Showing 3001 words to 6000 words out of 19982 words

Chapter 2 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf


matukar ni na ke Sarki a wannan gari, ba zan yarda ka zauna a cikinsa ba. Saboda haka yanzu zan
kore ka ka tafi can wani wuri inda ba hannuna. Kuma har yanzu ban hana ka tashi da iyalinka ba.
Kowace mace cikin matanka in tana son ka sai ta bi ka ku tafi tare, in kuwa ba ta sonka, tilas ka
bar ta.”

Makau ya ce, “Ranka ya dade, na ji na karba. Amma ina roko a cikin darajar mulkinka ka bar ni in
yi 'yan kwanaki kadan a nan domin in sami dan guzurin da zan ci a hanya, domin ka sani yanzu
zan tafi wuri ne inda ban sani ba."

Sarki ya daga kansa zamani guda, kana ya amsa wa Makau cewa ya yarda, amma kwana hudu
kawai ya ba shi ya shirya kaura tasa.

Makau ya yi godiya, ya taso ya zo gida, ya tara iyalinsa duka babba da yaro, maza da mata, ya ce
da mu, “To kun gani yadda Allah ya kaddara wannan al’amari bisa gare ni. Sarki ya ce sai in bar
masa kasarsa, amma ya yardam mini in tafi da mace wacce ta ke son ta bi ni, kuma bayan
wannan ya ce kamin kwana hudu dole in bar garin nan. Yanzu abin da na ke so idan a cikinku
akwai wacce ranta ya riya mata za ta iya daurewa ta bi ni, to”.

10

Duk iyalina sai muka fashe da kuka gaba daya muna cewa, "Wallahi tallahi, ba wata kasa za ka
tafi ba, ko da lahira in ana rakiya, lalle ba shakka ma raka ka."

Makau ya yi mana tambayoyi uku na shari'a, dukammu babu wanda bakinsa ya sake.

An Fitad Da Makau Daga Garin

BAYAN Makau ya aikata wannan abu wajen iyalinsa, sai ya fita zauren kofar gidansa ya zauna
yana tunanin kasar da zai tafi, sai mutane da yawa sahibansa da makamantansu suka yi ta zuwa
gare shi suna gaishe shi da wannan bakin ciki, yawancin mutanen in sun zo sai in ga suna kuka
da hawaye, wadansu ku kuwa sai su zo da 'yan kudi su danka masa, suna cewa ga dan wannan
ko ka sha ruwa a hanya.

Da almuru ta yi, sai Makau ya tashi ya yi alwala ya yi salla. Ran nan kuwa ran tuwon gyatumata
ne. Bayan da aka gama hira duka sai Makau ya shiga gida domin ya kwanta. Da ya shiga sai ya
wuce dakin uwata, ya same ta tana kuka babu yadda ta ke. Da ya ga haka sai ya ce mata,
"Wannan abu ba na kuka ba ne, ya wuce kuka. Kuma ko ba haka ba, tun da ya ke Musulma ce
ke, ya kamata ki tuna cewa dai dukan abubuwa daga Ubangiji su ke samun mutum saboda haka
abin da ya fi kyau a garemu duka sai mu yi tawakkali ga Allah wanda ke aikata kome yadda ya
so.”

Uwata ta amsa ta ce, “To, Makau yanzu ni kuwa a duniyan nan me zai hana mini kuka ? Ka ga dai
dukan fadin garin nan ba ni da dangin uwa balle na uba, kuma ban da wannan dan maraya ba ni
da kowa sai kai da Allah ya hada mu. Bayan wannan abin da na ke tunani yanzu shi ne wannan
sharri da ya same ka. Domin lalle a duniyan nan abin da ya taba ranka nima ya taba nawa.
Amma babban abin da na ke tunani shi ne wannan dan yaro, na rasa yadda zan yi da shi. Har
yanzu kuma da ina da bukata in kun dawo daga wajen harin nan in tambaye ka izni in je
garimmu in gano iyayena in dawo, to, ga abin da ya auku."

