Showing 1 words to 3000 words out of 21648 words

Chapter 1 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf

[5/12, 11:27 AM] Abidah: *NAZBEER*

*Written by*
*Zainab Laminu Sani*
(*Abeedah*)✍️




Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/FP7D2LzvLM6Asy82NpHTIF

My channel

Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
_________________________



*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And trusted writer's of the Nition*)☀☀☀



*SHIMFIƊA*

Wannan labarin ƙagaggen labari ne, banyi shi dan wani ko wata ba, duk wanda suna ko hali ya
zo ɗaya arashi ne, labarin *NAZBEER* labari ne daya ƙunshi tarin abubuwa, kama daka kan
zazzafar soyayya, haɗi da cin amana, makirci da kuma sarƙaƙiya, ba zanyi muku alƙawarin farin
ciki ko akasin zalla ba, haka zalika tafiyace miƙaƙƙiya, kudai mu tattaro mu haɗe acikin labarin
dan jin abinda ciki, fatana dai shine ku karɓi labarin da hannu bibbyu. Na gode

*MU ANTAYA CIKIN LABARI*


*PAGE*____ 1

Bismillahirrahmanirrahim.


Tafe take adajin sai zabga uban sauri take kai kace sama zata tashi, hankalinta a matuƙar
ƙololuwar tashe, ta ko kallon gabanta, burinta shine bai wuce ta ganta a gaban Boka Darmuuje

ba.

Wata nannauyar ajiyar zuciya tasauke saboda hango bukkar Boka Darmuuje, tana ƙarasawa
bata jira komai ba takutsa kanta cikin bukkar, ganinta yasa Boka Darmuuje yakwashe da wata
mahaukaciyar dariya, wanda aƙalla Sai data ɗauki adadin mintuna biyar bata gushe ba, baƙar
fuskarsa me ban tsoro ya haɗe yana kallonta da ƙwala-ƙwalan idanunsa masu kamar gauta.
"Kinyi kuskuren barin yabanyar araye, da'ace tun wancan lokacin kinyi abinda mukace ba tare
da kuskure ba, da aikin ki bai lalace ba". Ya faɗi da muryarsa me amo mara daɗin sauraro.


"Ba haka muka yi da kai ba, ya kai sarkin Bokaye, tun waccen lokacin na sanar dakai cewa na
gusar da yabanyar kuma allon tsafi yanuna hakan, Kuma yanzu kacemin haka?, kada ƙwarin
gwiwar da nake dashi akanka ya zama na banza".


Wata razananniyar tsawa aka dakamata damurya maradad'in sauraron, Boka Darmuuje da
yake sakin gurnani mara dad'in ji ya kalle ta da jajayen idanunsa, "Balaraba!". ya kira Sunan ta
da murya me amo, a razane ta ɗago ta dube shi, jin yadda ya kira Sunan nata.

"Balaraba, kin sanni kinsan abinda zan iya aikatawa, ba tun yau ba muke tare dake, badan
mahaifiyar ki ba danayi miki abinda biki tsammata, ke muka ba zaɓi Kuma kika zaɓi wanda yayi
miki,
amma kamr yadda na faɗa albarkaci mai ƙosai mahaifiyarki kika ci, dan haka ki tashi ki koma
zamu sabunta aiki akanshi, har abada bazai sake tuna ta ba balle ma abinda ke tare da ita".

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sake saukewa sannan ta miƙe ta fice daka bukkar.

A can kuwa ɗaya ɓangaren
Inna Hadiza ce tsaye akan mahaukaciyar matar da duk da tsananin haukan da ta ke ciki jaririyar
ƴarta sabuwar haihuwa tana hannuta ta matseta a ƙirjita ƙam, cike da tausayawa Inna Hadiza
ke kallon mahaukaciyar matar, "Baiwar Allah ba cutar da ita za mu yi ba, zan mata wanka ne, ke
ma kisamu kiyi kici abinci". Ta faɗi cikin tausayawa, domin har ga Allah matar tausayi take bata.
Shiru mahaukaciyar tayi tana saurarar Inna Hadiza kamar tana fahimtar abinda take cewa,
idonta tamayar akan kyakykyawar ƴar tata itama shiru tayi tana kallon ta kamar maitunanin
bada ita, idonta ta ɗago tasake kallon Inna Hadiza saita sake kallon jaririyar ta, Baba Halliru da
yake tsaye yana kallon duk abinda ke faruwa yayi magana a sanyaye.
"Hadiza ƙyaleta, wata ƙila bata yarda damu bane, tana ganin kamar zamu cutar da itane, daka
ganin alamun ta kinsan akwai abinda ke damunta".

