Showing 15001 words to 18000 words out of 27791 words

Chapter 6 - ZARINAT (زرينة) book 1 free page's by zainab dodo.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

1636

" faruk
ya fad'a tare da kama hannun matarsa suka nufi 'bangaren husna yah ansar gaba suna biye
dashi a baya



Waje ya basu suka zauna ya wuce uwar d'aki dan kiran husna,

Tana nan kwance tana abunda ta saba ( chart kenan) sanar mata yayi ta fito sunyi bak'i, tace "
To bak'i kuma daga ina? Su waye? " Idan kika zo zaki gansu " yana fad'in haka ya fice

Yatsina fuska tayi tare da jan tsaki tace"Mutum na tsaka da jin dad'insa azo a katse masa" ta
fad'a tare da Mik'e wa ta nufi hanyar falo

Tana zuwa bako sallama ta samu waje ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya tana
dannar waya, zarah ta saki baki tana kallanta

Yah ansar yayi gyaran murya tare da fad'in "Husna miye haka kinyi bak'i amman zaki shigo ki
zauna ko sallama baza ki musu ba" D'agowa tayi tare da fad'in " Ohhhhhhhhhhh I'm very sorry i
forget wallahi kasan abubuwan ba d'aya ba ina wani abu ne a phone shiyasa hankali na ma
baya nan sorry fa, ta fad'a tare da kallan su faruk zarah ta cika sosai dan taga wulak'ancin na
husna yayi yawa wato ma bata ko lura dasu ba bayan kuma akan su aka kirata ta fito

Yah ansar yace "Abokina ne faruk wanda nake baki labari sai kuma matar sa zarah"

" Ayyah Sannun ku" Yawwa sannu fatan kuna lafiya ya amarci?" Faruk ya fad'a" fine " ta fad'a
tare da ci gaba da latsar wayarta

Zarah ta sakarma faruk harara na kula ta da yayi

Yah ansar shima baiji dad'in yarda ta musu ba

Zarah tace" Muje muga d'ayar sai mu wuce dan inaga ba dad'ewa zamuyi ba "Okay ku tashi
muje" duk suka Mik'e

"Amarya mu mun wuce" faruk ya fad'a ba tare da ta d'ago kanta ba tace " Okay sai anjuma" Mu
jima da yawa" zarah ta fad'a tare da yi gaba ta barsu a baya, suma biyota sukayi



'Bangaren zarinat suka nufa

Bakin su d'auke da sallama suka shiga, wani irin daddad'an k'amshi ne ya ziyar ci hancinsu,
suka shiga raba ido musamman zarah da take d'auke da jaririn ciki, ba kowa a falon sai TV
dake kunne tana aiki, zarah ta rik'a kallan falon ba k'arya kayan sunyi masifar kyau sun mata
kyau ga yarda kuma aka tsara komai zaa kyau

Yah ansar ya nuna musu waje su zauna, ya nufi bedroom d'in ta dan kiran ta har ya kusa kai sai
gata ta fito ta sauya kayan d'azu tana sanye da abaya black tasha kyau sosai, mayafin abayar
ta d'aura sa saman kafad'arta ta kama gashin kanta da white ribbon hannunta rik'e da
wayarta, tana tunanin yarda zatayi da alaler da ta dafa tunda su saudat sunce ba zasu samu
daman zuwa yau ba sai wani lokaci

Yah ansar ta gani tsaye a gabanta, baki ta bud'e zatayi magana yayi saurin cewa "Kinyi bak'i
muje ki gansu abokina ne tare da matar sa"To,ta fad'a tare da d'ora mayafinta a kai suka k'ara

so cikin falon sallama tayi duk suka amsa ta zauna tare da fad'in " Sannun ku da zuwa ya
hanya" Alhamdulillah,duk suka fad'a, zarah ta sake fuskarta dan da ganin zarinat tasu zata so
d'aya ba irin husna ba ce tare da yaba kyawon zarinat a zuciyarta


Mik'e wa tayi ta nufi kitchen taje ta d'auko lemon juice ya d'au sanyi sosai da cup's uku ta d'ora
saman filet takawo, ta ajiye tare da zuzzubawa ta Mik'a ma kowa zata Mik'a ma yah ansar sai
da tad'an duk'a cikin bangirma ya amsa, yana jin dad'in yarda ta kar'be su

Zarah tasha lemon tare da fad'in "Waiii kin sanyayamin zuciya ta daga 'bacin rai da ta shiga"
Yah ansar da faruk duk sun gane mai take nufi

