Showing 3001 words to 6000 words out of 21648 words
Chapter 2 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf
haka na isketa kwance, haawayen
tausayin ta ya gangaromin.
Har gabanta na isa, hannunta na kamo cikin nawa, ido na zuba mata, "Ammita dan Allah ki
buɗe baki ki min magana ko da sau ɗaya ne". Na faɗi muryata na rawa, ido ta zubamin kawai
ba tare da tace komai ba, "Ina son sanin ɗin wacece?, kuma suwaye danginmu?, duk bani da
wannan amsar, ke kaɗai ce zaki iya bani ita".
Na ƙarasa ina fashewa da kuka me tsuma zuciya, na sake tabbatarwa da mahaifiya bango ce
ga rayuwar ƴaƴanta, tabbas duk wanda ya rasa mahaifiya yayi babban rashin da har abada ba
zai sami madadin ta ba.
Na ɗauki tsayin lokaci ina kukan kafin na gaji dan kaina nayi shiru.
Sai da yamma liss sannan na yiwa matar Malam sallama na koma gida.
Mu haɗe daku a next page don jin cigaban labarin, labarin nan fa na faɗa muku salonsa na
dabban ne.
Like an share my lovely fans, ina mugun yin ku wallahi, i love you irin wujiga-wujiga ɗin
nan.
*Taku*
*ABEEDAH*✍️
[5/13, 9:12 PM] Abidah: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------
*NAZBEER*
*Writeen by*
*ABEEDAH*✍️
*FISRT CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️
*PAGE*------- 3
Bismillahirrahmanirrahim.
*KANO STATE*
*NASARAWA G.R.A*
Hajiya Balaraba
Ahankali take jan motar ta daga inda ta fakata bayan fitowar ta daga gurin boka Darmuuje, a
hankali ta cigaba da ratsa kwazazzabai da duwatsun nan dake hanyar, domin kuwa ƙumgurmin
dajine da me karatu ba zai taɓa tunanin wani ɗan Adam zai iya shiga cikinsa ba.
Amma saiga shi saboda neman biyan buƙatar duniya da neman a durƙusar da rayuwar baiwar
Allah da bata jiba ba ta gani ba, Balaraba ta shigo shi.
Duniya ina zaki da mu ne?, wai yanzu har ɗan uwanka musulmi zai nemi ya saka ka a tsaka
mai wuya, haba 'yan uwa yau shena zamu aje san zuciya da sankan mu,mudubi gaskiya
mugane cewa wannan duniyar ba matabbata bace, wai a hakane muke kiran kanmu musulmai,
kuma har kaje kaɗauki buta kayi alwala kaje kai sallah kana me tunanin samun rabauta a
duniya da lahira.
wannan hanyar bamai ɓullewa bace da muka ɗaukarwa kanmu, ya kamata mubuɗe zukatanmu
mu kalli gaskiya, mudawo kan turba tagari, wanda zamu amfanar da kanmu.
A haka ta cigaba da tafiya har tafito cikin gari, kai tsaye tahau titin da zai sadata da Nasarawa.
Hon tayi a gaban katafaren get ɗin gidan, da hanzari me gadin ya taso ya wangale mata get ɗin,
hancin motar ra danna cikin gidan.
A gurin da aka tanada don ajiye motocin gidan tayi parking, cikin gidan ta nufa tana ta zabga
sauri kamar zata tashi sama.
"Mami har kin dawo?". Ɗaya daka cikin ƴan matan dake zaune a falon ta faɗi tana cigaba da
latsa wayar data ke yi.
Biba da bata ce komai ba tun shigowar Mamin ta kwashe da dariya, wacce ta jawo hankalin
Abdul da Anas da Tijjani dake can gefe na falon suna buga gema.
"Wai Mami daka ina kike haka?, kinga fuskarki kuwa?". Biban ta faɗi har lokacin bata daina
dariyar ba.
"Mami kamar wacce kura ta biyo". Anas shima ya faɗi yana riƙe dariyar dake cinsa.
"Ban sani ba dan gidanku!, ni zaku ce kamar kura ta biyo?". Mami ta faɗi tana sakin huci.
