Showing 45001 words to 48000 words out of 151322 words
Chapter 16 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
ba, please
dont leave me i cant live without you" Jikin Rafeeq yayi sanyi ganin Uncle Zaid na hawaye a
kanshi, wani irin so Uncle Zaid ke mishi, ya dan dago ya share mai hawaye.
Washegari Zaid ya je Umaru Musa Yaradua University, Maalesh ya mai jagora gurin HOD
dinsu, Zaid ya gaya musu matsalar Rafeeq, yana so a bashi shawara, Level Coordinator na su
Rafeeq yace "Inaga yayi deferring semester din, har sai ya dawo normal, so that it wont affect
his CGPA" HOD yace "Gaskia, ne, Yayi Deferring Semester din wato zai Jiginar da Semester
din, ba wai yayi spilling bane, only disadvantage din shine, Mates dinshi zasuyi Graduating
shikuma zai dawo" Zaid yace is better ai hakan, InshaAllah zuwa next year din zai dawo normal
self dinshi sai ya zo ya cigaba daga inda ya tsaya" nan suka tsaida Magana.
Zaid ya samu Yayan shi ya mai bayanin komai, Yayan yayi naam da hakan, yace to kai Zaid
meye plans dinka kan danka? Ina tsoron Zuciyar Rafeeq tunda har ya iya ikirarin shiga dunia,
kar abokanan shi suyi influencing dinshi, su koya mai wasu halayar" Zaid yace " nayi tunanin
haka, shisa nace za mu danje hutu da shi, zan dauke shi muje Embassy muyi purchasing Visa"
Alhaji Habib yace "hakan yayi, K'ila ya dan washe ya dawo daidai". Zaid ya sanar da Rafeeq
zasuje dan hutu a kasar waje, ya fadi any country of his choice, Rafeeq beyi wani murna ba don
shi a ganinshi be kamata ace yana jin dadi ba, be ce komai ba, Zaid yace ko muje Dubai, ko
London, ko Saudi? Rafeeq dai be ce komai ba.
Zaid dai ya yanke hukuncin zuwa Paris Bayan sunje sunyi Umra, ya gama musu komai, ya
dauko Hutun Wata 3 a Gurin Aiki, suka wuce Saudi Arabia da, sai da sukayi kwana 7 kafin suka
wuce Paris.
Watan su Biyu a Paris daga shi sai Zaid a daki daya a Gado daya, Yanzu Ba yabo ba Fallasa,
kadaran-kadahan dai, da kyar ya ke bin Zaid gurin bude ido, Zaid be da wani burin da ya wuce
ya ga ya kyautata ma Rafeeq,hakan ya sa Rafeeq ya sa Zaid a zuciyar shi sosai, yaji duk
duniya be da wanda yake so sama da Zaid, ya sama mishi gurbi a ranshi, shima ya kudurta a
ranshi InshaAllah zaiyi k'okarin kyautata ma Rafeeq.Haka suka dawo Nigeria.
Nigeria ta na nan yanda suka barta, ba wani cigaba game da binciken Hafiz, ba wani leads,
Alhaji Habib yace a barsu Allah e Zai isar musu, Mayya kuwa Wato Meema, son Zaid kamar ya
kasheta, ba gun bokan da bataje ba ya karkato da hankalin Zaid gareta amma a banza, da taga
ba sarki sai Allah sai ta fara chusa kanta gunshi, tana nuna maitar ta fili, tuni Zaid ya dagota,
amma shi ya datse ma kanshi, shi Mijin Mace daya ce wato Safiyya. Zaid ya kasance mai taka
tsantsan da Sauda, duk da be ga wani alamun Sauda na da wani hali ba, amma be cin
abincinta be kwana gidan, dadin shi daya ba ruwan Rafeeq da cikin Gidan, shisa yake siyo
mishi abubuwan bukata na kayan kwali da gwangwani.
