Showing 1 words to 3000 words out of 27791 words

Chapter 1 - ZARINAT (زرينة) book 1 free page's by zainab dodo.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

1619

 ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️









Paid book ne


Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only


Dedicated to my daughter Narnah khadija( Muhibbaty) allah ya albarkaci rayuwarki my daughter
much love for you fisabillilah ♥️ ♥️♥️♥️♥️♥️♥️


_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________

________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣


Gida ne mai kyau gwaurgwadan gidan talaka bawan allah mai rufin asiri, d'aki biyu ne a gidan
sai dai ba'a jere suke ba d'aya na dubin wannan 'bangaren d'aya na dubin wannan,


Wani mutum ne ya shigo ahankali yake tafiya kamar mai tsoron kar a kamasa, ahankali har ya
isa bak'in k'ofar d'aya d'akin, sai da ya juya bayan sa yaga ba kowa yayi sauri ya shige ciki


Zaune take saman sallaya tana lazumi, ganin sa yasa ta saki murmushi tare da saurin Mik'ewa
tsaye tana fad'in " Sannun da zuwa" Hannu ya d'aga mata alamun tayi k'asa_k'asa da muryar
ta, kana yace " Ina inna ne? " Tana d'akin ta "Ungo kar'bi wannan bara na d'auko takalmi na kar
ta gane na dawo" To" ta fad'a tare da sa hannu ta kar'bi ledar hannun sa,


Cikin sand'a ya sake komawa bak'in k'ofar yasa hannu ya d'auki takalmi sa juyawar da zai yi ya
koma yaji muryar inna ta doki kunnuwa sa tana fad'in "Allah ya toni asirin ka fito fito naganka"
Sumi sumi ya juyo tare da zube takalmin k'asa ya fito, inna ta k'arso wajen


"Wato dan kar insan ka dawo ne shine ka shigo gida kamar 'barawo to allah ya nunamin kai "
Inna ba haka ba ne nayi sallama banga kowa ba shiyasa nayo d'aki" Ohh so kake dai kace
k'arya nake maka ko toma dai idan ba haka bane su talakmin da ka dawo d'auka ina zaka kai
su? " Shuru yayi tare da sosa kai kana yace" Inna daman naga alamun akwai hadari ne shiyasa
nadawo na d'auke takalmin kar ruwa ya jikasu su lalace "

Inna ta saki baki tare da d'aga kanta sama"Kai nasuru kaji tsoron allah ina hadari yake wanga
waje ga rana nan tarmasisi kace min wai dan kar ayi ruwa takalmin ka su jik'e to naji ina ledodin
da ka shigo da su? " Suna d'aki ya fad'a yana k'abar fuska

"To d'auko su Mik'omin nan nagani " Bai ce komai ba kuma bai motsa ba ganin haka yasa inna
cewa" Au bazaka shiga ka d'auko ba ne to ni bara nashiga na d'auko ai ba kunyar shiga d'akin
nake ba" ta fad'a tare da bangaje shi ta shiga d'akin ya biyo bayanta


Tana shiga bata tsaya ko ina ba sai gaban matar da ta hango ledodin a hannun ta, tana zuwa ta
Mik'a hannu tare da fad'in " Mik'o min" Mik'a mata tayi tasa hannu ta amsa, ta bud'e ledar kayan

miya ne aciki ta ajiye ta bud'e d'ayar d'aurin nama ne gassashe guda biyu a ciki babba da
k'arami, bud'e k'ara min d'aurin tayi ta jefa tsoka d'aya a baki tana fad'in "Wai sau nawa ina fad'a
maka ba'a sabama mata da cin dad'i ne idan ka siyo ka rik'a mik'o min na kamma bata wannan
ai yayi mata yawa " ta fad'a tana k'ara jefa d'aya a baki

"To inna allah ya bani idan ban siya mata ba wazai siyo mata ai kuma kinga ba koda yaushe
bane nake siyowa ba sai idan na samu kud'i ne nake siyo muku " Uhmm haka ne kuma to ku
kar'bi wannan" ta fad'a tana Mik'a masa k'ara min d'aurin data bud'e take ci " Inna wannan ai
naki ne bakiga wancan yafi yawa ba wancan mubiyu ne wannan kuma ke kad'ai ce" Nagani
Nasuru nace nagani amman wannan zan baku wai kai bakasan gata ne nake muku ba bana
son ku saba da cin irin wad'an nan abubuwa kamata yayi nida nake tsohuwa na rik'a cinsu baku
ba kar'bi ka gani naje naci nawa " ta d'aura masa a hannu ta fice


