Showing 18001 words to 21000 words out of 21648 words
Chapter 7 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf
na san baki da damuwa, ina so ke ma ki ɗauke
ta tamkar ƴar uwarki".
Murmushi ta yi ta ce "Ba komai in Allah ya yarda zamu zauna lafiya kalau kamar Yaya da
ƙanwa". Murmushi shima ya yi ya na maida kallon sa akan ta ya ce "Muna sauraron ki, ina so
ki ba mu labarin ki, da sunan ki dama inda kika fito?".
Nisawa ta yi "Kamar yadda na faɗa maka ni ƴar a salin ƙasar kalponiya ce, mu uku iyayen mu
suka haifa". Haka ta cigaba da bashi labarin tana hawaye har inda ƴan fashin nan suka tashi
garin su da kashema ƴan uwan ta guda biyu da mahaifan su, sannan tace masu ita sunan ta
Abida.
Sun tausaya ma ƙwarai, kuma suka yi alƙawarin maye mata gurbin ƴan uwan ta da tarasa, in
har suna raye baza ta taɓa kukan rashin iyayen ta da ƴan uwan ta ba, godiya ta yi masu sosai
godiyar da
baki bazai iya misaltawa ba, sai da Momy Safiyya tazo ta ɗaga ni daga durƙuson da na yi ta
kalle ta ce "Haba ƴar uwarta, ashe baki yarda munza ɗaya ba?, tunda har kike mana irin
wannan godiyar". Kai ta jinjina masu ta ce "Anty Safiyya godiya ai tazama dole". Kai Momy
Safiyya ta girgiza ta ce "A'a sai dai in baki ɗauke mu a matsayin ƴan uwan ki ba".
Dady Abubakar ya ce "Gaskiya Safiyya take gaya, saidai in baki yarda da muba a matsayin ƴan
uwan na ki bane".
Hawayan idon ta ta goge "Ba haka bane...".
Momi Safiyya ta katsema hanzari "To yane?". kai ta girgiza tace "Ba komai Allah ubangiji ya
bani koda ƙanƙanuwar hanya ce da zan iya saka alkhairi da alkhairin da kukai min". Dariya
suka yi su duka suka ce "Amin".
Fita ya yi zuwa gurin aikin shi, su kuma suka yi zaman su tare a gidan kamar dama sunsan
juna, dan Momy Safiyya tana da saurin sabo, ita kuma Abidar bata da damuwa dan tasaki jikin
ta da Momy Safiyyan, haka kuma sukaci gaba da zaman su babu wata matsala, amma ance
zomu zauna zomu saɓa shine zama, to sumadai suna samun saɓanin, dan harshen da haƙori
ma suna saɓawa, to suma koda saɓani ya shigo tsakanin su, suna ƙoƙarin ganin ɗayan su ya danne zuciyar sa,
domin suga sun zauna lafiya.
Wata rana sun ta shi Momy Safiyyan ba lafiya hakan ne yasa suka nufi asibiti cikin gaggawa,
suna zuwa aka amshe ta aka shiga da ita, su nan tsaye cikin jimami sai ga wata likita ta fito
tana murmushi ta kalle su "Kai ne mijin ta?". Ta yi maganar ta na kallon Dady, jiki na rawa ya
ce "Eh, nine me ya faru?". Ya faɗi a ɗan rikice, dan baya fatan ace wani abun ya sami Safiyya,
hannu ta miƙa mai "Fara bani goron albishir".
Aljihun sa ya shafa ya ji ba komai a ciki, fahimtar hakan da likitan ta yi, tace "Na biyoka bashi,
madam nada juna biyu".
kwatanta maku irin farin cikin da muka shiga ma ɓata lokaci ne, dan ko na yi wa Momy Safiyya
murnar wannan rabon da Allah ya bata, dan tana tsananin son haihuwa sai yanzu Allah ya
kawo mata nata rabon.
