Showing 9001 words to 12000 words out of 151322 words

Chapter 4 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf

Advertisement

16 Mar 2025

9622

"to Alhamdulilah Allah ya ji kansu ya gafarta musu". Duk suka amsa da "Amin"
yace to ku sai ku shirya ku koma bakin karatun ku ko? Suka amsa da "to baba" yace to ku na
sallame ku. Hafiz da Zaid suka tashi suka tafi.

Alhaji Tijjani yace "Habibullah, wani nauyi Allah ya dora maka, ina fatan zaka rike amana? Yace
"InshaAllah baba, mungode kwarai, Allah ya saka da Alheri Allah ya ja kwana" Alh. Yace "To
Amin".
Yauwa Baba karshen wata zan tafi Cairo, zanje magana kan Engines din nan wanda marigayi
yayi order su, har yanzu ba su iso ba" Alhaji Tijjani yace "Toh Allah shi kaimu yayi jagora Amin,
Habib mata fa? Habib yayi daria yace InshaAllah baba an kusa".

_Bibilicious Biebee_

KE ALHERI CE ‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg

CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT

"Assalam Alaikum, that's my seat" ta dago fararren idanuwan ta ta kalleshi tace "oh sorry" tare
da mik'ewa ta rabe ya shige ciki ya zauna itama ta zauna. Wayar shi ya ciro ya kira Alhaji Tijjani
Salam Baba gani nan cikin jirgi yanzu zamu tashi" dsga bangaren Alh yace to ya an dace?
Habibullah yace "Eh baba, zuwa karshen sati zasu iso" Alh yace toh MashaAllah, Allah ya kawo
ku lafiya Amin"

Sanarwa akayi jirgi zai tashi kowa ya sa seat belt dinsa, duk suka yi yanda aka umarta, cikin
mintuna kalilan jirgi ya fara yunkurin tashi.

Runste ido ta kusa dashi tayi, da yazo daidai tashi ta yi saurin dafa Habib tare da ririke mai
hannu gam, ba yau ta fara hawan jirgi ba, amma Duk sanda jirgi yazo tashi haka take tsintar
kanta cikin tsananin tsoro.

Sai da Jirgi ya daidai ta a sararin samaniyya ta dawo hayyacin ta, da sauri ta kalli Habib baki
bude, tace "donAllah kayi hakuri, i'm always like this duk sanda jirgi zai daga" Habib ya kalleta
baki bude, yace "dama kinajin hausa" ta harareshi cikin sigar wasa tace "wai ma, ga zahiri ka
gani"
Habib dai kasa magana yayi, yana satar kallon ta. Kwata-kwata bata yi kama da bahausa ba,
tafi kama da larabawa, a hankali ya karance ta; Fara ce sol, mai siririyar fuska, hancinta kamar
fensir, tana da dan tsawo, sanye take da bakar Jallabiya ta nade kanta da bakin gyale, kai duk
yadda akayi ta hada iri da Larabawa. Tana sane da irin satar kallon ta da yake yi, murmushi
kadai tayi ba tace komai ba, ta ciro wani novel daga cikin handbag dinta.

Habi dai ya kasa hakuri sai da ya tanka ta, yace " Erhm, amma ke ba bahaushiya bace ba ko?"
ta dan daga kai sama tarw da murmushi tace "bahausa ce mana, bakaji hausa na radam ba
amma meyasa kace haka?" yace "anya kuwa ke hausa ce?" kila zama da hausawa ya sa kika
iya hausa, ko kadan bakiyi kama da hausa ba kinfi kama da balarabiya" dariya takeyi sosai,
tace toh Baba na bahaushe ne gaba da baya mama tace yar kasar lebanon" Habib ya dan tafa
hannayen shi biyu, yace "Ahap, ga magana nan ta fito, kin dai hada jini da Larabawan" dariya
tayi, haka suka cigaba da fira har suka iso Aminu Kano Airport.