Inna Hadiza taɗago ta kalleshi "Ba yarda ne ba ta yi da mu ba, tantamar bamu yarinyar take yi,

don tana ganin zamu iya guduwa da ita".

Jinjina kai Baba Halliru yayi, shima yana durƙusawa a gabanta yace "Baiwar Allah ba cutar da
ke za mu yi ba, ko wani muka ga zai cutar da ke sai inda ƙarfin mu ya ƙare".

Ga mamakinsu sai suka ga tayi murmushi tana miƙo masu yarinyar, Inna Hadiza jiki na rawa ta
miƙa hannunta ta amshi jaririyar.


"Tabarakallahu masha Allah". Ta faɗi ganin tsananin kyawun da yarinyar, ta ɗago ta dubi Baba
Halliru tace "Malam zo ka ga yarinyar,kyawu kamar ƴar larabawa".

Shima amsar yarinyar yayi yana dubanta, "Gashi bamu san ko mai game da matar nan ba,
kuma ga dukkan alamun bata magana, balle musan dunan yarinyar". Yayi maganar cike da
jimami.


"Malam kai mata huɗuba da Abida kawai". Faɗin Inna Hadiza, Murmushi yayi yace "Allah ya
raya Abida". itama murmushin tayi da cewa "Ameen".

*Abuja Nigeria* *ASOKOTO G.R.A*


wasu lafifayyun motoci ne,suke fitowa daga cikin wani layi, kai daka ganin motocin kasan
mamallakin su yaci ya tada Kai.

Ɗaya daka cikin motocin data kasance kalar baƙa na leƙa dan ganin wanne gwarzon ne a ciki,
ba kowa na gani ba face shahararren matashin nan mai ji da kuɗi da lokaci wanda ƴan uwan sa
matasa suke masa laƙani da young millonian wato NAZEER BASHIR RIMI C.E.O NA company
NAZBEER INVESTMENT NIGERIA LIMITED.

Company nin da yake fitar da kayan masarufi wanda yana daga cikin manya company nin da
muke dashi anan nahiyar Africa.
wanda suke da manyan rassa a nan Abuja da Lagos da sauran manya hajohin Nigeria, dama
ƙasashen ƙetare.



Motocin nasa basu tsaya ko ina ba sai a babbar harabar company nin sa, ma'aikatace babba da
aka yi mata gini na zamani, domin kuwa kusan rabin ginin anyishi da glass ne.

Gad ɗin shine suka fito suka zagaye motar da yake ciki, kai kace zasu iya hana malaikan

ɗaukar rai zuwa inda ya ken.

Ɗaya ne ya matsa kusa da murfin motar ya kama handil ɗinn motar ya buɗe haɗi da ja baya,
dan bawa na ciki damar fitowa.

Sai da aka ja kusan minti uku kafin mutumin dake cikin motar ya ziro da kyawawan fararen
ƙafafunsa sanye cikin wani silba ɗin takalmi rufaffu,Sai da ya ƙara jan wasu mintocin da zasu
iya kaiwa biyar sannan ya fito gaba ɗayansa.

"Ma sha Allah". Na faɗa domin ganin tsantsar kyawun da ubangiji yayi masa, kamar shi yayi
kansa, fari ne sosai irin farin da zaka rantse bai haɗa jiƙo da Africa ba, saye yake da suit kalar
blue me duhu, sosai kayan suka dace da kalar kyakykyawar fatarsa da hutu ya ratsata,
idanunsa saye cikin farin siririn farin glass daya fito da asalin kalar shuɗiyar ƙwayarsu,
kwantaccen sajensa ya kwanta luff, sosai yayi kyau kamar ka sace shi la gudu.