11

Da Makau ya ji wannan magana, sai ya yi kurum yana ta tunani. Bayan da aka jima sai ya amsa
mata. “Hakika kina da abubuwa na bakin ciki tare da ke, amma ko da ya ke haka ne Allah mai
sawwake kome ne. Share hawayenki babu kome cikin nufin Allah. Amma a kan zancen da kika ce
na wajen zuwa duba iyayenki zan ba ki shawara guda. Yanzu tun da ya ke ya zama haka, ga kuma
halin da mu ke ciki, ni kuwa ban san wani gari ba takamaimai inda zan zauna, saboda haka na
yarje miki ki tafi ki duba gida, ni kuwa yayin da na sami wurin zama sosai zan aika miki ki same ni
can. Yaron nan kuwa da ya ke ba za ki iya tafiya da shi ba, ya kamata ki bar shi a nan a wurin
wani amintaccen mutum, har ki tafi ki dawo ki same shi."

Gyatumata ta ce, “To."

A kwana a tashi ran nan wa'adin da Sarki ya diba wa Makau na kwana hudu suka cika. Tun da
sassafe Sarki ya aiko a gaya masa, yau fa alkawari ya cika, sai ya shirya ya yi dakon manzonsa
wanda zai zo ya raka shi ya fitad da shi iyakar kasa. Tun kafin safiya ta yi Makau ya rigaya ya
shirya sarai, amma manzon Sarki bai tashi zo masa ba sai bayan an yi sailar azahar. Makau yana
zaune yana ta duban hanya, sai zuwa can ya ga Sarkin Zagi da wani wai shi Simili suna zuwa akan
ingarmunsu. Da suka iso inda ya ke ba su ce masa kome ba, sai “Bismilla!"

Makau ya tashi, sai suka tambaye shi, “Wace jihar ka ke so mu fitad da kai ?"

Sai ya ce, “Ta wajen fuskar kasar zazzau.“

Suka ce, “Wuce mu tafi."

Suka sa shi a gaba suna ta ingizarsa har suka taho da shi kan iyaka. A nan suka bar shi inda tun
da Allah ya yi shi bai taba zuwa ba. Suka ce masa, “Yanzu kuma sai ka san inda za ka, mu dai nan
Sarki ya umarce mu mu tsaya, nan kuwa za mu bar ka, ko ka mutu, ko 'yan hari su same ka su
kama babu abin da ya miskile mu."

12

Makau ya ce, "Haka ne, in kun je ku yi mini godiya wurin Sarki, ku kuwa Allah ya fishe ku daji,
amin."

Makau Ya Sadu Da Maharbi

Da suka bar shi sai ya nemi gindin wata babbar itaciya ya zauna yana ta tunani, yana kiran
Ubangiji da Ma’aikansa, har kwadayinsa ya fita. Da ya ta da kai sai ya ga wani maharbi yana
yawo, daga shi sai kwari da baka. La’asar kuwa ta yi, Makau a lokacin nan kishirwa kamar za ta
kashe shi. Maharbin nan da ganinsa sai ya nufo inda ya ke, ya same shi ya gama kai da gwiwa.
Da ya iso sai ya yi masa sallama, Makau ya ta da kai ya amsa masa.

Bayan da suka yi gaisuwa, sai maharbin ya ce wa Makau. "Kai kuwa, bawan Allah, daga ina ka
fito ? Ina dalilin zuwanka wannan wuri a wannan lokaci ? Ko kuwa kun je hari ne, rana ta baci
muku kuka fantsamu cikin daji ?"

Makau ya ce, “Ko daya. Yanzu abin da na ke so tukuna ka ba ni ruwa in sha, kana in hankalina ya
komo na ba ka labarin zuwa na wannan bigire."

