Showing 111001 words to 114000 words out of 151322 words

Chapter 38 - Ke Alkhairi Ce Book (Complete) BIEBEE ISA--.pdf

Advertisement

16 Mar 2025

9665

miki ba daidai ba,
amma ki yarda dani, Everything happened sooo fast, bansan dalilin da ya sa na yanke hukunci
cikin fushi ba, bansan dalilin da ya sa na Sakeki ba, Wallahi na yarda dake, na san ba zaki
aikata wannan mumunnan aika aikan ba, duk da abun a Sark'e yake Allah kadai zai
warwareshi, bansan na furta miki kalmar Saki ba, sometimes inaji a jikina kamar controlling dina
akeyi" Mami ta share hawayenta ta kalleshi a raunane tace "Habibi, meyasa sai yau kazo? I've
waited for you my life" Kneel down yayi da cewa "Wallahi i dont know why i never cme back for
you, i'm sorry for taking so long, but i'm here now, i'll be with you again and Nothing can
seperate us now" ita dai Mami kuka takeyi, ta san tayi missing tsohon mijinta sosai kuma idan
ba shi ba ba zata iya rayuwar Aure da wani ba, tunda har ya bata hak'uri na sakinta da yayi, da
rashin binciken da beyi ba dukda ya ga abu clearly, dukda ba wanda zai fidda ta daga kangin
Sai Allah, to meyasa ba zata yafe mishi ba? Ai tunda be k'yamaceta ba, itama bazata k'yamace
shi ba, a hankali tace "ka tashi donAllah be kamata ka durkusa min da guiwowin ka ba, Na yafe
maka Habibi, ka yafe min, Wallah bansan komi da ya faru a wannan ranar ba" da sauri ya mik'e
tare da hugging dinta, for the first time in a very long time suka sauke numfashi a tare, sunyi
missing juna, yace "shhh, kar kice komai, na san ko ke wacece Shatu na, amma na miki
Alkawarin gano gaskian lamarin" tace "its been long Habibi let it go" yace "Never, i'll see to it
that whoever is behind this will pay" wani tunani yazo ma Mami, da sauri ta raba jikinta da nashi,

