Showing 9001 words to 12000 words out of 19982 words

Chapter 4 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf


wadannan kaya babu mai irinsu sai yan sane ko 'yan kwanto. Guzurin nan nasa kuma irin na
masu sane ne."

Bayan ya fadi haka, sai ya juyo ya tambaye ni wadansu tambayoyi wadanda har abada ba zan iya
tunawa da su ba. Ya yi ta magana a banza, ban kula da abin da ya ke fadi ba balle in ji. Ina ta
wasan kasa abina tare da 'ya'yansa kanana.

An Sake Ba Da Ni Riko

Da ya ga ban mai da hankali gare shi ba, sai ya ce wa daya daga cikin matansa, "Wance, ke ce ba
ki da da, to, ga shi Allah ya ba ki, sai ki rike shi, Allah ya sa na moriya ne." Ta durkusa ta yi
godiya, kana ta dauke ni ta tambaye ni sunana, na fada mata ta yi murna.

25


Bayan wannan sai suka fada aikin gona, suka yi ta yi, mu kuma muna wasa har azahar ta yi. Sa'an
nan suka taf rafi suka wanke jikinsu. Bayan da suka gama suka dawo gindin dorawa wajen da mu
ke, suka zauna domin a sha ruwa, kana a tafi gida. Sai na ga wata ta bude wani masaki, ta fito da
gaskami ta garwaya da gari, ta sa ruwa, ta ba kowa nasa. Mu kananan yara aka ba mu namu a
ludayi muna lakuta da yatsummu.

Bayan da muka gama shan dorowan nan sai kowace mace ta dauki danta ta saba a baya. Ni
kuma uwata ta dauke ni ta saba, muka kama hanyar gida. Maigidammu yana baya da kwari da
baka a rataye, kuma kannensa biyu suna gaba da nasu kayan fada a rataye. Mu yara da mata
muna tsakiyar su.

Mun rabu da gonar ke nan kadan, sai muka rika jin dirin dawaki cikin daji, da mutane suna cewa,
"Kama hau, yau gadonku zai kwana wofi!"

Cikimmu duk ba wanda ya kula da abin nan da su ke fadi, sai ta tafiya mu ke yi. Amma ko da ya
ke a cikimmu ba wanda ya nuna alamar ya kula, lalle kowa zuciyarsa ta raurawa, babu mai
sauran laka a jikinsa, kowa sai jefa kafa ya ke yi. Muna dai ta jin sukuwar dawaki da maganar
mutane, amma ba mu ga kowa ba.

Can an jima sai muka hango wani barde mai kilin doki ya sunke cikin sulke, ya sako ingarmansa
bisa gare mu yana fadi, "Yau gadonku zai kwana wofi!".

Cikimmu duk ba wanda ya kula da abin nan da su ke fadi, sai ta tafiya mu ke yi. Amma ko da ya
ke a cikimmu ba wanda ya nuna alamar ya kula, lalle kowa zuciyarsa ta raurawa, babu mai
sauran laka a jikinsa, kowa sai jefa kafa ya ke yi. Muna dai ta jin sukuwar dawaki da maganar
mutane, amma ba mu ga kowa ba.

Can an jima sai muka hango wani barde mai kilin doki ya sunke cikin sulke, ya sako ingarmansa
bisa gare mu yana fadi, "Yau gadonku zai kwana wofi!"

26


Da jin haka sai maigidammu ya ce, "In Allah ya yarda kai ne gadonka zai yi hasara, domin
watakila yau kan sabara, ka ke kwana"

Nan da nan sai na ga ya mika hannu a jikin kwarinsa, ya zaro wata fasa wadda har jikin
kyauronta yabi ne, ya dana, ya durkursa yana jiran barden. Shi kuwa barden tun da ya sako doki
bai zame ba. Maigidammu kuma yayin da ya ga ya yi kusa da shi, sai ya tattare jikin bakansa, ya
sau masa kibiya. Nan da nan ya sa garkuwa tasa ya tare, kafin a ce maigida ya sami damar zaro
wata kibiyar barden ya kade shi, ya bar shi rigingine sumamme kamar ransa ya fita.