Juyowa yayi ya Kalli matar sa yace " Fatima kiyi hak'uri kinji in Sha Allah komai zai wuce karki
damu "Murmushi ta saki tare da fad'in"Lahhh wallahi babu komai ai gaskiya inna ta fad'a ita ya
dace ace ta rik'a cin wad'an nan ba mu ba "Uhmmmmm " Nasir ya fad'a Dan yasan ta fad'i
hakan ne kawai dan kar ya damu
"Kar'bi ki ci ni daman ba ci zanyi ba" Miyasa to? " Naji cikina na d'an murda min idan naci sa
ciwon zai iya zama babba 'Subhanallah sannu ka sha magani kuwa?" Eh nasha gama sauran a
aljihu" Okay sannu to ko zaka k'ara sha ne sai ka d'an kwanta ka huta " Wa ni rufamin asiri na
kwanta yanzu kar kisa inna ta shigo d'akin nan ta kasa ta tsare"Hhhhhhhh " Dariya tayi tare da
fad'in" kai Abban humaira"Ai kema kinsani sarai basai na fad'a ba " To yanzu dai bara na d'ebo
ma ruwa ka k'ara Shan maganin"To shikenan "

Ta cire hijabin ta wuce dan d'ebo masa ruwan, da kallo yabi bayanta har ta fita ya lumshe
idanunsa, allah ya gani yana buk'atar kusantar matar sa shine ma dalilin da yasa ya dawo gida
amman yasa ba daman yin haka tsaki yaja a k'asan ransa


Har ta d'ebo ruwan ta kamo hanya sai ga inna ta fito da d'akin ta, ta tsare ta tare da fad'in " Ina
zaki je da ruwa kuma cikin d'aki ko wani abu kika ci nashan ruwa? " Aah kai masa ne zanyi
yasha magani "Au wai daman bai koma ba to meya tsaya yi haryanzu bai koma ba" Cikin sa ke
ciwo " To maza kai masa ruwan yasha ya koma kasuwa"To " ta fad'a tare da wuce wa tayi d'aki

Tana zuwa ta Mik'a masa ruwan ya 'ballo maganin yasha ta kar'bi kofin ta ajiye tare da
fad'in"Sannu yanzu ya kake ji? "Da sauk'i sosai "ya fad'a tare da janyota ta fad'o jikin sa, bakin
sa yakai satin kunne ta yad'an ciza kad'an tayi y'ar k'ara cikin shagwa'ba tana yarfa hannu tace
"Da zafi fa"Dagaske? " Kai ta gyad'a masa"Uhmmm i need you maman humaira ta " Zaro ido
tayi waje tare da fad'in"Yanzu?" Kai ya gyad'a mata tare da mairairaice face " Tabb kai ma fa

kansan inna baza ta bari ba ka bari har anjima idan ka dawo kaji"Wayyoooo ki tausayamin
mana nafa dad'e banyi ba " To ai ba laifi na bane inna ce bata bari da mun shigo d'aki tace mu
fito waje " Uhmmmmm, ya fad'a yana shinshinan wuyan ta


Inna ce ta k'aullah masa kira" Nasuru! !Nasuru! Kai wannan nasuru" dak'yar ya iya furta kalmar
"Naam inna"Uban me kuke a cikin d'akin har yanzu da baka fito ka wuce ba "Gani nan
fitowa"Aah karma ka fito ku dangoma a ciki "


Fatima ta tashi daga saman k'afafunsa, ya Mik'e, ta mik'o masa hular sa ya saka, hannu yakai
zai janyota tayi saurin jan baya "Muje dan allah kar mu k'ara wani laifin" ba tare da yace komai
ba ya kama hanya ya fito ta biyo bayansa


Yayi ma inna sai ya dawo tace "Allah dawo lafiya,har ya kusa fita ta dakatar dashi tare da
fad'in"Yawwa idan zaka dawo kad'an biyomin da abu mai d'an dad'i dad'i wanda zan sama
bakin salatin nan nawa "To" ya fad'a tare da fita


"Wannan! wannan ! Anyi bita zaizai awajen nan kai gaka dad'ah duk inda mata ta jaka kana can
ohhh inda ranka kasha kallo"Inna ta fad'a tare da juyowa ta kalli wajen da fatima take tsaye

"Ke tsohuwar munafuka tsanyuwar uban mekike yi anan baza ki wuce d'aki ba, juyawa tayi ta
shige d'aki

"Shegiya kamar wata mutuniyar kirki idan ka ganta simi simi da ita................