Sallamar mu a kai muka koma gida jikin nata da sauƙi, mun cigaba da rainon cikin Momy
Safiyya cike da kulawa dan ko bana barin ta, tana yin komai a gidan, ni nake yin komai.
Kuma a wannan lokacin aminin Dady Abubakar wato Alhaji Bashir ya kawo ziyara gidan, dan
daga gurin aikin shi yake dan andawo da shi nan Abuja shima, ya ɗan jima a nan kafin ya yi
mana sallama, suka fita shi da Dady da zai mai rakiya zuwa wajen motar sa, har gurin motar
tasa suka ƙarasa Dady Abubakar ne ya kalle shi yace "Na ga tun da muka fito kake so ka yi
magana amma ka kasa cewa komai da matsala ne?".
Ajiyar zuciya Alhaji Bashir ya sauke ya ce "Yarinyar da na gani a cikin ƙanwar matar kace?".
Dadi Abubakar "Wai Abida kake nufi?". Alhaji Bashir yace "Eh to ita ɗin ce". Kai Dady ya
gargiza yace "A'a ba ƙanwar tace ba". Nan ya labartawa Alhaji Bashir yadda ya tsinci Abidah,
sosai Bashir ya tausaya mata.
"Yarinyar ta yi min, kuma da gaske ina son aurenta". Alhaji Bashir ɗin ya faɗi ya na duban
Dady.
Dady Abubakar ne yace "In ko haka ne zan baka aurenta, matuƙar ta amince, amma bana so
ka dubi tarihinta wata rana ka goranta mata". Kai ya jinjina "In sha Allah ba zan baka kunya ba
abokina". Da wannan suka ƙarasa gurin da motar Alhaji Bashir ke fake.
"Na san inda Abidah ce ba zata bamu kunya ba". Dady ya yi maganar lokacin da suka isa gurin
motar.
Ko da ya koma gida zuciyarsa kullum cikin tunanin Abidah take, ya kasa samun sukuni, domin
kuwa sonta ke nuƙurƙusar jiki da ɓargonsa.
Sai da aka sami kusan kwanaki kana Dady ya tunkari Abidah da batun Alhaji Bashir, "Ba zan
tilas ta ki ba, matuƙar bakya son shi to kada ki ji komai ki sanar dani, ni kuma zan sanar da shi
yanda zai fahimta". Dady ya faɗi ya na dubana.
Momy Safiyya ce ta dafa kafaɗata, "Kin gai idan har bakya son shi to kada ku cuci kanki, amma
wallahi Alhaji Bashir mutumin kirki ne, domin idan haka ta faru ina tabbatar miki ba zaki taɓa yin
kuka da aurensa ba, ki tsaya ki yi nazari".
Nisawa na yi "Anty tunda har kin ce haka to nima na amince, Allah ya sa shine alkhairi".
"Amin". Suka haɗa baki gurin faɗi.
Bayan kwana biyu da maganar Dady ya sanar da amininsa Alhaji Bashir, yadda su kayi da
Abidah, ai kuwa ya yi farin ciki, dan ji ya yi kamar ya yi tsuntsu ya ganshi a gaban Jadda ya
sanar mata a zo a nema masa auren Abidah.
"In sha Allah a satin nan zan shigo garin". Ta faɗi cikin murnar data kasa ɓoyuwa a muryarsa.
"Kai mutumina, irin wannan murna haka, kamar wanda aka cewa an ɗaura?". Faɗin Dady ya na
dariya, "Ba zaka gane ba ne, bakan san yadda son yarinya nan ya gama kassarani ba ne".
Da wannan suka ajiye wayar kowa na cikin farin ciki.
