Showing 3001 words to 6000 words out of 23360 words
A wannan shekaran na taso da wani irin hatsabibanci,duk nabi na addabi kowa a gidan, don
duk wanda yayi ma Ammyna rashin mutunci ni ma sai na yi masa, don har Alhaji ban raga
mawa, hakan ya jawo mun tsana a wurin 'yan gidan especially Yayyina maza da yayyina mata
da sukayi aure,Don duk wacce tazo tayi ma Ammyna rashin kunya, nima kafin ta tafi sai na yi
mata wanda yafi nata,hakan ba karamin duka yake jawo mun ba musamman wurin Alhaji da
Yaya Farooq wanda shine ya kasance babba a gidan bayan auren Yaya Baffa.Duk sanda ko
ake dukana Ammyna da Asma'u zasu shiga daki suyi ta kuka, saboda yanda suke zage karfi su
dakeni zaka dauka wani Gardi suke duka,haka zasu min likis, amma haka bashi zai hana in ka
ma Ammyna ko Asma'u da kannina wani abun ni ma in karta maka nawa Rashin Mutunci.
Aikuwa wata rana fada ya hada Ammyna da Ummy, sai Yaya Farooq ya shiga ma Ummy yayi ta
zagin Ammyna,a lokacin da abun ya faru ina school,ina dawowa na kira Almajirinmu na
tambaye shi mai ya faru da bana nan,don naga idon Ammy yayi jawur alamun taci kuka,aiko ya
kwashe ya fadamun(dama indai na dawo naga Ammyna a wani yanayi, Almajirinmu nake
tambaya don nasan ita ko Asma'u baza su sanar dani ba, saboda sanin bana yafiya).
A Hankali na shiga part din Mazan gidan,nan na hango Yaya Farooq yana wanki,ga Radion shi
a gefe yana shan disco,wata bishiya na samu na make ina kallonsa,lura da nayi Manyan kaya
yake Wankewa ya tunasar dani washegari zasu je Nadin Sarauta Kudan(kakana yayi murabus
ya bama Kanninsa saboda rashin lafiyar da yake fama da shi da kuma maida Aurensa da Za ayi
da Hajiya Kaka),Aiko nan farin ciki ya rufeni don na samu hanyar da zan Rama ma Ammyna
zagin da yayi mata,Shigowar Yaya Ibrahim ne ta katse mun tunani,inaji ya na cema Yaya
Farooq wai sabon kaya ne yake wankewa,shi kuma ya bashi amsa da Kyamar kayan yake yi
Saboda ya dade a wurin Tailor,dariya Kawai Yaya Ibrahim yayi ya ajiye Bucket ya fita,Ina nan
make har Yaya Farooq ya gama wankinshi ya shanya ya fita, sai dana kara kamar 5minutes
sannan na fito daga maboyata,kitchen na nufa direct naje na dauko Almakashi,Wurin kayansa
na nufa na ciro su a Igiya na samu kayan nan na yankasu kuci2 da Almakashi na zubar mai a
wurin na kama gabana,dakinmu na nufa nayi kwanciyata a Gadon Ammy nayi baccina.
Cikin bacci naji an kwada min mari wanda zafinshi ya sani sakin fitsarin da ban shiryaba,haka
ya jani ya fita dani harabar gidan ya jefar dani gaban kayan dana yanka,daka mun tsawa yayi
tare da tambayata wa ya yanka kayannan ya karashe tambayar yana nuna min kayan dake
gabana,bakina na rawa na amsa mai da ni ce,saboda wani tsoronshi da ya dirar mu a zuciya
ban shiryaba,zare belt yayi ya shiga jibgata,ni Kuma ina ihu,ihuna ne yayi raising din Alarm din
da kowa sai da fito har da Ammyna dake Kitchen,duk taron yawan gidanmu an rasa mai kwata
ta a wurin Yaya Farooq,haka ya ringa jibgata sai da yaga na dena motsi tukunna ya yarda belt
din,da gudu Ammy da Asma'u sukayo kaina suna girgizani,amma ina ba labari,Ammy ce ta
kwala ihu tare da Fadin "shikenan Farooq ka kashe min ita,wallahi bazan yarda ba,ke Asma'u
miko min Hijab dina in kaita wurin Hajiya".da gudu Asma'u ta shiga daki ta dauko mata Hijabi ta
saka,haka ta ciccibeni ta goya ni a bayanta tayi hanyar gate din gidan,tana fita suka ci karo da
Alhaji ya dawo daga masallaci,ko kallonsa batayi ba ta rabashi ta wuce,shi kuma ganina goye a
bayanta ga Asma'u na binmu yasa shi rufa mana baya.
