Showing 12001 words to 15000 words out of 19982 words
Chapter 5 - Shaihu Umar Book Complete Writing by Sir Abubakar Taɓawa Balewa.pdf
dakinsa, su kuma suka tafi. Tun fitarsu da safe ba su
dawo ba sai bayan sallar azahar. Ina cikin zamana a dakinsa sai na fara jin hayaniyar mutane da
muryar Gumuzu. Kan a jima kadan, sai na ga Abdulkarim ya shigo cikin daki. Na yi masa barka da
zuwa, shi kuma ya ce mini, "Shi ke nan. Tafi gida".
32
Da fitowata daga dakinsa, in dai duba haka, sai na ga bayi cikin kangi an shanya su kawai a rana.
Da na dada dubawa cikin bayin nan, sai na ga uwata da uban nan nawa, wadanda aka kamo ni
da su daga gona. Daga nan sai zuciyata ta karai, tsorona kuma a ya yi yawa. Ai da na ga haka sai
na sunkuyad da kai na wuce, hawaye yana zuba a idona. Na tafi gida, aka ba ni abinci, ga shi ina
jin yunwa amma dole na bar shi. Ba abin da na ke tunani sai bayin nan. Yayin da duk na
sunkuyad da kai sai in gan su. Kai, na dai zama sai ka ce wanda aka kawo masa labarin ubansa da
uwa tasa sun mutu. Na dame, duk na rasa abin da ya ke mini dadi cikin duniyan nan, yo ai dole
sai na tafi dakin uwar goyona na yi kwance sai ka ce wanda ciwon ajali ya kama shi. Na yi kawai,
na daga kaina ina duban rufin daki ina ta tunani."
Yayin da Ina cikin ninkayar tunanina, sai na ga mai gida Gumuzu ya shigo cikin gida. Da shigarsa
kuwa sai na ji ya kama sunana, ina Wane ? Ni kuwa da jin haka, sai na yi firgigi na tashi, na ce,
"Ga ni."
Na tafi gare shi, ya kama hannuna ya ja ni zuwa wajen gidan da Abdulkarim ya sauka. Muka zo
muka shiga cikin gidan muka iske shi yana karatun Alkur'ani cikin Suratul Bakarati. Da shigarmu
sai ya rufe littafi, ya ce wa Gumuzu, "Har ka same shi ?"
Ya amsa ya ce, "Ai ko da ma shi ba mai yawo ne ba kamar Sauran yara."
Daga nan sai suka shiga maganganu wadanda ba ni iya ganewa sosai, wadansu na kan ji,
wadansu kuwa kamar yare ne. A karshen maganarsu sai na ji Gumuzu ya ce, "Abdulkarim, ai ka
cuce ni da ka raba ni da wannan yaro, domin tun da na ke ganin yara ban taba ganin mai hankali
mai lura da kansa kamar wannan ba. Gama ka ga tun ran da Allah ya sa na zo da shi gidan nan
ban taba jin wata daga cikin matana, ko wani nawa, ya ce tir da yaron nan ba."
Abdulkarim ya amsa, "Irin wannan hali shi ne Larabawa su ke so, mutum na duniya duka in ba
shi da hali ko shi wane ne, ko Fari ko Rawaya ko Baki, kamar dabba ya ke. Domin hankali da
basira da hikima ba su tabbata daga cikin kome sai daga kyakkyawan hali."
33
Da jin wadannan maganganu fa, sai na fara sakawa a raina cewa, "Lalle ba shakka Abdulkarim
zai tafii da ni kasarsu.
Ina cikin sakar zuci sai Gumuzu ya juyo gare ni ya ce, "Umar, ga Abdulkarim ya roke ni arziki yana
sonka. Son nan kuwa da ya ke maka ba wai ka zama bawansa ne ba. Yana so in ka dauka a ranka,
ka ga za ka iya zama da shi, ka zama dansa gama ba shi da da, ko dan dangi ma babu a gare shi.
