Showing 18001 words to 21000 words out of 23360 words
har yau baki
tambaye ni inda zan ijiyeki".
Lumshe ido nayi tare da fadin"indai zan zauna tare da kai, ko daji ka ajiyeni ba damu wata
bane"
Murmushi yayi tare da fadin"wannan dadadan kalaman naki,shi yasa nake karaa sonki,
Bahijjah zan hadaku keda matata ta biyune kasancewa no wacce cikin matana gidanta daban,
to ke kinga yanda aurenmu yazo a kurarran lokaci babu time din gina miki naki gidan amma
insha Allah kema zan miki naki daban, sannan kinyinmu babban laifii,hakan kuma yaja na fara
tunani baki damu da lamarinaba"
Bakina na rawa kuma cikin sigar shagwaba nace"haba sweetheart me nayi maka,don Allah kayi
hakuri".
Cikin sanyin murya yace"duk lokacin da muka dauka tare baki taba tambayata sana'ata ba
kuma nasan baki sani ba"
A kunyace nace"sorry sweetheart, amma ni a tunanina tun ran farko da muka hadu kai ya
kamata ka sanar dani".
"Gaskiya ne abunda kika fada gimbiyaata,to nidai sana'ata itace siyar da GOLD".
Cikin jin kunya nace"Allah sarki,Allah ya bada sa'a".
Haka dai muka cigaba da hirar mu sai wurin goma muka yi sallama.
Ina shirin kwanciya kuma sai ga text ya shigo,ina dubawa sai na ga number Tasi'u ne cikin
sauri na bude sai gani nayi ya rubutu _wallahi_ _Bahijjah baki isa kiyi aure ba indai ina raye,ba
wani dan akuya daya isa ya shigarmun gonata,dan haka mu zuba ni dake shege ka fasa._
Wallahi nayi nan kafin 'yan Bahijjah team su fasa ma Tasi'u kai,azo ace dani a ciki♀️♀️.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah_*✍
[4/18, 8:00 PM] ~Fateeyzah✍✍:
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page5⃣1⃣to5⃣5⃣_*
Ina gama karanta text din shi na tuntsire da dariya don a tunani na sanda Tasi'u yayi
typing din text din kamar kwakwalwarshi ta juya, ban tsaya wani tunani ba na kashe wayata na
kwanta don na riga na fitar da Tasi'u da duk wata matsalarshi a raina, don a yanxu na riga nayi
mai nisa,yarana kuma kullun bana fashin addu'a akansu, Allah ya rayasu, ya shiryasu a tafarkin
addinin musulunci.
Washe gari da safe, wurin karfe goma na bude inda aka ajiye kayana,duk kayan sun lalace duk
gara ta cisu,kallonsu nake nama rasa ta inda zan fara,shawara kawai na yanke a zuciyata akan
kudin da Suleiman ya bani na lefe inyi amfani dashi in canza gado,saboda yaya Arsala shi yace
zai mun kujeru, ina tsaye inata tsake² sai ga kiran Aunty Aisha a wayata, bayan na dauka muka
gaisa take cemun inbar gyaran gadon don sunyi magana da yaya Al'amin zai canza min
gado,nan naji wani farin ciki ya lullubeni, tsakanina da 'ya'yan Hajiyar Sokoto sai dai addu'a don
sunyi mini abunda ko wadanda muke uba daya sun kasa yiminshi, nan dai na koma na sanar da
Granny, ita ma tayi murna tare da sa musu Albarka.
Haka na kira Aunty Asma'u na sanar da ita, sannan nakira Ammy, bayan na sanar da ita itama
ta tayani murna sannan tace "Bahijjah Baffa yazo ya bama Alhaji hakuri, ya amsa ya hakura,
amma yau da safe yace min ince miki kafin ki wuce Sokoto ki biyo ta zaria yana nemanki".
Cikin rikicewa nace "Ammy Mai kuma nayi?"
Ta amsa da"nima bansani ba,abinda dai yace kenan"
Cikin sanyin jiki na sanar da ita text din da Tasi'u yamin, nan dai Ammy ta kuma kwantarmun da
hankali tare da nuna min in dogara da Allah ba abunda ya isa yamun.
Kamar jiya,yauma bayan nagama waya da Suleiman sai ga text din Tasi'u, ina budewa sai naga
ya rubuta:
_(Bahijjah don ke aka yini,haka nima don ni aka yiki, don Allah Bahijjah karki aure wannan jakin
mutumin, na miki alkawarin zan maida ke dakinki tare da Alkawarin rayuwa mai inganci, rayuwa
ta jin dadi, ki taimaka ki dawo ki rungumi yaranki)._
Wannan karan text dinshi ya daga mun hankali tare da tambayar kaina wai mai Tasi'u yake
nema a gurina, duk abinda yayi min bai isheshi ba sai ya kuma dasa mun wani bakin cikin,
ganin bani da mai ban amsar tambayata yasa na kwanta, wanda sai wurin karfe biyun dare
bacci ya daukeni.
Sha biyu dai² na shiga Gidan Alhaji wanda direct palourn shi na wuce, nan na tarar da shi da
Ummy a parlourn,bayan na zauna muka gaisa, duk suka amsamin fuska ba yabo ba fallasa,
take jikina yayi sanyi, don dama zuciyata tun jiya take bani akwai wani abu da ya faru, daukar
waya yayu ya kara a kunne, an sai da yayi kamar sakon biyar tukunna yace kisa meni a parlour.
Bayan mintina kadan sai ga Ammy ta shigo da sallama, samun wuri tayi ta zauna tare da
fadin"sannuku da hutawa".
