Showing 3001 words to 6000 words out of 27791 words

Chapter 2 - ZARINAT (زرينة) book 1 free page's by zainab dodo.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

1627

lallai yaro mayar dani k'aramar yarinya
tunda bansan aikin da nake yi ba ta saka ka d'aki ta rufe ta bud'e maka kana lasa "

Wata irin kunya ce ta kama nasir kamar ya nitse duk da bayau ta saba da fad'in abun da duk
yazo bakin ta ba, harta fatima da take bakin k'ofa la'be kunya kamata tayi

"Ina ita tsohuwar munafukar take? " Fatima jin ta fad'i hakan yasa tayi saurin fitowa kanta a
k'asa

" To a wuce ga keso can na shimfid'a aje a zauna kuma kusha iskan duniya ace duk wannan
iskan mai dad'i da ke kad'awa ku sunk'e cikin d'aki kamar wasu sabbin aure to a wuce" Fatima
gaba nasir biye da ita a baya suka nufi keson

" Wannan! Wannan! anya ba'a baka ka shanye ba wannan bita zaizai haka mtswwww" inna ta
fad'a tana nuna nasir


Dukan su zama sukayi saman shimfid'ar, sunyi shuru bamai cewa uffan gwauda ma inna tana
d'an magana duk da mafi yawancin maganar tata fad'a ne


Suna zaune hadari ya taso nan da nan ruwa suka sauko, duk sukayi d'aki har inna ta biyo su
d'akin, dukan su da mamaki d'auke a fuskarsu suke kallan ta, inna ko ta nemi waje ta zauna

Nasir ya d'auko lema yace "Inna gashi ki kunna sai kiyi d'aki kar ruwa su jik'aki kinga dare nayi
kuma ruwan nan kamar zasu d'an jima kafin su d'auke" Mai suwa ka aje dan anan zan kwana
yanzu fisabillilah wannan ruwan da akeyi masu k'arfi so kake naje d'aki ni kad'ai gina ta fad'o
min ko?" Ta fad'a tana kallan fuskarsa "Yi hak'uri ba nufina ba kenan allah ya huci zuciyar ki
"Amin"


Fatima ranta yayi mugun 'baci, kar tayi magana kuma ace bata da kunya


Nasir ya juyo ya kalleta, tayi saurin d'auke kanta tare da hayewa gado tayi kwanciyarta tare da
jan bargo ta lullu'be jikinta


Ansar kwance saman makeken gadon sa hannunsa dafe da waya a kunnen sa "Please stop
crying baby" idan banyi kuka ba beb mezanyi yanzu ace harda wata za'a d'aura maka aure
bayan ni"Nafa gaya miki komai nima ba'a san raina za'a yi auren nan ba zuciya ta ke kad'ai ce
wacce take so da burin kasancewa a tare da ita " Uhmm har kasa naji wani sanyi acikin rai na
love you so much my dear" Love you too baby ni ba wannan ba wai yaushe zaki dawo gashi
antura anje anyi magana auren nan fa ba jansa za'a yi ba idan ma anjasa da tsawo bazai wuce
1 month ba amman kina ejib zaman ki kamar ba amarya ba "Hhhhhh kai dear next week in Sha
Allah zan dawo da yanzu ma jibi zan dawo amman saboda auren nan dayazo girshi yasa mom
tace nazauna a can akwai shirye_shiryen da za'a min gobe ma mom zata zo nan"



" Okay wane irin shirye_shirye ? " Abun sirri ne" To shikenan tunda baza'a fad'a min ba " Meya
hanaka zuwa office yau? " Wallahi na d'an d'auki hutu ne na kwana biyu " Hutu tun yanzu tun
kafin mu fara cin amarcin mu"Ai lokacin hutu na mussaman zan d'auka "Ai kam dan kasan ba
d'aga k'afa zamu gurji amarcin mu yarda ya dace "

Haka dai suka ci gaba da hirarsu har aka fara kiran sallah, sukayi sallama ya wuce masallaci














☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
"Princess! Princess! Princess "Naam mom" zarinat ta fad'a tana saukowa upstairs, sanye take
da atamfa mai kyau d'inkin riga da siket, d'inkin ya kama jikin ta shafe d'in ta ya fito, mace ce ita
mai diri,
Tana sanye da fashion hijab irin mai shape d'in nan tayima hijabin kyau sosai, fuskarta ba
makeup sai man baki da ta shafa, ta gyara girar ta kamar wacce aka zana, tana rataye da
fashion bag hannun ta rik'e da papers sai mukullin motar ta

Yarinyar kamar ita tayi kanta, ta had'u sosai

Tun da ta 'bullo mom ke kallan ta tana k'ara yaba kyawon y'ar tata, ganin tayi kuma tad'an rame
mata


