Showing 6001 words to 9000 words out of 21648 words
Chapter 3 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf
daɗin
sauraro tayi maganar, taya ma zai haɗa nasararmu da wannan matar?". Nan dai kowa ya
cigaba da tofa albarkacin bakinsa.
Abinda ya kawo wannan mahara kuwa shine, daren jiya ne suka sami kiran gaggawa daka
gidauniyarsu ta tsafi, sun tattauna abubuwa da dama da suka sahifi ƙungiyar da cigaban
tsafinsu, har ma da nasarar da suka samu a shekarar, wanda hakan nada nasaba da mutane
biyu dake hannunsu.
Abinda Dodo ya faɗa daga ƙarshen tattaunawar tasu ne ya tashi hankulansu, dama duk wanda
ke da alaƙa da maganar daya faɗa ɗin.
Magana ce guda uku Dodo ya faɗi, wanda duk suka ƙara tada hankulan mazauna ɗakin na sirri,
wannan fa shi ake kira rana zafi inuwa ƙuna.
Su ta inama zasu fara neman yarinyar da Dodon ya ambata? daɗin daɗawa ya tabbatar musu
da samun yarinyar nan shine babban nasararsu da suke dakon jiran zuwanta, abinda ke ƙara
tada hankalinsu kuwa bai wuce bincinko yarinyar nan dai-dai yake da bankaɗo labulen asirin
sirrinsu, dan kawota a matsayin matar Nazbeer ba abu bane me sauƙi.
Dodo ya sake tabbatar musu da lallai-lallai su tabbata sun shigo da yarinyar cikin mantion ɗin
nan, wata ƙatuwar laya ya basu da cewa da zarar sun ajiye a ƙofar da ita yarinyar zata taka
shike nan ba zata yi musu musu ba akan duk abinda suka saka ta, su kuma da wannan za suyi
amfani gurin sadata da Dodo Jak, shi kuma ya cika musu aikinsu da ita.
Inda matsalar take shine, ina zasu ga yarinyar?, kuma a ina take?, tunda Dodon bai sanar dasu
komai akan hakan ba.
Magana ta biyu da Dodon yayi ita ce ta samo mace me cindo a ƙaramin yatsanta na hagu, ,
nasan da yawa zasu ce meye kuma cindo?, a cikin mutane akwai wanda ubanginji ke azurtasu
da yatsu shidda, wannan na shidan shi ake kira da cindo, kuma shine Dodo Jak ya umarta da
su kawo.
Za'a yanko shi tare da idon macen na dama, kuma macen ta kasance me shakaru ashirin da
shida da kwana takwas, sannan za'a samo namiji shima me cindon, amma shi saɓanin ita
macen, shi za'a ciro na ƙafar shi na dama tare da idonsa na hagu, shi kuma me kimanin
shekaru arba'in da ɗaya a duniya.
Magana ta ukun kuwa sun saba jinta dan ƙa'ida ne indai sun zauna mitin ko wani taro, to sai ya
gaya masu ita.
sun sha tambayar sa me wannan kalmar ta ke nufi, baya ce masu komai akan haka ɗin, sai dai
yayi dariyarsa mara dad'in ji.
yace musu shima har yanzu yaka sa gane menene ma'anar kalmar.
amma dai ya san tabbas akwai ta.
wannan maganar kuwa ba kowacce magana ba ce.
face kullum suka tashi daga taro ko mitin sai ya ce masu, "Akwai tafiyar da ba dawowa". Sun
kasa gane, meta ke nufi.
kuma kamar kullum yau ma bata sake zani ba dan da suka tashi zasu fita ɗin, sai da ya sake
maimaita musu ita.
Abinda ya faru ke nan a daren jiya ɗin, da ya saka su yin mitin ɗin gaggawa, sun so su zauna
tun jiyan sai hakan baiyu wuba, dan basu suka baro gurin Dodo jak ba.
sai da misalin ƙarfe 3:40 na dare. kuma sanda suka zo gida, wasu masallatan ma harsun fara
kiran farko, shi yasa suna dawowa kowa fat ɗin shi ya wuce. kamar yadda suka fita ta
ɓarauniyar hanya.
to yanzu ma tanan suka dawo.
shiya tunda safe ya turawa kowa saƙo ta hanyar da suke haɗuwa bayan ɗakin miti.
suna gani basu yi ƙasa a gwiwa ba suka zo dan babu wanda yake cikin kwanciyar hanli.
