Showing 30001 words to 33000 words out of 151322 words
Chapter 11 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf
Bayan Minti Talatin(30 mins Later)
Bakin Gate Hafiz ya dinga Horn, ba alamun Baba mai gadi, to ko ina yaje? inji Alh Habib, daidai
nan Rafeeq ya danno motar shi kwanar Gidan, ya k'araso, Ganin Motar Uncle Hafiz tsaye ya sa
shi fitowa daga nashi motar, zuwa yayi ya k'wank'was kofar side din Uncle Hafiz, yayi winning
"Sannun ku da zuwa Uncle Hafiz, Daddy Sannu ya hanya? Bamu san yau zaku dawo ba" Suka
amsa mishi gaisuwan su, Uncle Hafiz yace "mu kam Rafeeq bude man gate dinnan, Bansan
inda Baba yaje ba" Rafeeq ya kalli Gate din yace "to ko ina yaje? Its unlike him" ya karasa tare
da shiga gidan don bude Gate, Uncle Hafiz ya shigo da motar sa, Rafeeq ma yaje ya shigo da
tasa. Sauda na jin dirin motar su ta fara tsalle, ta gyara zaman kan kujera tarw da rafka Uban
tagumi hannu bibbiyu.
A tare su 3 suka shigo parlorn, Alhaji Habib na ba Rafeeq labarin Bussiness trip din su, suka
shiga da Sallama, Ta dago ta amsa a sanyaye, Sannun ku da zuwa Alhaji, Hafiz sannu" "sannu
ya gidan? Rafeeq yace "Auntyn mu lafia naganki haka?, u look disturbed" tace "Rafeeq, wallahi
Mami ce naji ta shiru, tana daki tun da na tashi, na kwankwasa na kwankwasa shiru, na zata ma
ta fita ne amma baba maigadi ya bani tabbacin kai kadai ka fita yau" Rafeeq yace "toufa, its
unlike her baccin Safe, This is just 12:30" Sauda tace "nima dai haka nagani" Hafiz maybe she
needed the sleep, shes just sleeping" Alhaji Habib da yaji Hankalin shi ya ki kwanciya, yace "kaii
Rafeeq, je ka tado ta, Azahar ma ta kusa" Rafeeq ya haye sama, Sauda ta cigaba da cewa "tun
dazun da mukayi waya da kai na lek'a don in gaya mata dawowan kuamma shiru na jita
wallahi".
K'wank'wan "Mami kina ciki?", ya murda k'ofan sai dai damk'e ya jita, yace "mammy, ki bude
Rafeeq ne, ko duk baccin ne haka? "Mammy mana, ki bude Daddy ya dawo" nan ma shiru, duk
ya rude ya shiga k'wankwasa kofar iya karfin shi.
Alhaji Habib ya dan daga murya yace "Rafeeq Har yanzu ba ta bude ba?" daga sama Rafeeq
yace "Daddy ba ma ta magana, kuma kofar is Jammed" da Sauri Alhaji Habib ya mik'e ya hau
Saman, su Hafiz suka rufa mai baya. Shima knocking ya fara yana cewa "Shatou na, kina ciki?
Are you okay" Shatou taso ki bude mana k'ofa" Sama sama sukaji a na magana, da suka kasa
kunne sukaji muryan namiji ne na cewa, "Mun shiga 3, Aisha ki tashi, tashi maigidan ki ya dawo,
Haba Aisha duk gajiyan ne, ai ya kamata ki tashi daga baccin nan haka, ki tashi ki nemo min
hanyar fita"
Rudani da firgici ya ziyarci zuciyar Alhaji Habib, kirjin shi kamar ya tsago daga rigar shi ya fado
don tsoro, hannu ya sa ya toshe bakin shi don wani kuka da yaji ya zo mai, yana k'okarin lalibo
adduar "Innalillahi wai inna illaihir raji'un"
"Allahumma arjirni fi museebati wa akhlifni khairin minha.
Hafiz kuwa take Ran shi ya bashi wannan makircin Sauda ne, ya kai duban shi ga Sauda yana
mata kallon tuhuma, da ta lura da kallon da Hafiz ke mata, ta girgiza kanta alamun ba ruwan ta,
tayi saurin kawar da kanta daga duban shi.
