Showing 15001 words to 18000 words out of 21648 words

Chapter 6 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf

masamagana dan tana so taji gaba ɗaya shirin su akan Ummin, amma bai ce mata komai
ba, duk da taji haushin abinda yayi matan, amma haka tasake kashe muryar ta tace, "Yanzu ke
ban ban can-canta naji damuwar ka ba?, idan kace damuwar Ummi da ta yara ba da muwata bace, wannan maganar tana nufin banda
mashimmanci a rayuwar a halin ka ke nan?".










Labari fa yana tafiya dai-dai, ku dai cigaba da kasancewa dani domin kaiku inda muke nufin
zuwa.

Mu haɗe daku a next page don jin yadda zata kaya.



Likes and comments my fans, ina yin ku oba wallahi

*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/24, 10:28 AM] Abidah: *NAZBEER*




*Written by*
*ABEEDAH*✍️



Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------

My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------
Follow me on telegram

https://t.me/+3USo7e9asLpmNzc0
_________________________

*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️



*PAGE--------10*

Bismillahir Rahmanir Rahim.


*NAZBEER*

Sashensa ya wuce, fitilun falon ya kashe kafin ya haura saman, a can ma sai da ya kashe duka
fitilun falon saman, sannan ya shiga cikin ɗakin, zaune ya kai akan sofa da take guda ɗaya a
cikin ɗakin, janyo tebur ɗin da yake tsakiyar ɗakin ya yi, dogwayen ƙafafuwan sa da suke farare
tas da su ya ɗora akai, loptop ɗin shi ya ɗauka da take ajiye agefen shi, ya ɗora ta akan
ƙafafuwan na sa, sai ta komai na kan ta ya yi kafin ya aika da kira tahanyar video call, ta ɗan yi
jin kirin shiga kasancewa ba number ƙasar ya ke kira ba, sai da har ta tsinke ba'a ɗaga ba.

Har zai sake kiran sai kuma ya rabu da shi, ai in yazo yaga kiran nashi zai biyo, dan wata ƙila
baya kusa da wayar tasa ne, ko kuma yana cikin aji shi yasa ma ya rabu da shi.


Aikin shi ya cigaba da yi har zuwa ƙarfe 3 na dare, kafin ya ta shi ya ɗauro alwala ya fara
nafilfilu, ya daɗe ya na kai wa ubangijin sammai da ƙassai kukan shi, dan shi ne kawai zai iya
ya ye masa damuwar da ya ke ciki, ya daɗe ya na nemawa mahaifiyar sa waraka dama duk kan
sauran musulmai baki ɗaya.

Sai da aka fara kiraye-kirayan sallar farko, kafin ya miƙe da yaƙinin ubangijinsa ya karɓa masa
dukkanin ad'di'oinsa, saida ya yi raka'atanil fajir raka'o'i biya, da annabi Muhammad sallahu
alaihi wasallam, yace sunfi duniya da abinda ke cikin ta.


Masallaci ya nufa, koda aka idar da sallah zama ya yi ya na lazimi har gari ya yi haske, sannan
ya fito cikin gidan ya shiga sashen sa ya wuce, shiri ya yi cikin kayan juging jesi masu karar
blue mai haske da ratsin fari a jikin su, sosai kayan suka fito da asalin ƙirarsa ta gwarzon namiji
me jini a jika, ƙafarsa ya rufe cikin farin rufaffen takalmi ya dace da kayan jikin nasa, juging ɗin
ya fita.


Sai wajen ƙarfe tara, sannan ya shigo gidan, kai tsaye sashen sa ya nufa, yana zuwa wanka ya
shiga, a nan ma sai da ya kwashe kusan awa ɗaaya a wanka sannan ya fito.

A hankali yake shiryawa cikin natsuwar shi, sai da ya gama shiryawa cikin suit ɗin shi kalar
ruwan ganye, sun yi matuƙar yi masa kyau, agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa me cike da
gargasa ta kwanta luf, alamun hutu.