Da wuri ko suka hallara, saboda suna so su samu matsaya guda ɗaya.
sun ɗauki tsayin lokaci suna tattaunawar, sun ko samo mafitar da suke gani ta dace.
Ɗaya ne daga cikin su ya kalli wani ɓangaren da ke cikin ɗakin da yake ɗauke da daskararrun
mutane, dan kuwa akafe suke babu alamar rai, koda yake ina zaka yi tsammani ganin mutum
mai rai anan tunda suna cikin gilas ne.
Tsaki me sauti ta ja, "Nifa banga amfanin ajiye wannan yarinyar da uwarta da Dodo Jak yasa
aka yi ba".
Wani shegen kallo wanda yake zauna ne agefen ta yayi mata.
"Aiko badan wannan ɗin da uwar ta, ta ba, da kema baki mallaki abinda kika mallaka ba, kin
san kuwa ajiyensu da aka yi yasa muke samun abinda bamu taɓa samu ba, tunda ko muka fara
wannan harkar".
Ɗayan dake tsaye a fusace yace, "Wai me kuke yi haka ne?, shida yasa muka ajiye su ai yafi
mu sanin amfaninsu, tun da mu amfanin da suke mana shine kawai su kaimu ne ga cin nasarar
mu ne".
Ba tare da wani ya sake cewa komai ba suka shiga ficewa ɗaya bayan ɗaya, ruf ɗakin ya koma
ya rufe bayan sun gama ficewar, kai idan ka gani ba zaka taɓa cewa da ƙofa a gurin ba, balle
kayi tunanin wani zai iya shiga.
*KANO STATE*
Hajiya Balaraba.
Suna gama wayar da Hajiya Turai.
miƙewa tayi tafara rage kayan jikinta sai da ta gama cire kayan nata sannan tanufi banɗaki dan
yin wanka.
Fitowa tayi bayan ta gama shirin, kai tsaye kitchen ta nufa dan ganin abinda ƴan aikin ke yi.
Karo sukaci da Autarta Baby, "Mami kizo Dady ya dawo, yana falonsa". "To Auta, gani nan".
Falon nasa ta nufa, a falon ta iske duka yaran Tijjani ne kawai baya nan, kai suka ɗago duka
suka zuba akan Mamin haɗi da amsa sallamar data yi.
Gurin da Dadyn ke zaune akan kujera me zaman mutum uku ta ƙarasa ta zauna a gefensa,
"Sannu da zuwa". Dubanta yayi "Yauwa, sannu, ya gidan?".
"Alhamdulillah". Ta faɗi tana miƙewa ta nufi ɗakinsa dake cikin wani korido, ruwan wanka ta
haɗa masa kana ta fito, "Idan ka biye surutun waɗan nan baza su barka ka huta ba".
Dariya sukai gaba ɗaya kafin ya miƙe ya shiga ɗaki.
kafin yace komai, sai ga T.J ya shigo kamar an korosa yana mazurai da ido,
ya kalli in da Anas yake "Kai Nas zoka bani key ɗin da ka ɗauka a ɗakina, ya ƙarasa maganar
yana ciccijewa irin na tantiran yaran nan.
Nas ɗin da yasan ya ɗauki motar tasa yasa ya miƙe, "Haba Bro, ganin baka shirya ba ne yasa
na ɗan fita da motar".
Shi kuwa sake haɗe fuska yayi ya miƙa masa hannu alamun ya bashi, babu musu kuwa ya
miƙa masa key ɗin.
Fisgewa kawai yayi daga hannun nashi ya juya ya fita a hanzarce, bai ko bita kan su Momi dake
falon ba, nisawa Dady yayi, ƙasan zuciyarsa cike da taikaicin halin T.Jn, "Bari na watsa ruwan".
Bai jira cewar Momy ba ya nufi ɗakinsa.
