Showing 27001 words to 27791 words out of 27791 words

Chapter 10 - ZARINAT (زرينة) book 1 free page's by zainab dodo.pdf

Advertisement

04 Jun 2025

1635

kafin ka shigo duniya muke yin shi
" shi dai baice komai ba ya wuce


D'auka guda tayi takai baki" Uhmuhmm amman ko tayi dad'i yan banza " jug d'in koko ta bud'e
ta kur'ba, ta k'ara bud'e k'afafu ta fara ci




Nasir da fatima suka fito waje suka shimfid'a tabarma bakin k'ofar d'akin su suna breakfast,
Fatima ta Mik'e taje d'aki ta d'auko wata kulla, Nasir yace" Wannan kular fa? Ta waye ?" Aunty
larai ce ta bayar a kawo min " ta fad'a tare da bud'e kular arish ne da kwai ( dankalin turawa)
rabi ta zuba a filet tace " Nasan wannan ya ishe mu anjima sai muci wannan" ta rufe kular ta
mayar ta dawo suka fara ci


Suna tsaka da ci inna ta fito idanun ta akan filet d'in da sauri ta isa wajen tare da rafka salati
tace " Me zan gani haka? Nasuru! Nasuru kuji tsoron allah ni ku bani koko da k'osai ku kuci kwai
da wannan abun" Aah inna wallahi ba daga ni bane nima yarda kika gansu haka na gansu daga
gidan su ne aka aiko mata " Gidan su?" Eh" shuru tayi, ita dai fatima cin abinta kawai ta ke yi,
inna tasa hannu ta talla'be filet d'in tare da fad'in " Ko daga gidan su aka kawo koma daga ina
aka kawo wannan ku ya shafa ba abunda yamin zafi nima ga nawa wannan rabona ne

ehhheeeee da kake kawowa ai duk tare ake ci sai yanzu za'a nuna min wariya to ni bansan
wariyar ba mutanen banza wallahi yaran nan ku rik'a kyautatama iyaye to " ta fad'a tare da
juyawa tayi d'akin ta


Nasir yayi tagumi yana kallan fatima, tayi murmushi tare da fad'in " Karka damu bara na d'auko
muna wancan sai mu ci"
















Yau faridah bata je school ba, bata jin dad'i, zarinat kad'ai taje duk sai taji ba dad'i, malamin da
zai shigo musu ya kira yace bazai samu daman shigowa ba dan haka kowa ya watse

Zarinat na tsaye waje bakin gate d'in makaranta tana tunanin yarda zatayi, gashi ta fad'a ma
driver time d'in da zai zo ya d'auke ta ashe bazasu kai lokacin ba kuma wayanta na hannun yah
ansar har yanzu bai bata ba bare ta kira sa ta sanar dashi, hn d'in da aka mata ne ya dawo da
ita daga tunanin da take yi
Motar Dr abbas ce, glass d'in motar ya saukar murmushi d'auke fuskarsa yace " Drivern bai zo
bane? Kai ta gyad'a masa yace" Okay let me drop you " Aah nagode zan hau taxi " Kar kice
haka mana please kizo muje akwai maganar da nake son muyi dake mai muhummanci" Sir
nagode " ta fad'a tare da tare wata taxi ta shiga, Dr abbas yabi bayansu dan yau son yake
ayita ta k'are ya gaji da DAKON SOYAYYAR da yakeyi gwaunda ya bayyana mata abunda ke
zuciyar sa, tafiya suke yana binsu ba tare da zarinat tasan yana binsu a baya ba har suka iso


Fitowa tayi cikin taxi taga motar Dr abbas,ya bud'e murfin mota yana k'ok'arin fitowa, saurin
bud'e jakarta tayi ta ciro kud'i ta Mik'a masa ta kama hanya, Dr abbas da gudu yasha gabanta
tare da fad'in "Haba zarinat kamar baki ganni ba kike k'ok'arin shigewa"Sir dan allah kayi hak'uri
"Nayi hak'uri akan me"Saboda bai dace na tsaya ina magana dakai ba "Saboda me?" Saboda

ni matar aure ce" ta fad'a tare da bi gefensa zata wuce d'aga kanta da tayi sai ga fuskar yah
ansar, gabanta yayi mugun fad'uwa yana tsaye bakin k'aramar k'ofar gate hannayen sa nad'e a
k'irjin sa, dawowar sa da masallaci kenan zai shiga cikin gida yaga taxi ta tsaya tun lokacin yake
tsaye

Juyawa tayi taga Dr abbas na tsaye har yanzu, rasa abunda zata yi tayi, Dr abbas ganin yarda
ta sauya yasa ya juya tare da kallan wajen da take kallo, yah ansar ya gani tsaye yana kallan su
ba tare da yace komai ba ya k'wank'wasa k'ofar mai gadi ya Bud'e masa ya shige,

Sun kai mints biyar a haka kowa da abunda yake sak'awa a ransa, sai da taja doguwar ajiyar
zuciya sannan ta kama hanya ta k'wank'wasa mai gadi ya Bud'e ta
wuce...........................................................










Alhamdulillah anan na kawo k'arshen free page's wad'an da sukayi payment sai mun had'u dan
jin yarda zata kasan ce tsakanin yah ansar da zarinat







Comment and share fisabilillah ♥️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login