Rafeeq ko da be fahimci komai ba ya cigaba da k'wank'wasa kofar, "Mami na Open up please,
you are making us worried" ji yayi an taba k'ofar, ya matsa baya yana murmushi ya kalli Daddyn
shi, yace "Dad, she's opening up, she's fine". Bawan da yace da shi komai, sai k'ofar da suka
tsura wa ido.
Mak'ale na cire key ya murda kofar ya danna a guje har yana buge Alhaji Habib da ke kan
hanyar shi, duk suka bishi da ido, Hafiz yayi yunkurin binshi da gudu Alhaji Habib yayi karfin
halin rik'o Hafiz, ya girgiza mai kai alamun rabu da shi, Rafeeq cike da alamun tambaya yace
"Daddy waye shi?" Alhaji Habib be ce komai ba face hawayen da ke zuba daga idanun shi, ya
matsar da Rafeeq gefe yaym shiga dakin Aishatu, burin shi ya ga Aisha ta ce mishi "mafarki
yake, this is not true" don so yake ya tashi daga wannan mummunan baccin da yake, Hafiz ma
ya bi bayan shi, sauda ma ta rufa musu baya suka kutsa dakin Mami Aisha.
Rafeeq da shifa kwatakwata k'wak'walrshi ta dode, be gane komai ya bi su a baya. Hafiz yayi
saurin dauke kanshi daga duban Aisha, Sauda kuwa daura hanayenta tayi guda biyu a kai,
Alhaji Habib ya zame k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai, Rafeeq da ke tsaye
kamar mutum-mutumi (Robot) don duk wasu daurar da ke aiki a k'wak'walwar shi ta dauke dif,
sakamakon abun da ya gani. Mahaifiyar shi ce Kwance Zindir ba kaya haihuwar Uwarta. Rafeeq
da karfi yace "Mammmmmmmiiiiiiiiiiiiiiiyy" firgigigit Mamy Aisha ta tashi.
_Bibilicious Biebee_
KE ALHERI CE ♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣5⃣
Da karfi Mami Aisha tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ne zan gani haka?" ta fada tare da
neman abun da zata kare jikinta dashi, da sauri Sauda ta bude Closet dinta ta ciro mata zani
da hijab ta bata, ta amsa da sauri ta suturta jikin ta. Ta bisu da kallo daya bayan daya, ta fashe
da kuka, me ya faru dani? Aljannu suka shige ni ko? Suka min tunbur? Kumin magana" Sauda
ta fara kukan munafurci tace haba "yaya, ya zaki ce haka? Kwarto fa kika kawo cikin daki,
amma yanzu kina neman cema na ba kisan me kikayi ba? Zurum ta zube a kasa, don
kafafuwan ta sun gaza daukar ta, a ranta tace kwarto? Ta dago taga yanda Alhaji Habib ke
zubar da hawaye da sauri ta rarrafa gurin shi, ta rik'o hannun shi, Kamar wanda shocking ya
taba, yayi saurin janye hannu shi tare da mik'ewa, ya nuna ta da yatsa yana kuka, "Aisha, kin
cuceni, kin haince ni, kin ci amana ta, was it hard for you to wait for me?" kuka take yi sosai, ta
kasa cewa komai sai girgiza kanta da takeyi, da kyar tace "kayi hakuri Habibullah" wannan
magana da tayi ne ya sa shi tabbatar da zance, shikenan Aisha ta ci amanar shi, ta kawo
kwarto har cikin dakin ta da tsakar rana, ba tsoron Allah. Da kyar yace "Aisha na sake ki saki
daya" ya fice daga dakin, Sauda ta hau kururuwa ta bishi a baya "haba Alhaji be kamata kayi
haka ba, be kamata ka yanke hukunci kana bacci ba, Alhaji ka maidota yanzu pls" tsawa ya
daka mata yace "Saudat, kina so ki bita kenan? Da sauri tayi shiru kar daga neman kiba ta
nemo rama. Ba ta ji dadin saki dayan da Alhaji ya mata ba, duk a zaton ta saki 3 zai mata,
amna dayan ma ba laifi, zata tabbatar Aisha ba ta dawo gidan ba har abada.