Jakar loptop ɗin sa ya ɗauka ya fito daga sashen nashi, kai tsaye ma'adanar motocin gidan ya
nufa, da hanzari gad ɗin nasa dake zaman dakon fitowar tasa suka buɗe masa wata haɗaɗinyar
mota ƙirar lexus ash me duhu sai walwali take.


Sauran motocin gad ɗin suka shiga, sannan suka fice daka harabar gidan, kan titi suka harba
motocin suka shiga zuƙa gudu, kasancewar ma titin babu yawan kai kawo na jama'a.


Cikin ƙanƙanen lokaci suka isa company, motar aka buɗe masa ya fito, P.A ɗin sa ya zo da sauri
ya karɓi jakarsa dake riƙe a hannun gad ɗin shi.

Lifta ya shiga wacce zata sada shi da office ɗin na shi, a hawan ƙarshen liftar ta buɗe masa ya
fito, cikin office ɗin na shi ya shige, sakatariya da hanzari ta shiga gaida shi, hannun kawai ya
ɗaga mata ya wuce ciki.


Ita kuwa sakatariyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai da kallon ta akan PA, kayan hannun shi ya
miƙa mata, amsa ta yi ta nufi office ɗin da kayan, ba ta same shi a ciki ba, hakan yasa ta ajiye
kayan a saman teburin dake gaban kujerar sa.


Fitowa ya yi daga cikin wata ƙofa ta gilas hannun shi rik'e da wasu file kan kujerar sa ya ƙarasa
ya zauna yana ajiye file ɗin da ya ɗakko akan teburin dake gabansa, loptop ɗin ya kunna ya
shiga shigar da baya nan cikin file ɗin.



Aikin sa ya ke ta yi, dan so ya ke ya gama shigar da bayanan zufa ya keyi duk da kuwa A.C da
take cikin office ɗin, hakan bai hana shi yin zufar ba.


Khalil ne ya shigo da Sallama a bakin shi, dan tun ɗazu ya ke a tsaye a bakin ƙofar, tsabar aiki
ya ɗau zafi bai ma ji nocking da ya ke yi ba.


Shi kuwa Khlil ko da ya shigo ya ganshi yana aiki, bai yi zaton aikin ya keba, dan yasan halin
wulaƙancinsa ko da ba aiki ya keba ya na jinka za kai ta nocking ya yi ban za da kai.


shi ya sa ma ya shigo kansa tsaye, kuma ya zo ya same shi yana aiki, bai juya ba sai ma
ƙarasowa cikin office ɗin da ya yi, wajen da firij ya ke ya nufa, buɗewa ya yi ya ɗakko ruwa me
sanyi tare da gilas cup, tsiyaya ruwan ya yi a cikin cup ɗin sannan ya isa ya ajiye a gabansa.


Tsayaqa ya yi da danna loptop ɗin da ya ke yi ya yi, hannu ya kai ya ɗauki ruwan, dan dama ya
na buƙata, bismillah ya yi ya kai bakinsa, sai da ya shanye ruwan kana ya sauke ajiyar zuciya
me nauyi, kallonsa ya kai kan Khalil dake zaune a kujerar gaban teburin nasa, "Malam wa ya
baka izinin zama?". Ya yi maganar cikin wasa.
"Oh, da ka samu ka dawo hankalin ka ko?". Khalil ɗin ya faɗi ya na aika masa da hararar wasa,
"Ka kama kan ka fa, da a gidan mahaukata ka ganni?.

*KHALIL*

Ɗan taɓe baki ya yi yace "Kusan haka ne".
hararar ya sake jefamai kamar idon sa zai faɗo ƙasa.
shi ma taɓe bakin nasa yabyi ya ce "Kai kasanwa kanka dai".