*BAYAN SATI UKU*
A wannan sati ukun abubuwa da yawa sun faru, daga ciki kuwa har da sa ranar aure na da
Alhaji Bashir, da kuma haihuwar Momi Safiyya, dan a daren na jiya ne Momi Safiyyan ta tashi
da naƙuda, asibiti muka nufa duk da dare ya yi amma mun sami wasu likitocin sune ma suka
shiga da Momi Safiyya lebo room, da take a cikin mawuyacin hali, kafin babban likitan da Dady
Abubakar ya kira tun a hanyar mu ta zuwa ya ƙaraso, ba'a jima da shiga da ita sai ga shi ya
shigo, hannu ya bawa Dadyn suka yi misabiha kafin ya ce "Tana ina?". Dadyn ne yace "Sun
shiga da ita cikin lebo room ɗin".
Bai sake cewa Dadgn komai ba ya shiga cikin ɗakin da take ciki, bai fi wasu mintina da shiga
ba, sai suka jiyo kukan jariri, kallon juna suka yi ita da Dady Abubakar kafin su sauke ajiyar
zuciya, suna godiya ga Allah, dan ni har hawayen daɗi na yi, dan dai yau ga jinin Anty Safiyya a
duniya "Alhamdulillahi". Na faɗa dan kuwa shine a bin godiya.
Nuse ce ta fito ɗauke da jariri a hannun ta, har rige-rigen amsar jaririn suke da yake hannun
Nuse ɗin, Dady ne ya fara amsar jaririn yana kallon yarinyar ya na murmushi.
Abida ce tamatso "Dady mace ce?". Kai ya ɗaga mata "An sami ƴa mace". Ya faɗa ya na miƙo
mata yarinyar, amsar ta ta yi ta na kallon yarinyar cike da so da ƙauna, dan a kallon farko da ta
yiwa yarinyar taji Allah ya ɗora mata ƙaunar yarinyar, ko da yake irin soyayyar da iyayen ta suka
nuna mata, ai zata ji fiye da haka ma akan jinin su.
Izinin shiga aka bamu, shigar kuwa mu kayi muka same ta akan gadon asibitin a zaune ta na
kallon kyautar da allah ya bata, ɗago kanta ta yi ta na kallon su kafin ta sakar masu murmushi,
saurin ƙarasawa na yi inda take zaune, nima zama nayi a gefen ta muna kallon yarinyar tare,
Dady ne ya ce "Oh! wato kun samu ƴar ku ni kuma an manta dani ko?".
Dariya suka yi duka kafin Anty Safiyya tace "Haba dai har na isa na manta da kai, kafin na
ganta wana gani?". Dariyar shima ya yi ya ce "To na sani ko har an manta da ni". Kai ta girgiza
mai tace "Ina zan iya mantawa da kai". Kafin ya sake yin magana tace "Wai dan Allah yau she
zasu sallame ni?, dan wallahi na gaji da zaman asibitin nan, kawai kasa su sallame ni, na koma
gida".
Dafata na yi na ce "Haba dai Anty Safiyya ki bari ki ƙara jin sauƙi mana, ko zuwa gobe sai a
sallame ki". Fur Momy ta ƙi.
Sallamar ta ta aka yi muka koma gida, kuma tun da safiyar yau muka fara amsar baƙi, dan
Dady tun daren ya fara kiran ƴan uwan sa da na ita Momy Safiyya, shiya ma yau tun safe ƴan
barka suka fara zuwa har ma da wasu daga cikin dangin Momy Safiyyan, haka kullum muke
amsar ƴan barka har ranar suna, ranar suna yarinya taci suna Maryam suna ce mata Sanah
dan taci sunan mahaifiyar Momy Safiyya shi yasa ma suke mata laƙani da hakan.
Bayan sunan Momy Safiyya da wata uku aka yi bikina da Alhaji Bashir, anyi biki mu lafiya su
Momy Safiyya sune iyayen biki dan kuwa ta zage tayi biki irin na nu nawa sa'a.