Hafiz ya kalleta cike da tausayi tabbas wannan aikin Sauda ne ya rasa me zaice shima ya fita
ya rage daga Rafeeq sai Mami, har yanzu tana nan duk'e inda Habib ya barta, Rafeeq ko na
nan tsaye, ya kasa motsi, abubuwan ke dawo mishi kai, ya kasa yarda da Abun da idon shi
yagani, da ya runtse ido Mami yake gani zindir, Mami ta dago kai a hankali ta sauke su kan
Rafeeq, da jijiyoyin kanshi sun mimike, fuskar nan tayi Ja, idanuwan sa ma sun kada sunyi jazir,
Mami bata damu da halin da take ciki ba ta mike ta nufo Rafeeq, yanayin da ta ganshi ya firgita
ta matuk'a, ba ta taba ganin Rafeeq a haka ba.
Hannu ta cire zata riko shi don ta zaunar da shi kan gado, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar
daga mata hannu, yace "dont touch me, Kar ki taba ni" cike da mamaki ta kalle shi, tsana da
kiyayya taga ni kwance kan fuskar Rafeeq, yace "bana so in sake ganinki" baki na rawa tace
"Rafeeee--q" yace "Wallahi na tsane ki" kafin ya sake wani magana yaji wani lafiyayyen mari
tassss a fuska, hannu ya sa ya dafe kuncin sa, ya na dagowa ya sake ji a kara sakar mishi da
wani marin da ya fi na dazu, duk a zaton shi mamin sa ce ke marin shi, dagowa yayi don sake
yab'a mata wasu bak'aken maganganu, sai ya ga akasin haka, Hannun Mami ya gani rik'e da
hannun Uncle Zaid da ke niyyar sake marin Rafeeq karo na 3, ta tare shi ta hanyar rike hannun.
Huci Zaid keyi, ya nuna Rafeeq da hannu "How dare you Rafeeq?" kasan da wanda kake
magana? Rafeeq be bi takan Zaid ba ya kalli mami ido cikin ido, yace " i wish i had a different
mother" ya juya ya fice. Cikin zafin rai Zaid yace" Rafeeq Habib Lema, come back here" Mami
tayi saurin cewa "Zaid, laifi na ne, na mishi babban laifi, na ma kowa babban laifi, i dont know
what exactly happened but i know i didnt do what they are accusing me of'' Zaid yace " Mami
wai meke faruwa ne? Na rasa ganewa, tun kafin in shigo katsina na dinga neman layin ki, be
shiga, na shigo gida na ga alamun ba lafiya, don Hafiz na k'asa na kuka, na tambaye shi me ya
faru ya kasa magana, ban bi takan kowa ba na hayo sama gunki, na iske wannan mugun
kalamai da Rafeeq ke fada miki, ina zargin Rafeeq koya fara Shaye shaye"
Mami na kuka sosai tace "ko daya Zaid, Rafeeq na da hujjan yin hakan, kaji kaji abunda na
sani" "inalillahi wa ina ilaihir rajiun" inji Zaid, Mami har tayi nadaman gaya ma zaid, a zatonta
shima yarda zaiyi da zargin da ake mata na kawo kwarto cikin gida. Tace Zaid "Wallahi ban san
komai game da hakan ba, ni dai kaji yanda na tashi na tsinci kaina" Zaid yace "yi shiru mami
kar kiyi zunubi, na san halinki,Wallahi akwai wata k'ulalla, akwai wata a kasa, tabbas wannan
wani irin tuggu ne aka shirya miki, to wa??" Mami tace "Allahu Aalam, Zaid ka saurareni da
kyau, wannan boyayyen alamari ne da ba wanda yasani sai Allah, Habib ya sake ni, i wont be
there to protect my children, whoever came for me is coming for my kids, is defintely coming to
hunt my Childeren down, sunci nasara a kaina, Zaid kar su ci nasara a kan 'ya'ya na, Zaid i
want u to protect them"
Zaid na kuka yace "Mami yaya ya yi saurin yanke hukunci, baya cikin hayyacin shi ne sanda ya
sakeki, mu bari ya sauko, sai ayi magana nasan gaskia zata fito, ya maido ki dakin ki.