Bayan sun gama Clearance ne suka fito wajen Airport din, Habibullah yace "nan garin kike?"
tace "aa, katsina nake" Habib ya zare ido yace "Lah,ashe yar garin mu ce" yace toh zaa zo

daukan ki ne? Tace noo ai bama su san yau zan dawo na, i want to make it a suprise" yace
"that's nice, toh muje mu yi shatar motar chan" ya fada y na nuna motar kwamkwasiya da
sukayi layi a chan gefe, tace "kar ka damu, i can take myself home" ya harareta ba tare da yace
mata komai ba ya ja trollyn ta ya yi gaba, bata da zabin da ya wuce ta bishi a baya tana
murmushi.

Kafin ta isa har sun daidaita da da mai motar ya sa akwatin ta a booth, Habib ya bude mata
baya yace "Bismillah", ba gardama ta shige baya, shi kuma ya bude kofar gaba ya shiga direba
ya ja suka dau hanyar Katsinan Dikko dakin kara.

Karfe 8 suka iso, Yace wani unguwa kikayi tace "GRA Bayan gidan Govenor", ya juyo da sauri
yana fuskantar ta, yace ai unguwar mu ce, tace wai dagaske? Ya ce eh, to wani gida kike?" tace
gidan Alhaji Tijjani Masanawa ai nan Habib ya hangame baki Yace u must be kidding me, Gidan
Baba na kike? Itama da mamaki tace "nifa bana son zolaya" yace dagaske ba wasa ba" shine
last person da nayi magana da shi a jirgi, Abokin baba na ne sosai, he's like a 2nd father to me
and my siblings" tace "banyi mamaki ba, its a small world afterall, yace "haka ne but ya akayi ni
ban sanki ba? Tace "da yake a Cairo nayi College zuwa Masters dina, so ban fiye zama a
Nigeria ba, ko na zo banyin 1month nake koma wa" Habib yayi mamaki matuk'a yace wai ko
kece Aisha?" Tayi murmushi tace ya akayi kasan sunana? Yace ai na kanji baba na waya dake,
na taba tambayan shi wacece suke yawan waya?" Yace "kanwarka ce Aisha, tana Misra tana
karatu" a haka suka iso Gidan Alhaji Tijjani, wani tangamemen Gida ne, har ciki direba ya shiga
dasu.
Habib ya fito ya bude mata ya ciro kayan ta yace" Shatu, Allah ya huta gajia ko?" sunan da ya
kira ta dashi ya bata daria, tace "wato ba zaka shigo ba? Ko daman labari ne kawai ka keyi?"
yayi darian shima yace mutum da gidansu sai an gayyace shi ciki?" karki damu inaso naje gida
na huta, zuwa da safe zanzo ma gaida Baba " tace to shikenan, ta shige gida, shikuma ya koma
mota suka fita daga gidan.

_Bibilicious Biebee_

KE ALHERI CE ‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣1⃣

Washegari
Habib yayi sallama parlon Alhaji Tijjani da Asuba, duk'a wa yayi har kada yace "Baba Barka da
Safiya" Alhaji ya dago kai yace "lafiya lao Habibullah, ya gajiyar jiya? Habib yace "gajia ta bi jiki

baba" Alhaji ya tambaye shi game da ayyukan da yajeyi a Cairo ya shaida masa komai na tafiya
daidai.

