Showing 1 words to 3000 words out of 151322 words
Chapter 1 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
KE ALHERI CE♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg1⃣
KATSINA
Duk wanda ya san Jami'ar Umaru Musa Yaradua dake garin Katsina yasan wajen gari take, a
k'alla ba a kasara ba tafiyar minti arba'in da biyar (45) ne zuwa cikin gari.
Daliban aji d'aya, na (Department of MicroBiology) ne suka fito a gajiye daga aji misalin karfe
shidda da minti biyar (6:05) na yamma kasancewar sunyi lectures 4-6.
Mimi tayi wujiga-wujiga don tsabar gajiya, ta kalli kawayenta biyu tace
"Wayyo Allah! da alamun zamu kwana a Hostel yau, ji yanda garin ya hade rai, ko dai ruwa
zaayi?"
Usheey cikin damuwa tace "kai! dole captain ya nema mana sauki gun lecturer nan, a yi
rescheduling lectures din, ko wednessdays ne da safe, don bala'i 4-6 ran saturday?"
Dayar me sanye da nikaf tace
"Don Allah ku mu daga kafa, kar su cike bus din, kun dai san mazan nan ba hakuri zasu yi ba,
balle yanda suka ga hadarin nan kowa so yake ya tafi gida." Miemee tace "nikam i dont have
dat strength."
Usheey tace "aikam tafiyarmu zamu yi mu bar ki, suka cigaba da tafiya.
Mai sanye da nikaf din tace "laahhh! kun gani ko, school bus2 sun tafi." Miemee tace "wallahi
kina da damuwa, mu kadai ki ka ga bus din ta bari?"
Mai nikaf din ta dauke kai don tasan da ta sake bude baki tana iya fashewa da kuka. Usheey
tace
"Ai ke Mimi ko karfe nawa zamu kai na san ko a jikin ki."
Daga nan ba wacce ta kara magana, ko da suka karasa Student center duhu ya fara yi, kuma
matan da ke gurin daidaiku ne, wasu an basu lift. Miemee tace "ko mu zauna a kujerun SUG
kafin bus ta dawo?"a Usheey tace "chap sabod gamu gantaIallu ko?"
Dayar tace "to ya zamu yi? ko mu karasa gate kila mu samu ko commercial a chan?"
Mimi tace "chap wallahi bazan iya tafiyar minti ashirin ba."
Usheey tace "toh bari mu barki nan."
Tafiya su ka fara yi miemee tace "bala'i wlh ba za ku barni nan ba, ta bi bayan su da sauri.
Tafiya su ke yi suna fira jefi-jefi, dare kam har ya fara yi ga hadari ya kara haduwa, Agogon
wayar ta karfe7 saura minti 15, Idon mai nikaf ya ciko da hawaye, tsiraran motoci suke wucewa,
miemee tace "wlh a ruwa muke, dama mu samu lift. Usheey tace "eh wlh".
Ba su rufe baki ba sai ga wata bakar mota mai bakin gilashi ta danno a guje, har ta dan gifta su,
sai kuma motar ta fara dawo da baya da baya. Miemee tayi saurin gyara zaman rigarta, tace
"yauwa ai nasan na annabi ba sa karewa, ga lift nan na zuwa" usheey tace "Barkan mu Allah ya
takaita mana wahala ba sai mun je gate ba" me nikaf cike da mamakin kawayenta tace "yanzu
motar nan mai tint zaku shiga? Kuna jin sauti na tashi kamar ba dare ba?" Usheey da miemee
suka buga tsaki a tare, Usheey tace "kinga dai Besty idan muka bar motar nan ta tafi, ba mu
san lokacin tafiyar mu gida ba, daga cikin makaranta ta fito balle mu ce sace mu za ayi, "
Miemee cikeda takaici tace "Abu mai sauki, idan ba ta shiga sai mu yi tafiyar mu mu barta nan"
kafin tace wani abu motar nan ta iso ta tsaya daidai su.