A kusan tare muka shiga gidan Hajiya tawa,kukan da ammy take yine yasa Hajiya fitowa da
sauri zani a hannu tana tambayar lafiya,shimfideni tayi tare da fadin "shike nan Farooq ya
kashemun ita",salati Hajiya ta dauka tare da fadin"garin yaya?", babu wanda ya bata amsa
tsakanin Alhaji,ammy da Asma'u,ganin baza ta samu amsa bane yasa ta maida hankalinta
kaina,ganin alamun suma nayi yasa ta shiga daki da hanzari ta debo ruwa a fridge ta zo ta
watsamin,sauke ajiyar zuciya nayi hade da fashewa da kuka,rungume ni Ammy tayi a jikinta
itama tana kuka,ba wanda yace hanamu,sai da muka yi shiru don kanmu,sannan Hajiya ta
nemi sanin dalili,nan Asma'u ta fada mata abunda ta sani,juyo wa tayi ta tambayen mai nayi
masa nan na kwashe na fada mata,aiko nan ta hau sirfamin zagi sai da tayi mai isarta sannan
ta koma kan Alhaji,shima ta zageshi tas,sannan tace mu tashi muje Gida gatanan zuwa
itama,da taimakon Ammy na mike don duk jikina a fashe yake,don na daku.
Isarmu gida mu ka tarar da duk ' yan gidan a harabar gida,kallonsu kawai zakayi kasan suna
cikin tashin hankali,ganin shigowarmu yasa duk sukayo kanmu har da uban gayyar(Yaya
Farooq),duk jikinsu a sanyaye,suna mana magana amma ba wanda muka tanka,ana cikin haka
Hajiya ta karaso ko zama batayi ba ta fara surfa bala'i,sai da ta zage kowa tas,sannan tace duk
ranar da wani ya kuma dukana koda Ammy ce bata yafe ba, tace ma yaya Farooq ya biyota
gida, ta fice daga gidan.
Haka Ammy ta dafa ruwan zafi ruwan zafi ta Gasa mun jiki,sannan nasha ruwan Lipton da
paracetamol na kwanta.basan ya aka kare ba tsakanin Hajiya da yaya Farooq,na ga dai da safe
Ummy ta hada kaya ta tafi kano da sunan yaji(abun kunya tsofai2 da ita).
*Fateeyzah* ν ½νΆν ½νΆ
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*( _Burunmu mu fad'akar, mu nishad'antar, mu wa'azantar da al'umma)_*
*GIDAN NAGOGGO*ν ΌνΏ¨
*_A true life story_*
*_Written by fateeyzah_*ν ½νΈν ½νΈ
*_Wannan page din Nakune_ HIKIMA WRITERS _Allah ya kara basira da daukaka_*
*Bismillahir rahmanir rahim*
_Page_ 0β£9β£&1β£0β£
Haka su Alhaji suka tafi suka bar Yaya Farooq,saboda bashi da manyan kayan da zai saka,
kasancewa duk kayansa Jeans ne da T_shirt ne.
Kwana biyu na dauka ina jinyar jikina saboda ba karamar illa Yaya Farooq yamin ba,godiyar
Allah ma weekends ne babu school.
Sai da Ummy tayi sati daya tukunna Mahaifinta ya dawo da ita,don ba yanda Ammy batayi da
Alhaji ba akan yayo bikonta,shikuma ya dage bazai jeba tunda bashi yace ta tafi ba, ita ta tafi da
kanta,gaskiya a cikin satin da Ummy tayi bata gidan ba karamin wata yawa mukayi ba,su kuma
'ya'yanta ina lura duk a takure suke.
Bayan Wata biyu,Yaya Farooq ya samu soja ya tafi,a lokacin ba karamin dadi naji ba don na
lura duk cikin yaran Ummy yafi kowa tsanata,A dai dai lokacine kuma Tasi'u ya samu admission
a A.B.U zaria(Tasi'u kani yake wurin Alhaji don da Babanshi da kakanmu Alh Akilu 'Ya'yan mata
suke),anan Gidan Hajiya Kaka aka Bashi daki,kasancewa duk 'yan uwan da yazo karatu daga
Kudan Gidan Hajiya Kaka suke zama har su gama,daki guda ake ware musu kusa da dakin
Aunty Amina(inba ku mantaba itace babbar 'ya wurin Alhaji kuma ita ke auren Babban d'an
Hajiyar Sokoto,Yaya Kabeer,kasance wa auren Zumunci ne sai Alhaji ya basu daki anan gidan
Hajiya),shima nan Tasi'u ya zauna, wanda ni nake kaimai abinci Don Alhaji yace kwanonshi
yana dakin Ammy ne.