Sai maharbi ya bai wa Makau ruwa. Bayan da ya sha ya jima kadan har duk hankalinsa ya komo
jikinsa, sai ya ce wa maharbi, "Alhamdu lilahi, na gode, Allah ya saka maka da alheri bisa kan
wannan taimako da ka yi mini. Ka ji ka ji sanadin zuwana wannan wuri."

Da maharbin ya ji wannan labari, sai ya yi mamaki yana cewa, “Hakika yadda Allah ya kaddaro
abu haka ya ke faruwa. Mai gaskiya kuma har abada bai taba tabewa ba,"

Makau ya ce, “Ina dalilin wannan magana taka ?"

13

Shi kuwa ya ce, “I, na gani ne da Allah ya sa ka gamu da wani ne daga cikin 'yan'uwana, ba ni ba,
lalle da ka zama bawa tuni. Amma ka ga da ya ke a kan gaskiyarka ne wannan sharri ya same ka
abin ya zo da sauki, Allah kuma ya dada sawwake shi, ya taimake mu bisa dukan abin da za mu
aika, ya hawad da mu bisa kan abokan gabammu. To, yanzu kuma wane gari ka ke yi nufin ka tafi
?"

Makau ya ce, "Wai da ni bukatata ina so in tafi wani dan kauye ne wanda ya ke tsakanin Zazzau
da Kano, in yi zamana. Amma kuma ina so kauyen nan da zan zauna ya zama kasar wurin tana da
kyau wajen amfani. Domin bukatata yayin da na sami matsuguni sosai sana’ar da zan yi ita ce
noma. Bayan na zauna kuma na dan gyara gida ina so in aika iyalina su zo."

Ka Zauna A Makarfi

Maharbi ya ce, “Kai ! Lalle wajen daukar sana'a ka yi babban zabi. Tun da ya ke haka ne zan ba
ka wata ’yar shawara kadan in ka yarda, to, in kuma ba ka yarda ba, to. Shawaran nan ita ce a
gaba da Zazzau a hanyar Kano, akwai wani dan gari sunansa Makarfi. Mutanen garin kuwa
sanannu ne wajen aikin gonaki, noma a can yana da riba, amfaninsu kuwa kullum mai albarka
ne. Ina tsammani ya fi kyau a gare ka ka tafi wurin ka zauna. Ka ga a can kuma babu wani wanda
zai dame ka, duk mutanen garin babu wanda ya ke shiga cikin sha’anin dan’uwansa, domin kowa
a cikinsu yana da gwargwadon samunsa. Ka kuwa sani tsegumi ba ya yin yawa a wurin da yalwa
ta ke, sai dai wurin da fatara ta kafe gindinta.”

Makau ya sunkuyad da kansa ya dade, sa’an nan ya ta da kai ya ce, “Wallahi, ni yanzu abin da ka
fada mini duka zan yarda, domin dai na ga babu shakka kana kaunata. Saura ina so in tambaye
ka wani dan asiri wanda ya ke zan yi in kubuta daga hadari wanda zan hadu da shi kafin in kai
Makarfi.”

Sai maharbin ya kawo wata 'yar laya mai sasari ya ba shi, ya ce masa “Wannan ita ce abar da na
taimake ka da ita, kuma ina fata ka isa laflya. Allah ya kau da bacin rana." Suka yi ban kwana,
sa’an nan suka rabu, ko wanne cikinsu yana kuka.