Zarinat tayi murmushi


"Ni nama manta ban gabatar miki dasu ba" yah ansar ya fad'a yana kai cup bakin sa " Wannan
abokina ne faruk duk cikin abokai na dashi muka fi shak'uwa wannan kuma matarsa ce Zarah in
Sha Allah muna sa ran nan da wata shidda zata haifo muna d'an mu" Lahhhlahhhlahh kace har
an kawo ma rahoto " zarah ta fad'a cikin wasa" Tun yaushe kedai allah ya sauke ki lafiya
"Hmmmm amin ai kaima kamar gobe ne za'a cemin matarka zarinat nada ciki, zarinat ta kalli
zarah tare da sunkuyar da kanta k'asa yah ansar ya kalleta tare da sakin k'ayataccen murmushi
" Waya sani ma ko ta harbu" faruk ya fad'a" Wallahi fa abu a duhu waya sani"zarah ta fad'a

Zarinat ta Mik'e tare da fad'in"ina zuwa" ta nufi kitchen, yah ansar yace" kun gani ko kun korar
min mata kunya gareta sosai " Uhmmm kunya ko duk nan muka fito takalmin mu suka tsinke"
cewar zarah duk suka sa dariya



Kulolin abinci ta kwauso daga kitchen takai dining ta aje ta koma kitchen ta d'auko filet guda
uku, ta bud'e kular da alalen ke ciki ta banye leda uku uku ta zuba a filet, kasan cewar manyan
d'auri tayi shiyasa ta zuba ma ko wane filet uku_uku amman banda d'ayan bata zuba na d'aya
filet d'in ba tasa spoon ta yayyanka tsakiyar a lalen, ma sha Allah mai kwai ce a ciki tayi, ta zuba
sauce d'in da tayi mai kayan ciki a ciki abun sai wanda ya gani gwaunin burgewa sai k'amshi ke
tashi

Ta d'auko ta nufi falo, ta ajiye d'aya gaban zarah d'aya kuma gaban faruk ta koma kitchen ta
d'auko musu ruwa masu sanyi, ta koma dining dan had'ama yah ansar nashi

zarah k'amshin alalen ya bugi hancin ta yawunta harsun kawo ta d'auki filet d'in ta tare da fad'in
"Kaii allah dai ya biyaki matar nan kamar kinsan abunda nake so" ta fad'a tare da kai loma d'aya
sai da ta lumshe ido tun da take bata ta'ba cin alalen da tayi mata dad'i sosai ba kamar wannan
"Ma sha Allah wallahi alalen nan tayi dad'i sosai" Uhmmmm" faruk ya fad'a dan ko magana ya

kasa, yah ansar dariya sa yake yi ganin yarda suke yaba girkin


Dawowa tayi falon hannunta d'auke da filet wanda ta Had'oma yah ansar d'auri hud'u ta saka
masa, aje filet d'in tayi taja table d'in dake wajen takai gabansa ta d'auko filet d'in ta aza tare da
turawa gabansa taje ta d'auko masa ruwa, koda ta dawo harya fara ci shima girkin ba k'ara min
dad'i ya masa ba duk da bai ta'ba cin alale ba amman yaji dad'in ta sosai,

Kowa ya cinye tasa tasss, bare yah ansar da ya kwana biyu baici abinci irin haka ba kullum tea
ne

Zarah tace "Gaskiya sai nazo kin koyamin yarda ake irin wannan alale mai dad'i haka"Murmushi
Kawai tayi

To ciki ya d'auka aka fara fira zarinat tun tana kaucewa har itama tasa bakin ta cikin firar, Kiran
sallah ne ya tada su maza sukayi masallaci sukuma sukayi alwala suna gama sallah suka ci
gaba da fira,

Su faruk basu shigo gidan ba har sai da akayi sallahr la'asar

Basu wani jima da dawowa ba suka tashi zasu wuce, zarinat ta bama zarah abu cikin leda ta
kar'ba tare da yi mata godiya suka fito itama ta rako su sun fito babban falo sai ga husna ta fito
daga 'bangaren ta kallan mamaki take musu dan ita duk a tunanin ta sun wuce tun d'azu k'ara
sowa tayi tare da fad'in "Ashe kuna nan baku wuce ba" Eh wallahi muna inda akasan
darajjarmu " Zarah ta fad'a
"Okay " husna ta ce dan bata gane abunda take nufi ba, zarinat ta musu sallama suka wuce ta
koma 'bangaren ta....................................................