A wannan shekarar abubuwa sun faru da yawa,ciki harda aurar dasu Aunty Asma'u,Aunty
Fatima da Aunty Khadija,wanda Aunty Asma'u ta auri Suleiman(Yaron Alhaji ne da yake jamai
Trailer Zuwa Lagos),aka kaita dan gaba da Gidanmi don nan Mijinta ya gina gida,Aunty Fatima
kuwa ta auri Salihu,shikuma yana aiki ne a Embassy na Egypt,Ita kuma Anguwan k'aya aka
kaita kafin su wuce can Egypt din,Aunty Khadija kuma auren zumunci aka mata da Yaya
Al'amin ('yan Hajiyar Sokoto)can Sokoto aka ajiyeta Gidan Hajiya.
Bayan Bikinsu ne kuma da Wata Biyu,Allah yayi wa Hajiya Kaka rasuwa(Allah ya
jikanta),Rasuwarta ta girgiza mu especially 'yan dakinmu da'ya'yan Hajiyar Sokoto(duk ita ta
rikesu,su biyar,har aurensu),aka raba gado,kowa ya watse.
Bayan wasu watanni aka yi passing out don Yaya Farooq,wanda ya fito da mikamin second
Lieutenant,Anyi POP da sati biyu aka daura mishi aure da Aunty Zeenatu,shi ma dai auren
zumunci ne don da Babanta da Alhaji cousin ne,wannan bikin ne akayi biki da ba a taba yi a
*GIDAN NAGOGGO* ba,don sai da akayi event kusan hudu da kuma crossing of
sword,tukunna aka dauko Amarya daga Kaduna aka kawo ta nan Gidan Hajiya Kaka(ta gaban
gidan Alhaji ya fitar mai da part dinsa kuma yace ya mallakamai wurin).
Haka rayuwa taci gaba da tafiya watarana Farin ciki ko bakin ciki,wanda bakin cikin yafi
yawa.Acikin Shekarun nan an hayayyafa sannan anyi Rashi,wanda har da Alhaji Kaka da Allah
ya mai rasuwa.
Acikin shekarar da na gama School,Abubuwa marasa kyau sun faru,daga ciki akwai Rikicin da
ya faru tsakanin mijin Aunty Asma'u da Alhaji,inda Alhaji yace yana cutarshi bai kawo mai
balance da yawa,shi kuma yace motor na bashi matsala,kudin na Tafiya a gyaran motor,Haka
Alhaji ya rufe idoshi ya karta mai rashin mutunci kamar ba Sirikinshi ba,kuma daga baya ya
karbe motarsa,Dalilin haka har auren Aunty Asma'u ya kusa mutuwa,Allah dai ya taimaka suka
samu masalah.
Yaya Al'amin Mijin Aunty Khadija kuma ya kara aure,inda suka yi ta samun matsala
tsakaninsu,har dai ya saketa,ita kuma ta aje mai Jariri dan wata biyu ta tawo Gida,ba tare da
Alhaji ya tsaya yabi ba'asi ba yace ta fitar mai gida Bashii bata,kuma yace in Yaya Al'amin ya
maida ita gidanshi,shima sun raba Hanya kuma sai ya tsine mata, ya kuma hana a bata d'anta
haka Alhaji ya raba Jariri d'an wata biyu,haka tattara ta koma Dagin Mahaifiyarta.
A shekarar ne kuma Tasi'u ya gama degree ya tafi services,ni kuma na ci gaba da zaman
gida,saboda Alhaji baya bari mu shiga university sai munyi aure,shima sai mijinki ya barki.Haka
na kara wata shekara a gida ba tare da na samu miji ba,don Alhaji ba bari yake in fita ba.
Bayan Tasi'u ya gama service ne ya samu aiki a wani filling station a Lagos,wanda aka bashi
matsayin manager,a lokacine Sarki (sarkin kudan) yace yazo gidan mu ya zabi mata,yana zuwa
aka tura mu wurinshi ni da Halima muka gaisheshi,bayan ya tafi ne yaje ya sanar da sarki ya
zabeni,shikuma ya Sanar da Alhaji,nan ko Halima tayi ta murna don dama ita da wanda take
so,nan muka fara soyayya da Tasi'u ba a dauki dogon lokaci ba aka daura mani aure
dashi,Halima kuma da Salis saurayinta.