"Mami sannu da zuwa". Tijjani da duk abinda ke faruwa bai ce komai ba yayi maganar.
"Yau ɗan albarka". Ta amsa, ba tare da ta sake tanka su ba ta haye sama ta barsu suna cigaba
da dariyar.
Yaran Mamin uku ne, Tijjani, shi ne babba, sai Abdulwahab, sai kuma auta Habiba da suke kira
da Biba, Anas da Sadiya ƴaƴan ƙanwar mijinta ne.
Jagwab ta zauna akan katafaren gadon ɗakinta, hannunata dafe saman goshinta, abin duniya
duk ya isheta, dan ba ƙaramin tada hankalinta maganar boka Darmuuje tayi ba.
Kamar wacce aka mintsina ta miƙe, ɗakin ta shiga zagayewa tana naushin hannunta, "Inaa!,
hakan baza taɓa yuwuwa ba!". Ta faɗi cikin ƙaraji.
Wayarta ta jawo, number aminiyarta Hajiya Turai ta shiga aikawa kira, cikin sa'a kuwa bugu
ɗaya Turan ta ɗaga kamar me jira, ko da yake dama jiran take.
"Ya ake cike ne aminiya?". Hajiya Turai ta tambaya, huci Hajiya Balaraba ta sake saki, "Ina
cikin tashin hankali Turai, abubuwa na shirin kwaɓemin".
"Me kuma ya faru Hajiya?". Ta tambaya tana dafe ƙirji, nan ta labarta mata duk yanda suka yi
da boka Darmuuje, dan ta yarda da Turai ɗari bisa ɗari.
Nisawa Turai tayi kana tace "Ka da ki damu da maganar Darmuuje, kinsan suma fa wani lokacin
suna faɗar abinda ba haka bane, ki kwantar da hankalinki muke da nasara, nima ina son na
ɓulla gurin boka Kagalmu akan lamarin naki".
Ajiyar zuciya ta sauke a karo na biyu tace "Shi ke nan Turai, duk yanda kukai sai ki sanar dani".
Da haka suka yi sallama suka ajiye wayar.
Dariya me sauti Turai ta saki bayan ta ajiye wayar,"Muje zuwa Balaraba, ai wallahi matuƙar ina
raye saina rabaki da gidan Alhaji Ahmad, kamar yadda ke ma kika rabashi da tashi matar, ba ke
kaɗai kika iya wasan ba". Ta faɗi tana sake kwashewa da dariya.
Kamar yadda tace zataje gurin boka Kagalmun zata je a sake sabunta aikin dake jikin Humaida.
Dan kamar yadda ta faɗa Humaida baza ta taɓa dawowa cikin ruyuwar Ahmad ba, "Kai har
abada Humaida baza ki taɓa samun lafiya bama balle ki tuna wacece ke harma ki tina kin taɓa
rayuwa da wani mai suna Ahmad ba wannan alk'wari nane".
Falo ta fito zuciyarta cike da wannan alwashin.
"Mamina". Minal dake zaune a falon tana kallon serias ta faɗi, "Na'am ƴar Mami, ya aka yi?".
Tayi maganar tana zama gefen Minal ɗin, kai Minal ɗin ta ɗora akan kafaɗarta.
Kanta Mamin ta shafa, "Babyna menene?".
Hawayene suka sakko mata, ai ko nan da nan hankalin Hajiya Turai ya tashi, a rikice take
tambayarta abinda ke damunta.
Cikin kukan Minal tace, "Mami T.J ne, jiya na ganshi a gurin birthday Khairy nayi masa magana
yaimin banza".
"Akan wannan kike asarar hawayenki?, ki rabu dashi ya gama hayaƙin rashin mutumcinsa
kamar ya aureki ya gama".
Mamin ta faɗi cikin lallashi, "Mami da gaske?". "Ƙwarai ma kuwa, ke dai kawai ki kwantarmin
da hankalinki".
Cikin farin ciki ta rungume Mamin, "Love you more Mamina".
