Showing 54001 words to 57000 words out of 151322 words
Chapter 19 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
da ta na nan ba zan gaji da jiran layin nan ba" lubbatu tayi daria, tace " nima bangan ta
ba yau, da ta na nan da ta dinga mitar har yanzu ba a soya min nau ba?, ko kuma tace ta
rigaka zuwa nan" daria yayi yace "aiko idan zan wuce gida zan biya gidan ta inji ko lafiya yau ba
ta fito siyen k'osai ba" lubbatu mai k'osai tace "anya Maigadin Gidan Lema ba da Aminene
za'ayi ba?" ya fashe da darian jin dadi yace "ai na fi k'arfinta" Nasiba da ta yi k'ask'e tana jin su,
a ranta ta maimaita "Maigadin Gidan Lema? Isit possible gidan su R-Lema yake Gadi?" Don
tana da tabbacin wuraren nan gidan su R-Lema yake, kuma tabbas maganar Nenen ta suke yi,
Allah sa haka ma, Don ta fara aiwatar da aikinta tun wuri.
Ba jimawa a aka sa ma Baba Maigadi Gidan Lema k'osan shi, cikin saa a ka zuba ma Nasiba
nata, Baba Maigadi yayi Gaba Nasiba tabi bayan shi, tace "ina kwana baba?" da faraa yace
"lafiya lao Jikata" haka suka cigaba da tafia har Nasiba tazo gida, zata shige kenan yace "Jikata
dan tsaya?" cikin gidan nan zaki shiga?" tayi murmushi tace "eh, Baba" yace "ko Aminene na
ciki? Na jita shiru yau bata zo siyan k'osai ba" tace "eh ta na nan, bata ji dadi bane jiya da
daddare " yace "Assha! DonAllah kice da ita, Maigadin Lema na Sallama" bawai don tana da
tabbas ba tace "Baba kai Maigadin su Rafeeq ne?" ya washe baki yace " Yo eh, ai nine
Maigadin su, tun lokacin Iro Kakan Rafeeq kenan" Murmushin Nasara Nasiba tayi, tace "Baba,
barin maka Sallama da Nenen" ta shige gida.
"Nene ana Sallama da ke?" Nene tace Sallama kuma? Wanene? Seebi cikin sigar zolaya
tace "bazawarin ki" ke zan saba miki, badai Zaidu bane don yanzu ya kira yace an turashi Ingila
aiki zaiyi wata Guda" Haka kurum Nasiba taji ba dadi, zata yi kewan Zaid, tace "wani Maigadin
gidan Lema" murmushi Nene tayi tace "Danrainin wayau, nasan zuwa yayi jaje na yau be ganin
ba a gurin siyan K'osai" Nasiba tace "Toufa, har kun saba da Shi, ko dai ko dai?" harara Nene ta
jefeta da shi, tace barin je mu gaisa" Nasiba tayi saurin cewa aa, barin dai ce ya shigo sai ma in
shek'a mana koko, Nene ba ta ce komai ba Nasiba taje ta shigo da Baba Maigadi.
Bayan sun gama kalaci ya musu Sallama, Nasiba tace "barin raka ka baba" yace to Jikata, ya
kalli Nene yace to "Aminene, Allah ya kara sauk'i, sai na sake zagayowa" cikin wasa tace " Idan
zaa dawo a dawo da karin ciwo, bawai azo a isheni da dimin surutu ba" Gabaki daya suka sa
daria..
_Bibilicious Biebee_
KE ALHERI CE ♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣6⃣
A hanya, Nasiba ta dinga jan shi da fira, da yake Baba Mai gadi saurin sabo ne dashi, nan
da nan yake bata amsar tambayoyin da ta ke mai, Nasiba a ranta tace "Hanya Mafi saukake da
zan san ko kai waye Rafeeq" Baba mai gadi yace "ke Nasiba, kinga har kin rakoni Gida, na jaki
da yawa" tace "lahh har mun iso? Ya nuna gidan da yatsa, yace "ga gidan nan" gabanta ya
yanke ya fadi, wani irin Tamfatsetsen gida ta gani, gidan ya hadu, a ranta tace "So this is where
you live R-Lema" Baba yace to ki koma gida Nasiba, sai nazo gobe, ta dan marairaice fuska
tace "Baba nasan Nene ta koma bacci, idan ba damuwa in zauna nan in tayaka fira" bench ya
dauko ya ajiye gaban Gidan, ta Zauna, yayi daria yace wani irin fira zamuyi? tace "labari zaka
ban" "wani iri kenan" a ranta tace "Astagfurullah Zanyi karya" ta sausauta murya tace "Baba
labarin Rafeeq zaka bani, Makarantar mu daya, da ni budurwar shi ce, yana sona sosai, amma
rana daya ya sauya min, ina son shi kamar me, amma sai naga ya daina kulani, yanzu ko gani
na yayi kallo ban ishe shi ba, shine nake tunanin ko yaudarata dama chan yakeyi?" da sauri ya
girgiza kai yace " kar kice haka, Rana daya Rafeeq ya sauya ma kowa, Rana daya K'addara ta
gifta ma Rafeeq" Nasiba tace Baba ka ban labari *Wanene Rafeeq* Ajiyar Zuciya yayi, yace
Rafeeq D'a ne kamar kowa, mai fara'a da son Jama'a, kinji kinji................ Tsaf Baba maigadi ya
kwashe ya bata labarin duk abunda ya sani game da Gidan Habib Lema har zuwa zaman da
sukayi yau. Sosai Nasiba ke kuka har da Majina, lokaci daya tausayin Rafeeq ya lullube ta, Sam
bata ga laifin Rafeeq ba, lallai Rafeeq abun tausayi ne, Lallai Rafeeq na buk'atar taimako.