Ido suka zuba ma bak'in windon motar, a hankali glass din ke sauka, idanuwan 'yan matan nan
3 tsam cikin halittun da ke zaune gaban sits din motar, Su biyu ne, daya na zaune sit din direba,
dayan kuma na zaune a kujera me zaman banza, da alamu abokai ne, Mimi da fara'arta tace
"sannun ku fa, please, cikin gari kukayi"? Me tuk'in motar ya dan yatsina fuska, a tak'aice yace
"Eh" dayan ko kallon su beyi ba, ba tare da bata lokaci ba mimi ta sa hannu ta bude baya, zata
shiga kenan me tukin motar yace "ba dai da Ninja din chann za a shigar min mota ba?" Mimi ta
kalleshi da mamaki, tace "ninja kuma"? Yace ehmana wanchan me Nikab din, Ushee a hankali
tace Seebi daga nikab dinki, wacce aka kira da Seebi ta kalli Ushee cike da takaici tace bazan
daga ba, ba zan kuma cire ba, sai a sannan Abokin ya juyo don kallon mai nikab, itama ta dago
kai kenan suka hada ido, sun dauki kusan seconds goma suna kallon-kallo, yayi saurin dauke
kai, ya maida kallon shi ga Abokin shi, murya kasa-kasa kamar bai son magana"yace Maalesh
donAllah mu tafi" wanda aka kira da Maalesh ya kalli miemee yace "Malama kulle min kofa ko?"
Miemee za ta yi mar magiya kan yayi hakuri mai nikaf tayi saurin kulle kofar, Maalesh ya ja
motar sa a sittin ya bar gurin.
Mimi cike da fada tace "Haba SEEBI menene haka?" kin wargaza mana damar da mu.ka
samu na tafia gida, Ushee tace aa fa mimi, shima ya sa wulakanci a alamarin shi, menene abun
ce mata Ninja? kuma har sai ta cire nikab zai taimaka ya dauke mu?
Mai nikab din tace "Dama chan basuyi niyyar daukar mu ba". Ushee tace Seebi kin lura da na
gaban motar? Side view din shi kadai nagani, amma nagane Azababben guy ne ko kallo fa ba
mu ishe shi ba, Uhm kadai Seebi tace a yayin da ta tuno kallon-kallon da suka yi da shi,
Miemee cike da masifa tace tunda dai sun tafi ai shikenan, Seebi ta mana Bukulu, kila da ko
numbern mu sun amsa, Usheey ta ce ke kuma matsalarki kenan sun amsa number? Harararta
mimi tayi Seebi me nikab ta sa daria don ta saba ganin haka gun kawayen ta biyu, yanzu ba
wannan ba burin ta a yanzu be wuce ta bude ido ta ganta a gida ba.
_Bibilicious Biebee_
KE ALHERI CE♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg2⃣
Haka suka cigaba da tafiya har suka fita gate, suka tsallaka titi, a lokacin kuwa dare yayi don
bakwai ta gota. Zuciyoyin su ya fara karaya, tsoro da fargaba ya mamaye su, barin ma mai
nikab din da ta fara hawaye a cikin nikabin ta.
Sunyi nesa da gate Ushee tace "idan ba so kuke mu karasa cikin Gari a kafa ba ku tsaya mu
samu mota ko daga cikin wadannan masu wucewa ne" Miemee please ki taran mana lift,
Miemee ta tabe baki, tace "ba zan tsaida ba" donAllah mana miemee inji Mai nikab, in tsaida ki
k'i shiga? Da sauri ta zame nikabin fuskarta, tace "kinga na cire gabaki daya" Miemee tayi
murmushi tace "eh lallai dagaske kike" ta dan matsa bakin titi ta sa hannu, motoci goma suka
wuce da karfi ba tare da sun tsaya ba, Mimi tace ba fa zasu tsaya ba, ni na gaji. Ushee tace
"Dont give up" Miemee ta wurga mata harara tace malamai kuzo ku sa hannu kila mu samu
wani ya tsaya. Ushee tayi daria ta matso kusa da mimi suka sa hannu.