Ni na yarda ku tafi tare da shi yanzu yardarka ce kawai mu ke jira."
Bayan wannan sai na daga kai kawai ina duban nisan kasarsu Abdulkarim, kuma ina tunawa
gyatumata tana da rai ba ta ma san ta inda Allah ya shilla da ni ba. A wurin fa sai duniyan nan ta
taru ta yi mini baki kirin, ban san sa'ad da hawaye ya zubo mini ba. Da ganin haka sai Abdulkarim
ya tambaye ni wai ko ba ni sonsa ne ? Ni kuwa na amsa masa ba haka ba ne, ba ni so ne in rabu
da kasarmu. In na bi shi yaushe zan dawo gida ? Shi kuma ya ce mini kowace shekara in zai zo
lalle zai zo da ni domin in duba mutanen kasarmu.
Na ce, "To, na yarda." Don kada su ce na cika rashin kunya bayan kuwa da sun yabe ni. Bayan da
aka gama wannan magana sarai, na yarda, sai Gumuzu ya ce mini in koma gida. Da na tashi zan
tafi sai Abdulkarim ya kawo kantu babba ya ba ni game da wadansu dabinai kekasassu wadanda
babu irinsu ga zaki.
Sai na durkusa na karba, na mike tsaye na kunshe su a cikin babban bantena na saki, wanda
Gumuzu ya saya mini. Na fita na kama hanyar gida. Na isa gida duk raina a bace, sai na tafi wurin
uwar goyona na zube mata a kan mawanka na koma jikin shamaki na takure, na gama kai da
gwiwa, na zama dai abin tausayi ainun. Da ganin haka sai ta fashe da kuka tana ta tambayar abin
da ya same ni. Ni kuwa na habarta mata labari tun daga farko har karshe. Ta yi ta kuka tana
cewa, "Babu kome, Umar, kai dai ka rike a ranka Allah shi ne Sarki."
Muka yi ta tadi har Allah ya sa Gumuzu ya shigo ya fada mata da bakinsa zan tafi kasar Masar
tare da wani Balarabe abokinsa. Ta ce "To, Allah ya ba mu jinkiri dai."
34
Ya ce, "Amin."
A kwana a tashi ran nan bayan an yi wannan magana da kwana goma sha bakwai sai Abdulkarim
ya yi niyyar tashi. Domin ya rigaya ya shirya sarai, bukata tasa duka ta biya, ya sayi bayi iyakar
sayensa. Ban da bayin nan kuwa ya sayi wadansu guntayen bakaken rawuna da bakaken
zannuwa da makamantansu don guzurin hanya. Bayan ya gama shirin nan nasa sosai, ana kamar
gobe zai tashi, sai ya aiko aka kira ni na tafi, ya shaida mini cewa ya gama shiri, gobe zai tashi da
sassafe, in je in yi sallama da abokaina da kuma iyayena mata, watau iyalan Gumuzu.
Na ce, "To." Na tashi na koma gida na yi wa dukan jama'a ban kwana, sa'an nan na kunso 'yar
tabarmata a hammata na nufo gidansa, domin in kwana can kada in makara. Na same shi a
zaune wajen la'asar, bayan ya kirga bayinsa ga kuma wadansu a daure guda goma dabam
wadanda Sarki ya aiko masa da su sallama tasa. Dare ya yi muka shiga daki da shi, muka kwana
kan shimfida daya har asuba ta yi.
Mun Fita Birnin Kano
ASUBA na yi sai na ji ana busa wani abu kamar kaho, kuma ana buga kuge. Dajin wadannan sai
na dimauce na tashi a firgice, na ta da Abdulkarim na gaya masa. Shi kuma ya ce mini wai
wadannan alamomi ne na matafa, watau sauran 'yan'uwansa sun shirya ke nan za su tashi. Ai
nan da nan sai ya bude kofa ya fita, ya je ya jawo wani farin rakuminsa mai tozo biyu. Sa'an nan
ya tafi shamaki inda bayin nan su ke shanye a filin Allah kamar tumaki, ya tashe su, muka mika.