Had'aden saurayi ne zaune gaban ammin sa fari ne soll kamar balarabe ga kwantacen sajen sa
wanda ya k'ara masa kyau ya had'u tako ina,

Marairaice face yayi kamar zaiyi kuka ya kalli ammi tare da fad'in" Ammi please"

"Ansar auren nan fa ko kanaso ko baka so dole sai anyi shi danma ka sani abbanku sun riga da
sun yanke hukunci "Yanzu ammi ba abinda zaki iya yi akan maganar auren nan " Babu dan bani
da ikon da zan sa ayi kuma bani da ikon da zan hana ayi " Innalillahi haba dad yazakumin haka
wallahi akwai wacce zuciyata ke so kuma mun riga da munyi alk'awarin aure a tsakanin mu "
iKon Allah to sai a warware alk'awarin shikenan" Ammi dan allah ki taimakemi kimin wata
alfarma dan allah ammi na"Tame kenan? " Yawwa ammi dan allah a had'a da wacce nake so a
d'aura muna auren nasan idan ke kika jema dad da maganar zai amince amman wallahi ni idan
naje ko tsayawa saurarena ma bazai yi ba dan allah ammi ki taimakamin wallahi muna son
junan mu sosai"Ammi ta kallesa tare da nazarin kalamansa

Sannan tace "To shikenan zan gwauda amman kasani idan bai amuntaba"zai ma amince in Sha
Allah "Allah ya yarda yasa kuma hakan shi yafi zama alkhairi"Amin ammi na










☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Kyakkyawar budurwa ce fara ce sosai, gata da manyan ido eyelashes d'in ta zagar_zagar ga
dogon hancinta bakin ta dan dai_dai la'b'banta pink dasu girar ta cikakka fuskarta ma haka, ga
fuskar sumul_sumul gwaunin burgewa

Tana sanye da abaya mai shegen kyau tayi rolling kanta da mayafin abaya, hannun ta sanye da
wani tsadadden agogo mai masifar kyau, tayi tsaye bak'in k'ofar wani d'aki ta k'wank'wasa k'ofar

"Shigo" Bakin ta d'auke da sallama ta shiga

"Wowwwwww my princess irin wannan kyaun haka ma sha allah tubarakallah " Murmushi
Kawai tayi tare da k'arasawa wajen matar ta zauna kusa da ita, tare da gaidata cikin
girmamawa, ta amsa


" Daddy baya nan ne " ta fad'a" Eh suna wajen meeting "Okay allah ya taimaka"Amin kin San
dalilin da yasa nace kizo zamuyi magana "Aah mom"To zarinat ina son ki natsu ki bani aron
kunnuwanki anan wannan maganar mai muhummanci ce" To mom" Zarinat "Naam"Kin san dai
bazamu za'ba miki abunda zai cutar dake ba ko?" Eh " ta fad'a tare da d'aga kai " To daddyn ku
ya yanke hukunci zai aura miki d'an uwanki Ansar"da wani irin mahaukacin sauri ta d'ago tare

da kallan mom tana tunanin ansar! Ansar! To wane ansar kenan?


Mom kamar tasan tunanin da take yi yasa tace "Ansar d'an kawunku" Wani irin harbawa zuciyar
ta tayi da k'arfi nan da nan saiga hawaye sun zobo mata...............................................


ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 2️⃣

Kuka ta fashe dashi mai sauti, mom ta janyota jikinta tare da bubbuga bayanta alamar lallashi,

"Ya isa haka mana princess" mom ta fad'a tare da d'agota takai hannunta gefen gado ta janyo
tissue tasa tana goge mata hawayen fuskarta

" Princess kiyi hak'uri ki d'auki wannan hukunci da mahaifin ki ya zartar akan ki ina san ki
kasance mai hak'uri da juriya mai tawakkali a wajen allah idan kika kasan ce a hakan sai kiga
al'amurra sun zo miki da sauk'i duk da nasan kina yi ni kaina ina son naga kinyi aure kinje d'akin
mijin ki, kinsan wani abu kuwa princess? " Mom ta fad'a tana kallan fuskarta, Kai ta girgiza mata
tana sauke ajiyar zuciya


"Kinsan irin wannan auren shi ne ake kira da auren gata saboda bako wace mace bace take
samun irin wannan auren ba sai yan gata kamar princess d'ita " Mom ta fad'a tare da shafo face
d'in zarinat, murmushi tad'an yi, tare da fad'awa jikin mom ta kwantar da kanta gefen kafad'arta,
mom ta rungumota tana bubbuga bayanta tace " Zarinat"Naam" ta fad'a cikin muryar kuka
" Nasan ba'a kyauta miki ba bakya son wannan auren amman ki d'aure kiyima iyayenki biyayya
in Sha Allah zakici ribar wannan biyayyar "