Murmushi d'aure akan face d'inta ta k'araso wajen mom " You look so beautiful my princess
"Oooh Thank you mom "Ta fad'a tana karyar da wuya"Welcome, princess meyake damun ki ne
kodai daga ido na ne naga kin rame ko wani tunanin kika sakama ranki har ya ramar dake"Ni ba
komai" ta fad'a tana turo baki cikin shagwa'ba" Mom tayi murmushi tare da fad'in" To shikenan
tun da kince ba komai, har kin fiton kenan? " Eh " Okay allah ya bada sa'a, kiyi saurin dawowa
yau su yayanki zasu zo "Lahh mom shi ne ba'a gayamin ba sai yanzu"To nima sai da suka taso
ne suka sanar da ni nasa a gyara musu d'akin su "Okay sai na dawo mom"Allah ya tsare ya
bada sa'a da rabo yasa a samu abunda akaje nema " Amin mom" banda tuk'in ganganci saman
titi " In Sha Allah mom bazan yi ba" Good girl "




Fitowa tayi ta nufi compound d'in ajiye motoci, ta nufi wata had'ad'd'iyar mota black, motar tayi
kyau sosai, ta bud'e bag d'in ta ta ciro key, ta latsa wani madanni daga jikin mukullin nan da nan
motar ta bud'e ta shiga ta zube kayanta saman d'aya mazaunin dake gaba ta tada motar, tun
kafin ta iso bakin gate d'in an jima da bud'e mata, ta tsaya suka gaisa da mai gadin ta
wuce.................................................












Comment and share fisabillilah

ZARINAT ( ةنيرز )

Mallakar
Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 4️⃣

Fitar ta keda wuya sai ga motar su ta danno kai, hl sukayi mai gadi ya bud'e musu gate, cikin
wata dalleliyar mota suke, parking sukayi,

Kusan duk a tare suka bud'e murfin motar suka fito, su uku ne,
mutumen da ka gansa kaga kamannin zarinat a tare da shi sosai, kallo d'aya zakayi masa
kasan hutu ya zaunu a jikin sa,

matar fara ce ita ma sosai ba laifi tana da kyauwonta, tana sanye cikin wani material onion
colour, mai shegen kyau ga cikin ta jikinta da ya fara girma, sai yarinyar da bazata wuce 7 to 8
years ba, kammannin su d'aya da baban ta


Mai gadin ne ya k'ara so wajen su da sauri, cikin girmamawa yana gaidasu, suka amsa, yah
bilal ya basa key d'in motar dan ya shigo musu da kayan su, suka wuce



Suna shiga babban falon gidan, yarinyar ta ruga aguje ta hau upstairs tana kiran " Granny!
Aunty! Granny! Aunty"mom da take k'ok'arin saukowa ta tarbe tana fad'in "Kai lale lale lale
marhaban manyan bak'i ne haka suka iso " Yarinyar ta washe bakin ta yan hak'oran ta k'ananu
suka bayyana, dimple d'in ta ya lutsa "Ina grandfather?" Yayi tafiya "Mom ta fad'a suna saukowa
k'asa " To ina auntynaa ban gantaba " Yanzun nan taje school" Shine tayi tafiyar ta bancin kuma
tasan zan zo "To afrah nidai dan allah yi hak'uri ki adana rigimar ki idan tadawo sai kuyi
tayi"Mom ta fad'a suna k'ara sowa wajen su yaya bilal


"Sannun ku! Sannun ku! Kun sha hanya fa sannu"Yawwa mom fatan mun same ku lafiya "yaya
bilal ya fad'a"Wallahi alhamdulillah "




Aunty maryam ta d'urk'usa k'asa tare da gaida surukar tata cikin girmamawa, mom ta d'ago ta
tare da fad'in "Wai dan allah maryam sau nawa zan fad'a miki banason irin wannan gaisuwar
idan zaki gaidani ba dole sai kin duk'a ba bare kuma ga ciki a jikin ki ai sai ki wahalar da kan ki,
Aunty maryam tayi murmushi tare da fad'in"Yi hak'uri mom in Sha Allah ba za'a sake ba
"Hmmmmm allah sa dan wannan kalmar nasha jin ta a bakin ki amman hakan baisa kin daina
ba" Ita dai aunty Maryam murmushi kawai tayi tana k'ara jin k'aunar surukar tata a ranta dan
mom mace ce mai dad'in zama bata da matsala irin wacce ake fad'a ta suruka,




"Yanzu dai duk ba wannan ba kuje ku samu kuyi wanka ku huta dan nasan kun d'ebo gaji "
Wallahi fa mom " yawwa idan kuka huta sai ku fito kuci abinci "

"Mom wai ina amaryar ne? " Aunty maryam ta tambaya" Wallahi kamar kinsan abun da yake rai
na tun d'azu nake son tambaya " Yaya bilal ya fad'a