Daga nesa suka hango wata Jan Mota ya doso da full light dinsa, suka dage wurin daga hannu
yanda za a gansu daga nesa, Motar ta cigaba da dosu har ta gifta su, Ushee da karfi tace "kaii
yau mun shiga 3" Seebi da ke gefe hawaye kadai ke zuba daga idanuwanta.
Horn suka ji ga baki dayan su ka kallo inda suka ji horn din,Miemee tace "lahh ga wata BMW
na na zuwa da baya da baya, mai jan motar nan ne ya dawo, ushee tace muyi sauri mu karasa
gunshi kafin ya chanza ra'ayinshi, sauri-sauri suka nufe me motar nan.
Mimi ce gaba suna biye da ita a baya har suka iso inda mutumin yayi parking motarsa, ta
window miemee tace Assalamu Alaikum, mutumin ya sauke glass din motar sa, hade da amsa
sallamar Mimi, Waiyo Allah! Mimi bude baki tayi tana kallon mai motar, don ya hadu iya haduwa
kamar shi yayi kanshi. Ganin kallon da Mimi ke mishi ne ya sa shi cewa "Cikin Gari zaku?"
Ushee da ta lura kwatakwata hankalin kawarta mimi be jikinta ya sa ta matso kusa, itama kusan
abun da ya faru da Mimi ya kusan faruwa da ita, amma ta dake tace ina wuni? Cikin gari
zamuje, donAllah ko zaka rage mana hanya? Yace Bismillah, Ushee tace Mungode, tayi saurin
zunguran Mimi, Mimi ta wayance tare da saurin shiga gaban motar, Ushee ta bude baya ta
shiga tare da kallon kawarta da ke tsaye waje, tace "Seebi shigo mana" cikin sanyinta ta shigo
da Sallama, ya dan waigo ya amsa sallamarta ya dauke kai, bayan ya kwashe takardun da ke
bayan sit din.
Gaishe shi sukayi duka ya amsa musu, yace Students ne ku, suka amsa mishi da eh, amma a
hostel kuke ko? Ushee tace No day, cike da mamaki yace Day students kuma?ya akayi kukayi
dare haka? Mimi cike da yanga ta bashi bayanin dalilin su na yin dare, ya jinjina kai, yace ya
kamata a san nayi, in rescheduling lectures din za'ayi tok, idan kuma Buses za a karo don
tabbatar da an kai kowa gida, is very risky a bar dalibi mara abun hawa a nan, balle ku mata.
Allah shi kyauta suka amsa da Amin. Haka ya cigaba da tukin shi, Ba wanda ya sake magana,
ba kajin komai sai karatun Qurani mai Girma kira'ar Sudais.
Dif-dif sukaji, Alamun shigowar waya, mimi ta lek'a wayar kirar Iphone 6s da ke jone jikin radion
mota (AUX) taga Meema jikin screen din, Mutumin yace ma mimi dan taimaka ki min swiping,
da sauri mimee ta yi yanda yace.
Ba tare da ya kanga wayan a kunnesa ba yace "Hello Assalam Ailaikum" wata Zazzakar murya
su Ushee sukaji ta cikin speakers ba cewa "Hello Uncle Zaid kanajina?" Yayi murmushi yace
"Ohh Meema, so nawa zan miki maganar amsa sallama? Oh sorry Waalaikum Salam, Uncle
Zaid baka iso bane har yanzu? Meema ina cikin katsina, but sai naje masauki, idan na huta
zuwa anjima ko da safe sai na zo gidan ko? A shagwabe tace "haba mana Uncle Zaid, You
promised to come see us immediately you arrived" Ya sauke ajiyar zuciya, yace "toh bani
30mins zan karaso InshaAllah" tayi dariar murna, yay Uncle Zee Thanks, u d best" yace "erhm,
Rafeek na gida?" tace "No be dawo ba ko" ya danyi shiru yace "toh sai na iso" kafin tace wani
abu ya latse wayar.