*NAZBEER*
A hankali ya kai hannunsa me ɗauke da zoben daimon da azurfa ya kunna loptop ɗin dake ajiye
a saman table ɗin na shi, sai da komai ya saitu sannan ya shiga tura bayanai, wani file ne ya ja
hankalinsa hakan yasa ya jawo wayar dake office ɗin ya aika kira, bugu ɗaya aka ɗaga, "Ka zo
yanzu". Iya abinda ya faɗi ke nan ya katse kiran ba tare da ya jira amsar da za'a bashi ba.
Hmmm, akwai ƙura fa
To koma dai yaya ne mu haɗe daku a next page don jin yadda zata kaya.
Share and comments my lovely fans, i love you irin wujiga-wujiga ɗin nan
*Taku*
*ABEEDAH*✍️
[5/14, 7:24 PM] Abidah: *NAZBEER*
*Written by*
*Zainab Laminu Sani*
(*Abeedah*)✍️
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/FP7D2LzvLM6Asy82NpHTIF
My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
_________________________
*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualites And Trusted writer's of the Nition*)☀️☀️☀️
*PAGE*----- 4
Bismillahirrahmanirrahim.
Bai fi mintina uku da kiran wayar ba, sai ga sakatariyar shi ta shigo, tayi nokin shiru ba amsa,
hakan yasa ta shigo ɗin, dan tasan idan ƴan rashin mutumcin sa na kusa haka yake, yana ji za
kai ta nokin yayi banza da kai ya shareka, kuma yana ganin ka ta C.C. T.V dake office d'in".
Sallama ta sake yi a karo na uku, amma bai ko ɗaga kai ba, balle ya amsa mata,
sai dai ya amsa a zuci, dan ƙasai ta baza ta barshi ya iya amsawa a fili ba, sai ka ci sa'ar gaske
ne zaka ga lips ɗin shi ya motsa.
sanar da shi zuwan, Mukhtar tayi hannu kawai ya ɗaga mata, wuce wa tayi dan ta gane me
ogan nata yake nufi.
"Zaka iya shiga". Ta faɗi idonta akan Mukhtar ɗin kana ta koma mazauninta ta zauna.
Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga office ɗin na Nazbeer, ciki-ciki ya amsa sallamar, "Have a
sit". Ya yi maganar kamar baya so.
Zama Mukhtar ɗin yayi yana fuskantar shi, shiru ya gifta na ƴan mintuna kafin Nazbeer ta katse
shirun ta hanyar watsawa Mukhtar ɗin tambayar data rikito da kayan cikin shi, ji yayi wata
gudawar na neman kufce masa.
"Ranar 4/1/2025 an fitar da kaya da sa hannunka, amma kuma a jerin docments ɗin da ka bawa
company babu na wannan kayan". Yayi maganar yana tsatstsare Mukhtar da idanunsa masu
rikita mara gaskiya.
Zuface ta shiga karyowa Mukhtar kamar wanda ta haɗiyi kunama, cikin in-ina ya ce, "Babb bani
da masaniya akan fitar kayan sir".
Zai yi magana Tahir ya shigo, hakan yasa ya fasa maganar da yayi nufin yin, takowa Tahir yayi
har gaban teburin da Nazbeer ke zaune, file ɗin daya anso daka office ɗin Khalil ya ajiye a
saman teburin, "Sir daka office ɗin Khalil ne". Yayi maganar bayan ya ajiye file ɗin.
Kai kawai ya gyaɗa, "Ka kira shi Khalil ɗin". Ya faɗi cikin muryar mara hayaniya, "Ya fita yanzu,
dan tare muka fito da shi ni nayo nan shi kuma ya fita".
"OKay". Ya faɗi yana mai da hankalinsa kan loptop ɗin dake gaban shi, shi ko Mukhtar zufa ta
gama jiƙe shi sharaf, dan yasan shirun nan da Oga yayi ba wai ya ƙyale shi ba ne.
Har ya yunƙura da nufin magana Nazbeer ya dakatar da shi da faɗin "Zaka iya tafiya".