Koda ya shiga cikin ɗakin bai iya shiga wankan ba, saboda yadda yake jin kansa na sara masa,
dole ya nemi gefen gado ya zauna.
saida ya ji, kan nasa ya daina sarawar sannan ya miƙe ya shiga wankan.
Zaune ta kai a kujerar dake kusa da ita, abin duniya ya haɗe yayi mata yawa, damuwar T.J ma
kaɗai ta isheta, kai har ma da sauran yaran mata gaba ɗaya.
Biba ce taja tsaki da cewa "Kai ka jiyo can dai da mugun halinka". Ta faɗi cike da rashin kunya
kamar ba Yayan ta ba, ita fa Allah ya gani bata shiri da T.Jn dan baya ragawa kowa in ka cire
Momy.
Sadi da ke zaune gefen ta, tace "Kin ga Biba ki iya bakinki, dan kin san halinshi, wallahi kaɗan
daga aikinsa ya dawo yayi miki shegen duka, a tom ni dai ba ruwana, dan tashi ma zan yi daga
gurin balle ma ya gama dukan naki ya dawo kaina".
Sake jan tsaki Babir tayi, duk da tasan gaskiya ta faɗa "To ina ruwan ki?, ke dai ki je can da
wahalar ki, ke kika ga zaki iya, ta faɗi tana sake mai da kanta ga T.V da suke kallo.
Shiru Sadin tayi, dan tasan hakan ne, dan yadda ta mutu akan son Tijjani tasan ko kanta batai
wa hakan, shi kuwa baima san tana yi ba, wai kunu a wani gida.
Ita kuwa Momy tana zaune tana jin duk abinda suke cewar, ta daɗe da sanin irin son da Sadi ta
kewa Tijjanin, amma hakan tasan ba mai yuwuwa bane, dan zaren ba kalar yadin bane, tasan
ma ko sama take cizo mahaifiyar Sadiyan ba zata taɓa bari hakan ta faru ba, saboda
tsumammiyar tsamar dake tsakaninsu, tunda da ɗin su ƙawayene ita da mahaifiyar Sadiyan,
sanadiyyar wani abu daya gifta a tsakaninsu yasa sukai uwar watsi a tsakaninsu.
*Hajiya Turai*
Kwanaki biyu da yin wayar su da Hajiya Balaraba, ba tashirya tafiya EDO
tare da ƙawarta Itoro, da yake ita Itoron ƴar can ce.
Ita ma tayi mata hanyar Boka Kalgamu ɗin, sun shirya tafiya Edo a washegari, tunda zasu bi
jirgin da zai tashi ne, daga Kano zuwa Edo awashegarin.
Tun da sassafe ta tashi ta gama shirya wa saboda karsu ɓata lokaci.
Misalin 7:20am sai ga Itoro itama a shiryan ta, basu tsaya ɓata lokaci ba suka fito, a harabar
gidan suka iske drivern da zai kai su airfort ɗin, motar suka shiga ba tare da sun tsaya jinkirin
komai ba.
Shi kuwa driver mota ya bawa wuta suka fice daga cikin gidan, kai tsaye airfort ya wuce da su,
koda zuwan sun sun tarar an fara kiran fasinjojin jirgin, saboda holdaf ɗin daya riƙe su a hanya,
ba dan ma sunyi zagaye ta wasu unguwannin ba, da har yanzu ma suna can basu fita daga
cikin wannan ƙaddararran holdaf ɗin ba.
Babu jimawa ko jirgin ya tashi zuwa sararin subhana.
To su Hajiya Turai dake da ƴar rakiyar taki sai muce a sauka lafiya.
To meye kuma a tsakin Hajiya Balaraba da mahaifiyar Sadiya?
A she dai rikici bai ƙare ba, da alamun ma yanzu aka fara buga wasan
To dan jin yadda zata kaya mu haɗe daku a next page.
Likes and comments my lovely fans, ina yinku irin oba ɗin nan wallahi
*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/17, 7:15 AM] Abidah: *NAZBEER*
*Written by*
*ABEEDAH*✍️
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------
My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on
WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------
*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualites And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️
*PAGE*------ 6
Bismillahir Rahmanir Rahim.