tace "Sorry, we cant touch eachother, ba aurenka a kaina" kanshi ya dafe yace "Oh Allah, now i
cant even touch my wife?" tayi murmushi tace "Your ex wife, bazawara ce ni, ina da zaurawa da
yawa, mai rabo ka dauka" ta k'arashe tana mai zolayar shi, ya harareta yace "me wuri yazo me
tabarma ya nade, inshort i cant wait any longer, Nearby mosque za a daura auren mu bayan
Azahar, ba zan iya bari har in koma Katsina ba" Mami ta tabe baki tace sai Walliyi na ya
amince" Daddy yace "Walliyin ki? Wanene shi? Na san dai walliyin ki ya rasu" Mami tace "Zaid
ne Waliyyi na" Daddy ya kalleta da mamaki yace "Zaid? Wani Zaid?" Murmushi tayi tace "Zaid
Iro Lema My saviour" "bangane ba?" gyara tsayuwarta tayi ta kwashe labarin tun randa ta bar
gidan shi zuwa yau, hawaye yakeyi yana k'ara rok'on ta gafara, wani Son Zaid na k'ara shiga
ranshi, be taba tunanin Zaid na da kaifin tunani kamar haka ba, Lallai Zaid ALHERI ne,
wayarshi ya ciro tare da dialling Numbern Zaid, ringing sukaji kusa dasu a tare suka waiga,
Zaid, Rafeeq da Maalesh tsaye a kofar kitchen, Zaid yace "Welcome back to your Senses
brother" sukayi daria, Daddy yace dole kayi welcoming dina, ya rungume Zaid sosai, yace
"Thank you Brother, Allah ya biyaka" Murmushi yayi ya kallo Mami yace "kuka ya k'are ko
Mami? Tayi Murmushi tana share hawayenta, ganin sabon kuka zata fara Feeq yyi saurin cewa
"What a reunion in the kitchen" Sukayi daria, ta kalli Daddy tace "kuje Parlor i'm coming out with
lunch" Daddy ya kalleshi yace "Okay Zaid and His sons Out you go " sukayi daria duka suka
fice. Taimaka mata yayi da tray din, ita kuma ta dauko sauran kayan suka fito Parlor, Rafeeq ya
kalli Mahaifansa, yanda ya gansu ya ji dadi, hakan ya faru ne saboda Uncle Zaid, me zai ma
bawan Allahn nan ya ji dadi shima, dole ya samo mai farinciki a duk inda yake"
********
Su biyar zaune a Kan dinning suna cin Abinci like before, Daddy yace "R-lema nikam yaushe
ku kazo Kaduna? Kamar ba zai tanka ba yace "Jiya" "oh shine ba ka min sallama ba?" a
tak'aice yace "lokacin da na fito baka tashi bacci ba" Zaid yace "Mami kinga Nenemu ko?" tace
"aikuwa na ganta, waya gaya maka tazo?" yace "Ai da mukayi waya da Seebi ta shaida min sun
rako Yaya gunki ita da Nene" Rafeeq ya zaro ido yace "Wait, Neh-neh na Kaduna? " Ehmana"
Daddy kai ka kawota? Saboda mene? Daddy do u have to bring her along? Omg, dole in koma
Katsina like right now" Rafeeq my child me yayi Zafi haka?"Mami that woman is the most
craziest person i've ever seen, she's Delusional " Mami taba ta rai tace "ka min shiru, tsaraka
ce? Dont talk about her like that, me ta maka ne? Maalesh ya chafe, ya basu labarin haduwar
su ta k'arshe da Nene daria sukeyi sosai banda Rafeeq da ya daure fuska don shi be ga abun
daria ba, Daddy yace " Yihuhu ina dunkum din yake" aiko suka sake tuntsirewa da daria,
Rafeew ya tashi ya dibi abincin shi a plate ya bar musu wurin" Zaid yace kunga ku rabun min da
Yaro na ko ince ba zan bada Auren ba" da sauri Daddy yayi shiru Mami da Maalesh na daria
k'asa k'asa.
******
Bayan Zaid ya shaida ma Baba Tj komai, Baba Tj yace "Zaidu ai kaine Uban Aishatu yanzu, na
baka wuk'a da nama, duk yanda kayi daidai ne" Zaid yaji dadi, baba Tj ya sa musu Albarka.
Bayan Sallahr Azahar ne Mutanen Unguwar Malali da suka halarci Sallahr Azahar a Massalcin
ne suka Shaida Auren Aishatu Tijjani, da Angonta Habib Iro Lema bisa sadaki Naira dubu 50.
Inda Zaid ne Waliyin Amarya, Abiin Seebi ne Waliiyin Ango. Daddy baki ya ki rufewaji yakeyi
kamar yau ne aurenshi na farko. 4:30pm