"Na gode Oga". Ya faɗi yana miƙewa cikin hanzari ya nufi ƙofa, da kallo ya raka bayan shi yana
jijjiga kai, kafin ya saki wani mugun murmushi, irin na zan lailaya kanku a titin nan.
"Mutumina ya aka yi ne?, shigowata ke nan aka ce kana kirana, shi yasa ko office ban shiga ba
nayo nan, kuma nasan wannan murmushin naka ba alkhairi bane ga wanda aka yiwa shi".
Khalil dake zaune a cikin ɗaya daga cikin jerin kujerun dake jere a office ɗin ya faɗi.
Ɗan murmushin gefen baki ya saki, "Hmm". Kawai ya faɗi yana duban Kalil ɗin, "Kaya ne da
zasu kai na kimanin miliyon talafin da takwas, aka fitar dasu, amma a document na company
babu su".
Ido Khalil ya zaro, "Miliyon talatin da takwas!". Ya faɗi cike da mamaki, kai Nazbeer ya jinjina
masa alamar tabbatarwa.
"Amma ka binciki managa kuwa?". "Shine nake ƙoƙarin yi, shi yasa nace masa ya tafi kawai".
"Ya kuma zaka ce ya tafi?". Murmushi ya sake yi kana ya ce, "Na ɗaure shi ne ta yadda bazai
iya fitar da kansa ba, so nake ya kawo kansa da kansa".
Shiru ya ɗanyi, shi kaɗai yasan abinda yake saƙawa a zuciyarsa.
Nan dai suka tattauna batutuwan da suka shafi aikin nasu kafin suka fito sallah.
A hanya Nazbeer ɗin yake sanarwa Khalil fitar da zasu da yamma, "Allah ya kaimu". Da
"Amin". Ya amsa suka cigaba da tafiya.
*ABIDAH*
A hankali take tafiya kamar me tsoron taka ƙasa, wanda bai sani ba zai ɗauka iyayi ne, haka
tsarin halittarta take, sam bata da haniya ko surutu.
A ƙofar gidan nasu ta ci karo da Yaya Hashim, shima dawowarsa kenan daka gurin aikin
kanikancin da yake yi.
Da murmushi ya kalle ta yace "Ƴan mata a don gari, daga ina haka da wannan yammar?".
Murmushin dake ƙarawa fuskata kyau nayi, "Kai Yaya, wacece ƴan matan?".
"Gata nan a gabana, ni indai kina gabana ai bana kallon wata mace a matsayin mace, ke ka ɗai
ce". Ya yi maganar idonsa akaina.
Zanyi magana na fasa, sakamakon hango Baba Habibu ya nufo inda muke yana baza babbar
riga, "Kin ci gidanku, shegiyar yarinya me siffar ifritan ƙarnin farko, iskancin naki bai tsaya a iya
waje ba sai kin haɗa dana gida?, to bazan lamunta ba ki lalata min yaro, sam bazata saɓu ba".
Yaya Hashim ya buɗe baki zaiyi magana Baban ya tare numfashinsa, "Kai tafi can ka bani guri,
me zaka cemin akan wannan yarinyar?".
"Wallahi Baba Abida mutuniyar kirkice, sam zaton da kuke mata ba haka bane". Yayi maganar
da muryar da ke nuni da ɓacin ran da zuciyarsa ke ciki.
Dan Allah ya sani baya son yaji ana danganta Abida da wata mummunar kalma.
"Ehh laillai Hashimu wuyanka yayi kauri, ni zaka duba ka cewa ƙarya nake?".
Da sauri ya ɗago kai ya dubi Baban, "Kayi haƙuri ba haka nake nufi ba".
Sosai maganganun Baba Habibu masu kama da saukar bulala a zuciyata suka shigeni, da sauri
na kutsa kaina cikin gida, ina shiga na iske wani tashin hankalin duk a kaina.
Anna mahaifiyar su Baba Halliru na iske tana ta faman yin masifa, Baba Halliru duƙe a gabanta
sai faman bata haƙuri yake, "Nifa Halliru na gaji da ganin yarinyar nan a gidan nan, sai kace kai
ne sarkin taimako daka ganin mutane ka yayubo mana, dan haka na baka kwanaki biyu ka fitar
mana da ita daka gidan nan".