*FLASH BACK*
Hajiya Mardiyya mahaifiyar su Sadiya da Anas, ƙanwa ce ga Alhaji Ahmad.
kuma kawar Hajiya Balaraba ce tun ta ƙuruciya, dan kuwa unguwar su ɗaya tare suka so.
Tun suna ƴan mata Allah ya jarabci Balaraba da matsancin son Ahmad yayan ƙawarta
Mardiyya, har kuma kawo yanzu da tayi aure har mijinta ya rasu soyayar Ahmad na maƙale a
zuciyarta.
Hakan yasa ta tuntuɓi amiyarta ta da maganar
Aikuwa Mardiyya tayi mata alƙawarin auren Ahmad, sosai Balaraba taji daɗin maganar.
Tun daka wannan rana Mardiyya ta shiga ƙoƙarin ganin ta shiga da Balaraba ga yayanta.
Shiko Ahmad bai ma san suna yi ba, dan tuni ya riga ya miƙa zuciyarsa ga matarsa Humaida,
kyakykyawar farar mace me zubin ƴan ƙasar Kalfonya, yana matuƙar sonta, kuma sosai yake
tarairayarta da bata kulawa, itama tana son abinta.
Ganinfa da Mardiyya tayi hankalin yayan nata baya kannƙawarta yasa ta shiga aibata Humaida
a gurin Hajiyarsu, tun Hajiya bata ɗauka har ta fara ɗaukar zancen na Mardiyya akan fa lallai
tsintacciyar mage bata mage, ta ina zasu amince a auro musu macen da ba'asan asalinta ba.
Wanan yasa Hajiya ta zaunar da Ahmada ta bashi zaɓi biyu akan ya zaɓi ɗaya a ciki.
*ALHAJI AHMAD*
Zaɓin da aka ba shi ba ko wanne zaɓi bane face.
ya zaɓi ɗaya a cikin biyu, kodai ya saki matar sa ko kuma ya auri Balaraba.
Ya shiga cikin tsaka mai wuya, dan kuwa yasan ba zai iya rabuwa da Humaida ba, hakama
bazai iya auren Balaraba ba.
Shi yasa ya nemi alfarmar iyayen nasu da subashi zuwa wani ɗan lokaci, zai nemi wata ya
aura, amma suka ce sam basu yarda ba.
Ganin har yanzu Ahmad yaƙi amincewa da auren Balaraba yasa mahaifiyar Balaraba, wato mai
ƙosai, wadda asalin sunan ta shine Talatu, sakamakon tayi Sai da ƙosai yasa ake kiran ta da
mai ƙosan, ta kai Balaraba ga Bokanta, Boka Darmuuje, ai kuwa Darmuuje yayi musu alƙawarin
wannan aure babu fashi, da haka hankalinsu ya kwanta.
Suko iyayen Ahmad suka birkice akan dole sai ya auri Balaraba, a cewarsu tunda a baya sun
barshi ya auri zaɓinsa to yanzu dole ya auri zaɓinsu.
Ba shida tawa mafitar dayawu ce ya auri Balaraba in dai yana son zama da matar sa farin cikin
sa, dole ya yiwa iyayen sa abinda suke so.
Koda yayi yiwa Humaida maganar zai ƙara aure bata wani tashi hankalinta ba, sai dai jin wacce
zai aura ɗin ya tada hankalinta, dan tasan Balaraba, tunda suka zo da Mardiyya gidan.
zauma yayi yai mata baya nin da zata fashimce shi, babu yadda ta iya face ta ba shi goyan
baya ya yiwa mahaifansa biyayya.
Anyi aure lafiya kuma amarya ta, tare a ɗakinta, dan kuwa bawani shagali ka aka yi ba, a
cewarsu tun da ba yara bane.
Bayan sati biyu da biki suna zaman su lafiya, kafin mahaifiyarta ta sake ɗora ta akan keken
ɓera, dan kuwa tunzuwan da sukai gurin Boka Darmuuje a lokacin auren Ahmad, bata sake
zuwa ba.
dan kuwa ita bata shiga gidan bane dan tafitar da Humaida ba.
Amma zigar da mahaifiyar ta da ta Mardiyya yasa ta, takoma, dan kuwa a lokacin Humaida
naɗauke da tsohon, kuma ganin maganarsu Mardiyya na kan hanya da suka ce da zarar
Humaida ta haifi namiji, to komai na Alhaji Ahmad Humaida ce zata shi.