A lokacin nan basira duk ta bace mana. Sai muka zuba ido kawai, muna kallon abin da aka yi. Kan
a jima kadan sai muka ga dawaki wajen bakwai sun nufo mu a sukwane. Da ganinsu kowa a
cikimmu ya sunkuya ya ranta cikin na kare. Duk sauran mata suka gudu suka bar uwata tana
goye da ni ba ta iya gudu domin ta sare kafarta da masassabi.

Barde Ya Kama Mu

Da barden da ya kade maigidammu ya ga haka, sai ya sauko daga kan dokinsa, ya jawo uwata
tare da ni a goye, ya hada da maigidammu, ya daure mu tam da asalwayin dokinsa. Sauran masu
dawaki da dai suka ga haka, sai suka rufu a bayan 'yan'uwammu, ban san kuma yadda suka kare
ba. Ga zatona dai sun kama su, domin ko wacce tana da goyo.

Bayan da barden ya kukunce mu, sai ya tasa mu a gaban dokinsa, yana tura mu zuwa garinsa.
Muka yi ta tafiya har gari ya waye. Da safiya ta yi sai ya karbe ni daga bayan uwata, ya aza ni a a
kwacciyar sirdinsa, domin ya ji tausayin uwata da te ke goye da ni. Muka yi ta tafiya wajen
kwana uku, sai ga mu a Birnin Kano. Shi mutumin kuwa daya daga cikin manyan bayin Sarki ne,
fatara ce ta kama shi ya fita dan yawo, domin ya zo ya sami abin bukata. Sa'ad da muka iso cikin
gari babu wanda zai so ganimmu, saboda tsananin azaba game da bakin cikin.

Gyatumata Ba Ta Da Labari

27


DUKAN abin nan da ya auku gare ni gyatumata ba ta da labarin ko daya. Domin da ta kai Fatika
ta tarar an kama ubanta a kan maganar maita, aka tafi da shi Zazzau. Tana can tana jiran
dawowarsa, sa'an nan ta zo ta dauke ni zuwa Makarfi wajen Makau. Bayan ta yi wata biyu da
kwana goma sha daya a garinsu, sai ubanta ya dawo daga birni. an sako shi, magana ta kare.
Domin yayin da suka je shari'a, Sarki ya zagi manyan mutanen Fatika a kan sharrin da suka yi
masa, ya ce babu wani abu wai shi maye a duniya. Amma fa Sarki bai yi wannan magana ba sai
da uban uwata ya waka masa shanu biyu duka na tatsa. Yayin da zai fito Zazzau, Sarki ya hada
shi da wani bafade su zo ya tafi da shanun. Suka zo tare da bafade aka ba shi shanun Sarki. Da
aka ba shi ya ce, "A'a. Ni haka za a bar ni in tafi ? Nan da nan ba wani musu sai uban uwata ya
kawo wata 'yar burguma ya ba shi, ya kora zuwa gida. Aka bar uban innata sai wata 'yar karsana,
da wani bunsuru mai buzurwa har kasa.

Mutanen gida suka yi ta murna saboda mai gida ya dawo lafiya. Jama'a da yawa masu kaunarsa
suka yi ta zuwa suna yi masa barka da kubuta. Bayan dukan masu zuwa sun tafi sai uwata ta iske
shi a daki ta yi masa barka da arziki. Yayin da ta shiga dakin sai ta fashe da kuka, ka san irin farin
cikin mata. Ya tambaye ta labari, duk ta habarta masa tun daga farko har zuwa karshe, ba ta
manta da ko daya ba. A nan ya sa mata albarka, ya ce ta yi kokari, ta yi niyya, bayan yan kwanaki
kadan ta koma Kagara ta dauko ni, sa'an nan ta zo ta wuce zuwa wurin Makau. Sai ta fara shirin
tafiya. Bayan ta gama shiri ran nan ana kamar gobe za ta tshi, sai ta tafi wajen ubanta ta roke shi
wani daga cikin 'ya' yanta ya raka ta.