Hawaye ne masu zafi suka zubo mata"Princess kin san banasan ganin xubar hawayenki d'aga
min hankali suke yi please ki daina wannan kukan ko kinasan na shiga cikin damuwa?" Da sauri
ta girgiza kai
"Yawwa to kidaina idan ba haka ba zan iya shiga cikin damuwa, abu d'aya nake so dake
princess ina san ki kasan ce surukar kirki mata ta gari " Mom taya zan iya hakan bancin ban
shiryama wannan al'amarin ba"Shiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii babyna bana son kina fad'in haka nasan zaki iya
in Sha Allah zaki iya " da haka mom tayi ta bata kalamai masu sanyi
( Wacece zarinat)
Su biyu ne a wajen iyayen su sannan manyan mutane ne attajirai masu ji da nera, daga ita sai
yayan ta, lokacin da aka haifi yayanta bilal, an d'auki tsawon shekaru kafin mom ta sake samun
wani ciki, iyayen su naji dasu sosai suna basu gata da kulawa yarda ya dace kuma sun basu
tarbiyar da ta tadace, zarinat

Yarinya ce da tunda ta taso bata ta'ba yin k'awa ba ko saurayi ita kad'ai take rayuwar ta itama
abun na damunta sai dai ba yarda zatayi tunda allah bai kawo mata ba , sai da aka kaita
boarding school sannan ta samu k'awaye, tunda suka kammala school shikenan duk suka rabu
Saboda babu wacce suke gari d'aya amman suna chatting, har group d'in makaranta suka
bud'e, haryanzu duk da tana university amman bata da k'awa,
Tana da timetable tasan lokacin da suke da lecture dan haka tun kafin lokacin zataje ta zauna
har ayi a gaba ta wuce,

Wannan kenan











Bayan dad ya dawo, ammi taje masa da zancen ansar, yace "ina sam hakan bazai ta'ba
yuwuwa ba" Ta sanar ma ansar yarda sukayi, ya shiga cikin damuwa da tashin hankali, can
wani tunani yazo masa, dan haka ya shirya ya nufi gidan su zarinat, ya samu daddy ya fad'a
masa duk abunda ake ciki nak'in amincer da dad yak'i yi akan auren sa da waccen, daddy ya ce
yaje Kawai in Sha Allah daga ya Fito daga gida zaije ya samesa akan maganar kuma zai
amince,

Ansar ya tashi da farin ciki dan yasan, shi kad'ai ne wanda idan yacema dad ga abunda za'a yi
bazai musaba saboda tsananin k'aunar da yake yima d'an uwansa shiyasa baya iya yin musu
dashi


( Ansar da zarinat d'iyan wah da k'ane ne Mahaifin ansar shine babba Mahaifin zarinat shi ke
bimasa, suma su uku ne ga iyayen su,

Alhaji abubakar, dad kenan Mahaifin ansar, Alhaji sani, daddy Mahaifin zarinat, sai hajiya rabi,
k'anwar su)

Ansar su biyar ne a wajen iyayen su maza hud'u mace d'aya, wacce ita ce ta zamo y'ar autar
su, kuma ita ke bima ansar

Daddy na fita kamar yarda yayima ansar alk'awari kuwa sai da ya fara zuwa wajen dad, da yaje
ma dad da maganar duk da baya iya masa musu akan magana amman wannan sai da yayi
dak'yar daddy ya shawo kansa ya amince









☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Abincin fa baka ciba" Fatima ta fad'a
" Hmmmmmm ni yanzu bata wannan nake ba zo ki d'an ji " Uhm uhm harfa na zuba kar yayi
sanyi"lallai naki wasa ne yarinya" ya Mik'e tare da zuwa ya rufe d'akin ya dawo ya cire kayan
jikin sa ya rage daga shi sai gajeren wando, yasa hannu ya d'ago ta, tana sanye da hijab dogo
har k'asa hannu yasa ya cire hijabin daga ita sai wata y'ar riga lahelahe marar nauyi ita kad'ai
ce a jikin, ya janyota jikin sa tare da had'e bakin su waje d'aya, ya tallabe ta suka fad'a gado,
suka shiga farantawa junan su...........................................
ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣

Bubbuga d'akin inna keyi da k'arfi " Nashiga uku na nasuru cikin wannan uban zafin zaku shige
d'aki ku rufe wai zaka zo ka bud'e k'ofar nan ko kuwa, kajimin d'an banza tasakaka d'aki tana
baka kana shanyewa kana tsotsewa zaku bud'e k'ofar ne ko sai na fita na samo majiya k'arfi
sunzo sun 'balle k'ofar "

Nasir da sauri ya Mik'e daga saman fatima ya lalubi jallabiyar sa ya zura, itama ta janyo rigarta
ta mayar,

Koda ya bud'e k'ofar har ta juya, ai kuwa da sauri ta juyo tana kallansa"Cikin wannan uban zafin
me kukeyi a d'aki salon wata cuta ta kamaku azo ana 'barnatar da kud'i wajen neman magani "
Yi hak'uri inna bamu jiki bane bacci muke yi"Iyyeeeee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login