Shi ma hakan take a gurin Dady Abubakar, dan kuwa ya nuna bajinta sosai, dan duk abinda
uba ya kewa ƴarsa to Dady Abubakar ya yi min, dan har kayan ɗaki da na kitchen da Alhaji
Bashir ɗin ya ce ba sai ya yi ba, amma bai saurare shi ba dan kuwa ya yi min kayan da ko wata
ƴar mai kuɗin sai haka, dan ko nasa ni koda iyayena ne iya abinda zasu min kenan.
Dan kuwa wa'in nan bayin Allah sun maye min dukkan wata kewa ta iyaye sun hana ni na yi
kukan maraici, bani da wani abinda zan iya biyan su dabshi face nai tai masu addu'a har
ƙarshen rayuwar ta.
Allah sarki Ummi, to ko ya yata kaya?, mu haɗe daku a next page.
Likes and comments my fans, ina yin ku oba wallahi.
*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/26, 11:51 AM] Abidah: *NAZBEER*
*Written by*
*ABEEDAH*✍️
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------
My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------
Follow me on telegram
https://t.me/+3USo7e9asLpmNzc0
_________________________
*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️
*PAGE--------12*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Na tare anan gidan shi da yake Abuja, gida ne me kyau da tsari,dan kuwa ko makaho ya laluba
yasan an narka dukiya gurin gina shi.
Ƙalubalen farko da na fara samu da a halin shi, dan kuwa ƴan uwan sa sunce sai dai ya dawo
da ni nan Kano cikin nasu matan, dan bafin suna na yi ba da za'a ce ni a can zan zauna, sai da
mahaifin su ya tsawatar akan hakan, sannan yace wa ita mahaifiyar su Alhaji Sunusin dan ita
tace da sauran yaran ta sukace basu yarda ba, ya aje ta a can ba sai dai ta dawo cikin su, dan
ita mahaifiyar tasu abinda yasa tace haka don tana ganin yaran ta ne manya agidan amma, a
ce sai abin da yaran Jadda suka ga dama ake yi a gidan dan sune suke riƙe da gidan.
Balle ma shi Alhaji Bashir ɗin tunda ko a cikin yaran nata ya fi dukan su hali, dan kusan ma shi
ke ɗaukar ɗawainiyar ta harma data yaran matan, kai harma da ta mazan, dan kuwa ba wata
sana'a suke ba.
Amma da yake ɗan Adam mai manta alkhairi ne, shi ne fa bayan bikin da ya ce shi a can ya ke
so ya zauna saboda aikin shi kar hankalin shi ya rabu gida biyu, amma su Alhaji Sunusin su
kace basu yadda ba kuma mahaifiyar su ta goya masu baya. Sai da Alhaji Babba ya rufe ido
yaci mutumcinsu kana suka bar zancen.
*BAYAN WATA TAKWAS*
A wa'in nan watanin takwas ɗin abubuwa da yawa sun faru, na fari ciki harma da na baƙin ciki,
daga cikin abin farin cikin da yasa meni, shine har da ƙaruwar da Allah ya bani, dan kuwa a
watan da ya wuce, mu ka je asibiti dan zazzaɓin da ya sakoni gaba, gashi duk abin da na ci ko
na sha to ba zan taɓa zama lafiya ba har sai na amayar da shi, amma in ba haka ba to ba
zaman lafiya.
Ganin da Alhaji Bashir ya yi abin ya ƙi ci ya ƙi cinyowa, yasa ni a gaba muka tafi asibitin.
Gwajin farko suka gane ina da shigar ciki, har na sati biyu. Tabbas duk kan wani masoyina ya
taya ni murnar wannan rabon da Allah ya bani.
Ban ƙara tabbatar da irin son da Momy Safiyya ta ke min ba sai da na samu wannan cikin, dan
kulawa ta daban take bani, kullum ne saibta yi min abin ƙwalama taka womin, kama daga tuwon
madara da gillisuwa da tuwon fulanto, kai harma da dagin su aya da gyaɗ, dama duk kan
abinda tasan mai ciki tana so.
