Showing 12001 words to 15000 words out of 21648 words

Chapter 5 - NAZBEER Book Complete by Zainab Laminu Sani Abeedah.pdf

ita Itoro kiristance. Amma ita ma bata yi ba
kawai kwanciyarta ta yi sai bacci.


Ba ita ta farka ba sai da rana ta fara shigar mata ido, kafin ta miƙe zumbur kamar wadda aka
tsunkuna, Itoro ta tambaya yanzu k'arfe na wane?, kallon ta ta yi ta ce "Ai lokaci bai wuce ba,
saura minti talatin yanzu tara da rabi ta yi". Wanka ta shiga bayan ta gama jin bayanin na Itoro.


A gurguje suka ƙarasa shiryawa kafin suka fito, me tasi ɗin da zai kai su airfort suka ɗauka,
gaf ko da jidgi zai ta shi suka isa, dan haka ba ɓata lokaci suka shige sai Abuja.

Kada suka sauka sun iske direban Hajiya Turai yana jiran su, kawai shiga sukai sai gida, a
farkon layi aka sauke Itoro, ita kuma aka wuce da ita can gidan ta.


Tana shiga Baby ta taso da gudu ta rungumeta da faɗin "Momy oyoyoo, momy nayi missing
ɗinki". "Ni ma haka Babyna, yanzu dai bari na shiga naɗan huta, dan na gaji sosai". Ta ƙarasa
maganar ta na janye Babyn daka jikinta, "Okay Momy, sai kin fito".

*ABIDA*

Bayan fitar Inna, kayana na cire na ɗaura zani na fito na shiga wanka, ina fitowa na tarar Inna
har ta ajiye min abinci, shiryawa na sake yi cikin kayan islamiyyata,kalar blue.

Abincin na ɗauka na fara ci, jifa-jifa muna hira da Inna dake zaune a bakin murhu, hannu na
wanko bayan na gama cin abincin na zura gijabina har ƙasa sannan na ɗauki jakata na yiwa
Inna sallama na fice, ba tare dana yiwa sauran ƴan gidan magana ba, dan du ƴan ganin dama
ne, sai sun gama dama suke zuwa uslamiyyar, shi yasa ma bana wahalar da kaina wajen biya
musu.


Gidan su Amina na shiga ina ko zuwa na tarar ta shirya, gaisawa mukai da Mamanta dake

tsakar gidan tana tankaɗe, da kulawa ta amsani, haɗi da tambayar Inna, "Tana nan lafiya
ƙalau". "Ya jikin Ammin taki?". Ta ƙara tambayata, ido na lumshe jin Mama ta taɓomin
indabyake min ƙaiƙayi, dan rabonta da Ammin tun ranar bata sake zuwa ba,amma gobe in Allah
ya yarda zan je nadubata, da wannan zancan zucin suka fito da ita da Amina suka wuce
islamiyyar su, dan bata da nisa daga gidan su Aminar, suna zuwa ajinsu, suka wuce, dan kuwa
sunyi sauka tun a watan biyun nan da ya wuce, dan kuwa akusan ƙarshensa suka yi, ranar
25/2/2025 suka yi saukar, yanzu sun juya hadda ne da sauran littattafan da basu ƙarasa ba.

Shiga su kai suka tarar sauran ƴan group ɗin su, duk sun zo suna shiga ajin ya ƙara hautsinewa
da surutun su, dan kuwa Abida ba daka baya ba agurin surutu, amma in aka zo ɓangaren
karatu, to a nan ma ƴar ba sauƙi ce, dan kuwa tana mai da hankali a karatun ta, daga na bokon
har islamiyya, sai dai tafi bawa karatun addinin ta mahimmanci, dan kuwa su duka ajin antara
zaƙaƙurai ne, haka suka cigaba da shirar su, har malamin su ya shigo, karatu suka fara, har
sauran malaman nasu, kuma kowa ya gabatar da nasa karatun kamar yadda ya ke atsarin
makarantar, ƙarfe shida na yamma suka tashi,

tare suka fito su duka group ɗin nasu, dan haka suke kullum sai dai kowacce idan aka zo layin
gidan su, sai suyi sallama ta wuce, sukuma su cigaba da tafiyar su dan ko sune ƙarshen shiga
gida dan ko ita sai tasauke Amina agidan su, kafin itama tawuce nasu gidan.