Takawa ya fara yi cike da sadaukantaka, ko wanne taku yana fito da asalin jarumtarsa, a
hankali ya ke sauke ƙafafun nasa bisa ƙasa,

Kallon sa ya kai akan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa wanda sai yanzu ne na lura
dashi, agogone mai azabar kyau, na companynin Rolex.

"TAHIR". Ya kira sunan P.A ɗin shi a hankali kamar me tsoron yin magana, cikin hanzari da zafin
nama TAHIR ɗin ya matso kusa da shi, "Sir!".

Ya faɗi cike da girmamawa, "Ina buƙatar ganin file d'in kayan da aka fitar jiya na office ɗicn
KHALIL". Yayi maganar babu alamar wasa a tare dashi,"Okay boss!". Ya faɗa yana mai bin
wata hanyar daban ba wacce suke ba, cikin takunsa me girgiza zukatan mahassada ya cigaba
da ratsa companyn, Kai tsaye lifta ya shiga don ta sadashi da office ɗin shi dake hawan ƙarshe,
mintuna ƙalilan liftar ta tsaya a dai-dai ƙofar office ɗin na shi dake maƙale da sunansa NAZEER
BASHIR RIMI.

ƙofar office ɗin da takasance ta gilas ya nufa, a gaban ƙofar ya tsaya, sakon ɗaya biyu, ƙofar ta
zuge kanta ya wuce, sassayanan k'amshin air freshener da sanyin A.C suka had'u suka bada
yanayi me dad'i, a hankali ya taka har cikin office ɗin daya gama k'awatuwa da kayan k'awa,
gaban kujerarsa ya Isa ya zauna, idanu ya lumshe yana juya kujerar a hankali hannunsa a
saman goshinsa, idonsa ya bud'e hankali ya sauke a kan makeken hoton iyayenaa dake sak'ale
a gefen teburin nasa, wani ya d'an matse a tsakanin k'irjinsa, tunawa da Umminsa da kuma
halin data ke ciki. "Allah ya baki lafiya ummina". Ya fad'i a saman labbansa.

Share and comment my lovely fans❣️❣️❣️

Taku har kullum

Abeedah.....✍️
[5/12, 8:27 PM] Abidah: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------
My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------

*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*

(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation*)☀️☀️☀️


*PAGE*------- 2

Bismillahirrahmanirrahim.

Katafaren manshion ne me ɗauke da mabanbantan al-uma da suke rayuwa a cikin sa, mutane
ne da zasu kai kimanin 7 suke ta kai kawo a farfajiyar manshion ɗin, wanda kallo guda zaka yi
ka shaida ƴan aiki ne, sanye suke cikin tufafi iri guda, kalar baƙi da fari, shi ne tufafin masu aikin
gidan mazansu da matansu.
Bayan wata ƴar budurwar nabi ganin ta nufi wata ƙofa, da alama itace ƙofar data sadaka da
cikin babban falon dake ɓangaren hagu daka cikin jerin gine-ginen da suke iri guda.

Nima sai na shiga dan ganin me ake yi a sashen, ido na lumshe dan ganin irin tsaruwar falon,
sosai aka narka dukiya a cikinsa, kujerun falon kalar jajaye ne da adon ruwan zinare, hakan
yasa komai na adon falon ya kasance ja da ruwan zinaren.

Idona ne yayi tozali da wata hamshaƙiyar mace wacce aƙalla zata kai shekaru 40_41,
sanye take da farin lashi wanda yaji adon duwatsu koraye, kai daka gani kasan me tsada ne,

idonunta sakaye cikin wani siririn farin glashi, laptop ce a saman cinyarta tana daddan nawa,
BARISTA NA'IMA ISMA'IL RIMI ke nan.


Ɗago idon ta tayi ta sauke kan budurwar dake zaune a kujerar gefen ta, "Rukayyah baki ji ana
sallah bane?". Barista tayi maganar idonta akan Rukayyan, budurwar da aka kira da Rukayyah
ta ɗago kai ta kalli Barista, "Naji mana".