"Wai ma me ya kawo ka?, tun da bani na nemeka ba". Nazbeer ya yi maganar ya na duban
Khalil ɗin, shi ma Kalil ɗin hararar sa ya yi ya ce "Ai ni ba sai an neme niba zan zo, zan shigo
duk lokacin da na ga dama, kuma na fita a lokacin da na ga dama".

"Oh,da haka ka ke taƙama ke nan ko?".
"Eh ko da yadda za ka yi dani?". Khalil ya yi maganar ya na ɗage gira, kai kawai Nazbeer ya
jinjina, "Ok, daga yau duk wanda ya sake barinka ka shigo min ba da izinina ba to a bakin
aikinsa".

Dariya Khalil ya kwashe da ita, "Ai sai ka yi na gani idan zaka iya wuni guda baka ganni ba, dan
nasan zama da Khalil dole".


Miƙewa ya yi ya na ɗaukar filon da ke ajiye a kujerar da take guda ɗaya a office ɗin ya jefawa
Khalil ɗin ya na nuna masa hanyar fita, ya na sake ɗaukar wani
da sauri Khalil ɗin ya miƙe ya fita ya na dariya.


Ƙugu kawai ya riƙe ya na hura do gon hancin sa, duk da ya san abinda Khalil ɗin ya faɗa
gaskiya ne, dan ko ya na yiwa Khalil ɗin so ne irin na ƴan uwan da suka fito ciki ɗaya, dan
yadda ya ke son ƙannen sa guda biyu to haka ya ke son Khalil, kuma yadda ya ke masu
kyakykyawar fata da dacewa a rayuwar su hakama ya ke wa Khalil ɗin.
Dan iyayen Khalil ɗin sun taimaki mahaifiyarsa a lokacin da take cikin buƙatar taimakon, sun
tallafi rayuwarta, dan kuma Momi Safiyya tamkar ƴar uwarta ta jini haka ma Dady Abubakar ya
ɗauke ta tamkar ƙanwar sa, shine sanadidyar zuwan ta gidan.


Dan kuwa a wata tafiya ne da ya yi ta gaggawa zuwa Lagos dan daga gurin aikin shi ne suka
tura shi.

Bayan ya gama abinda ya kai shi can ɗin a ranar da zai dawo ne, ya bige mutun a hanyar sa ta
dawowa gida, da hanzari ya fito dan duba abinda ya buge ɗin, koda ya fito sai ya isake mutum
kwance kamar babu rai a tare dashi, sai da ya ƙarasa ne ma ya fashimci ashe mace ce.

Ɗaukar ta ya yi da hanzari ya sakata a bayan mota, shiga ya yi ya nufi asibitin da ya ke kusa,
suna zuwa aka amshe ta, aka wuce emergancy da ita.

Har zuwa safiya likitocin basu ce ma sa komai ba, sai kusan zuwa a zahar ne babban likitan ya
buƙaci ganinsa.


Gurin zama likitan ya nuna masa a office ɗin na sa, duban sa likitan ya yi bayan ya zauna,
"Babu abida ke damunta, sai dai damuwar data ke ciki tana neman taɓa ƙwaƙwalwarta, amma
kada ka damu in sha Allahi normal zata farka, sai dai ayi ƙoƙari a magance mata damuwar da
take cikin, saboda kada abin ya wuce haka".

Kai Dady Abubakar ya jinjina yace "In allah ya yarda za ayi ƙoƙarin aga an magance mata
damuwar da take cikin". "Hakan ya kamata, in sha Allah zuwa anjima za'a iya sallamarta, tun da
ba wata matsala". Likitan ya faɗi, hannu ya miƙa masa su kai misabiha kana ya fito daka office
ɗin likitan.