Zaid ya koma bakin aikinshi, Mami ta rok'i Zaid da ya nema mata dan karamin Gida, ba zaiyiwu
ta cigaba da Zama a cikin shi ba, da iyalan shi, wata rana zaa gaji da ita, duk yanda Zaid yaso
tankwara ta ya kasa, be da wani choice da ya wuce nema mata Gida a Malali, tayi Parking ta
koma chan, tana me kewan Safiyya da ta sha kuka ranar rabuwar su.
Bayan wata 1
Su Maalesh sunyi Graduating, suna ma jiran ayi posting dinsu Service (Bautar kasa).
Rafeeq ya kira Zaid a waya, Zaid yayi mamakin ganin kiran wayan shi, da sauri ya amsa,
kamar ba zaiyi magana ba Rafeeq yace "an fara registeration, nayi, idan anzo 2nd Semester
zan koma Makaranta" dadi kamar ya kashe Zaid, ya dinga shima Rafeeq Albarka, yasan yayi
hakan ne don shi, don ya sa shi jin dadi, kuma ya sa shi din".
A yau Asabar Safiyya Matar Zaid ta haifi diyarta Mace kyakyawa Kamar Rafee'ah, Jini ba wasa
ba, Murna gun Zaid kamar ya rungume Iska, Ranar Suna aka radawa diya Suna Rafee'ah, yan
Katsina sunzo suna, Sanin zasu zo ya sa Mami tak'i Zuwa sunar tayi zaman ta Gidanta, Rafeeq
ma ya zo, ya dauki diya ya rungume yaji sinta har cikin jinin jikinshi, dadi biyu, Ga ta jinin mafi
soyuwar Halitta Uncle Zaid, ga ta da Sunar Rafee'ah.
Bayan Yan suna sun watse Safiyya jini ya barke wa Safiyya, ta fara tsinkau tsinkau,Zaid ya
tsorata matuka ya danna kiran Aunty Aisha, suka dunguma suka kaita Asibiti, Nan dai Safiyya
tace ga garin ku nan. Inalillahi wa ina ilaihir rajiun. Bayyana Rudun da Zaid ya shiga bata baki
ne, kowa ya ji mutuwar Matar Zaid Safiyya, sai dai mu roki Allah ya sa Aljanna ce makomarta.
Zaid ya Zare kamar zautattace, don yana kaunar Matarshi fiye da tunani, yana tausayin su
shi da diyar shi Rafee'ah-Ayman, Rafeeq da Baban shi da Maalesh sunzo janaizar, sun sauka
masauki, Meema ji take yau Sallah a gunta don ba karamin farinciki mutuwar matar Zaid tayi ba.
Kwana 3suka tafi, banda Rafeeq da yace shi zai tsaya da Zaid don yasan yana bukatar shi,
kamar Lokacin suna, Mami bata bari sun ganta ba, sai Bayan da suka tafi ta dawo gidan Zaid
tana kula da diyar shi.
Rafeeq ya fito daga mota ya shiga gidan Uncle Zaid, Kai tsaye yayi Parlor, Tsaye ya ga Fuskar
da ba zai taba mancewa ba, Fuskar Mahaifiyar shi, tsaye take rungume da jaririya, Jikin Rafeeq
ya hau kyarma, idon shi ya rufe da sauri ya je ya fizge Rafeeah-Ayman, daga hannun ta, ya
rungume ta, Zaid ya mik'e da sauri yace "Rafeeq" yace "me wannan Matar takeyi a gidan nan?
Har ta ke taba min k'anwa? Zaid ya sausauta murya yace "Shes been here for a while" Rafeeq
cikin bacin rai yace "and you never bothered to tell me? Zaid yace" coz u never asked, u never
wanted to talk about her" Idan har kana so ka kara ganin kafana a gidan ka, This woman has to
leave, bana so in sake ganinta, kar kuma ki sake daukar min kanwa don kar ta koyi baki da
mugun halinta" Zaid ya kaura mai Mari, ya nuna shi da yatsa" I wont let you disrespect your
mother" Baby ta fashe da kuka, Rafeeq ya rungumeta, be damu da marin da ya sha ba yace "yi
shiru kinji fee'ah, zan samo miki me raino, mace mai mutunci ba kamar wasu matan ba" Zaid
yayi saurin kwace diyar shi daga hannun Rafeeq, yace "bata da wata mai raino da ya wuce
Mami, ba ta da Uwa da ta wuce Mami, itace Uwarta, duk me zakayi kayi" Rafeeq ya kalli Mami
da fuskarta yayi jazir saboda kuka yace "Ba zaka sake gani na a gidan ka ba" ya fita a fusace,
Mami ta bishi da gudu tana "Rafeeq, ko kallonta beyi ba" Zaid ka bishi kar ya dauki hanyar
Katsina yanzu, kar wani abu ya same shi" haka Zaid ya bishi a hanya, ya dinga lallashi, da yake
Rafeeq din be iya fushi da Zaid, nan da nan ya sauko amma dole ya bar Kaduna a ranar ya
wuce Katsina a ganin shi zaman shi be da amfani.