Nene ta tasa Mami a gaba tana mata fadan Sakaci da addua, da yanda ta bari har aka kulla
mata sharri bata ji bata gani ba, da yanda ta jefa rayuwar danta a garari, "to salan in kin koma
yanzu ki k'ara Sake, har a sake kulla maki wani mugun sharri, sai fa kin mike tsaye don kina da
kishiya, ai mu ba boka ba Mallam muke cin uban mutum, ta inda Nene ke shiga ba tanan take
fita ba, in kunga yanda takeyi sai ku rantse da Allah ita ta haifi Mami ko kuma ta dade da
sanninta kamar ba yau suka fara ganin juna ba, A ganin Nene Sakacinta ne Ya sa aka mata
Asiri kalakala, duk da bata fito tace masu ga abunda ta sani game da Saude ba, sun dago wani
abu, amma ko wa ya share" Nasiba na Allah allah kar Nene ta ballo musu ruwa, ta cigaba"ai
akwai magungunan da zan baki, sai dai mun kebe don kawar zaman taki 'yar yi ce" kunya ya
kama Ummi, Seebi da Mami, don Nene ta fara sakin layi, Surutun ta suka fara isar Rafeeq
gashi Daddy ya hanashi fita, ya buga tsaki tsut hankalin ta ya koma kanshi, tace "Kai dunkum
dangin tsaka, ka fita idona, kar ka sake min Tsaki, kar ka ga ka tsira wanchan karan, yanzu na
ritsa ka sai dai uwarka ta sake haifo wani d'an"duk suka rike dariar su, Zaid yayi murmushi yace
"Nenenmu da har ina cewa Ke zaa kai yar zaman dakin Rafeeq?" tace "Yo ai duk matar da ta
auri Dunkum ta zama abar tausayi, don Zama da dunkum Sai Ni, ni kadai na san maganinshi,
amma idan ya auri mace shirushiru kamar Seebi zata mutu da bakin ciki, don irinsu akwai kunsa
bakinciki, kyanta ya samu irin mu" Ummi tace "to ko ke za a aura mai?" "Ai Ko wallahi da duk
dare sai na kulleshi daki na ci ubanshi" Abbi da kamar ya nitse kasa don kunya yace "Nene ba
na hanaki irin maganganun nan ba?" ta kallo danta galala tace "Nabari, ubana Mamman" Zaid
yace "kiyi hakuri Nenenmu" tace "yiriri angon bana, nayi hakuri, kuma dai tsaya ai tunda an
hadu haka ai gwara a sa bikin su Zaidu bawan Allah da Seebina ko? Daddy yace "Ashe
soyayya akeyi su Baban Rafeeq" Zaid ya rasa ta cewa, Daddy yace "Abu yayi dadi, barin ji ta
bakin diyata, Kinason sa Seebi?Nene ta chafe tace"tsohon zance, in kaji yandatake narke mai
tana wannan abu a waya sai ka rike baki, da baka sha wahalar tambyarta ba" Seebi kamar
k'asa ta tsage ta shige ciki, Nene ta gama kasheta, Abu yayi kyau, to Mallam ya kagani? A sa
bikin yanzu?" Abbii yace duk yanda kukayi daidai ne, Daddy yace to tunda gamu duka anan, sai
a saka ko? Zaid yayi saurin cewa" Yaya, donAllah minti daya".
*******
"Wani irin magana ce wannan kakeyi Zaid? Wa zai ma Rafeeq aure yanzu? DonAllah bar
zancen nan, banson shashancin banza, kai Nasiba take so, kuma kai zan bata, shi kuma idan
ya isa aure ya samo wata chan ko yar gidan wanene zan aura mai ita" Daddy ya shige ya bar
Zaid a k'ofar parlo, ba me fahintar shi. A nan aka sa biki bayan nasiba ta gama Level 1, dukaduka be wuce Wata Daya da kwanaki ba,
Abbi yace "Alhaji da ka bari anyi komai a tsanake, ina ganin kamar wata 1 yayi kusa" Daddy
yace "kar ka damu Mallam, daurin aure kawai nake bukata kazo, don bikin nan na YAR GATA
CE, da dan gata" sukayi daria, Rafeeq ya dago ya kalli Seebi, itama shi din take kallo, suka
k'urawa juna ido sun kasa karantar junarsu.
********
"Shatu na ina muka kwana? Ni bazan barki nan Kaduna ba, don ba zan iya hure rashin ki a
kusa dani ba kina da option din inda zaki zauna, ki zabi Daya daga cikin gidajen da zaki zauna
a Katsina, don gobe zamu wuce gaba ki daya saboda karatun yaran nan" Mami tayi murmushi
tace "Habibi na, ba sai na zabi ko wani gida ba, I want to live where it all started, nan Main
house din, There are lot of Wonderful Moments i shared with all my loved ones there I want to

live there again, that is if my room is not Occupied yet" ya rungumeta yace "your Room is
waiting for you, Thank you shatu, i love you so much" i love you more Habibi" yace "We leave
tomorrow"

WasheGari
* Katsina*

Tun daga bakin gate Nene ke rangada Guda, bayan ta Nade Mami cikin lafaiyarta,Ummi na
rike da Hannun Mami, Mom din Maalesh da hajjo suka iso gidan, dama Maalesh ya kirata
lokacin da suka shigo KT yace "tazo gidan su Rafeeq tarban k'awarta" ta rungume kawarta
suna hawaye, Nene tace "Hajia yau ba ranar kuka bane yau ranar kunsawa wasu bakin ciki ne"
kamar ya?" matsa ki gani, wanda be da hanci ya ja gefe, Nene ta shiga rangada guda, Hajjo ta
tayata gabaki daya suka kama hanyar shiga gidan.