Gaskiya na ga tsantsar soyayya a gurin wa'in nan bayin Allah. Tare da su muka cigaba da
rainon cikin jikina da taltali da kulawa, har Allah ya kawo haihuwa dan kuwa a ranar wata litinin
na tashi da matsanan cin ciwon mara, Momy Safiyya da Alhaji Bashir ya kira ta tun lokacin da
na fara jin alamun ciwon, ce ta iso tare da duk abin da ake buƙata ga mai haihuwa.
Dai-dai isowar ta faya ta fashe min. Da hanzari ta ƙaraso in da nake duƙe a kan gwiwowina na
haɗa uban zufa kamar wadda ta haɗiyi kunama, koda yake ni harma gara haɗiyar kunamar a
gurina, a kan abin da nake ji.
Riƙeni ta yi ta na min sannu, to ni ko jintama ba na yi saboda azabar da nake ji, zufar tashiga
share min, amma da tashare da wata ta fito, wani irin nishi na saki ina sake rirriƙe Momy
Safiyya, kai na take shafawa zuwa gadon bayana, tana ce min ki daure da haka kowa ya ke
farawa.
Sake riƙe ta na yi ina sakin wani nishin, sai ga kai ya fara fitowa, "Kin kusa daure dai, tunda kai
ya fito". Ina bana ma jin abin da take cewa, Alhaji Bashir ne yace "Hajiya Safiyya ko asibiti
zamu tafi ne tun da dai abin ya gagara agidan".
Kai ta ɗaga mai ta ce "To hakamma ya yi, bari na shirya kayan da zamu buƙata". Fita ya yi ya
na jiran fitowar ta su.
Ƙaƙƙarfan nishin da na saki ne ya da katar da Momy Safiyya daga yunƙurin saki na da tayi,
sake riƙeni ta yi, "Yanzu zamu tafi asibi...". Kukan jaririn da Momy Safiyya taji ya hana ta ƙarasa
maganar da ke bakin ta, da sauri ta kai kallon ta kan jaririn da yake ta tsala kuka.
Da hanzari ta isa kan jaririn tasa hannu ta ɗauke shi tana nufar inda ta ajiye sabuwar rezar da
tazo da ita, sai da ta yanke masa cibiya kafin ta dawo gurin da nake zaune ina mai da nunshi.
Sannu ta sake yi min tana kama ni zuwa banɗakin da yake cikin ɗakin, shi kuwu Alhaji Bashir
da ya gaji da jiransu agurin mota, sai ya kashe motar ya fito, cikin gidan ya shiga a bakin ƙofar
ya tsaya yace "Hajiya Safiyya lafiya naji ku shiru?". Ƙofar ta buɗe ta na dariya tace "Oh!,
wallahi ni harna manta ma da mun bar ka kana jiran mu, kasan na ga sabon ango shi yasa ma
na manta da kowa".
Kallon ta ya yi da sauri yace "Hajiya Safiyya ta haihu ne?". murmushi tasake yi tace "Allah ya
sauke ta lafiya, an samu ɗa namiji". Hamdala ya shiga yi yana sake yiwa Allah godiya da
kyautar da ya ba shi.
Nan fa ya shiga kiran ƴan uwa da abokan arziƙi ya na sanar musu, har su Jadda sai da ya kira
ya sanar musu suma.
Sai da Momy Safiyya ta shirya mu tsaf ni da jaririn kana ta huta.
Jadda ta zo tare da Autar ta Mubinat, tare su ka cigaba da kula da ni da Jaddan da Momy
Safiyya, wata kulawa Jadda take bani ta daban.
Ranar suna yaro ya ci suna Muhammad Nazeer, an yi shagulgula sosai, an yi ɓarin nera, kamar
ba'a san zafin nema ba, na samu kyaututtuka daga abokan arziƙi, wasu ma ban san suba.
Taro ya