*Karfa a manta paid book ne ba tsada 200 only haryanzu muna cikin free page's ne mun kusa
gama free page's *

Comment and share fisabilillah ♥️

ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️












Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣3️⃣

"Mik'o min nan ki gani" inna ta fad'a tare da zafce ledar hannun fatima
"Haba inna kin dai san naman nan idan na dafa ba ci zanyi ba sai na kawo miki ki d'ebe muna
namu" Baci zakiyi ba oho wannan kuma ke ya dama amman nama sai na lissafa naga ko tsoka
nawa ce a ciki " Fatima ta girgiza kai tayi tsaye tana jiran ta gama lissafawa ta bata

" Yawwa kingani gwaunda da na lissafa gashi nan an samu ka'rin tsoka biyu da ban lissafa ba
nasan wufff zakiyi dasu " Fatima hannu Kawai tasa ta kar'bi naman tayi kitchen, har ta wanke
naman zata zuba a tukunya sai wata zuciya ta bata mezai hana ta ragema naman girma in yaso
sai ta kaima inna adadin tsokokin da ta lissafa
Haka kuwa akayi ta d'auko wuk'a ta fara rage musu girma, daman tsoka goma sha biyar ce da
k'ashi uku,
Tsoka goma ta ragema girma sauran biyar d'in ta barsu suka kama tsoka ashirin da k'ashi uku
"Hhhhhhhhhh inna in kinsan wata ai bakisan wata ba"ta fad'a tare da sakin murmushi ta k'ara
wanke naman ta zuba a tukunya tare da yanka albasa da kayan k'amshi




Tana kitchen tana aikin ta, taji sallamar nasir ta fito kusan a tare suka fito ita da inna " Sannu da
zuwa" Fatima ta fad'a "Yawwa"
" Har ka dawo?inna ta fad'a" Nazo ne na kawo mata abun nan na koma " Nagani me aka siyo
muna banga ledar na matsk'iba" ta sa hannu ta kar'bi ledar kayan kwalliya ne a ciki su powder,
jan baki, lipgloss, jagira, barbad'a kumatu, k'yalk'alin balaga, duk sune a ciki inna ta washe baki
tare da fad'in "Aah kayan kwalliya ne aka siyo muna " Nasir yayi dariya najin furucin inna yace
"Haba inna in banda abunki ina ke ina kuma wasu kayan kwalliya wannan fa fatima na siyoma
ai ke kin wuce lokacin wad'an nan kayan "

" Bangane ba "inna ta fad'a tare da kallan nasir"Nice na fad'a maka na wuce yin kwalliya ko
kuwa? Ohhh so kake ka mayar dani tsohuwar k'arfi da yaji ko to baka isa ba yarda kasan matar
ka zata shafa tayi kyau nima haka zan shafa dan ba'a fini kyau ba kuma nima ina san da an kalli

fuskata aga tayi haske kai wallahi da ganin powder nan zata min kyau " ta fad'a tare da ciro
k'yalk'alin balaga tana murmushi " Nasan yarda take k'yalk'alin nan nima haka zan rik'a yi
amman na lura kanasan ka mayar dani baya haba wannan ai muma lokacin mune zamanin mu
ne" powder da lipgloss ta ciro ta Mik'a ma fatima tare da fad'in
"Ungo kar'bi naki wannan kuma nawa ne nima ina da hak'k'i akan kayan d'ana" To inna nagode
" Fatima ta fad'a
Nasir yayi tsaye yana kallan inna ganin ita fa bilhak'i take yama rasa mezai ce kar kuma ya sake
magana ta rufe sa da fad'a yama gode allah da yasa matar sa bata raina Mahaifiyar sa ba dan
wannan abun da take wallahi yasan da fatima bata da hak'uri da an dad'e da samun matsala


"Maman humaira ni zan koma"To allah ya bada sa'a "Amin ya allah, ya wuce itama taje takai
nata kayan d'aki ta fito inna na nan tsaye hanyarzu tana duba kayan" Waii ai da ganin wannan
kasan kud'ad'e ne ya kashe a wajen nan haka kawai ni kuma sai na bari ya kwaushe ya Mik'a
mata ai nima ina so koda banda mijin da zanyi ma nayi abuta naga shawa allah sarki malam
allah ya gafarta maka da yanzu kai ne zakaga wannan kwalliyar" ta fad'a tare da share y'ar
kaullahr da ta zubo mata

Ita dai fatima na jinta ta kama hanya tayi kitchen, har zata shige inna ta kira sunanta ta tsaya
tare da juyawa, inna tace" Ki tabbatar kin muna irin miyar jiya d'in nan mai d'an banzan dad'i kai
miyar nan ta jiya tayi dad'i sau uku ina cin abinci cikin dare" Yau fa miyar kuka ce bata alayyahu
ba"Auu shin kuka ce ko to kidai yi mai dad'i " Fatima ta juya ta shige kitchen

Bayan ta gama girkin ta tsame naman ta cire tsoka goma ta ajiye ta rufe ta d'auki sauran ta
kaima inna, inna na dubawa tace" Uhm uhmm uhmmm ya akayi naga naman nan duk ya tsuke
"Dahuwar da yayi ne sosai shi yasa ya koma haka" inna ta d'auki tsoka d'aya ta kai baki
" Kai gaskiya kam na yau yafi dahuwa da dad'i to daga yanzu ki rik'a barinsa yana dahuwa
sosai kamar haka"To " Yau tunda kinyi abun k'aurai bari a baki tsoka biyu kema kisama bakin
salati"

Ta Mik'a mata tsoka biyu da k'ashi biyu, sannan ta sake Mik'a mata tsoka uku da k'ashi guda
tace "Wannan nasa ne tashi kije" ta Mik'e ta nufi kitchen tana dariya k'asa_k'asa....