Da sallama na shiga wajen mu, Inna na tarar tana alwalar sallar magariba kallona ta yi tace
"Har kin dawo?". Amsa ta nayi, ina shiga cikin ɗakin kayan makarantar na cire kawai nima na
fito dan yin alawar, ɗaki na shige bayan na gama, salla na kabbara na shiga ganawa da
mahaliccina.

Ina idarwa kuwa na fito dan jin maganar Baba, ledar hannun shi na karɓa ina yimai sannu da
zuwa amsamin yayi da kulawa haɗi da samin albarka, wucewa ɗakin Inna Salame ya yi, dan
yau a can yake, sai da yayi wanka kafin aka shimfiɗa babbar tabarma, dan ƙa'ida ne in dai
abincin dare ne to, tare ake haɗuwa aci, dan da tare ake haɗa ma abinci da Sakina, amma
uwarta ta ce baza ta yarda ba, sai dai a rabawa kowa kwanon sa.

Gudun fitina Inna ta cewa Baba a raba mana kwanon kawai, haka kuwa aka yi.

Zama nai a inda na saba zama na fara cin abincin, cikin natsuwa, Sakina na gefena, tana latsa
wayarta me madannai.

Kai kace wata waya ce babba, dan ranar da aka kawo mata Inna Salame yini ta yi tana
habaice-habaice akan ƴarta tayi goshi, wasu ko a haka zasu ƙare a gida a zaune babu
mashinshini, duk da Inna tasan da ni take amma bata ko ɗaga kai ta kalle taba, harta ƙaraci
baƙaƙen maganganunta ta gaji.

Wayar hannunta aka kira murmushi ta saki, kafin ta ɗaga wayar, ta fara magana ƙasa-ƙasa,
dan ko ni da nake kusa da ita bana jin abinda take cewa, balle su Inna da suke can gefe ɗaya.

Dan su tare suke cin abinci da su da Baba, duk yadda Inna Salame ta so ta hana cin wannan
abincin tare, hakan ya gagara, dan Baba tsayayen namiji ne a gidan sa, amma ba dan haka to
da Inna Salame juya shi zata rinƙa yi.

Wayarta ta cigaba da yi cike da nishaɗi harna gama cin abinci na, bata gama wayar ba, sai ma
tashi da ta yi ta shige ɗakin su, ni kuwa littattafaina na islamiyya na ɗakko.

Na fara duba karatun mu na yau, in da bangane sai naja fansul saboda karna manta inna je
gobe sai na tambayi ko Amina kowasu daga cikin ƴan ajin namu.
in basu sani ba kuma sai mubari sai Malam yazo sai mutambaye shi.

Inna ce ta kira sunana a hankali "Abida". kai na ɗago na kalli Innar, "Ki ta shi kije ki kwanta dare
yayi fa". Da "To". Na amsa kana na shiga tattare kayana, a jaka na zuba na shige ɗaki ina yiwa
Inna sai da safe.

Shirin kwanciya na yi haye gado sai bacci.










Yanzu fa aka fara wasan, mu haɗe daku a next page don jin yadda zata kaya.




Likes and cimments my fans, ina yin ku oba wallahi



*Taku*
*Abeedah*✍️
[5/22, 8:22 AM] Abidah: *NAZBEER*


*Written by*
*ABEEDAH*✍️



Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/J9oI2KlySOW3LbV89O51aJ
----------------------------------------

My channel
Follow the NAZBEER FANS CLUB channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029VbAxsXB7IUYWz4OBH713
----------------------------------------
Follow me on telegram

https://t.me/+3USo7e9asLpmNzc0
_________________________

*FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*
(*Home of Qualities And Trusted writer's of the Nation)*☀️☀️☀️



*PAGE--------9*

Bismillahir Rahmanir Rahim.