Bayan Shekara Daya (A gurguje)
Abubuwa da dama sun faru a shekarar da ta gabata, Kamar yanda Sauda ta sha k'okarin
Kashe Rafeeq ta hanya da dama bata samu nasara ba, har ta hakura ta barshi na wani lokaci,
kila yayi amfani, Daga abubuwan da suka faru, ciki kuwa har da Spilling din da Rafeeq yayi a
Makaranta, an rasa gane dalilin spilling dinshi, don an binciko takardun shi an ga Yayi passing,
an rasa ta ina aka samu tangardan(Ni dai nace Boka na kan tudu), Rafeeq kuwa ko a jikin shi,
dama da Uncle Zaid ya koma karatu last year, amma yanzu ko sama zata hade da kasa ba me
sashi komawa School, Su Maalesh sun fata bautar kasa.Zaid yayi Mamaki matuka, dole kenan
sai ya sake dawowa? Matsalar shi daya yanda zaiyi convincing Rafeeq ya sake wasting
shekara daya, Sai da Zaid ya hada da kuka kafin Rafeeq ya amince da zai sake dawowa, da
sharadin idan ya sake failing ba shi ba boko har abada, Zaid yayi saurin Amincewa da hakan, a
ganin shi Wannan karon akwai nasara.
A wannan karon ne Seebin Nene suka Shiga Jamiar Umaru Musa Yaradua.
*Wacece Alheri?*
Ta yaya ta zama Alheri?
*Shin Sauda zata cigaba da Samun Nasara a duk abunda ta sa gaba?*
*Rafeeq na tava dawowa daidai kuwa?*
Da tambayoyi da dama da kuke son amsoshin su, ku biyoni sannu a hankali.
***********
CIGABAN LABARIN.
KE ALHERI CE ♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣2⃣
*UMYU Katsina*.
"Nasiba Muhammad, maabociyan sa nikab, yanzu da hukumar Makaranta tayi hani da sa
nikab sabo da matsalolin tsaro ya zakiyi?" Miemee ce ke maganar nan, ta na yi tana daria,
Ushee tayi saurin shafewa tace "Ahh, k'ila zata daina zuwa Makaranta, yajin aiki zasuyi ita da
yanuwanta Ustazai masu sa Nikab" suka sake fashewa da daria. Nasiba ta dan harare su, tace
ba abun daria bane "Dollah ku bar dariya, its not like its funny, ni ban ga amfanin hana mu sa
Nikabi ba, idan yan Boko Haram din sun tashi shigowa Makaranta Nikabi zasu saka?" Miemee
ta sake fashewa da wani dariyan tana cewa "Seebi dangin Shekau" Ushee ta tuntsire da daria,
duk suka k'ular da ita, ta san cewa idan ta biye musu zata iya fashewa da kuka, sai ta tashi ta
bar musu Ajin, su kuma daria taci k'arfin su, sun kasa bin ta.
Tafiya takeyi tana mita, R-Classes ta nufa, hanyan da tasan ba kowa ta bi, tana ta tafiyar ta
ta na tunanin yanda zata cigaba da zuwa Makaranta ba Nikab taji kamar K'andagare ya hau ta,
wani irin tsalle ta daka sai ta ji ta buge wani abu, a firgice ta dago, tsoro ya kamata da ta ga
R-Lema, yana lulaya goshin shi don anan ta kaimai karo, ta tattaro nutsuwar ta tace "donAllah
kayi hakuri, K'andagaru suka biyo ni, ban ganka a gabana ba, sannu kaji? rabawa yayi ta
gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, Mamaki ya turnike Nasiba, a baiyane tace "shi
kuma wannan wane iri ne?".