Yah ansar daga rakiyar su faruk bai dawo ba da can ya fita sai da akayi sallahr magrib sannan
ya dawo d'akin hunsa ya je ya tarar da ita kwance masu aikin ta na mata tausa tana charting
gefen ta kuma shinkafa zube cikin filet wanda yah ansar ya kasa tantance ko wane irin abinci
ne, dan shinkafar ta ca'be
Ya tsina fuska yayi a zuci yace" Allah ya kyauta nima da wannan abincin ne zan rik'a ci"

Ganin sa yasa masu aikin suka dakata da abunda sukeyi

D'ago kanta tayi tare da fad'in "Dear"Uhmm, tana k'ok'arin tashi yace tayi zaman ta zaije yayi
wanka, ta koma ta kwanta ya fice, suka ci gaba da aikin su


D'akin sa yaje yayi wanka, har ya shiga kitchen zai dafa tea sai kuma wata zuciya tace "Mezai
hana yaje ya tambayi zarinat ko akwai sauran abun nan da suka ci d'azu, kai haka ma za'a yi

Ya fad'a tare da fitowa daga kitchen ya bud'e d'aki ya fito

kai tsaye ya nufi 'bangaren ta,
murd'a hannun k'ofar yayi tare da shiga, yana shiga tana fitowa daga kitchen tana sanye da
hijab d'in ta blue black dogo har k'asa mai hannu, hannun ta rik'e da gorar ruwa faro da cup

Yah ansar kallanta yake kamar yau ya fara ganin ta tayi kyau sosai cikin hijab d'in hijab na mata
kyau sosai

Zama yayi cikin kujerun falon, ta k'ara so tare da yi masa sannu da zuwa, dining ya fara lek'e
yaga baiga komai akai ba zarinat na lura da shi, ganin bai ce komai ba yasa tace " Yah wani
abun kake so? Kai ya d'an sosa tare da fad'in" Nace ko akwai sauran abun nan da muka ci
d'azu yama sunan nasa?" Zarinat tayi dariya ganin yarda yayi maganar
Tace " Alele" Eh shi " Wallahi babu" okay " Ganin kamar yunwa yake ji kuma gashi bata dafa
komai ba sauran alaler zarah ta bama taje da ita bata raga ko kad'an ba saboda batayi tunanin
zai nema ba


Zarinat tace *Sai dai ko na dafa maka wani abu" Eh to dan allah dafa min bara naje masallaci
na dawo " To" ya Mik'e saboda kiran sallah da aka fara ya fice
Ita ma ta nufi bedroom d'in ta, sai da tayi sallah sannan ta fito ta nufi kitchen, ta tsaya tunanin
abunda zata dafa masa mai sauk'i spaghetti ta yanke shawarar dafawa, ta fara aiki

Da yaje sallah bai dawo ba sai wajen k'arfe tara da rabi koda ya dawo ta dafa masa spaghetti
mai d'ankaran dad'i ga kifin da ta zuba a ciki, duk da ta zuba kifi idan kaci zaka iya rantsuwa
kace ba kifi a ciki sai dai idan ka gansa saboda ta cire masa k'arni, ai kuwa yah ansar yana ci
sai shi mata albarka yake yi a zuci daidai wacce zai ci ta dafa gaba d'aya ta zube masa a filet
sai da ya cika

Yah ansar gaba d'aya ya tashi da filet d'in ya kaunkaud'i lemo mai sanyi da ta kawo matsa ai sai
gaytsa ciki ya cika,

Ta kaushe kayan takai kitchen ta dawo, yana part d'in ta har goma da rabi tayi suna kallo
sannan ya tashi tare da mata sai da safe ya wuce yayi part d'in
husna................................................
















Comment and share fisabilillah ♥️

ZARINAT ( ةنيرز )







Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number
09046495943
Chart only




_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
T. W. F

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣4️⃣

Yau monday, tun da tayi sallahr asuba bata koma bacci ba, tayi karatun k'ur'ani mai girma, ta
had'a breakfast, doya da kwai ne sai ta d'an soyata da yawa yarda zata isheta har dare saboda
tasan koda zata dawo school ta gaji bata ji zata iya yin girki ba, ta gyara d'akin ta kunna turare
sai k'amshi ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login