Murmushin takaici tayi, tace " Zaid kenan, yanzu dai bawanan ba, Rafeeq yayi fushi sosai,
fushin da be taba yin irin shi ba, ina tsoron kar zuciyya ta kai shi yin aikin da na sani, ina tsoron
zuciyar Rafeeq, Zaid ka bishi donAllah, Ka kula min da d'a na" kamar wanda aka tsunkula ya
tashi zumbur, don ya mance halin da ya ga Rafeeq dazun. Yace "Mami ki jirani i'll be back and
everything is going to be Alright" a hankali tace "Go Zaid, Go" be sake magana ba ya fice da
Sauri. Matakala bibbiyu, uku uku Zaid ya dinga hadawa ya sauka k'asa, sai dai ga mamakin shi
Wangale yaga gate, ya duba gefe ya ga ba motar Rafeeq da yagani Parke a gefe hankalin shi
ya daga, daidai nan sai ga Baba Maigadi ya shigo gidan da Cefane da Lettuce din da Sauda ta
aike shi a hannu, Zaid yace "baba ina Rafeeq" Baba yace " Zaid yanzun nan na ga motar shi ta
wuce fiyauu, na tsorata da yanda naga yana tuk'i, da alamu sauri yake" Hankalin Zaid ya tashi,
ya na tafiya ya na magana yace "akwai matsala a gidan nan baba, matsala babba" Zaid ya
fada motar sa ya bi bayan Rafeeq baba Maigadi ya mishi Allah ya kiyaye.
Zaid na fita itama ta hada kayan ta, kana ganinta kasan hankalin ta a tashe yake, duk ta dauki
abubuwan buk'ata, ta sauko k'asa ta bude motar ta da ta siya da kudinta ta tura Akwatin ta, da
sauri Baba Maigadi ya nufo gunta, "Hajia Lafia? Tafia zakiyi? Ince dai lafiya fuskar ki tayi Jaa,
kuka kikeyi ne?" da kyar tace mishi "Baba, Habib ya sake ni" Salati maigadi ya saki, yau mun
shiga uku, shi habibun ya sake ki?" me yayi zafi haka?" Murmushi tayi tace baba barin tafi, don
Allah a kula da su Rafeeq, akwai wata Musiba da ta shigo gidan nan" Baba da ya fara kwallah
yace InshaAllah, Allah shi yaye ya sa ku daidai ta da Alhaji ya maidoki dakin ki, don Wallahi ba
shi kadai yayi rashi ba muma munyi". Tace nagode ta bude motar ta ta shige ta bar Haraban
Gidan Habib Lema.
Gudun da Rafeeq keyi na tashin hankali ne, kamar zai buge mutane, Allah dai ya cigaba da
kare shi, don be ganin gabanshi shi dai yasan tuk'i yake, ba tare da yasan inda ya dosa ba,
Kiran Zaid ya shigo wayar sa, amma yanda sauran kiran suka shigo suka yanke haka wannan
ma ya katse, Zaid ya damu matuk'a da kyar ya kira Maalesh ya ji in gidan su Rafeeq ya nufo
Maalesh ya bashi tabbacin tun wurin 11 suka rabu. Zaid gudu yake yana duba hagu ko dama
inda zai ga Rafeeq, kawai dai ya yanke hukuncin bin Hanyar Jamia ta wurin Ring road, speed
ya k'ara, ba jimawa kadan Zaid ya hango motar Rafeeq daga chan nesa, gudu yake kamar dan
tseran mota, hamdala Zaid yayi ya k'ara gudun motar shi, horn yake ta mai amma yak'i
tsayawa, ta mudubin motar Rafeeq ya gane motar Uncle Z, shima ya kara gudun motar shi,
Shima Zaid ya kara na shi, Gudun da sukeyi yafi kama da na masu race, ba me niyyan
tsayawa, Burin Zaid ya tarar da Rafeeq, shi ko be da wani burin da ya wuce ya ta tafia har sai
ya manta da wani damuwar shi.