Nan Alhaji yace tunda ba dani zai tafi Lagos ba, ba sai ya kama hayaba,nan muma ya bamu
daki a gidan Hajiya Kaka.
Ya zaman zai kasance tsakaninmu:
Aunty Amina
Yaya Farooq(abokin fadana)
Ga kuma ni Bahijjah.
Karku manta dukkanmu 'ya'yan Alhaji NAGOGGO ne,sai mun hadu a next page.
*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*
*Fateeyzah* ν ½νΆ
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(Burinmu mu fad'akar,mu nishad'antar,mu wa'azantar da al'umma)_*
*GIDAN NAGOGGO*ν ΌνΏ¨
*_( A true life story)_*
*_Written by fateeyzah*ν ½νΈ_
_Bismillahir rahmanir rahim_
*_Page_* 1β£1β£
Tunda aka daura aurena na tsinci kaina a cikin farin cikin samu FREEDOM,ta wani 'bangaren
ina bakin cikin rabuwa da Ammy da Kannina.
Ammy ko tana can bedroom tana Kukan tausayina,don a ganinta ba a rabu da bukar bane an
samu habu,domin an aurar da nine,amma har yanxu ban bar *GIDAN* *NAGOGGO* ba.
Karfe hudu nayi Alhaji ya umurci su Yaya Amina a fara shirya Amare domin karfe biyar yake so
kowacce ya danka ma mijinta(yana daga cikin Al'adar *GIDAN* *NAGOGGO*,duk yarinyar da
aka ma aure Alhaji dakanshi zai kai ki dakin miji,zai hadaki da kanniki maza sune 'yan rakiya).
Bayan an gama shiryamu ne aka fara kaimu wurin Ummy don yi mana fada,daga nan kuma aka
wuce damu dakin Ammy,nan ma dai fadan ta mana,sannan aka wuce damu palourn
Alhaji,gyaran murya Alhaji yayi tare da kiran sunanmu"Halima,Bahijja"bai jira amsawarmu ba
yaci gaba"Allah ya kawo mu yau na sauke nauyinku da ya rataya akaina,ba wata doguwar
magana zanyi ba,don nasan duk abunda zan fadi,iyayenku mata da 'yan uwa sun fada
muku,abinda zan tunatar daku kusan Gidan nan ba a yaji(barkonoν Ύν΄ͺ),duk abunda ya hada ku
da mazagenku Ku ringa hakuri ba wai ku kwaso 'kafa ku tawo gida,don bazan dauka ba,sannan
ke Bahijja(ya nuno ni da yatsa)ki kiyayeni wallahi in naji ance kiyi ma Amina ko Zeenatu wata
rashin kunya wallahi zanyi mummunar sa'ba miki,kibar ganin wai yanxu da aurenki,zan iya zuwa
har dakinki in zane ki,don Amina ya isa ta haifeki,kina da shekara biyu a duniya aka mata
aure,don haka ki kiyaye,ku tashi muje Allah ya muku Albarka,yasa ku shiga dakin miji a sa'a.
Halima muka fara kaiwa gidan ta dake Tudun wada kasancewa ita ce karama,muna zuwa Alhaji
ya kira mijinta a waya,ya damka mai matarshi,sannan muka juyo muka dawo,Alhaji da kanshi ya
rike mun hannu ya kaini har cikin dakina,sannan ya tafi ya barni,bude idona nayi na kare ma
dakin kallo,ba laifi,Dakin ya tsaru.Gab da Sallar magariba sai ga su Aunty mamy, Aunty
Amina,Aunty Zeena da Aunty Asma'u sunzo,suka kara gyara dakin,sannan suka sani inyi
wanka, in dauro Alwala,anan ne nace musu banda tsarki sai zuwa gobe zanyi wanka,Nan Aunty
Mamy ta kwashe da tariya tare da fadin "lallai bahijjah kina ruwa".haka dai suka karasa gyaran
daki tare
da mun 'yan nasihohi,suka mana bankwana ni da su Aunty Amina suka tafi.
Bayan sallar Isha'i Aunty Amina da Aunty Zeena suka mun sallama kawacce tayi dakinta.
Sai wurin karfe tara tukunna Tasi'u ya shigo,sai ya umurceni da in tashi muyi nafila,ina dan
nokewa na Sanar dashi ban da tsarki,muka dan yi ciye ciyen mu muka kwanta.