Yace "Jiya sai ku ka ga bak'uwa", Alhaji yace " Aisha ko? Sai da tace min tare kuke na gardama
mata, amma daga baya na yarda da na tu a kaima fa jiya ka dawo, amma ya akayi ka shaida
kanwar ka, don na san ba ku san juna ba?" Habib ya kwashe komai ya gaya mai, Alhaji ya
jinjina kai yace "haka Allah ke abunshi".
A kwana a tashi Habib da Aisha sun yi wata irin shak'uwa da junan su, har so ya shiga tsakanin
su, soyayyah mai tsafta sukeyi, Alh. Na sane da su amma yayi shiru, a zahiri kuma yana farin
cikin wannan abu don Habib mutumin kirki ne, irin shi yake so aura ma Tilon yarsa, amma tunda
sun hada kansu tun wuri toh falillahil hamd.
Wata rana Habib ya shigo gidan don zuwa kiran Baba tijjani, ya aika a kirashi, Bayan gaisuwa
Alhj ya muskuta yace " Habib dalilin kiran ka shine in shaida maka yau za muje mu kai kayan sa
bikin Aisha, tunda kai kadai ne yayan ta, ina so ka hallara wurin zuwa, idon Habib ya rufe, be
san sanda yace "baba, wace Aishar? Ban gane ba? Yace " Aisha kanwarka ko? Aishan Misra"
Habib ya zabura yace "what?, Baba kar ka min haka, wallahi nike son Aisha, kuma tana sona
baba kar ka rabu mu don darajan Allah, cikin fushi yace kuma ai a aladance zuwa ake gidansu
yarinya a daidaita tsakani, ba wai da ga gidansu yarinya zaaje gurin Namijin ba, hala dan sarki
ne" ya fada a fusace.

Sosai Alhaji Tijjani yayi daria, sai da ya tsagaita yace " Habib in banda abinka, ya zaayi dangi
mata suje kai kayan biki? Ai ko a masarauta ba a haka, kwantar da hankalin ka d'a na, Kayan
Biki zamu kwasa ni da kai muje chan gidan k'anena kuma waliyyin Aisha, in nema maka
aurenta gun shi. Kunyar duniya ta lullube Habib, a take ya bar parlorn don kunyan baban da
yakeji yana murmushi.

Aisha tsallen murna takeyi da Habib ya gaya mata abunda ya faru tsakanin shi da baba dazun,
tayi daria sosai tace "wato kai loverboy ko?, ka mance baba kana ta sakin layi" yayi daria shima
yace "sanki ne ya jawo hakan" tace ni ba "ruwana".

Yau bakin Habib har kunne don ko Baba Auwal kanin Baba Tijjanj yace wata daya kawai ya sa
bikin 'yarsa. Baba Tijjani yace " ni da dana muna godia da wannan abu, Allah shi kaimu lokacin,
na maka Alawarin dana zai kula da diyarka yanda ya kamata" duk sukayi daria.

Baba Auwal yace "Yaya, ya maganar aikin Aisha a Wannan Oil and Gas Company din da
Gwamnan Kaduna ya bata? Yace duk sanda taso yin aiki ta kai offer din nan, unlimited time ya
bata, don yace ko ba shi ke mulki ba, ya riga yayi signing kuma dole a amince da offer" Alh ya
tabe baki, yace " Kaduna fa? Toh gashi kuma kace aurar da diyar ka zakayi nan da wata, kaga
ko aiki wani gari ma be tashi ba, in ma zatayi aiki, to wannan hakkin mijinta ne ya barta ko ya
hanata, kuma dole sai inda zasu zauna"
Habib ina kake so ku zauna? "Habib yace Baba nan gidan Marigayi da nake Gyara ginin nake

so mu zauna, amma muna iya komawa Kadunan, sai na dinga zuwa katsina duk weekends,
"sam ba zaayi a hakan ba, inda kayi niyyar zama nan zaka zauna, wato nan Katsina, sai ka
zaba mata cikin ministries din nan, kaga wanne ya kamata tayi aiki a ciki, sai na kaima SSG CV
dinta ya bata offer" sosai Habib yayi godia, yaji dadin adalcin Baba Tijjani, dama shi be da burin
zama a gidan da aka haifesu, balle shi da ya ci gadon Gidan Ubansa.
Yace Baba Nagode, Allah saka da Alheri, ina ga kuma tunda Public Admin ta karanta, zata iya
aiki almost ko ina, ko za a duba BOA (Bank of Agriculture)? Baba Tj, yace "duk yadda kagani,
ga baban ta nan kuyi shawara, ni idan ma zai yarda da kun barta da aikin nan, don na tabbata
ba zata rasa komai ba da yardan Allah, kar taje ta wahalar da kanta gurin wani aiki" da sauri
baba Auwal ya katse shi da harara yace"haba yaya, bari mana, diya ta fa Masters ne da ita,
abar ta ta amfana da karatun ta mana" Baba Tijjani yayi daria, yace "daga bada shawara, yau
Auwal harda harara na? Allah baka hakuri nima da karambani na na shiga maganar diyarka" ya
kalli Habib yace "tashi muje kaji d'ana kafin a sake mana karnuka " Habib yayi dariya.