"Meema me nakeji haka?" Sis guda ne!" anya gidan nan ne kuwa? Jin gudar na matsowa kusa
ne ya sasu tabbatar da hakan, Saude ta sauko da kgar daga kujera don zuwa ganin ikon Allah,
Meema tace "Sis ina zakije da wannan kafar taki duk ya ja ruwa" Bata kulata ba, ta shiga
dangyasawa tana cije baki ta fita daga dakin, ji tayi gudar na kusantosu, sai ganin Nene tayi da
wasu mutane biye a bayanta,banda Seebi ba wanda ta shaida, Saude ta daka wata uwar tsawa
"Ke jarababiyar tsohuwa, wani salon iskanci ne wannan? Zaki shigo mana gidan kina guda, sai
kace gidan biki wanda suka dauko Amarya" Nene tace "banda abunki ai duk inda akaji guda an
sna da Amarya a gun" Saude cikin rashin fahimta tace bangane ba, ina fa zaki gane bayan
kanki cunkushe yake da duhu, to Amarya ce aka kawo, Amarya Habibu Lema, Kuma ta shigo
kenan, ba boka mallam tuggu, kisisinar da zai fiddata, ta shigo kenan, mutu ka raba takalmin
kaza, wanda be iya ganin hakan sai fita dan uban mutum" gaban Saude ya yanke ya fadi, ta
kasa gasgata zancen Nene, Alhaji ba zai taba yi mata haka ba, amma ta lura akwai wacce aka
lullube, ta maida hankalinta kan wacce ke lullube da farin lafaya, a ranta tace Amarya?
Zuciyarta na dukkan tara tara ta taka har gaban su, ta sa hannu ta yaye mayafin,
Yanda kukasan taga Dodo haka ta sake mayafin da sauri tare da ja da baya, gani takeyi kamar
Gezau, wata ta gani kamar Aishatu, haba ba ita bace, idonta ne, Na kan tudu yace ba zata sake
taka gidan ba, jin muryar Nene tayi inda take cewa " ita din dai ce, Nana Aishatu Masoyiyar
Asali, wacce k'addara ta rabata da gidanta, kuma Allah ya maidota, bawani dan buta uban da
ya isa ya fidda ta kuma" Saude cikin kidima ta sake ihu tace "Aishatu, kai k'arya ne, ba ita bace"
Mami tayi murmushi tace "Nice Saude, Nice" Luuuuu Saude ta fadi k'asa sumammiya.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼â€â™€

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu
Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxiesâ¤
Pg5⃣6⃣