*Malali, Kaduna*.
"Ayman, ga Daddyn ki" dugul dugul ta tako tana ta washe baki, Zaid ya daga ta ya wulla ta
sama ya chafe, ya rungume ta yana juyi da ita, ita ko sai dariya take tayi. Mami da ke kallon su
tace "ka ga, kar ka sake min d'iya ta fadi" Zaid yayi daria, yace wane ni in kada diyar
Mami?dariar tayi tace "ashe kana tafe? Ya hanya? Ya yan katsina? Yace "Alhamdulilah suna ta
gaishe ku" tayi dai murmushi don ta san in banda iyayenta ba wanda zaice a gaida ta, tace
"barin dora ma ka abinci, nasan ka gaji" yace "Wallahi kuwa Mami, Yunwa nikeji banyi breakfast
ba na taho" me kake so kaci? Yace "tuwo miyan kuka" tace "ahh ba yunwar kakeji ba, tuwo ai
zai dauki lokaci" yace "Wallahi ina jin yunwa, amma ina iya tsayawa har ayi tuwon" tace "sai dai
daddawata ta k'are" ya mike tsaye yace "kar ki damu na miki tsarabar daddawa da kuka, duk
sun bide min mota da wari, Wallahi kiris ya rage na wurgar dasu, ashe zasu min rana" be jira ta
cewarta ba ya fita, Ayman a hannun shi, har ya bude mota ya dauko ledar k'ullin ya dawo, ya
mik'a mata, ta bubbude tace "Zaid wadannan kayan daga ina? Yace " Wallahi wata tsohuwa ta
bani" Tsohuwa kuma a ina? Yace "a Katsina" tace Zaid ka santa ne ka amshi wadannan
abubuwan? What if shes upto something, number 1 lesson, u cant trust people?" Yace "Relax, i
trust this one, i trust Nene, yanzu dai ki sa daddawan da yawa, miya ya fi dadi" Mami ta kwashi
ledar ta na mita, tace "yanda na ga dama haka zanyi, in kayi fushi kayi aure and stop ordering
me around" Daria yayi sosai yace "yi hakuri Mamin mu".
Haka Mami ta gama tuwo miyan Kuka da ya ji busasshen kifi, Zaid ya ci sosai, yaji dadin Miyar
nan, ita ma Mami taji dadin Kukar, daga jinta sabuwar kuka ce, sai santi suke tayi, Mami ta
kwashe kwanukan ta kai Kitchen shi kuna Zaid yac cigaba da ma Ayman wasa, Yarinya
kyakyawa sosai, yar shekara 1 da yan watanni, idan ka ganta za kayi zaton tayi 3years din nan,
sabida yanda take yar b'ulb'ul da ita, kuma ba wai Nono ta sha ba, bayan Rasuwar Safiyya
Madara ta ke ta sha, NAN kuma aka ci saa ya karbeta, Dangin Mahaifiyar ta sunso su amshe ta
amma Zaid ya hana, yace shima Mamar shi(Mami) zata riketa, haka suka hakura, Little Rafeeah
na zaune tare da Mami a unguwar Malali, kullum Zaid sai yazo ya duba lafiyar su kafin ya tafi
Gidan shi, yana tausayin Ayman, amma idan ya tuna tana tare da Mami sai hankalin shi ya
kwanta don ya san Ayman ba za tayi maraicin Uwa ba.