Baba Maigadi yace "Nasiba mun dade zaune a nan, ki tashi ki tafi Gida" ajiyar zuciya ta
sauke tace "Baba, Labarin Rafeeq na cike da Abubuwan ban Alajabi da Mamaki, da tausayi,
baba yanda kasan a fim" Baba maigadi yace a takaice ma kenan, "zato zunubi amma ina Zargin
Matar Ubanshi Saude ga duk wani abun da ke faruwa cikin gidan nan, ban taba dai ce ma kowa
komai ba" da sauri tace "Saboda me kace haka Baba?" "Saboda randa aka ce an kama
Mahaifiyar Rafeeq da kwarto cikin daki, Saude ta fito ta aikeni siyan Gayen lataz, kafin na dawo
har an saketa, tun daga rannan komai ya sauya, Alhaji be kara maganar da kowa ba, kinga
kuwa beyiwu haka, ko yaya ne sai an maida magana, amma ko maganar ka mishi zai nuna be
ma san wacece Aisha ba, kinga ko anan akwai ayar tambaya, sai maganar Karatun Rafeeq,
makarantan ku daya, ke kinsan irin kokari da fasahar da Allah ya bashi, amma har yau ya kasa
gamawa, abokin shi Maalesh har ya gama bautar k'asa, nan ma akwai ayar tambaya, sai
maganan Rasuwar Rafee'ah, mutuwa dole ce ta na kan kowa, Ana gobe Rafee'ah zata rasu, ta
fito da Cooler abinci ta fito nan tana zolaya ta, tace dani "Baba, yau da Hammana zan ci abinci"
nace kice sanwa kika ma yayanki tace "Aa, antu saude ta dafa mana" ta shiga ciki, chan sai ta
fito, nace har kun cinye? Tace "be ci ba ya riga da ya siyo nashi, ni kadai naci, ko na juye maka
sauran a plate? Nace "aa Rafee'ah nagode" washe gari Rafee'ah tace ga garinku nan. Tunda
Aisha ta bar Gidan nan, ban kara cin komai na Gidan ba, don ba bani ake ba, ruwa Saude bata
taba miko min ba, Alhaji be taba cewa don me baa bani abinci ba, shi da ke ganin girma na da
darajata, Zaid kadai ke min ihsani, da idan kinga yanda muke wasa da daria da Rafeeq, abun
ba aa magana, amma yanzu komai ya jagule, ni Wallahi ina Zargin Saude, hanalina be kwanta
da ita ba". Nasiba ta nutsu ta na jin Zancen baba Maigadi tace "Allah shi saka ma wanda aka
zalunta" yace "Amin" horn akayi da k'arfi, jiki na rawa yace ina zuwa ya shiga gidan da sauri ya
wangale Gate din, Meema ce da Aneesa cikin wata katuwar Mota, Meema ta harari megadi
tace uban me ya hanaka bude gate da wuri? Yace "kiyi hakuri" tsaki ta buga ta figi motar da
Sauri Nasiba ta ja baya don kiris ya rage su bi ta kanta. Saida ya kulle gate din ya dawo gun
Nasiba tace baba su waye wannan? Yace "Kanwar Saude ce, da diyarta, in sukayi wani abun
sai ki rantse su 'yayan alhaji ne, ita Aneesar naji labari har ta koma Aneesa Habib Lema a
Makaranta" Nasiba ta jinjina kai tace "baba barin wuce" nan sukayi Sallama.