Duk sukayo kanta, Alhaji Habib yace "Ku taimaka a kaita Asibiti" Nene tace "wani Asibiti?
Ai kawai ruwa zaa yayyafa mata" Meema tayi saurin dibo ruwan fridge, Nene ta karba ta watsa
mata ruwan sanyi nan, Saude ta farfado idonta fes kan Mami, sake zabura tayi zata tashi,
Meema ta maidata ta kwantar a k'asa, Mami ta tsugunno zata dafa Saude, Saude tayi zumbur
tare da nunata kar ki tabani, wallahi kar ki tabani, Aljanna ce ke, it cant be, ance ba zaki sake
dawowa ba?" duk kallon mamaki suke mata, Meema tayi saurin cewa "Wallahi Daddy tundazun
Sis ke ta sambatu, ina jin Zafin ciwo ne, don wani Katon Maruru ya fito mata a guiwa" Daddy
yace Allah ya kyauta, ai sai ki mikar da ita ki wuce da ita daki, Ya shigewar shi ciki, Zaid yace da
su "ko muje Asibiti ne?" da sauri Saude ta girgiza kai tace "ai taje" Nene ta ta6e baki tare da
cewa "mun rike Allah da Annabi, ku mu shiga daga ciki ko?" Mom din Maalesh ta ja Mami cikin
gidan bayan Mami tayi adduar shiga Gida.
****
"Yo ai tunda ba a kai ga shara da gyaran dakinta ba ai ina ga dakin Mijinta kawai zaa safketa
ko?" cewar Nene, Maman Maalesh tace "hakan ne daidai, in yaso a gyara mata daki daga baya
ta koma" Dakin Alhaji Habib suka shiga da ita, bayan sun dan jima suka mata Sallama, Uncle
Zaid ya dauki Ummi Da Ayman ya kaisu gidan Baba Tj don chan za su zauna, Nene da Seebi
da suka shiga dakinsu don huta gajia.
********
"Na shiga uku na, tawa ta same ni, Meema ya zanyi da mutanen nan? Aishatu ta dawo, komai
ya jagule, nasan yin wannan Shegiar tsohuwar, nayi nadamar sawa a kona gidansu don yanzu
Reshi ya juye da majuyi. Ni gaskia ba zan iya bari Aishatu ta kwanta da mijina ba, zuwa zanyi in
lumama ta wuk'a ta mutu, na tsaneta na tsaneta" Saude ce ke wannan furucin cikin yanayin da
ya firgita meema, bata ta6a ganin Yayarta a wannan yanayi ba, Firgici da Tsoro take gani
kwance a idonta, tace "Sis ki k'okarta ki kwanta, komai zai zo a sauk'ak'e, gobe zanyi maganin
abun, trust me Sis". Saude ta dan jigina da pillow kamar me bacci".
******
Aneesa batayi wani tashin hankali ba data dawo daga makaranta taji labarin dawowar Mami,
hasalima murna tayi don ta tuna da, Mami ta kasance me kyautata mata, har Parlorn Daddy taje
ta rungume ta, tana mata sannu da zuwa, Daddy yace " kice ma Saude bayan Isha'i tazo ina
nemanta" tace "ok Daddy" ta fice ko da ta sanar da Mummynta Saude ta haruzka, don me
Aneesa zata je gun Aishatu, tayi fadan ta zage Aneesa tas, karshe ma Aneesa ta buga tsoki ta
bar dakin, ko a jikinta don ita bata tsoron fushin mamarta.
Sak'e sak'e saude ke tayi, bata san me zatayi ba, idearta duk ta k'are, duk wata dabararta ta
bace bat ta cije yatsa ta datsa lebe duk don ta samu sausauci amma a banza, Meema ta bata
shawara tayi acting kamar ba matsala kafin da safe ta nemo mafita.

Har wurin k'arfe 9 ba Saude ba Labarinta, Alhaji Habib ya latsa wayarshi ya kirata, K'in

dauka tayi sai da Meema ta rada mata wani abu a kunne, kafin ta dauka tana cika tana
batsewa, yace "Saude ina nemanki a dakina" a takaice tace "banda lafiya" yace "SubhanAllah,
kafar ne har yanzu? Gani nan zuwa" ya latse wayar ta kalli Meema, Meema tace "lets use this
opportunity ki kwanta ki ta juyi matsayin baki lafiya, kinga zai tsaya wurinki" ta dan mata rada a
kunne" Saude ta jinjina kai tace "Plan dinnan zaiyi aiki".
****
"Shatu nah, Saude ce bata ji dadi ba ina so in je in dubota" Mami ta dan hade wani bakin miyau
tace "Haba Habibi, matarka bata Lafiya shine sai ka tsaya tambayan wani izini, donAllah tashi
muje mu ganota" Daddy ya ji dadi tare da rik'o hannun Mami suka nufi Dakin Saude.

Kwance take kan gado tana ta mutsumutsu, ya k'arasa Gadon ta tare da kiran sunanta, ta
rungume hannunshi ta na wani kukan munafurci, Mami ta kauda kai, yace "Sannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login