14

Makau Ya Tasam Ma Zazzau

SAI Makau ya tashi a tsaye bayan da suka yi ban kwana da maharbi, ya dan jima kadan a wurin
da ya tsaya, domin bai san hanyar da zai bi ba ta zuwa Birnin Zazzau. Da maharbin ya ga haka sai
ya komo ya kama hannunsa, suka yi ta tafiya har suka fada a wani labi kusa da wani dan kauye.
Da suka tafi wurin sai maharbi ya ce masa, “Ka ga wannan dan kauye na gabam mun nan, ta nan
za ka bi, amma kada ka yarda ka shiga cikin garin, domin kuwa watakila in ka shiga ba za ka kara
fita ba har abada. Ya fi maka kyau ka raba ta gefen garin ka wuce. Kuma ka yi hankali lokacin da
za ka wuce, kada ka bi ta baryar arewa, domin a arewa da garin akwai gonar wani mutum wanda
ya ke mai sihiri da gaske. Ko wane mutum in dai bako ne, ko kuwa bawa wanda ya gudo daga
wata kasa yayin da ya iso inda gonan nan ta ke, sai ya tsaya a wurin, ya rasa hanyar da zai bi,
tilas sai ya shiga cikin gonar. Kullum kuwa shi mutumin nan bai taba rabuwa da gonarsa ba.
Saboda haka in ya ga mutum ya tsaya kusa da gonar yana dawainiya sai ya zo ya kama shi ya
maishe shi bawansa."

Makau ya ce, “To, na ji.” Suka sake yin ban kwana a wurin, Makau ya yi gaba, maharbi ya koma
da baya zuwa inda da ya hadu da Makau.

Makau ya kama hanya har dai ya iso inda garin nan ya ke. Da ya zo sai ya ki shiga ciki, ya yi aiki
da dukan abin nan da maharbi ya gaya masa. Tun da ya kama hanya bai waiwaya ma ya dubi
garin ba, sai da ya tabbata a ransa cewa ya ba shi baya da gaske. Yayin da ya ga ya tsere daga
garin nan sai ya nemi gindin wata itaciya ya zauna ya huta, ya kuma ci dan abinci.

Bai jima da zama ba sai ya ji kofatan dawaki a dama da shi, kuma ya ji maganar mutane kowa
yana ba dan'uwansa labarin abin da ya yi yayin da suka tafi hari a wadansu wurare. Da jin haka,
sai Makau ya hau bishiyar da ya ke gindinta, ya buya a cikin rassanta.

Da suka iso wurin sai wani daga cikinsu ya ce, “Kun ga a wannan wuri mun taba yin fada da
wane da wane yayin da mu ke dawowa daga hari. Ran nan ba mu sami kome ba sai wani dan
yaro karami wanda shekarunsa ba su wuce bakwai ba. Mu kuwa mu uku ne.

15

“Da muka iso nan muka tsaya muna hutu, sai wani daga cikimmu ya ce, “To, yanzu ina dabarar
da za mu yi da yaron nan ? Yaya kowane dayammu zai sami ladar wahala tasa daga gare shi ?"

“Da jin wannan jawabi sai wanda yaron nan ke wurinsa ya yi farat ya ce, “Wane, me ka ke nufi
da fadin wannan magana mara dadi haka? Ashe kai dai kaza ne. Yaya za ka ce wai kana son wata
moriya a jikin wannan yaro, bayan ni na sha wahala, ni daya na kama shi. In da dadi me ya hana
ka kamo naka ?"

“ Dayan kuwa da jin wannan magana, nan da nan ya zaro takobinsa, ya ce, “To, yanzu zan
tabbata maka cewa wannan yaro ba naka ne kai daya ba.

“ Da ya cira takobin bai fasa ba sai ya fille kan yaron, yace da maigidansa, “To, ka ce kai ka kamo
shi, dauki gangar jikin Iadan wahalarka, mu biyu kuwa kan ya ishe mu.

“Bayan da mutanen nan suka gama tadi suka huta, sai suka tashi, kowa ya dare bisa kan dokinsa.
Suka kama hanya sosai da hanzari. Da Makau ya ga sun yi nisa sai ya sauko. Yayin da ya ke
saukowa sai ya ga wani abu a gindin itaciya, ashe jaka ce daya daga cikin mutanen ya yar, babu
kome cikinta sai liyarai. Sai ya dauka, ya kama hanya yana take da sawunsu har kwana guda, ba
hutu balle ya tsaya ya ci abinci.