Washegari kamar jiya Baba ne ya ta sheni da asuba, dan shi yake tashin mun da asuba ɗin,
yauma tsaye ya yi a kaina har sai da yaga na tashi na fita yin alwala kana shi kuma ya wuce
masallaci, alwala naɗaura kafin na shiga ɗaki na tada sallah.

Kamar jiya ban koma bacci ba wanka nayi sannan nayi shirin makaranta, sai da nagama
shirina tsaf, kafin na ɗakko takalmi da jaka ta sai safa da hijabina, na fito gurin Inna dake zaune
tana fifitamin abin karina, zama na yi ina gaida ita.


Amsa min ta yi tana miƙo min abincin da ya yi sanyi yadda zan iya ci.
godiya na yi mata na fara cin abincin a natse, safata da takalmi na saka kana na goya jakata na
yiwa Inna sallama na fice.

Kamar jiya na tarar dasu duk sun shirya, ficewa mu kai daga gidan mu duka huɗun, a tare muka
jera muna tafiya har makaranta, muna zuwa muka tarar za'a fara taron latti ke nan, Sakina ce ta
ce "Kai Allah ya taimake mu". Dan kuwa muna zuwa a kace mu wuce, ajiyar zuciya muka shiga
saukewa, da sauri muka ƙarasa shiga cikin makarantar.
Kowa ajinsu suka wuce nima dani da Sakina ajin muka wuce, muna shiga kowa ya nufi gurin
zaman sa, a gurin zamana dake gaba na zauna.


Ina gama zama sai ga Malamin da muke da shi na farko ya shigo, karatu ya yi mana sosai kafin
ya fita, Malamai, huɗu ne suka, ƙara shigowa bayan sa, kafin ayi birek, jakata na ɗauka na fita,
zuwa nayi na siyo abinda nake so na dawo aji, ban ƙara fita ba har sai da aka ta shi, a hankalin
na ke fitowa daga ajin na nufi bakin get dan a can muke haɗuwa mu wuce gida.

Tafiya muke ba wanda yake cewa komai da haka har muka kai gida sallama mu kai muna shiga
cikin gidan, ido muka haɗa da Inna Laure wata muguwar harara tai min, da tasani dole na yi
ƙasa da ido na, baki ta buɗe zata fara magana, na yi sauri na shige wajen mu dan na san duk
abinda zai fito daga bakin ta akaina to bamai daɗi ba ne.

Inna da taganni na shigo kamar an koro ni, ta ɗaga kai ta dubeni tace "Lafiya ki ka shigo da
gudu". Idona ne ya kawo ruwa, na ce mata Inna Laure ce, kai ta jijjiga tace "To ya isa, bar
kukan haka, wuce kije ki cire kayan ki, kizo kici abincin sai kiyi wanka". "To". Nace mata
sannan na wuce na yi duk abinda ta umarceni.

Sai da na fara cire kayana kafin na zauna na ci abincin, sannan naje na yi wanka sai da na fito
na dubi Inna na ce "Inna zan je na dubo Ammita, yanzu idan na gama shiryawa". "To ma za ki
gama".

Ɗaaki na shige cike da farin ciki, da hanzari na gama shiryawa na fito, "Inna na gama shiryawa
zan tafi". "To a dawo lafiya ki gaida min da su, kwana biyu ban je na dubata ba, Amma in Allah
ya yarda zan je na dubota a satin nan".
"To Inna zasu ji". "Sai na dawo ni". Na faɗi ina fita daga gidan.

Hanyar da zata sadani da gidan Malam na nufa, a hankali nake tafiya har na isa layin gidan
Malam ɗin, wuce wasu samari dake zama a layin gidan Malam ɗin na yi, dan kullum idan zan
wuce ta gurin su ina jin maganar da suke a kaina, shi yasa ma bana yadda na cika kaiwa
yamma a gidan Malam, dan nasan yadda layin nan ba shida mutane sosai, dan kuwa sabuwar
unguwa ce wadda kangwaye suka fi yawa, dan duk yawan cin su amfara ginawa ne ba kuma a
ƙarasa ba.