Muka fita Birnin Kano da asuba ranar Asabar, uku ga watan Ramalan, sa'an nan hijirar
Annabimmu Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallama) tana da shekara dubu da dari uku dai
dai. Dukan masu zuwa kasar Masar sai da suka hallara a kofar gari tukuna. Na manta da sunan
kofar yanzu. Da aka gama taruwa kaf sai aka ba da alamar tafiya. Kafin mu tashi daga kofar,
Sarkin Kano ya aiko mana da masu dawaki wajen hamsin domin su raka mu.
35
Da za a tashi sai maigidana ya kira ni ya dauke ni ya dora ni a gabansa a bisa kan rakuminsa.
Muka yi ta tafiya, ni ban san jihar da mu ke nufa ba, har rana ta fito ta fadi ba a sauka ba. In dai
gajarta maka, tun tashimmu daga Birnin Kano ban ga mun kwana wani gari ba sai Birnin Kuka.
Da muka nausa daga Kuka dai ba mu tsaya ba sai a wani sarari mai yawan yashi. Ba gida ko daya
a wurin sai wadansu alamu kawai na bukkoki, a nan ne ayari su ke tsayawa su shirya su debi
ruwa kafin su shiga cikin babbar hamada. Muka kwana biyu, ba abin da Larabawan nan su ke yi
sai gyare-gyaren kayan fada, kuma ana ta debo ruwa a salkuna ana ta labta wa rakuma. Kafin
mu tashi sai wani Balarabe tsoho ya zo wajen Abdulkarim yana fada masa, ya shaida wa
mutanensa su shirya, domin inda za mu shiga wuri ne mai hadari. Daga nan fa sai na fara jin
tsoro, na yi tunani cewa ko za su yi yaki ne, shi ya sa na ga sun gyaggyara bindigoginsu da
takubbansu.
Bayan an jima kadan sai aka buga kuge, duka muka tashi gaba daya da la'asar, muka shiga cikin
babbar hamada. Kai! Cikin hamadan nan na ga abin mamaki, na kuma ji tsoron Allah, na gaskata
cewa abin nan da zaki ya ke fada wa kura gaskiya ne, "Dan Adam abin tsoro."
Tun da muka fara shiga cikin hamada ban ga wata bishiya mai girma ba, inda duk ka duba sai ka
hangi iyakar ganinka ba ka ganin kome sai yashi. Ba ruwan sama, balle wata ni'ima ta samu a
wurin. Akwai iska, amma ba irin ta wannan kasa ba. Iskarsu ba ta tare da kome ban da yashi.
Mutum duk wanda ya san yadda iskar hamada ta ke ba zai yi kwadayin ta same shi ba a cikinta.
Daga can dai in iska ta taso in ka duba sai ka ce hadari ne. Wani Balarab abokina ya ba ni labari
cewa wani lokaci in iskan nan ta sami ayarin mutane sai ta gigita su su rasa hanya, duk su
fantsamu cikin yashi. Kuma kome girman hanya a cikin hamada yayin da iskan nan ta bi ta wurin
sai ta bace. To, da fa muka shiga wannan wuri tausayin bayin nan ya kama ni. Yayin da duk na
dube su sai in gan su suna tafiya cikin yashi tubus tubus, duk gindinsu na baya-baya. Kai, ka san
abin da wahala a ce mutumin da ya saba da tsadari ya yi tafiya cikin yashi.