Kuma a lokacin Mardiyya ta tayar da tsohuwar yarjejeniyar su, abinda mutane basu sani ba
shine, Balaraba da Mardiyya sunyi yarjejeniya akan idan Ahmad ya auri Balaraba to itama zata
sa Yayanta Abdussalam ya auri Mardiyyan.
Idanu Balaraba ta murje tace sam bata san da wannan yarjejeniyar ba, nan fa rikici ya kacame
tsakaninsu, nan fa kowa ga fahimci abinda suka ƙulla ɗin.
Duk yadda Mardiyya taso Yayan nata ya saki Balabara abin ya ci tura, dan ko Boka Darmuuje
tsaye yake akan aikin dake jikin Ahmad ɗin.
Wannan lamari yasa sukai rabuwar ba daɗi, amincinsu na shekaru ya rushe.
Wannan ne dalin da yasa Momi bata ganin auren Sadiya da Tijjani zai yuwu, ko da kuwa
Sadiyan zata mutu.
Bari mubi ƴan Edo
*EDO STATE*
Hajiya Turai, sun sauka a babban airfort ɗin dake birnin na Edo, wani me takzi ne ya ƙaraso
gurin da suke "Hajiya tafiya ne?". Ya faɗi yana ƙoƙarin ɗaukar jakar Hajiya Turai dake ajiye a
gefenta, "Eh". Motar suka shiga suna tafe Itoro na yi masa kwatancen unguwar.
Tafiya suke tayi kamar zasu sake barin gari, sai da su kazo wajen wani ƙaramin ƙauye sannan
naga an sake ɗaukar wata hanyar anan ma sunyi tafiya mai yawa kafin suka tsaya a gefen wani
rafi.
Shiko me mota sai faman zazzaga masifa yake, dan bai san haka tafiyar take ba, da bai ɗakko
su ba, suko ƙala kanzul ba su ce masa ba.
"Gaskiya Hajiya kuɗinku dubu talatin ne". Ya ƙara faɗi bayan ya dai-daita tsayuwar motar, "Dubu
talatin?". Itoro ta faɗi ido waje, wacce tafiya aka yi da zasu biya har dubu talatin?.
"Kinga Itoro rabu da shi". Hajiya Turai tayi maganar haɗi da saka hannunta a jaka ta ciro kuɗin
ta miƙa masa ba tare data irga ba, baki me motar ya washe ganin kuɗin.
Ruwan suka durfafa kai tsaye ba tare da ko tsoro ba, ko da yake zuciyar tasu ta riga ta taurare,
babu abin da zai basu tsoron.
Tafiya suka fara yi a cikin ruwan da yake da girma da tsayi, sun ɗauki kusan mintuna goma
kafin suka isa ƙarshensa.
Ajiyar zuciya me ƙarfi suka sauke suna duban makeken daji me ɗaike da manyan bishiyu masu
siffar ban tsoro dake gaban su, su Hajiya Turai ko ajikin su, dan kuwa haka suke ta ratsa wa'in
nan bishiyun.
Sun yi tafiya me ɗan tsayi kana suka isa bakin ƙaton dutsen da Boka Kagalmu ke zaune, dutse
ne me girman gaske ga kuma gefen dutsen an zane shi da wasu rubutu wanda daka gani zaka
gane na tsafi ne.
Mamaki ya cika Hajiya Turai ganin dutsen ya tsage hanya ta buɗe ɗoɗar, kai kace dama can da
ita, ita kuwa Itoro ko ajikinta, dan wannan ba baƙon abu bane a gurinta.
*DAKWA*
Inna ce ta kama hannuna muka wuce ciki dan yin sallar magariba, shima Baba masallaci ya tafi,
baidawo ba sai da a kai isha sannan ya dawo, abinci Inna ta kawo mai nima fitowa nayi na
zauna akusa da su muna ci, muna hira.
Ganin tara ta kusa na yi musu sallama na shige ɗaki don gobe da makaranta, kasa bacci na yi
sakamakon tarin abubuwan dake dan ƙare a zuciyata, na jima