"Y'ar albarka tana wajen neman ilimi "Allah sarki allah yasa aci amfanin sa"aunty maryam ta
fad'a "Ai kowa d'an albarka ne"yaya bilal ya fad'a yana tafiya "Kaji nace akwai wanda ba d'an
albarka ba ne?" Dariya kawai yayi yayi gaba, aunty maryam ta Mik'e afrah tayi saurin cewa

"Nidai wajen granny zan zauna"Ai bance ki bini ba malama "aunty maryam ta fad'a tabi bayan
mijin ta, mom tace" Muje kici abinci kafin auntyn ki ta dawo"To " ta fad'a tare da kama hannun
mom suka nufi dining area,




Abinci ta zuba mata kad'an dan tasan bata cin abinci sosai, kamar ko ta sani dan ko rabin
wanda ta zuba mata bata ci ba, suka dawo falo suka zauna


Su yaya bilal suka fito, sunyi wanka sun sauya kaya,suka nufi dining suka ci abinci, suma suka
dawo falo suka zube gabaki d'aya hankalin su nakan tv suna kallan wani program da ake
gudanar wa harta afrah duk da ba ganewa take yi ba amman hankalin ta nakan tv


"Yeeeeeee babyna" jin muryar zarinat gabaki d'aya suka juyo suna kallan k'ofar

Da gudu afrah ta nufeta tana dariya, d'aukar ta tayi tana jujjuyawa suna dariya, sannan ta ajeta
suna maida numfashi, ta rik'o hannun ta suka k'ara sa Cikin falon


"Amarsu an dawo" aunty Maryam ta fad'a, zarinat ta turo baki gaba tare da zuwa gefen mom
suka zauna "Amarya wai miye sirrin ne naga sai wani shining kike mai d'aukar ido kin k'ara k'iba
"Kema dai kya fad'a"yaya bilal ya fad'a
"Mom wai me kike bama autar nan taki ne haka ahhh lallai ba k'arya da anganki anga amarya"
Mom kin gansu ko " zarinat ta fad'a cikin shagwa'ba"Barin dasu kawai princess, mom ta fad'a
tare da juyowa ta kalli gefen su yaya bilal dasuke ta dariya

" To ya isheku haka yarinya da dawowar ta makaranta ko hutawa batayi ba zaku demeta da
wani zance " mom ta fad'a tare da mayarda dubanta kan zarinat tace"Princess kyalesu kawai je
kiyi wanka ki fito kici abinci "To mom" ta fad'a tare da Mik'e wa afrah tace "Aunty nima zanyi
wanka" To zo muje kayan da zaki saka idan anyi wanka "aunty maryam tayi saurin cewa "Kayan ta na d'akin ki "Okay let's go" ta kama hannun ta suka wuce


Mik'o min cefanen nagani yau tsoka nawa ce, inna ta fad'a Fatima ta Mik'a mata ledar, ta
bud'e"kai yau naman nada kyau da gani na shanuwa ne " ta fad'a tana lissafa ko yanka nawa
ne
"Kar'bi jeki d'ora yanka goma sha biyu ne tsoka, k'ashi guda hud'u "To inna" ta kar'bi naman taje
ta fara girki

Bayanta gaba ta tsame naman cikin miya ta kawo ma inna, ta amshi robar ta sake lissafawa,
taga sune cif tace "To mik'o min hannun ki" Fatima ta bud'e tafin hannun ta biyu ta aza mata
tsoka d'aya da k'ashi uku yace wannan naki ne "To" ta sake aza mata tsoka biyu da k'ashi
gudan da ya rage tace "Wannan na nasuru ne shida ya wahala wajen nemowa gwaunda ya
d'an ci da yawa ya guyguya Kashi to tashi tafi wannan kuma nawa ne" ta fad'a tare da d'aukar
tsoka d'aya ta jefa baki tace " Uhmmm uhmmm uhmmm dajin naman nan miya tayi dad'i sosai
bara na tashi na zobo nawa naci"


Fatima ta Mik'e tayi kitchen ta d'auko d'an k'aramin filet ta zuba naman ciki takai
d'aki......................................................