Tayi maganar tana cigaba da danna wayarta, haɗi da jan guntun tsaki, "Ni kikewa tsaki
Rukayyah?". Barista tayi maganar tana jinjina rashin kunya irinta Rukayyan, baki Rukayya ta
tura, "Wallahi zama da Mami takura ne".


Tayi maganar ciki-ciki, hakan yasa Barista bata ji abin da take faɗi ɗin ba, Miƙewa Rukayya tayi
da nufin barin gurin, ƙarar takun data ji daka sama yasa ta tsaya, Hajiya Kulu ce take sakkowa
daka d'aya daga cikin matattakalar benen da suke guda uku a falon,
sakkowa tayi gaba d'aya da d'an hanzarin ta, "Saurin riƙo hannun Ruƙayya". "Me ke faruwa?".
Tayi tambayar idonta akan Barista.

Baki Ruƙayya ta tura, "Mami ce". "Wai dan Allah ke kam NA'IMA me yasa kike son takurawa
yaran nan ne?, wannan masifa har ina?, kin kaso auren ki shi ne bari ki zo ki takurawa yaran
masu gida ko?, to wallahi ba zai saɓu ba sam". Tayi maganar tana ƙanƙance ido tana duban
Barista, masifa take kamar zata cinyeta.

Hargagin Hajiya Mama ne ya fito da sauran jama'ar gidan, kowa ya fito sai dai ya koma gefe
ɗaya, don ba wanda zai iya da masifar Hajiya Maman.


Alha Sulaiman ne ya fito zai yi magana ke nan sai ga yayansa Alhaji Mutallab Shi ma hayaniyar
tasa ya fito, "Me ke faruwa ne?".

Yayi maganar yana duban Alhaji Sulaiman, "Wallahi Yaya nima fitowa ta ke nan".

"Hamma Bashir baya nan ne?". Tsaki ya ja me sauti, "To ina zaka gan shi, yana can gurin
waccen matar tashi mana".

Gaban Hajiya Mama dake ta sababi Alhaji Mutallab da suke kira da Abi ya isa, mugun kallon da
ya aika mata yasa ta haɗiye sauran maganar dake bakin ta, badan taso ba, dan tana mugun
shakkar mijin nata.

"Menene haka kike yi Kulu?, ƴar uwar tawa zaki tasa a gaba kina cin mutumci?".

Juyawa ya yi ya kalli sauran jama'ar dake gurin,
"Kowa ya wuce in da za shi".

Da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai suka fice a falon,
kowa da abinda ke bakin shi dan, ba hakan suka so wasan ya tsaya ba.

Sun so suga yadda za'a ƙare wasan, haka dai kowa ya koma sashensa.

Shi kuwa bawan Alhaji Bashir yana can gurin matar shi, farin cikin shi, uwar ƴaƴan shi, wadda
jarabawar lalura ta sameta .

*Abuja Nigeria*

*DAKWA*
*Abida*



Gida ne irin babban gidan nan, wata kyakykyawar budurwa da ba zata wuce shekaru sha 17 ba
na hanga zaune bisa kujera ƴar tsuguna, saman cinyarta faranti ne tana tsintar shinkafa,


Daga cikin ɗaki Inna Hadiza ce take cewa "Abida wai har yanzu biki gama tsintar bane?". "Inna
na kusa fa, shinkafar shagon Audu bata da kyau, shiya sa nace ki kawo naje bakin titi na sayo,
kika ce a'a". Tayi maganar cikin sanyin da take ɗabi'arta, Inna Hadiza tace "Oh!, ni ƴasu, ke
kam mita kamar tsohuwar data gaji da duniya". Daariya tayi tace "Kai Inna, ni ɗin?". "Ke kuwa".
Miƙewa tayi bayan ta gama tsintar shinkafar, "Inna bari na duba Ammita". "To, sai kin dawo, ki
bi a hankali". "To Inna" Abida ta amsa tana ƙarasa saka hijabinta ta fice, a ƙofa taci karo da
Inna Laure, "Za'a tafi yawon ta zubar ɗin ne?".


Wani abu ya tokare maƙoshin Abida, domin har ga Allah, ta tsani wannan kalmar da su Inna
Laure ke dan gantamata, ba tare da tankawa Inna Lauren ba tasa kai ta fice tana ɗauke ƙwallar
data faɗo mata.