Kujerar dake kusa da shi ya zauna, ya nisa cikin tunanin matar nan wayar sa ta yi ƙara, cirota
ya yi daga aljihu, Momy Safiyya ce, hakan ya sa ya amsa muryasa ɗauke da damuwa, dan shi
mutum ne me tausayi,"Fatan dai lafiya?, tun jiya muke tammatar ka amma shiru?". Momy
Safiyya ta faɗi bayan da suka gama gaisawa,

Nisawa ya yi, "Ina asibiti yanzu". Ya yi maganar muryarsa na bayyana damuwar da yake ciki,
"Subhanallah, kai ne baka da lafiyar?". Momy Safiyya ta tambaya cikin damuwa, nan ya labarta
mata duk abinda ya faru.

"Ayya, Allah ya bata lafiya". Da "Amin". Ya amsa ya ajiye wayar da yi mata alƙawarin zarar an
sallameta zai kamo hanya.

Ya na gurin zaune wata Nuse ta zo ta kira akan ya zo matar nan ta farka, a ha zarce ya miƙe ya
bi bayan nuse ɗin.

A zaune take ta juyawa ƙofar baya, ɗago fuska ta yi ta dube su bayan sun shigo, kallon rashin
sani take binsu da shi, shikuwa sannu ya yi mata kafin ya ɗora da bata haƙuri akan abinda ya
faru, abinda ya ɗaure masa kai shine gar yanzu kallonsa take yi.


A hankali cikin muryar masa lafiya ta fara magana, "Nan ina ne?". Ta yi maganar cikin harshen
turanci, hakan ya tabbatar masa da ba ƴar ƙasar nan ba ce.

"Baiwar Allah ke ɗin ƴar ina ce?, dan nan Nigeria ce". Ya yi maganar ta na ƙura mata ido, ya na
son gane ƴar wacce ƙasa ce, hawaye ne suka gangaro mata, cikin hawayen ta ce, "Kalponoya".
Ido ya fiddo waje jin daga ƙasar Kalponiya ta fito, "Ke kuwa baiwar Allah me ya kawo ki
Nigeria?". Ya sake tambaya cikin turanci yanda zata fahimce shi, "Ƙaddara". Bakinta ya faɗi.









Tofa kun fahimci wacece wannan baiwar Allahn kuwa?.
To mu haɗe daku a next page don jin yadda zata kaya.






Likes and comments my fans, ina yinku oba wallahi




*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/25, 8:23 PM] Abidah: *NAZBEER*




*Written by*
*ABEEDAH*✍️



Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ

----------------------------------------

My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------
Follow me on telegram

https://t.me/+3USo7e9asLpmNzc0
_________________________

*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️



*PAGE-------- 11*

Bismillahir Rahmanir Rahim.


Nisawa Dady Abubakar ya yi ya ce, "Amma in ba damuwa zanso na ji labarin ki, in har kin yarda
da ni, kuma in Allah ya yarda zan taimake ki".

Kai ta jinjina masa ta ce "Na yarda da kai, kuma zan baka labarina, kamar yadda ka buƙata".
"Alhamdulillah, zamu je gidana inda an sallameki daga nan, in yaso kya bani a can".

Murmushi kawai ta yi da faɗin "Ba komai". Tashi ya yi ya fita dan ya samo mata abinda za ta ci,
bai jimaba ya shigo hannunsa riƙe da leda, Nuse ya kira dan ta taimaka masa ta bata abincin,
sai da ta gama ci kana Nuse ɗin ta bata magungunanta, zuwa can wajen ƙarfe huɗu sai ga
saƙon sallamarta daka gurin babban likitan.
Nuse ɗin ɗazu ce ta sake taimaka mata ta shirya, inda Dady Abubakar yake jiran su suka fito,
har wajen mota taraka ta bata sauran magungunan ta, godiya Dadyn ya yi mata, kafin ta shiga
gaban motar tasa ya ja suka bar asibitin.


Kai tsaye hanyar Abuja ya ɗauka duk da yamma ta yi, dama ya ƙudure a ransa komai dare yau
a gida zai kwana in har sun sallameta, kuma tun da an basu sallamar, me zai tsaya yi?.