Haka muka yi ta tafiya cikin yashin nan kwana da kwanaki. Kai, kada dai in kai ka da nisa, tun da
muka tashi daga inda muka tsaya muka debi ruwan nan ba mu sake samun ruwa ba sai bayan
mun yi kwana uku tukun kana muka sami wani dan gari na wadansu Bugaje a bakin wadansu
'yan kananan rijiyoyi a cikin yashi. A wannan gari ne fa na ga abin mamaki. Duk mutanen garin
yaro da babba kowa yana da nadin bakin rawani misalin kamu uku. Daukacin wanda ka gan shi
36
da nadi kuwa duka ba shi da hula. Yawancinsu kuwa in sun yi nadi sai su jawo rawanin su rufe
fuskarsu da shi. Matan garin kuwa ko wacce ce daga cikinsu tana da wani dan kyalle wanda ta ke
rufe fuskarta da shi. Su irin mutanen nan na ji labari mafadata ne da gaske. Ni kuma da kaina na
ga alamar haka da jin magana tasu, gama kowace magana su ke yi sai ka rika jinta fada-fada.
Mun Taba Ciniki
Yayin da muka iso garin nan da na fada maka, sai muka tsaya a bakin rijiyoyin, muka debi ruwa
muka sha kowa cikimmu ya yi wanka. Bayan an jima kadan sai na ga mutanen garin mata da
maza suna barkowa zuwa gare mu. Kuma in duba haka sai na ga kowane bafatake daga cikimmu
ya kwance kayansa ya fito da bakaken rawuna da zannuwa irin wadanda a ke yi a Kano. Daga
nan kuma sai na ga wurin duk ya hargitse sai ciniki a ke yi. Fataken nan suka yi ta ciniki har rana
ta yi sanyi, zuwa can wajen la'asar sai na ga kowa ya kama kayansa ya daure. Da almuru ta fara
kusatowa sai kuma aka buga kuge muka tashi.
Muka yi ta tafiya cikin hamadan nan, ba mu fita cikinta ba sai bayan wata biyu da kwana takwas.
Ran nan fa bayan mun dibga tafiya mai tsanani sai ga mu a wani gari cikin kasar masar a yamma
da Kogin Nil, wai shi Ber Kufa. Garin fa nan ne garin su Abdulkarim, inda zan zauna har shekara
da shekaru. Da muka kusa isowa sai Abdulkarim ya ce mini garinsu ke nan, gidansa kuma yana
kusa da inda na ke hangen nan. Mu gusa kadan sai ga mu a cikin gari wanda ban taba ganin
irinsa ba tun da uwata ta haife ni. Da shiga garin bayan mun wuce gida uku sai muka kawo gidan
Abdulkarim. Muka sauka a wurin da bayinsa, saura kuma suka wuce zuwa gidajensu.
A lokacin nan bayin sun rigaya sun gaji tibis aka kawo musu ruwa da abinci, amma ba su iya taba
ko daya ba sabo da gajiya. Ni da isowarmu sai Abdulkarim ya dauke ni zuwa wajen matarsa ya
ajiye ni, kana ya fito. Bayan da bayin nan suka huta sarai, hankalinsu ya dawo jikinsu, sai suka
fada wa abincin nan, sai ka ce fara ta sami gona inda dawa ta fara tsirowa ta fada da figa.
Abdulkarim ya zauna a wajen bayin nan har suka gama cin abinci sarai , kana ya shigo gida ya
same mu muna zaune da matarsa, muna tadi da Hausa, domin ta iya. Dalili kuwa tun sa'ad da ya
fara ciniki da Kasar Hausa ya taba zuwa da ita, suka yi wajen shekara uku a Kano. Ya shigo ya ba
ta labarina sarai, ya gaya mata dukan abin da ya yi nufi da ni. Sai ta yi murna da gaske.
37
Bayan an kwana bakwai na saba sosai da matar Abdulkarim, ai ran nan ya ce yana so ya je bakin
teku, don ya sayad da bayinsa. Da can ma ya taso da bayi tamanin, amma ashirin da biyar sun
mutu a hanya. Kafin ya tashi sai ya ce wa mata tasa bayan ya tafi yana so ta kai ni wajen wani
malami makwabcinsa in rika karatu. Ni kuma ya kira ni ya gaya mini haka, kana ya tashi. Ran da
ya tashi da safe, da yamma ta yi mata tasa Zainab ta tafi da ni wajen Shaihu Mas'ud, wanda zan
yi karatu a gare shi. Ta habarta masa duka abin da maigidanta ya fadi. Da ta gaya masa haka sai
muka dawo gida tare, ta ce ba zan fara karatu ba sai gobe, in Allah ya sa muna da rai.