Ushee ta kalli Seebi, sukayi murmushi, matuk'a wanda aka kira da Uncle Zaid ya burgesu, daga
jin wanda su kayi waya da ita sun san yar gata ce, don yanda take shagwaba da magana, a
hankali ushee ta rada ma Seebi 'kila diyar yayar sa ce' seebi gyada kai tayi.
Zaid ya dago wayarsa, ya dan rage gudu, ya shiga neman layin nephew dinshi, callertune din
yazo karshe ba amsa, ya sake redialling, yanzun ma kamar ba za'a dauka ba, a ka dauka ba
tare da ance komai ba, Zaid yayi gyaran murya, yace "Rafeek" chan kasa sukaji ance "Barka da
yamma" Zaid yace "lafia lao, Kana ina?" kamar bazai tanka ba, yace "Gani nan Maalesh zai
saukeni gida" yace"Okay toh, ku je ku min booking Liyafa hotel" Ok kadai yace ya kashe wayar,
Zaid ya murmusa a baiyane yace "Rafeek ikon Allah"..
_Bibilicious Biebee_
KE ALHERI CE♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg3⃣
Zaid ya kallo Miemee yace"Ina kukayi?" mimi ta yi far da ido tace"dukkanin mu unguwanni
daban muke, ka ajiye mu a National, sai mu hau keke napep" yace "Junction din bus? No,
kubari na sauke ko wacce a unguwar su" mimi ta yi murmusi mai sauti tace "ji fa nayi ana
jiranka" yace kar ku damu, ya kalli mudubi daidai saitin Seebi, yace Malama wani unguwa
kuke? Seebi baki ya fara rawa ta kasa magana, da sauri ushee tace mu muna ta Wurin Gidan
Masari, Miemee kuma na GRA wurin motel. Zaid ya jinjina kai yace wace Miemee? Miemee na
murmushi tace "nice nan" ya sake kallon madubi yace kece wa? Ushee tace nice Ushee,
wannan kuma Seebi, Zaid yayi murmushin da ke kara ma fuskar sa annuri, yace "inyee!, sunan
yan gayu ne daku, Miemee, Ushee da Seebi" sukayi daria duka, yace toh bari mu fara sauke
Miemee, ku ta unguwarku nayi.
Da taimakon Miemee na nuna mai hanya Zaid ya iso har kofar Gidansu, yayi parking, miemee
ta sadakar zaid zai tambayi numbern ta, sai wannan yanga takeyi, amma shiru takeji, a ranta
tace kila zai tambayi su Ushee, ta bude murfin kofar tace "Thanks So much Uncle Zaid" ya yi
murmushi yace bakomai, ta juya ta kalli kawayenta tace "toh kar dai a manta a fito da wuri gobe
don muna da GSP karfe takwas (8:00)" Ushee tace "InshaAllah" Seebi tace "ki gaida Mummy"
Miemee tace "Zataji, dayanku ya dawo gaba" Ushee ta bude murfin motar ta koma gaba. Mimi
ta daga ma Zaid hannu, Ya ja motar ya bar layin ita kuma ta shige gida.
Shiru ba wanda ke magana, sai da yazo unguwar yace ta wurin ina kuke? Ushee tace "ka ajiye
mu a wurin Makarantar Salamah" ba wanda ya sake magana har suka zo daf da makarantar
Salamah, yayi parking, Ushee tace mungode sosai, Seebi ta bude murfin motar,
tace"Jazakallahu khair" Allah ya biyaka yanda ka taimake mu" da sauri ya waigo don yaji dadin
adduar nan, duk da be samu ya ga fuskar yarinyar sosai ba yace "Amin Nagode" Suka rufe
kofar ya ja motar sa yayi cikin unguwan, Ushee tace toh Seebi sai da safe, Allah ya kaimu
Ushee, ko wa tayi hanyar Gidansu.