Comment and share fisabillilah
ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________

________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 5️⃣

Sai da ta fara fito musu da kayan da zasu saka sannan suka fad'a toilet,

Ta fara yima afrah ta fito da ita ta kunna mata game a waya ta bata ta koma toilet, itama tayi ta
fito d'aure da towel

Shiryawa sukayi cikin wasu k'ananun kaya riga da wando pink color, ta d'aura after dress saman
kayan,
ta kama ma afrah kanta da ribbon pink and white, ta gyara mata face d'in ta, itama ta kama
kanta da ribbon white, gashin kanta bak'i k'irin sai k'yalli yake yi ga tsawo sosai ga man da ta
shafa masa ya kwanta gaunin burgewa, ta yafa k'ara min mayafin after dress d'in akai, ta feshe
musu jikin su da turaruka masu k'amshin dad'i, sunyi matuk'ar kyau sosai kallo d'aya zaka musu kaji sun burgeka


Pictures ta musu, sannan suka fito

" Aunty"Naam "Uhm muje mu siyo chocolate" To kina da kud'i ko? " Zarinat ta fad'a tare da
kallan fuskar afrah murmushi d'auke akan fuskar
"Banada " To dame za'a siyo chocolate d'in? " To ai ke kina da kud'i " Ni"zarinat ta fad'a tare da
bud'e ido " Eh " Hhhhhhh nikam banada kud'i " Uhm uhm uhmm" Bara mu ci abinci sai muje
shikenan "Yeeeeeee"Afrah ta fad'a cikin jin dad'i " suka k'ara sa cikin falo

Aunty maryam tace " iyyeee Wowwwwww ma sha allah yaran mom irin wannan kyaun
tubarakallah ma sha Allah kunyi kyau sosai " Thank you Oum twins"Wallahi a kanki dan allah
zubar da wannan yawun "Hhhhhhhhhhh wannan cikin ai daganin wannan girman da yake yi
kema kinsan ba d'aya ne a ciki ba" zarinat ta fad'a tare da zama kusa da mom dake waya, afrah
ta zauna saman k'afafun zarinat

"Ni bama zan biye miki ba" Hhhhhhhhh "

Mom ta gama wayar tare da mayarda dubanta kan zarinat ta sakar mata murmushi" Princess
kunyi kyau sosai iyyeee "Mom ta fad'a tare da shafo kan afrah, dake game a wayar auntyn ta


"Mom please idan muka ci abinci zamu d'an fita "Zuwa ina? " Supermaker " Okay amman kar a
dad'e"To nagode "Aha"Mom abincin fa yunwa nakeji"Muje na zuba miki "To "Afrah kema zaki ci?
" Kai ta gyad'a mata tare da fad'in " Tare da aunty zan ci"To y'ar aunty muje " Suka nufi dining
area

Aunty maryam tace"Wallahi mom gaskiya kina sangarta yarinyar nan sosai ace harta da abincin
ke zaki zuba mata " To idan ban mata ba wazai mata" mom ta fad'a, zarinat ta juyo tare da yima
aunty maryam gaulo
Dariya kawai aunty Maryam tayi,













Ansar dan allah zo ka kai auta supermarket driver baya nan na aike sa kai sak'o wani waje ita
kuma kasan bata iya driving ba" To ammie ta shirya ne" Eh " Okay ta sameni a moto" ya fad'a
tare da wucewa

"Auta!Auta! "Naam ammie " wata budurwa ce ta amsa tare da nufo ammie tana da tsayi kamar
ansar sai da bata kai hasken saba bata da irin hasken nan sosai tana sanye cikin wata atamfa
doguwar riga, rigar mai rafa ce ta yafa mayafi fari hannun ta rik'e da jaka

Ta k'ara so wajen ammie " Ammie gani"Yace ki same sa waje "To ammie sai mun dawo"Adawo
lafiya "









☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Sai da suka ci suka k'oshi, sannan suka tashi, zarinat ta koma d'aki ta d'auko ma afrah hula ta
d'auko key d'in mota, ta saka mata hular, ita kuma ta k'ara gyara mayafin rigar taje ta amso ATM
d'in mom suka fito, afrah ta rik'e hannun ta tana d'an tsalle_tsalle suka nufi motar ta ta bud'e
afrah ta shiga gaba itama ta zaga ta shiga, ta tayar suka wuce
Tafiya suke kowa yayi shuru sai karatun k'ur'ani da yake tashi cikin zazzak'ar murya zarinat na

biya, afrah ta kalle ta tare da fad'in "Aunty"Naam " ta fad'a amman hankalin ta nakan titi"Nima
ina son na iya mota "Haba? "Eh idan zanje school na rik'a zuwa da kaina basai baba drive ya
kaini ba "karki damu allah ya nuna kin isa fara driving da kaina zan koya miki"Yeeeeeeeee " ta
fad'a tana murna tace"Aunty da yawa fa zamu siyo "Miye? " Chocolate "Ohh sosai ma" muci
abun mu daga ni sai ke ko? " Afrah ta fad'a" Kwaurai kuwa bazamu samma kowa ba "Da biscuit
da sweet " Komai sai mun siyo " zarinat ta fad'a tana k'ok'arin parking a gaban wata katafaren
babbar supermarket, suka fito suka nufi ciki




Komai akwai cikin supermarket d'in in dai 'bangaren mak'ulashe ne, chocolate � sosai suka
kausa da biscuit �

"Aunty zarinat" d'ago kanta tayi jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login