Kashegari da sassafe ta ba ni sabuwar riga da hula da wando, da kuma abin kalaci. Bayan na
karya kumallo sai ta ce in yi niyyar zuwa makaranta. Na fita na tafi gidan Shaihu Mas'ud, na fara
karatu. Kai, ya zama dai har in na fara karatu ba ni ma son zuwa gida ko kadan sai don abinci.
Ban jima ba ina karatun sai abin ya zama mini kamar dara, gama ko ina na ke sai ka ji ina yi. Kafin
wata guda ai sai allo. Kafin Abdulkarim ya dawo daga bakin teku ina iya yin harda daga Alhamdu
har zuwa Sabbi.
Ran nan bakwai ga wata, ana cika ciki saura kwana uku, sai Abdulkarim ya dawo. Da zuwansa
Zainab ta ba shi labarina, ya yi murna ainun, ya sa aka kama rago aka yanka, aka yi mini sadaka.
Daga ran nan kome na ce ina bukata nan da nan sai a ba ni. Babu irin tufafin da ban sa ba.
Da shekara ta kewayo, Abdulkarim ya yi niyyar komawa Kano. Ya ce za mu tafi tare bisa ga
alkawarin da ya yi mini. Da na ji haka na kosa lokacin ya yi in je in gano kasarmu. Bayan da muka
shirya duka, sai aka kawo masa labarin abin da ya faru cikin Kasar Sudan. Shi ne Muhammad
Ahmad ya tayar wa Kasar Masar, ya ce wai shi ne Mahdi. Mutanen Kasar Sudan duk suka bi shi.
Aka aika masa da yaki daga Masar. (Domin jin labarin wannan Mahdi, sai a nemi wani littafi mai
suna ABDULKADIR SALADIN. Za a iya samun littafin a shafin Taskar Bukar Mada -
http://bukarmada.blogspot.com )
Da Abdulkarim ya ji haka ya ce gara mu dakata mu ga abin da zai faru, domin hanyar da za mu bi
ke nan. A sa'ilin nan kuwa kowa yana tsammani abin ba zai dade ba, nan da nan za a a gama mu
tashi. Muna cikin haka sai aka kawo labarin yaki ya baci. Jama'ar Mahdi suka yi nasara, dukan
Kasa ta yamutse. Aka sake aikawa da yaki daga Masar, abin ya rigaya ya shaddada. Da muka ji
haka babu damar tafiya, tilas muka zauna.
38
Ka san halin yaro, yau da gobe sai na fara mantawa da kasarmu, da dangina, har da uwata. Na yi
ta karatu har wajen shekara biyu na sauke. Na sauke Alkur'ani ranar Laraba sha daya ga watan
Muharram. Ran nan an yi biki wanda watakila ba zan sake ganin kamarsa ba. Da sassafe aka
kama shanu uku aka yanka, aka soke rakuma biyu, aka yanka tumaki da talotalo wajen tara.
Abincin da aka yi a gidammu da kuma wanda aka kawo gudummuwa ba shi da isani. Abdulkarim
ya shiga cikin soronsa ya fito da riga irin ta Larabawa tabbatacciya mai walkiya kamar azurfa, da
wandon Tunas wanda aka yi masa aiki har kubaka, da wata irin zulaika ta alharini, da hulad dara
mai tuntun farin alharini, da rawani rawaya. Dukan kayan nan ya ba ni in sa. Da na sa ya ce in
wuce gabansa zuwa makaranta inda gaggan malamai suka taru, domin in zo in yi 'yar takara su
ji, kana su yi mini addu’a. Na wuce gaba har muka zo makarantar. Muka zauna, kowa sai dubana
ya ke kawai yana mamaki. Shaihu Mas'ud sai ya