Ya ce "Shi ke nan, ku tafi da Dabo." Aka kira Dabo, aka shaida masa zai raka inna Kagara. Bayan
sun gama shiri wajen goshin a la'asar, sai ta dauki tulu domin ta debo ruwa a wata rijiya wace ta
ke daf da hanyar fatake ta zuwa Kagara. Ta jefa guga ta debo ruwa ke nan sai ta hangi wadansu
mata da rufin kai daga nesa da wani mai doki sun fito daga wajen Kagara. Nan da nan sai ta fitad
da guga, ta tsaya kawai ta zuba ido har suka iso. Da isowarsu, sai ta ga mai dokin nan ashe
Buhari ne. Da duba fuskokin matan sai ta sansance Amina. Sai ta yi wuf ta je ta rungume ta, tana
kuka tana yi mata maraba. A nan ta gangarad da tulun, ta karbi kayan Amina, ta wuce gaba har
zuwa inda Buhari ya sauka. Da ta ga saukarsu sai ta koma gida domin ta yi musu tanadin abinci.
A lokacin ba ta lura ba ni cikin tafiyar ba.

28

Ta dawo gida, ta shaida wa ubanta dukan abin da ya auku, ta ce a yi mata abinci mai kyau wanda
za ta kai wa bakinta. Nan da nan sai aka kama kaji biyu aka yanke, aka debo shinkafa daga
rumbun uwa tata aka dake aka bushe aka wanke aka dandara tuwo da ita.

Almuru na yi, sai inna ta dauka ta tafi ta kai masaukin su Amina ta ajye, ta dawo gida ta ci nata.
Bayan da ta gama jibi, kuma ta tabbata su ma a sun gama, sai ta tafi wurinsu domin ta ji labari.
Da isarta ta samu Amina babu yadda ta ke, tana ta kuka, duk idonta sun kunkumbura. Da ta ga
Amina cikin wannan hali, sai ita kuma ta koma waje daya ta tsuguna. ta yi tagumi.

Jim kadan Amina ta bar kuka ta share hawaye, suka gaisa. Sai inna ta tambaye ta dalilin da ta ke
kuka.

Ta ce, "Babu kome."

Inna ta ce, "Ke dai in da wani abu ne ya faru ki gaya mini, barin kashi a ciki fa ba ya maganin
yunwa."

Sai inna ta fara tsamnani a ranta ko Allah ya kiraye ni ne bayan tashinsu daga Kagara. Amina dai
ta yi shiru, ba ta ce kome ba.

Suna cikin haka sai ga Buhari ya shigo domin ya gaisa da inna. Ya zo ya same su suna zaune
zungum. Ya shiga ya zauna. Inna ta yi masa maraba, suka yi gaisuwa, ta tambaye shi labarin
yadda ya bar Kagara, da inda ya ke nufin tafiya. To, ka san namiji. Sai ya ka da baki ya ce mata,
"Kagara lafiya. Yanzu na yi niyyar zuwa Hausa in ziyarci kabarin babban waliyyi, Shaihu Usumanu
dan Hodiyo. Bayan wannan ina da bukata in je in dubo wadansu kawunnaina a Tureta, daga nan
kuma in wuce zuwa Dingyadi wajen gyatumata, domin mun dade rabommu da juna. To, bayan
wannan sabili da ke na biyo ta wannan gari domin in shaida miki abin da ya auku bayan tashinki
daga Kagara. Yaron nan dai bayan tashinki da kwana tara, wani dan sane ya sace shi. Aka yi ta
nema da gaske, ba a ji motsinsa ba. A lokacin kuwa ni ma ba ni gida, na tafi kauye, domin in
dubo wani abokina mara lafiya. Da na dawo na tarar da wannan labari. Amma mun ji labari daga