Washe gari na wuni ina ta karban baki 'yan ganin amarya,wurin la'asar na yi tsarki,a daren
ranar Tasi'u ya maidani cikakkiyar mace,wayewar garin ranar kuma yayi mini kyautar gold half
set(half set shine dankunne,da sarka) kirar Dubai.
Zamana da Tasi'u sai dai san barka saboda bai rageni da komai ba yana kokarin kyautatamin
dai dai gwargwado,yana gudun bacin raina.
Haka kuma zamana da Aunty Amina shima banda matsala haka 'ya'yanta na girmamani,don
wani zubin har tunani nake yanda Aunty Amina take jana a jiki,amma ni duk da haka na kasa
sakin jiki da ita saboda tun can dama ba wani sabo a tsakaninmu,saboda duk da muna
Anguwa daya bata cika zuwa gida ba,kasancewarta nurse ce yawanci a Asibiti take wuni. Ta bangaren Aunty Zeena ma banda matsala,saboda ita mutumce mai hakuri da kawaici,ni
dama tunanina ko da zan samu matsalah,wai wuce ta Yaya Farooq ba,amma sai naci sa'a a
week din da akayi bikinmu akayi masa transfer ya koma Ilorin da aiki.
A ranar da muka cika sati biyar da aurenmu,Tasi'u ya fara shirin komawa bakin aiki,Don washe
gari da daddare yake so ya wuce,karfe takwas ya umurceni da in shirya muje mu gaida
Alhaji,aiko nayi ta murna don nayi kewar Ammyna don ma muna waya,cikin shigarmu ta alfarma
muka kama hanyar zuwa gidan,direct parlourn Alhaji muka wuce,nan muka tarar da shi da
Ummy,bayan mun gaisa,Tasi'u yake sanar da shi yazo mushi sallamane ,nan Alhaji ya sa mana
albarka,daganan dakin Ammyna muka wuce,muna shiga na rungumeta ina murnar
ganinta,sannan suka gaisa da Tasi'u,nan ma dai albarkar aka samana tare da mai fatan sauka
Lafiya, tukunna muka taso muka tawo,bayan dawowarmu gidane ya shirya ya tafi Kudan.
Wajen karfe biyu sai ga Aunty Mamy da Aunty hauwa sunzo nan muka hadu dakin Aunty Amina
(kasancewa night duty gare ta ranar)mukayi ta hira,cikin hirar ne Aunty Mamy ke tambayata wai
anya ba ciki gareni ba,nayi saurin ce mata ni banda komai,sai ta kuma tambayata yaushe
rabona da menstruation nace mata tun lokacin bikina,anan Aunty Amina tasa mana baki tare da
fadin ai ita tun last week ta lura cikine dani,nan dai suka hadu su uku sukayi ta zugani kar in
yarda in haihu da wuri,su bana ganin su basu da yara da yawa(Aunty Amina nada yara
hudu,Aunty Hauwah uku,sai Aunty Mamy nada daya),nan da har na hau kai na zauna,nan
Aunty Amina tace tana da Maganin da zata bani cikin ya zube tunda tasan bai wuce 4 weeks
ba,a lokacin duk na manta kiyayyar da suke nuna mana mu da mahaifiyarmu,don gani nake
banda masoya irin su(kar ku ga laifina,alokacin shekarata 18),nan Aunty Amina ta tambayeni
yaushe Tasi'u zai dawo nace mata sai dare,tace ai ya isa cikin ya zube lokacin,haka tabani
kwayar nan guda biyu tace in Hadiya da ruwa,take ko na sha magani.
Har kusan 2hours ba labari,nan dai su Aunty Mamy suka tafi suka barmu cikin jiran tsammani,in
takaice muku har bayan isha babu bayani.
Wurin karfe tara sai ga Tasi'u ya dawo,nan dai nayi ma Aunty Amina sallama na nufi
daki,gabana na dukan uku uku don ko girki banyiba,Allah ya taimakeni karin in kirkiri karyar da
zanyi yace in dafo mai Lipton don bazai iya cin abinciba.
Around 10pm muna kwance sai naji wani azababban ciwon mara ya taso mun tun ina dauriya
dai har na fara ihu,nan Tasi'u ya rikice yana tambayata mai ya sameni,kafin in bashi amsa sai
ga jini na bin kafafuna.
Don jin ya zata kaya,sai mun hadu a next page.
*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*
*Fateeyzah* β
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*ν ΌνΏ¨
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah*ν ½νΈ_
_Wannan page din nakune masoyen *GIDAN* *NAGOGGO* a duk inda kuke,nagode da
kaunar da kuke nuna ma novel dinnan._