Sai da tayi tafia sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar gidan ta ga Nenen ta tsaye, da sauri
Nene ta rungumota tare da matse kwalla tace "Nasiba, ina kika tsaya haka? Duk kin tashi
hankali na, ince dai lafiya ko?" Nasiba ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Nene kiyi hakuri,
darasi mukayi 4-6, ko da a ka tashi ba mu samu abun hawa da wuri ba, sai da ma mu ka tako
har wajen gate kafin muka samu wani bawan Allah ya kawo mu har gidansu ushee" Nene tace
bakiji yanda na tada hsnkali na ba, don naga baki taba kai wa haka a makaranta ba, na ci kuka
na ni kadai, na fi minti 30 gaban gidan nan, ga shegen unguwar nan, ba wanda zaka aika. Da
na hana babanki ya sai man waya, amma saboda irin haka, dole xai siyo min, Seebi tayi daria
tace bari na shiga ciki in watsa, ko Laasar banyi ba wlh" Nene tace "yi maza, ga abincin ki chan
a madafa" ta amsa tare da shigewa cikin gidan.
Assalam Alaikum yayi sallama a kofar falon gidan, mamimakon a amsa mai, sai jin ihu yayi,
yayyy!!! Ga Uncle Zee oyoyo, wasu yanmata biyu suka zo suka rungumeshi, takaici ya cika
Zaid, be da yanda zaiyi sai dai k'irk'iro murmushin dole wanda hausawa ke cema Yak'e kafi
kuka ciwo, Babbar ta ja hannunshi zuwa dinning area, tace "Uncle Zaid, i know u must be
hungry" murmushi yayi yace "Aa meema, ciki na a koshe yake" ta marairaice tace "donAllah
kaci, ni da kaina na girka maka, wallahi na dade ina yi, please" Ya mata murmushin da ke kashe
ta yace "Meema i'm full wallahi, some other time ko?" be bari tace komai ba ya kalli dayar
budurwar yace "Aneesa Yaya na nan? Tace "eh Uncle Zaid yana sama" mikewa yayi ya hau
sama.
Ya shiga da parlorn yayan sa da Sallama, Yayan ya amsa mishi cike da farin cikin ganin
danuwansa, Barka da Yamma yaya, yayan ya amsa mishi da "Sannu da zuwa Engr. Zaid
Ibrahim Lema, Zaid yayi daria, yace ka fara ko yaya? Nan suka fara fira irin ta wa da kani cike
da aminci da kaunar juna, suna cikin firan ne Hajia Saude tayi Sallama ta shigo dauke ta tray,
tana kwarkwasa kamar wata yarinya, "Ahh! Zaidu, ka iso kenan? Ya amsa mata ba yabo ba
fallasa, ta dire tray din gabn mijinta ta na tsiyaya mai ruwan zafin shayi a dan karamin kofi, tace"
Kaima a zuba maka Shayin ko Zaid? Ya mike da sauri yace "aa nagode, bari inje masauki
nagaji" ya kalli yayanshi yace "Yaya bari na tafi zan shigo da safe in Allah ya yarda", Alhaji
Habib Ibrahim Lema yace "Allah shi huta gajia Zaidu".
A parlorn kasa ya iske meema da alamun jiran shi takeyi, tana ganinshi ta nufo shi da sauri,
Uncle Zee har ka gama da daddy? Yace eh nagaji ne, zan tafi na kwanta, tace yanzu ba za kaci
abun da na girka domin ka ba ko? Yace "sorry Meema" sai da na ci abinci kafin na karaso. Ba
haka taso ba sai dai ba yanda zatayi da shi tace "toh munje in raka masaukin naka" yace wa zai
dawo dake? Don ni bazan sake fitowa ba sai gobe, ta mai fari da ido tace"ba sai na kwana chan
ba" ya zaro ido, yace ke bana son shiririta, ta wayance tace "haba, kasan wasa nakeyi" ya
wuceta ta bi bayanshi "mai zan dafa maka da safe?" Yace "Nothing". Ta juyo a fusace tare da
fashewa da kuka haye sama..
Daidai haraban gidan mai gadi ya wangale gate, wata bakar mota mai bakin gilashi ta shigo,
Uncle Zaid ya tsaya