"Oh boy! wai ya maganar Gadon ku ne? Tunda tsohon ku ya rasu shiru nakeji, kasan zaka ja
kaya, ga ka da Gadon Uba ga ka daUwa, Oboi u rich oo" Abokin Hafiz ke wannan maganar, sun
dawo hutun aji biyar, da sun koma zasu shiga SS3.

Hafiz yayi murmushi, yace wai shi Anas meye damuwan ka da Gadon nan ne? Ince dai baka da
gadon baba na? Wannan naci haka, tunda na dawo kake tambaya na, to ba a raba ba, ba ma
bukkatar Gado yanzu, burin mu Allah ya gaffarta musu duka.
Anas ya shek'e da daria yace "kai ni zaka ma bariki? Ni zaka ce ma ba ka da bukkatar Gadon
ka? To bari kaji ina sane da an raba Gadonku, ka tashi da Miliyan 50 da Gidaje 3 da filaye. Hafiz
yayi daria yace " Ohh, Anas, to ka sani me yasa kake tambaya na? Kai ni fa ba abunda zanyi da
kudi" Anas ya sake shekewa da daria yace karya kake, kai ke ko da abunda zakayi da kudi, kai
fa nan Millionaire ne, ga ka da kyau da kwarjin, zakayi abunda kaga dama ba me ce maka don
me?, ka sa kallar kayan da kake so, ka hau motar da kake so, mata ma sai wacce ka zaba, kai
kasan if you have money u have everything"

Hafiz yace "na san da haka, amma yanzu karatu mukeyi, idan mun mallaki hankalin mu Yaya
Habib zai bamu hakkin mu nida Zaid, for now mun amince ya dinga juya mana kudin" Anas
yace "Ban taba sanin kai solobiyo mara tunani bane sai yau, dan Uba zaka sake ma ragamar
dukiyar ka kace ya juya maka? Lallai a ruwa kake tsundum wallahi" Baki bude Hafiz ke kallon shi, ya daure yace "kai Anas, ka iya bakin ka, Yaya Habib matsayin
Uba yake a gurina, kuma ba Gado na kadai ke hannun shi ba, harda na Zaid, kuma nasan zai
rike Amana" Anad yace kai ni rabani da maganar nan, zaka yi nadamar barin Gadon ka wurin
dan Kishiya, Aure zaiyi, Gida ya kera ma matarshi, daga Kasar Dubai ma ake Ginin, zai hada
kayan aure, duk a dukiyar wa? Kana zaton a na shi? To kai wawa ne indai kayi tunanin haka, a
cikin dukiyar ka zai yi duk wata hidima ta shi, da na ma kanin shi wanda suke Uwa daya,
Saboda me? Sabida kai dan kishiya ne, kuma ba za su taba sonka ba"

Idona hafiz yayi jaa sosai, da alamun zanttukan Anas sun shige shi matuka, Zuciyar sa ta fara
zafi, shaidan na dada ingiza shi, yace Anas yanzu meye abun yi? Anas yayi dariya ganin ya

samu nasara, yace "abu daya zakayi shine Ka karbi Hakkin ka".