29

wajen wani wai shi Amadu cewa lalle ya ga Umar a Birnin Kano a gidan wani babban bawan
Sarki wanda a ke kira Gumuzu, kuma ya ce ya ji shi Gumuzun da wani Balarabe ma sunansa
Abdulkarim suna magana wai yana son ya fanshi yaron, ya tafi da shi can wajen kasar Masar ya
ba mata tasa, watau ya zama kamar dansa. Wannan labari fa shi ne wanda zan iya gaya miki na
game da Umar, shi ne kuma dalilin da ya sa na biyo ta wannan gari. To, yanzu sai ki dauki hakuri
bisa kaddarar Allah, kuma ki tuna a ranki hakuri ya fi kome.'"

Innata ta yi jirim kawai. Bayan zamani mai tsawo ta ce, " To, mutum duk na duniya in bai yi
hakuri ba lalle ya ga bacin rai dubu. Allah ya sawwaka."

Da Buhari ya gama gaya mata wanan labari sai ya fita waje, ya bar ta da Amina su yi tadinsu.
Suka yi tadi har can tsakad dare, sa'an nan inna ta taso ta dawo gida. Da isowarta ta shaida wa
uwarta da ubanta abin da ya auku. Su kuma dukansu suka ce, "Allah mai iko !"

Da gari ya waye sai inna ta koma wajen su Amina domin su yini. Yayin da ta ke can sai ga wani
kanenta ya zo a guje, wai an aiko daga gida ya kira ta, ta yi bako daga wajen Zazzau. Sai ta yi
farat ta tashi ta tafi gida ta sami Isa ne, mutumin da Makau ya aiko shi ya tafi da iyalinsa
Makarfi. Ta marabce shi, ta kawo masa ruwa ya sha. Ta tafi ta shaida wa ubanta cewa yaron
mijinta ne. Nan da nan aka share masa daki, ta kai shi. Bayan da ya zauna ya huta kadan, sai ya
ce mata, "Kin shaida ni dai ?"

Ta ce, "Ai har in mutu ba ni mantawa da kai".

Ya ce mata, "Makau ne ya tsananta yana so ki yi gaggawa ki koma ki same shi tare da yaron nan.
Ya ce nan da nan mu tafi ga sawuna ga naki"

Inna ta ce, "To." Sa'an nan ta habarta masa dukan abin da ya auku bayan rabuwarsu. Isa ya yi ta
mamaki bisa hukuncin Ubangiji.

30

Da suka gama wannan zance, sai ta dauke shi zuwa wurin iyayenta don ya fada musu sakon
Makau da bakinsa. Isa ya shaida musu kome, sa'an nan ya koma dakinsa ya yi kwance sabili da
zafin ranar da ya dauko. Ita kuma bayan da suka rabu da Isa, sai ta koma wajen su Amina tana
murna. Ta shaida musu abin farin cikin da ya same ta. Dukansu sai suka yi ta farin ciki har suka
kusa mantawa da bacewata. Da inna za ta koma gida, sai suka yi ban kwana da su Amina dayani
domin su da asuba za su tashi. Da suka gama ban kwana sai ta koma gida. Asuba na yi sai su
Amina suka tashi suka nufi Kasar Hausa.

Inna dai daga komowarta gida ba ta yi wani dan jinkiri ba sai ta fara shirin tafiya wajen mijinta.
Bayan su Amina sun tashi da kwana biyar, sai inna da Isa su kuma suka tashi. Suka yi tafiyarsu
cikin kwanciyar hankali, bayan kwana hudu ran na biyar sai ga su a MaKarfi.

Yayin da suka zo sai suka iske Makau ba shi gida, ya tafi gewayar wata sabuwar gonarsa, a bayan
gari. Isa ya tura inna cikin gida wajen 'yan'uwanta mata, shi kuma ya tafi gida ya yi wanka ya
sake tufafinsa. sa'an nan ya fito ya tafi wajen Makau a bayan gari, ya gaya masa ya dawo lafiya.
Makau daga wurin da ya ke zaune bai ko dan dakata ba, nan da nan sai ya garzayo gida. Ya iso ya
shiga cikin gidansa yana mai dariya yana farin ciki da zuwan matarsa. Ya nuna mata daki ta shiga.