Tun kan hanya Nasiba ta hau tunanin yanda zata fara wannan Mission dinta har ta je gida tana
sak'a da warwara, ta rasa yanda zata yi, amma abun da ta kudirta a ranta, Zata taimaki Rafeeq,
zatayi yanda Rafee'ah ta bukace ta da tayi, nan Allah ya cire mata duk wani tsoron abun da zai
je ya dawo, ta san its not an easy thing, amma haka kurum zuciyar ta ta amince da duk halin
da zata shiga, zata yi sacrificing kanta, she's willing to take the risk, bayan jin ta bakin Baba
Maigadi, da hujjojinshi na Zargin Matar Baban su Rafeeq,komai zai zo mata da sauk'i, nan ta
gane ba Rayuwar Rafeeq kadai zata shiga ba, Rayuwar Gidan Lema gaba ki daya zata shiga
"So help me God". To tambayan shine "Ta yaya zan shiga Rayuwar su Gaba ki daya?" zuciyarta
tace "barin jira Rafee'ah a mafarki".
Da daddare sai juyi take don tayi Mafarki, amma Shiru ba Rafee'ah, washegari ma kwatakwata
batahi mafarkin komai ba, kwana 3 ta jera tana jira tayi Mafarki da Rafee'ah amma shiru, tace
ma kanta " it seems like i am on my own, Allah ka taimake ni."
*5:50pm*
"Sannu Nene" Nasiba tace cikin damuwa, tun kwana 2 da suka wuce Nene ke kwance, ta
rasa me ke damunta, ta k'i yarda suje Chemist, kuma ta k'i yarda Nasiba ta gaya ma Abban ta,
Nasiba duk ta shiga wani yanayi, a iya wayon ta, ba ta taba ganin Nene tayi ko da ciwon Kai ba,
cikin rashin kuzari Nene tace "Wai uban meye zaki tasani gaba ki zabga uban tagumi kina kuka
iyi? Ko kinga na mutu ne? Nasiba tace "Nene nifa ban taba ganin kiyi ciwo ba" Nene tace da
yake ni Waliyya ce sai in k'i ciwo, ko kullum in banda lafiya sai inzo inyi kwance kamar wata ke a
gurin, to Nasiba ko ciwon Ajali ne me zuwa ma mutu farat daya, to barin bar miki wasiyya" da
sauri Nasiba ta tashi ta shiga daki ta bar Nene kwance tsakar gida, don ta san Nenen k'arfin hali
kawai takeyi tana maganar nan, kuma idan ta biye mata sai ta sa ta kuka don Bakin Nene ba ya
shiru. Nasiba ta rasa yanda zatayi, ba ta san kiran Abban ta don ta san shi da damuwa, yana
iya kamo hanyar Katsina da Marecen nan, ya zatayi? Bata gama tunanin ba Wayar ta ta hau
ruri da sauri ta dauka + ta gani wato lambar waje ne, ta dauka da Sallama, a dayan bangaren
"Waalaikum Salam Seebin mu ni da Nene, ya kike ya karatu? Tace " Uncle Zaid, Alhamdulilah,
ya Aikin? Yace "Alhamdulilah, ina Nenen?" kamar jira take ta fashe da kuka, lokaci guda Zaid ya
rude, "me ya faru? Me ya same Nene? Wani abin yake faruwa a katsinar? Ki min magana
Nasiba" daga jin muryar shi kasan hankalin shi a tashe yake" ta dan tsagaita tace "Uncle Zaid,
Nene ba ta da Lafiya, tun kwana 5 da suka wuce, ina tsoron wani abu ya same ta, ban taba
ganin ta haka ba, amma ta k'i yarda muje Asibiti ko nagaya wa baba na" Zaid yayi dan shiru
yace "no wonder, randa na kira naji muryar ta wani iri, ashe ba lafia, kuma bata gaya min ba" "ai
ba zata gaya maka ba, don Nene wata irin mata ce me Zurfin ciki, nima don ta kai kuri na san
cewa bata jin dadi, har yanzu bakin ta ya ki mutuwa" Zaid yace "ki kwantar da hankalin ki, ki
tashi kuyi shirin Asibiti aje a dibo ta" Nasiba tace Uncle Zaid " ba zataje ba, Nene is so
stubborn" yace "trust me on this ki kai mata wayan".
Haka ta mik'e ta kaima Nene Wayar, Nene ta amsa da Sallama, Zaid ya gaida ta, "lahh, Zaidu
bawan Allah, kaine Ya Ingilar?" yace "Alhamdulilah, ashe ba kiji dadi ba?" saida Nene ta wurga
ma Nasiba harara kafin tace "Kai kalau nake" "Aa Nenen mu, ga muryar ki nan, ni dai ki tashi ki
kimtsa gashi na turo a zo a kaiki Asibiti, donAllah kar kice Aa" ba yanda zatayi tace "Toh Zaidun
Seebi, tunda yanzu maganar ta kadai kake ji" duk sukayi daria, ta mik'e da k'yar ta shiga
bandaki, yace "Nasiba, ku shirya za a zo a kaiku Asibiti" tace "Uncle Zaid ina iya kaita, ba sai an
zo ba" yace "don't be silly, zan sake kira inji ya jikinta" dif ya katse wayar. Nasiba tayi murna,
tace "Allah Sarkin Uncle Zaid, Our Guardian Angel."