Dan wa'innan samari da babu Allah a ran su tsaf zasu aikata min abinda ransu yake so.

Ɗaya ne daga cikin su ya taso zuwa inda ne, ni kuwa gabana banda faɗuwa babu abinda ya ke
yi, ina ta karanta duk addu'ar da tazo min baki na, a gabana ya tsaya "Ƴammata jimana,
gabana na faɗuwa na ɗago kaina na kalle shi, zai yi magana ke nan sai ga Malam a mashin
ɗinsa, tsayawa ya yi, ya kalli wannan saurayin "Ya aka yi ne? ko wani abu ta yi maka ne?".
Kai ya girgiza, Malam yace "Ai na zata ko wani abu ta yi maka".
kallona ya yi yace "Hau mu tafi". Aiko da sauri na hau bayan mashin ɗin, shi kuma ya ja muka
tafi, a hanya muna tafiya ya ke cemin na yi hankali da samarin nan, dan ba imani garesu ba,
dan su ci zarafin mace ba komai bane a gurinsu, kuma babu wanda zai iya yi musu komai,
tunda iyayensu sun ɗaure musu ƙugu.

Da haka muka ƙarasa gida, muna zuwa na sauka na shiga cikin gidan, da sallama matar sa ce
Mama Maryam ta leƙo "Au dama ke ce a gidan namu yau?". Dariya nayi na ce "Eh Mama
wallahi ni ce".


Murmushi ita ma ta yi tace "To ma sha Allah, ki ƙarasa ta na ciki". Shiga na yi da sallama,
kamar kullum tana zaune taƙurawa waje ɗaya ido, zama na yi a kusa da ita ina kama hannun
ta a cikin nawa.
*NAZBEER*

wanka yayi sannan ya fito, ɗaure da tawul a ƙugun shi, hannunsa riƙe da wani ya na tsane
ruwan jikinsa.

jin wayarsa tana baburetin ya sa shi kai kallon sa kan wayar dan ganin me kiransa a irin
wannan lokacin, duk da kuwa yasan ba zai wuce Khalil ko abbu ba, ai kuwa hasashen sa ya
zama gaskiya dan kuwa abbu ne ke kiran wayarta sa, sai da ya ja ɗan ƙaramin tsaki tare da,
dafe kansa da yake sara masa kaɗan-kaɗan.
Hannu ya kai ya ɗauki wayar da har ta tsinke, kikaran ya bi, ai ko bugu ɗaya aka ɗaga, daga
can abbu ya ce "wai baka dawo gidan bane?, tun ɗazu fa kasan kai nake zaman jira, don ina
so naje na kwanta amma ka barni a nan azaune ina zaman jiran ka".


A hankali kamar me tsoron magana ya furta "Gani nan zuwa". ya na ajiye wayar, mai ya shiga
shafawa a lallausar fatarsa da hutu da jin daɗi ya bayyana a jiki, sai da ya gama shafe-shafen
sa, kafin ya ƙarasa jikin wadrof ɗin ɗakin da tacinye bango guda, kayan bacci masu taushi kalar
ruwan sararin samaniya, marasa nauyi ya ɗakko turare ya feshesu da shi, kafin ya saka, sun yi
matuƙar kyau dan kuwa kaya ko ba kwalliya ya saka suba, suna amsar jikin shi sosai, silifas, ya

saka shima kalar kayan, wayarsa kawai ya ɗauka ya fita daga ɗakin.

Fita ya yi gaba ɗaya daga sashen na shi, ya nufi sashen iyayen nasa, ya ɗan yi tafiya mai ɗan
nisa kafin ya isa sashen iyayen nasa dan akwai tazara me ɗan yawa a tsakanin kowanne
sashe, kafin ka iske wani.