Zaid ya taka motar nan da karfi, har Allah ya bashi ikon shan gaban motar Rafeeq, Ran Rafeeq
ya baci, niyyan shi ya cigaba da tuk'in har ya buge motar Zaid, amma zuciyar shi ba zai bari ba,
Uncle Zaid ne fa a motar, mutumin da yake so sosai, ba zai so ya buge shi ba, be da wani zabin
da ya wuce ya tsaya da motar sa.
"Aishatu lafiya? Kinzo kin tasamu gaba kina ta kuka, wani abun ne ya faru?" Baba Tijjani ne
mahaifin Mamin su Rafeeq ne ke mata tambayar nan, duk ya tsufa sosai, mamar tace "haba
mama na, idan wani abu ya faru ki gaya mana, ba wai ki tasamu da kuka ba" da k'yar ta
tsagaita kukan ta ta labarta musu iyakar abun da tasani, Sallalami da Salati suka fara, mamarta
harda kuka, Baba Tijjani yayi shiru yana nazari, chan yace Aishatu, na san wa na haifa, na
yarda dake, ban haife ki don ki zama ma zinaciya ba, da mijin ki da 'yaranki, tabbas idan aka
duba wannan lamari zaa ga shiri ne a dunkule sai mai hankali zai gane" Mamar Mami tace
"amma shi kuma habib harda Saki? Baba Tj yace "sharri ne dai don a hadata da mijinta, ni ban
ga laifin Habib ba, don ko ya samu duk wani evidence da ya ke bukata, ko wani namiji haka
zaiyi, amma ina da tabbacin da Habib ya kwantar da hankalin shi ya duba lamarin nan zai gano
gaskia, tashi ki shiga daki Allah shi zai saka miki" tace baba ina so in bar gidan nan, don na san
Zaid ba zai taba bari na a nan ba, duk yanda zaiyi sai ya maida ni gidan Yayan shi, bana son
hakan ya faru na fiso Habib ya gano gaskia da kanshi kuma ina bukatar lokaci da zan huta in yi
idda na, ina neman izinin ka na barin garin" "Aa Aishatu, ba zan bari kiyi zaman kanki ba" Mama
tace "ta je Malumfashi gurin Inna mana" Baba Tijjani yace "kina iya zama malumfashi gun
kanwara mamarki?" tace "Eh Baba, idan ka min izini yanzun zan tafi" yayi shiru yace "Allah ya
kiyaye hanya, Allah ya tsare ki kula da kanki".
Ganin Rafeew be da niyyar fitowa daga motar shi ne ya sa Zaid fita da sauri ya nufe shi, har ya
tako gaban motar Rafeeq, ya bude gaban motar, ya sa hannu ya fito da Rafeeq, ya kalle shi,
shima ya tsorata da yanayin Rafeeq, fuskar nan ta yi ja, idanuwan nan sun kada sunyi jazir, ga
digon hawaye ko k'wallah, jijiyoyin kanshi sun mik'e. Zaid ya tausaya ma Rafeeq sosai yace
"Rafeeq" Ko kallon shi Rafeeq beyi ba, Zaid ya kara cewa "Rafeeq kayi hakuri, kayi kuka, cry it
all out, kar ka barshi a ranka, pour your heart out, i know this is hard for you, let it flow Rafeeq,
let it flow"
Da sauri ya rungume Zaid sosai, sai a sannan ya samu Hawaye suka fito daga idanuwan shi,
sai a sannan ya fara kuka a hankali yace "Uncle Zaid, Help me"
_Bibilicious Biebee_
KE ALHERI CE ?
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
*Assalamu Alaikum*
_Da farko zan fara da nuna godiata da jin dadin yadda kuke biye dani a cikin_ _littafina na *KE
ALHERI CE*_
_Nagode sosai Allah ya saka maku da alkhairi yabarmu tare._
_Kamar yarda korefe korefe sukayi yawa