_Bibilicious Biebee_

KE ALHERI CE ‍

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣2⃣

Anas ya cigaba da cewa "Ka same su kace su baka hakkin ka kana da bukatar su, duk yanda
zasu so shawo kanka ka fandare musu ka bada ma idon ka toka, duk inda suka bullo maka to
ka bulle musu" Hafiz ya jinina kai, yace "toh, bari zan gwada bayan bikin Yayan sai na bijiro
musu da bukata ta" Anas yace "bayan biki ai ya gama bushashar sa, yanzu ya kamata kaje ka
sake sa" Haifz ya mike yace "bari inje" Anas yace Allah bada sa'a kar ka manta, sai ka nada ma
idanuwan ka toka".

"Yadai Hafiz?" naga kamar bakinka akwai magana? Ya akayi ne?" Habib ne ke tambayan Hafiz
da tunda ya shigo dakin yake ta kame-kame. Hafiz yayi ta maza yace "Yaya, Gado na nake so
a bani in rike a hannuna, a bani hakki na" Habib cike da mamaki yace "Lafiyar ka Hafiz? Bakaji
me baba Tijjani yace ba? Sai kun gama Jamia za'a baku, Hafiz ya fandare ido yace "shidai a
bashi yana da buk'ata"
Habi yace "to shikenan Hafiz zan yi shawara da Baba Tijhani".
Hafiz ya dan yi ysaki yace "Yaya, Gado na ne ko? To nace abani kayana ban son ajiyar, ina da
hankalin da zan rike abu na, banga dalilin yin shawara ba, tunda dai shi da kanshi ya kira a ka
raba Gadon nan, toh ni dai nace a bani kaso na"

Yanda hafiz yake magana ya ba Habib Mamaki, zuciya taci Habib ya mike yace biyoni, ko kunya
Hafiz be ji ba ya bishi, a waje suka ga Zaid, da sauri ya taro su yace "lafiya? Yana ga fuskar ku
ba walwala? Habib yace "kaima biyo mu" ya fada motar sa ya bar gidan hanyar Bank yayi. Zaid
da Hafiz mota daya suka shiga, a hanya ne Zaid ke tambayan Hafiz" Bros, wai ya naga yaya
haka? Me ya faru? Hafiz ya dan tabe baki yace" ba fa abin da ya faru, kawai don nace yaban
Gadona a hannuna ba sai ya ajiye min ba, ni zan aje abu na da kaina shine ka ganshi haka"

Cike da mamaki da takaici Zaid ke kallon shi yace "Hafiz kasan me kake cewa kuwa? Me zaka
yi da Gadon ka haka? Idan wani bukata ne dakai ka sanar dashi, shi me iya baka ne ba tare da
ka taba Gadon ka ba, Haba danuwa na" da sauri Hafiz ya katse Zaid ta hanyar daga mai hannu
yace "in kai yaro ne, ni ba yaro bane, ina da damar da zance a bani hakki na, idan kao ba za ka
amsa naka ba, to ni zan amsa nawa, so please spare me the lecture"

Kasa magana Zaid yayi har suka zo Safe din babansu, inda ya ke ajiye kadarrorin sa, Tuni
Habib ya haye sama, suka bi bayanshi, Cikin Lokaci kalilan ya tattara duka Gadon su, da ma a
kashe suke, ya kalle su yace "tunda, baba ya rasu ban taba daukar ko sisi ba nayi amfani
dashi, duk kudin da kuka ga na taba to kudi na ne, hakkin gurin Aikina ba na Gado ba, to yanzu
Hafiz ka bukaci Hakkin ka, ni Musulmi ne na san hukuncin wanda ya danne ma wani hakki,
nikuma bana daga cikin masu dannewa mutane hakkinsu" ya tura mai wani dan safe box yace
"Wannan Miliyan hamsin da hudu(54) ne, a ciki akwai filaye 3 da location dinsu, da gidaje 2 a
garin Katsina" ya juya ya kalli Zaid yace kai kuma ga naka hakkin Miliyan hamsin da--" da sauri
Zaid ya katse shi ta hanyar cewa "Haba Yaya? Me zanyi da kudin nan? Ni bank'i a sadakar da
su Allah ya Jikkan su Baba, ba abunda zanyi da su, shi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login