*KATSINA*
"Me ya samu Nasiban Nene na ga ranta a bace haka? ko shi lapturo(lecturer) din ku ne ya
bata miki rai gobe in mishi asubanci inji dalili?" ba ta san lokacin da ta fashe da daria ba, tace
"Nene, Wallahi Hukumar Makaranta ce wai mu daina sa Nikabi saboda k'asa ba lafia, ana iya
yin Basaja a shiga Makaranta ayi barna" Nene tace "kai sun kyauta, ba ki san yanda na k'ijinin
in ganki da nikabi ba, kamar wacce tayi k'arya, ke da ba tsiraicin kika fiddo ba, amma duk ki rufe
fuskar ki ruf" Nasiba ta shagwabe fuska tace "Kai Nene, so kike ranar Makaranta ta kodar dani?
Kuma mutane suyi ta kallo na?" Nene tace "ke tafi chan, yo ai sai ki shafe fuskar ki da hoda,
kuma in ta kallo ne ai kin kai a kalleki, yar jikalle ta jikan Yan Sudan, donAllah ki dinga gyara
fuskar ki kamar wannan yar gayun, Meemo take ko wa?" Nasiba ta fashe da dariya, ta tashi ta
yi hanyar daki tana cewa "Miemee ake cewa ba Meemo ba" Nene tace "ni rabani da sunan
Aljannu, yarinya da sunan ta me dadi Maryam ta koma wata Meemai ko wace tsiya" ita dai
Nasiba daga cikin daki take ta daria, Nene ta cigaba da Mitar da idan ta fara bata san tsa tsaya
ba, "kema Baban ki ya bata miki suna wai ba a iya kiranki da sunan Yankan ki sai Seebi har ya
koya min nima" a hankali tace "Amma fa sunan fa da dadi, na yan gayu, Seebi, Seebin Nene"
me Nasiba zatayi in ba daria ba. Nene ma ta sa daria ashe ta na jinta, ta mik'e tana fadin "Uban
me ake ma daria cikin k'urya?".
Maalesh ya fito daga Motarshi da ya parka ta a haraban Gidan su Rafeeq, Aneesa na ganin
shi ta k'araso da sauri tana yauk'i tana karairaya, Maalesh ya fara mata murmushin da be kai
zuciyar sa ba, " Yaya Maalesh, howfa" yace "Anee baby ya kike?" Lafiya fa, dama ina so in kara
maka tuni kan Yaya Rafeeq, Wallahi son shi na cinye min yan Hanjina, na rasa me na mishi da
ko ganina ba ya son yi, idan na je gurin shi yanda kasan yaga bak'ar Jab'a, kallon arzik'i baya
min, gashi zuciya ta ta kasa hakura dashi, ya zanyi?" Maalesh da ya k'osa ta gama maganar ta
don warin gashin dokin ta ya cika mai hanci, yace "karki damu zan mai magana" dadi ya rufeta,
kafin tace wani abu Maalesh yayi gaba.
"Guy Yane?" Rafeeq ya dago kai ya kalli Maalesh da ya shigo yanzu, da k'yar yace "Normal"
Maalesh yace "ba ka kirani nazo nayi picking dinka yau ba?" kamar ba zai ce komai ba yace
"Da mota naje" "Ohh, is that so?" nan Maalesh ya shiga bashi labarai, abubuwan da suka faru
da friends din su, har zuwa inda Aneesa ta tare shi, Rafeeq dai be ce komai ba ya cigaba da
latsa wayan shi, Maalesh be damu da shariyan Rafeeq ba don inda sabo ya saba, wasu
lokuttan Maalesh na bashi labarai ne ba don yaji ta bakin Rafeeq ba, kawai don dai Yayi
keeping dinshi Company, kasancewar he's alone, Ba wai Rafeeq be gane Labaran da Maalesh
ke badawa bane, tsaf ya ke fahintar shi, don wasu lokaci idan Maalesh ya bashi daria ya na dan
murmusawa abu kadai ke mai wuya, Magana. Ya na jin k'yuwan Magana, yana ganin Asaran
Yin magana.
"Sis nikam Nagaji, ya zanyi wai da son Zaid?" Sauda ta kalli kanwar tace "Meema, dont give
up so easily, kafin ki samu abun da kikeso dole ki wahala, kar ki manta wahalar da na sha kafin
na samu kaina a Gidan nan, kar ki damu, ke dai kawai ki cigaba da jawo hankalin shi" wani
Jawo hankali? So