Sallama ya yi ciki-ciki, yana shiga cikin falon, Abbu ne ya amsa mai da yake zaune yana zaman
jiran nasa, kujerar kusa da Abbun ya kai zaune ya na gaida shi, amsa mass ya yi ya na
tambayarsa aiki, fuska ya ɗan yatsine "Abbu ba daɗi". Ɗan murmushi Abbun ya yi irin nasu na
manya yana cewa, "Haba dai, tun yanzu ma da babu nauyin kowa akan ka, kace haka ina ga
mata da yara sun ƙaru?". Abbun ya yi maganar fuskarsa da murmushi, fuska ya ƙara haɗewa,
murmushi Abbun ya sake yi, da yasan ɗan nasa baya son a nai masa maganar aure.


Ganin yadda yake sake haɗe fuska ya saka Abbun shima ya koma siriyos, magana ya fara yiwa
Nazbeer ɗin, akan ciwon mahaifiyarsa, saboda sunyi magana da Malam Sani, tun da shi an
gwada nashi ba'a dace ba, shine ya bada shawarar, akan kozasu jaraba zuwa gurin wani
mutum da yake a ƙasar TOGO ko za'a dace.
Nisawa ya ɗan yi ya ce "Dama gobe nima nake shirin zamu je gidan nasa da ni da Khalil, amma
zuwa yaushe za'a tafi ɗin?".

Abbu ya ce "Ehh, tom, Malam yace yanzu shi mutumin ya je umara ne, amma idan ya dawo zai
faɗa min sai musa lokaci ɗaya daga cikin mu sai ya je tun da Malam yace ba'a zuwa da mara
lafiyar sai dai wakilin shi mara lafiyar ya je, sai in abun ya yi tsananine to sai azo da shi mara
lafiyar daga baya.

"Ok". Kawai yace wa Abbun tare da cewa "Allah ya dawo da shi lafiya".
"Ameen". Abbu yace, "Yanzu goben zaka je gidan Malam ɗin?". "Eh haka nake so in Allah ya
yarda". "Allah ya kai mu hakamma yana da kyau ai".


Tashi ya yi ya na yiwa Abbu sai da safe "Mu tashi lafiya". Abbun yace da shi.
Hajiya shuwa da ke laɓe a jikin ƙafar bene ta yi sauri shigewa ɗakin ta, jin Abbun ya nufo
saman, tana shigewa ta fara kai kawo a tsakiyar ɗakin, wata dirowa ta buɗe ta ɗakko wata
ƙaramar waya, kai kace ma tawasa ce, saƙo ta tura da bai wuce kalma goma zuwa ashirin ba.
saurin maida wayar ta yi a inda ta ɗakko ta.


Gefen gado ta samu ta zauna tana ƙurawa wayar hannun ta ido, kamar yadda ko wanne sakon
da minti suke bugawa, to suna bugawa ne tare da zuciyar ta.

zabura ta yi dan ganin wayar hannun ta ta kawo haske alamun shigowar saƙo, da sauri ta buɗe
tana fatan ganin saƙon da take zaman jira, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke saboda
cinkaro da saƙon da take zaman jira, da hanzari ta buɗe tana karanta abinda saƙon ya ƙunsa
rubutu ne da baiwuce layi ɗaya ba.
GOBE MISALIN ƘARFE HUƊU NA YAMMA.

Abinda saƙon ya ƙunsu kenan.
shirin bacci ta fara dan yanzu kam hankalin ta ya kwanta, shiryawa ta gama yi tsaf, ta fito tana
ta baza ƙamshi, ɗakin mijin nasu tawuce, dan shi haka ƙa'idar shi take, sai dai mace ta je ɗakin
shi ranar kwanan ta.

To yanzu ma baraba kwanan yake ba tun da ita Ummi bata da lafiya, sai dai Hajiya shuwa, dan
kuwa ita ke ta baza mulkin ta son ranta.


shiga cikn ɗakin ta yi zaune ta same shi a gefen gado ya tafe kansa, zama tayi cike da kissa ta
fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login