Ya Ga Ganuwar Birni.

Yana cikin tafiya sai ya hango ganuwar gari dam gabansa. A lokacin nan kuwa masu dawakin sun
rigaya sun shiga cikin gari. Makau ya yi ta tafiya har ya iso kofar garin ya shiga. Ya ce wa Sarkin
Kofa, “Malam, wane gari ne wannan ?"

Sarkin kofa ya ce, “Birnin Zazzau ke nan, abokina."

16

Da jin haka Makau ya ajiye zuciya, ya ce, “Alhamdu lillahi Allah kai ne mai arzutawa !"

A nan bai gusa ba suka yi abota da Sarkin Kofa, har Sarkin Kofa ya ce, “Raina ya yi fari da
ganinka, lalle sai ka bakunce ni."

Makau ya yi murna, ya sauka gidan Sarkin Kofa. Da dare ya yi suka ci abinci. Bayan da suka gama
suka wanke hannayensu, suka shiga tade-taden duniya. Makau kuwa ya habarta wa Sarkin Kofa
dukan abin da ya same shi.

Sarkin Kofa ya tambaye shi, “Yanzu ina ka ke nufin tafiya ?"

Makau ya ce, “Na ji labarin wani kauye ne a kasan nan sunansa Makarfi, ina so in tafi can in duba
ko na iya zama, don na ji kasar tana da kyau ga noma."

Sarkin Kofa ya ce, “To, madalla, ni ma ina da wani shakikina a can sunansa Tanimu, in za ka tashi
sai in ba ka takarda zuwa gare shi."

Da gari ya waye, Makau ya nufi wurin Sarkin Kofa ya ce zai tashi amma yana so ya hada shi da
wani yaro su tafi kasuwa ya sayi wadansu kaya. Sarkin Kofa ya hada shi da yaronsa, suka tafi.
Makau ya sayi fartanya da gatari da masassabi da sungumi. Da ya gama saye-sayensa ya komo
gida. Suka yi sallama da Sarkin Kofa, ya kawo guzuri ya ba shi. Ya rubuta takarda zuwa ga
dan'uwansa Tanimu, ya ce:

“Bayan gaisuwa, ga wannan mutum sunanasa Makau, mutumin kirki ne, na turo shi gare ka. Sai
ka tambaye shi labarinsa, da kuma dalilin da ya sa ya fito daga garinsu. Kuma ya ce yana so ya
sami wurin zama ne ya yi noma. Ina so ka yi masa halin arziki, ka lura da shi, ka ba shi gona da
wurin da zai yi gida, domin yana da iyali suna zuwa daga baya."

17

Da ya gama ya ba shi. Makau ya yi masa godiya kwarai, suka yi ban kwana. Sarkin Kofa ya kira
yaronsa, ya sa shi a hanya. Makau ya kama hanya ya yi ta tafiya har ya zo Makarfi. Ya tambayi
gidan Tanimu, aka nuna masa, ya tafi ya ba shi takarda. Da Tanimu ya karanta ya yi masa
maraba, ya saukad da shi a gidansa ya kawo masa abinci. Bayan da ya gama cin abinci sai ya ba
shi dukan labarinsa.

Tanimu ya ce, “To, gobe idan Allah ya kai mu zan nuna maka gona. Akwai kuma wani gida inda
gyatumata ta mutu kwanan nan, in zai yi maka sai ka gyara ka zauna a ciki."

Ya Aika Iyali Su Taho

MAKAU ya yi zamansa a Makarfi, ya yi ta noma, ya gyara gidansa ya sayi bayi biyu da kudinsa da
ya tsinta, har ya soma arziki, ransa ya kwanta. Sa'an nan ya tafi wurin Tanimu, ya ce masa yana
so ya aika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login