"Ai kinsan ana fakewa da duba wannan mahaukaciyar uwar tata tana gantalinta". Inna Halime
ta karɓe zancen,

Ina tafe ina sharar hawaye, na rasa me na tarewa waɗannan bayin Allah, da suka ɗauki kara
tsana suka ɗora min, sun yanke duk wata alaƙa da zata haɗani da ƴaƴansu, farin cikin shima

suna so su daƙile min shi, sun mata cewa ko wanne ɗan Adam baya wuce ƙaddararsa, tabbas
da ace ɗan Adam yana dana ikon tsarawa kansa rayuwa da ban tsarowa tawa rayuwar haka
ba, sai dai ƙaddarata ta riga fata, Allah shine me tsarawa bawansa abinda ya dace dashi, kuma
yana sane dani da mahajfiyata da ya tsaro mana haka a cikin littafin ƙaddararmu.
Allah ya sani bani da wani bango ko madogara face waɗannan bayin Allah, Inna Hadiza da
mijinta Baba Halliru.

A yanzu bani da wani buri na samun lafiyar mahaifiyata, kullum na ɗaga hannu lafiya nake roƙa
mata a gurin Allah.

"Ku ko dan Allah me yasa kuke haka?, na rasa me yarinyar nan ta tare muku a rayuwa da kuka
tsangwa meta?".

Baki suka taɓe haɗi da cako kallabi gaba, Inna Laure ce ta gatsine fuska tace "Fili da yawa
mana Hadiza, nan naga muna zaman zamanmu kuka ɗakko mana wannan annobar dangin
mayu, ai daka gani kinsan sun haɗa iri da mayu, wannan kyawu kamar ita tayi kanta".

Aiko Inna Halime ta karɓe, "Wallahi kam, wama ya sani ko a can dangin nasu na mayu wani ya
kame kurwar mahaukaciyar Babar tata, kin san an ce wai a cikinsu ma suna ci".

"Uhmm, Allah dai ya kyauta, mudai kurwarmu kurr, maye ya ci kan shi yasha baƙin ruwa".

Inna Laure ta faɗi suna tafa hannu haɗi da shewa.

Kai kawai Inna Hadiza ta girgiza, da fatan Allah ya ganar da su Laure.

Ji nayi an ja hijabina ta baya, hakan yasa nayi saurin juya dan na tsorata ƙwarai, "Ke dai kin
cika tsoro". Ƙawata AMINA ta faɗi tana dariya, ɗan murmushi na yi mata, AMINA ita kaɗai ce
ƙawata kaf layin, da ita kaɗai nake zama nayi hira har wani lokacin nakan sanar mata da
damuwata.
"Ina zuwa haka da ranar nan?". "Duba Ammita zan je". "Allah sarki, ya jikin nata?". Ta
tambaya, "Alhamdulillah".

"Kinga badan Mama ta aikeni ba da munje nima na dubota". "Ayya babu komai, wani lokacin
sai muje".Da haka muka rabu.

Ina tafe ina tunani har na ƙarasa ƙofar gidan na Malam Salihu, Malam Salihu babban Malamin
addini ne dake koyar da almajira, kuma ya kan taimakawa bayin Allah da maganin da Allah ya
hore masa.

Malam Sani abokin Baba Halliru shi ya bada shawarar kai Ammi gurin Malam Salihun ko Allah

zai sa a dace, dan shi magani dace ne ba'a san inda za'a dace ba, mana sa ran nasara a
maganin na shi, dan ya sanar mana akwai sihiri me ƙarfi a tare da ita.

Da sallama na shiga gidan Malam ɗin, matar Malam Inna Zuwaira dake tsakar gidan ta amsani
da far'a, "Lale marhabun, Abidatu kece tafe da ranar nam?". "Ehh Inna, nazo duba jikin Ammi
ne". "Allah sarki ki shiga to". Da "To". Na amsa cikin raina ina aiyyana kirkin matar Malam.

Ɗakin data ke kwancen na shiga, kamar koda yahshe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login