Tafiya suke yi babu mai cewa kowa komai, dan akwance take cikin kujera idon ta alumshe, dan
ba bacci take ba kawai dai tazaɓi yin shirunne, dan bata da abin cewa. Shikuwa tuƙinsa kawai

ya ke yi, dan yana so su isa gida akan lokaci, baya son ya sake kwana ako'ina inba a gidan sa
ba, shi yasa ya ke ta sharara uban gudu kamar wanda zai tashi sama. Basu suka isa gida ba
sai biyar na asuba.


Suna zuwa ya danna hon mai gadi da yake alwalar sallar asuba, da ɗan gudun sa ya taso ya
buɗe get ɗin, ya na yiwa me gidan nasa barka da zuwa, hannu kawai ya iya ɗaga mai, ya
ƙarasa shiga cikin gidan, fakin ya gyara kafin ya kalli in da take kwance tana bacci, dan gukan
gefen kujerar da take kai yayi, ido ta buɗe a hankali tana bin gidan da kallo, "Nan kuma ƙaddara
ya sake shillo dani". Ta faɗi a ƙasan ranta.


Muryar shi ta ji ya na sake yi mata magana kallon ta tamayar kansa, ya sake ce mata "Ki fito mu
shiga ciki sai ki kwanta ki huta". A hankali na ziro ƙafata waje kafin na fito gaba ɗaya, gidan na
dinga bi da kallo, "Muje ko?". Bayan nasa na bi har muka isa wani haɗaɗɗen falon gidan, ɗaki
ya nuna min guda ɗaya daga cikin ɗakun nan da suke a falon.

Wucewa na yi ɗakin da ya nuna min na murɗa handil ɗin ƙofar sai ga shi ya buɗe, ɗaki ne
babba kamar na wata matar auren, ya ji komai na more rayuwa, ƙofar da nake tunanin bayi ne
na nufa, dan yin alwala, cikin sa'a kuwa na tarar bayin ne.


Daddumar dake shimfiɗe na nufa haɗi da ɗaukar dogon hijabin dake kai na kabarta sallah.


Kwanciya na yi bayan na idar da sallar, dan na gaji sosai, kuma ina buƙatar yin nazari, na rasa
ahalina da dangina baki ɗaya, anya na cancanta na cigaba da rayuwa?, duk an kashe min
sauran ƴan uwana, to nima me ya rage min?, "Baki san abinda Allah ya ajiye a rayuwar taki ba".
Wani sashe na zuciyata ya tunasar dani.

A haka bacci ya ɗauketa tana wannan tunane-tunanen, sai wajen azahar na ji kamar ana
tashina, a hankali na buɗe idona na sauke akan wata kyakykyawar farar mata, murmushi ta
sakarmin, "Ki tashi ki yi salla, sai ki ci abinci".


Tashin kuwa na yi na shiga bayi, saida na fara watsa ruwa kafin na ɗaura alwalar na fito, sallar
na yi ina idarwa sai ga matar nan "Yauwa kin idar kenan?,to ki fito kici abinci".


Bayan matar na bi har zuwa falon da muka shigo jiya, kan dining muka wuce a can muka sami
Dady Abubakar, gaida shi na yi, amsa min ya yi ya na tambaya ta gajiyar hanya, ɗan murmushi

kawai na yi,"Gajiya kam tabi lafiya". "Ma sha Allah".

Zama nayi aka fara cin abincin, har muka gama ba wanda ya yi magana. Tashi su kai daga kan
dining ɗin suka koma cikin falon, zama sukayi a cikin kujerun da suke cikin falon, kafin ya kalle
ta "Wannan mata tace sunan ta Safiyya, yau satin mu biyu da aure ke nan, ina so ki ɗauke ta
kamar ƴar uwarki, duk abinda ki ke so idan ba za ki iya yimin magana ba, to ki yi mata magana
zata faɗa min, ni kuwa in Allah ya yarda indai baifi ƙarfina ba zan yi maki shi".


Kallon sa ya mayar akan Momy Safiyya "Safiyya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login