Zantuttukan Anna ke nan da suka shiga kunnena bayan na shigo cikin gidan.
"Kiyi haƙuri Anna, riƙon yarinyar nan fa tamkar jahadi ne muke yi, kuma kin san ladan masu
jahadi a gurin ubangiji, tunda bazan bijirewa umarninki ba a matsayin ki na mahaifiyata, amma
ina roƙon alfar guda ɗaya gurinki, ita kiyi haƙuri ki janye wannan umarnin, danko Abida amana
ce me girma a gurina, bata da wata mafaka da wuce nan ɗin". Baba Halliru yayi maganar
kansa a ƙasa, idanunsa na duba da suka tara ruwa.
"Allah sarki Baba, mutanen suna ƙaunata tsakaninsu da Allah". Na faɗi cikin raina, hannu na kai
nayi saurin ɗauke ƙwallar data tarar min.
Take fuskar su Inna Laure dake zaune a gurin ta canza, dan ko ba hakan suka so ba.
Jikin Annan ne yayi da kalaman Baban, "Shike nan, Allah ya tayaka riƙo". Da "Amin". Ya amsa,
haɗi da ƙara yi mata godiya ya miƙe da nufin fita, karo sukayi da Baba Habibu dake ƙoƙarin
shigowa, sai sauri yake kamar wanda aka biyo.
"Lafiyarka kuwa Habibu?". Baba ya faɗi yana sake duban Baba Habibun, "Ban sani ba!, duk ai
kai ne ka ɗaurewa yarinyar nan, shi yasa take kallon kowa a wulaƙance".
Idona na runtse cikin zuciyata ina karanto duk addu'ar data zo bakina, idon na buɗe na sauke
kan Inna Hadiza dake can gefe tana sharar ƙwalla, nasan abin yafi ƙarfinta, dan ko Annar ba
ƙaunarta take ba, hakan yasa su Inna Laure suka fita fada a gurin Annar, kuma ba dan bata
kyautata mata ba, ita kuwa Inna Laure dama ƴar ƙanwar Annan ce, hakan yasa tafi kowa fada a
gurin Annar.
Hmm akwai ƙura fa
To mu haɗe daku a next page don jin yadda zata kaya.
Likes and comments my lovely fans
*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/16, 12:31 PM] Abidah: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
---------------------------------------
My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
_________________________
*NAZBEER*
*Written by*
(*Abeedah*)✍️
*FIRST CLASS WRITR'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualites And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️
*PAGE* -------- 5
Bismillahirrahmanirrahim.
*NAZMANTON*
Ɗaki ne mai duwar gaske, wanda ya kasance mallakin wasu daga cikin mutanen gidan, dan ko
ba kowa ya san da shi ba daga cikin jama'ar gidan, masu shi ne kawai suka san da zamansa a
cikin gida.
Abinda ya dugunzuma hankulansu, shi ne kwanakin baya ɗaya daga cikin mutanen gidan ta
taɓa jin wani sirrinsu, hakan yasa yanzu suke matuƙar taka tsan-tsan da al-amuransu.
Lokacin matar tayi yunƙurin sanar da wani abinda ta gani ɗin, wannan shi ne girman kuskuren
data aikata, dan ko tayi nadama, ko in cema tana kanyi, kuma zata cigaba da yi har ƙarshen
rayuwarta,
Yau ta kama ladaba, wacce hausawa ke mata laƙabi da ta bawa ranar samu, hakan take ga
ma'abota ɗakin duhu, domin yaune suke shirin shiga meeting domin tattaunawa akan meeting
ɗin da suka gidanar a bankadamiyar tsafinsu.
Ƙasa-ƙasa maganganun ke tashi wanda ba kowa ne hankalinsa zai kai kai ba, muryoyi ne
mabambanta ke fitowa daka baku nan jama'ar dake damfare a cikin wannan ɗaki.
"Nifa gaskiya ban gane abinda Dodo Jak ya faɗi a daren jiya ba". Wata murya mara