A karo na 3 Ya shiga lalluben layin Rafeeq, sai ya kusa shiga sai ya datse kiran, don yana
fargaban abun da zai ce mai, Rafeeq be son irin haka, amma ya zaiyi? He is his only choice,
chan dai yayi shahada ya sake kiran wayar Rafeeq, ringing biyu Rafeeq ya dauka ya kafa a
kunne ba tare da yace komai ba, Zaid yace "hello son, ya kake?" kamar ba zai yi magana ba
yace " Barka da Yamma" Zaid yace "Kaci abinci?" "Uhm" kadai yace, Zaid yace "Rafeeq ka tuna
Nene? Wacce kama granddaughtern ta Assignment last week? Kamar ba zai tanka ba yace
"yeah" " she's sick wallahi, she's been sick for days" a ranshi yace to why are u telling me? Allah
ya sa ba cewa zaiyi inje in gaishe ta ba don ba zuwa zanyi ba, shiru be ce komai ba Zaid yace
"Kaji ai?" da kyar yace "Allah ya bata lafia" "Amin, Rafeeq i want you to do something for me,
DonAllah ka dauke ta ka kaisu Asibiti" cike da mamaki yace "What??" Zaid yayi saurin kwantar
da kai, donAllah they need help, kaisu Asibiti kawai zakayi, this is all i'm asking for, Please" dif
Rafeeq ya kashe wayan, takaici uwa ya kashe shi, shi be san meyasa Uncle Zaid ke sa shi
yawan magana ba, in banda neman Magana shi zai kaisu Asibiti? Why they need help, shi First
Aid box ne? Kai akwai Sakel, shi be kai kanshi Asibiti ba zai kai wasu? Ga Maalesh baya nan,
to ko dai ya kira musu Ambulance? Amma Uncle Zaid ya fi k'arfin ya sashi abu ya k'i yi, be da
wani Zabin da ya wuce mik'ewa ya shiga mota.
Daga gidan su zuwa gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin
yanda zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text, "i'm there" don
be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta
shaida mai da yanzu zasu fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet
the sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid din yana sani
abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma motar shi ya Zauna" ba ayi minti
Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata
jan mota mai bakin Gilashi, da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai
karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na kallon su, ganin
zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji horn, ta ga haske a ta cikin motar nan
zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata
samu ta shiga rayuwar shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga bak'in
windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da
mu?" da sauri tace "ni ba haka nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi
parking, har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama ita ma
ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci
kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake
magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk wani abu da
yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka soma zubo mata ba, tayi
saurin sharewa don kar Nene ta gani ta tara mata mutane, be zarce ko ina ba sai Asibitin
K-Dara, ya shiga yayi parking, shiru shiru be ce musu komai ba, Nasiba tace "Nene anzo fito
mu shiga"suka fito, ga mamakin ta shima ya fito yayi gaba hanyar entrance din, suka bishi a
baya, Nene na mata mitar "shi kuma wannan haka yake dunkum?" Seebi dai bata ce komai ba,
Rafeeq ya tsaya ya yanki kati, ba layi, ya kira Dr Daran, yace "Baba gamu gaban Office dinka"
yace to Rafeeq ku shigo, hannu kawai ya nuna ma Nasiba Office din ya samu guri ya zauna,
Nasiba kuwa ta gane me yake nufi, ta sake rik'e Nene suka shiga cikin office din, yace kune
Patient din Zaid? Nasiba tace "eh" ai ya kirani ya sanar dani zuwanku" ya shiga yi ma Nene
tambayoyi, da gwajegwaje, kusan Minti 45, kafin yace " Inna Zamu baki daki, Hawan jinin ki ya
tashi" Nasiba ta zaro ido tace "hawan jini Dr?" meyasa ta samu hawan jini? Yace "Ke kuwa ta
tsufa, ai tsufa ce, don ma jikinta me kyau ne kuma tana regulating din shi,amma still zamu bata
gado don kar ta kamu da Diabetes, don na fara ganin Symptoms din a tare da ita, kar ki daga
hankalin ki, yanzu barin na muku processing gado, Suka fita waje da Dr din, Nasiba ta leleka
bata ga Rafeeq ba, a ranta tace "ya ma yi kokari da ya kawo mu" Dr ya rubuta aka