Bayan ta huta, hankalinta ya dawo, ba abin da ya fara tambayarta sai labarina. Ta gaya masa na
bace. Bayan Wannan ya yi mata tambayoyi, ita kuma ta kwashe dukan abin da ta sani ta shaida
masa. Daga nan sai tsoro ya kama Makau, duk ya kidime.

Wadannan abubuwa fa su ne suka auku ga uwata. Amma bayansu duka sai ta tsaida zuciyarta,
ta sani Allah daya ne. In Allah ya so sai ta dangano da inda na ke, in ba mutuwa ta yi ba.

An Sayad Da Ni Ga Balarabe

A ZAMANIN da Gumuzu ya kamo mu, akwai ayari na Larabawa a cikin Birnin Kano, wadanda
suka zo su sayi bayi su kai Kasarsu. Yawancinsu kuwa su kan yi abota da manyan bayin Sarki,
domin in sun zo kullum su ne su kan yi musu hanyar samu bayi. Ba kuwa ko yaushe su ke zuwa

31

ba, akwai ajiyayye lokacin zuwansu. Kuma kullum yayin da suka zo suka sayi bayi, in za su tashi
su koma kasarsu su kan yi alkawari da abokan nan nasu, su tara musu wadansu bayi kafin su
sake dawowa. Cikin Larabawan nan Gumuzu yana da wani aboki ana kiransa Abdulkarim na wani
gari cikin Kasar Masar.

Ran nan muna zaune bayan mun shekara biyu cur tare da Gumuzu sai na ga wani mutum fari
dogo, mai dogon gemu da gashin baki, ya taho gare shi. Da zuwansa sai na ga Gumuzu ya tashi
daga kan shimfidarsa, ya zaunad da shi a kai, yana ta ce masa, Maraba, sannu da zuwa ! Bayan
sun gama gaisuwa sai ya kira ni ya ce in je cikin gida in karbo wa bakon nan ruwa. Na shiga na
kawo masa ruwan surki mai zuma. Na zo na durkusa gaban bakon nan, na mika masa ya karba
ya sha. Bayan ya sha ruwa ya yi hamdala, sa'an nan ya juya wajen Gumuzu ya tambaye shi,
"Yaya, ban san wannan yaro ba, danka ne ?"

Gumuzu ya ce, "A'a, ka ji ka ji yadda na same shi, da ubansa da uwa tasa gaba daya".

Suka yi ta tadinsu, ni kuma ina tare da su har lokaci mai tsawo, sa'an nan kowa ya koma gidansa.
Gidan bakon nan kuwa kusa ne da na Gumuzu. Sarki ya ba shi wurin farkon zuwansa, domin
lokacin da ya zo duka ya sauka. Sa'ad da aka yi abinci duk sai a dora mini in kai masa
masaukinsa. Har dai ya zama muka saba da shi kwarai saboda abincin da na ke kai masa kullum.
Wani lokaci In na kai masa, ya kan tambaye ni ko ina sonsa. Ko yaushe na tafi sai ya kama ni ya
shasshafa kaina yana sa mini albarka. Wani lokaci kuwa in zan komo gida ya kan kawo dabino da
wani irin abinci ya ba ni.

Haka ya yi ta yi mini har wajen kwana goma sha shida. Ran kwana na goma sha bakwai sai na ga
Gumuzu ya dauke shi sun nufi wajen fada. Da za su tafi kuwa Abdulkarim ya tambayi Gumuzu in
ya yarda in jo in zauna masa a daki wajen kayansa kafin su dawo. Gumuzu ya kira ni ya shaida
mini. Na tafi gidan Abdulkarim na yi zaune a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login