Umm
Ummy ce kawai ta amsa sabanin Alhaji da daga kai kawai yayi tare da gyaran murya" Abinda
yasa na taraku shine jiya da daddare ina zaune a parlour nan sai ga sarki da Tasi'u sunzo,
bayan mun gaisa da sarki shine ya fadamin musassbabin zuwanshi wai Tasi'u ne yaje yana
tamai kuka akan shi baisan sanda ya saki Bahijjah ba, a taimaka a dawo mai da matarsa yana
sonta, jin abinda sarki ya fadine ya tunzurani nafara fad'a amma kuma sai ya dakatar dani akan
mu tsaya mu saurareshi, nan dai Tasi'u yafara bamu labari wai yaje karatu da akeyi ne tsakanin
magariba da isha'i sai malamun yafara karatu akan sihiri, daganan sai yafara karanto ayoyin da
suke karya sihirin, wai daganan sai kanshi ya fara juyamai, daganan baisan inda kanshi yakeba,
sai farkawa yayi ya ganshi a kwance a gaban malamin daga nanne kuma malamin ya fada mai
abunda ya faru wai Aljanu aka turo mai amma sun samu su fitar dasu, sannan ya fadamai
Aljannun sunce turo su akayi su shiga jikinsa don su raba aurenku, wanda ke ma akwai asirin a
jikinki wanda zaisa Tasi'u ya tsane ki, daga karshe dai har kuka rabu, sannan zaman da sukayi
a jikinsa sun taba masha kwayoyinsa na haihuwa" Alhaji ya karashe magana hade da goge
zufar da ta tsattsafo mai.
Dukkanmu damuke parlourn kasa magana mukayi, sai zufa datake ta tsattsafo mana, ni kuwa
har da wani firgice daya shigeni.
Alhaji ne ya ci gaba da cewa"malamin yace akai Bahijjah don yayi mata rukiyya,sannan ko za a
samu na jikinta su fadi wanda yayi musu wannan aikin".
Take Ummy ta zaro ido,zufa nata keto mata.
Pls manage
Not edited
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*Fateeyzah*✍
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_I dedicated this novel to my late father(Alh Babangida N.T.C)who die on 23rd August 2014,
may his soul rest in peace._*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page5⃣6⃣to6⃣0⃣_*
Cikin kidima Ummy tace "yanxu in aka yi rukiyyar zasu fadi wanda ya turo su".
Cikin mamakin tambayar ta yasa gaba daya muka kalleta, lura da tayi hankalinmu ya koma
kanta ne yasa tayi saurin cewa"Allah ya baki lafiya Bahijjah,Allah ya saka muki", gaba dayan mu
muka amsa da "Ameen"
Alhajine ne ya mike hade da fadin" Amina sai ki shirya kayan ki kema don gobe in Tasi'u yazo
dake zamu tafi, daga nan sai ki dan kwana biyu wurin Goggo tunda kin dau lokaci bakije ba"
Cike da murna Ammy ta amsa da "nagode Alhaji,Allah ya kara tsahon shekaru".
Amsa wa yayi da "Amin"sannan ya shige bedroom dinshi.
Nan muka tashi muka bar Ummy wanda tayi nisa cikin tunani don bata san sanda muka fita ba.
Yini ranar hirar mukayi tayi da Ammy, wanda yawancinta ta bata gidanmu ce kawai ba har da ta
matsalolin family dinmu gaba daya, duk yanda naso Ammy ta tsaya muyi magana akan aljanun
da akace an turo min da asirin da aka yomin taki, don dana kawo maganar take Zamora wanda
bansan dalili ba.
Wayewar ranar bakwai tayi ma Tasi'u a gidanmu bayan gaishe² muka kama hanya wanda Tasi'u
ne ke driving, sai Alhaji a gefenshi, sannan nida Ammy a baya,don Alhaji ya hana a sanar da
sauran yaran Gidan, saboda yace a bari dai muje mu dawo, yana ta satar kallona ta mirror,
damun hada ido sai ya dauke kai don na lura yanxu Tasi'u kamar kunya ta yake.
Muna isa kaduna, direct gidan malamin dake Malali muka wuce, bayan mun isa, Tasi'u ya kira
malamin a waya don neman iso, muna tsaye sai gashi ya fito, bayan mun gaisa yayi mana iso
cikin gida inda ya sauke mu a wani Babban parlour da aka lailayeshi da brown carpet sai wata
cabinet a wata kusurwa dake shake da manyan Qur'anai da sauran littafan Addini.
Bayan mun zauna Tasi'u ya yi masa bayani kamar haka"Allah ya gafarta malam wannan ce
tsohuwar matata da muka yi magana dakai kwana uku da suka wuce, wadannan kuma
iyayentane" ya karasa magana yana nuna Alhaji da Ammy.
Sai da malam ya kalleni for some minutes, sannan ya maida kallonsa kan Ammy daga bisani
yayi gyaran murya tare da cewa" Alhaji da Tasi'u ina tunanin zaku dan bamu waje" yayi magana
yana kallonsu.
Nan dai Alhaji ya amsa mai da"toh,babu damuwa"
Bayan fitarsu Alhaji, malam ya umurceni da inbashi tarihin aurena da Tasi'u, aiko nan na fara
bashi wanda kafin in gama na wanke fuskata da hawaye wanda Ammy take tayani.
Gyara zama yayi tare da fadin" gaskiya zan fada muku kuna da matsala dukkanku,don ke(ya
nuna Ammy da yatsa) dadadden asiri ne a jikinki wanda karya shi lokaci daya zai yi wuya,
sanna ke (ya nuno ni da yatsa)Aljana ne aka turo miki kamar yanda aka turo ma Tasi'u wanda
shi harda Asiri aka hada mai wanda kuma asirin yafi tasiri a jikinshi, sakamakon rashin maida
hankali akan ibada da azkar, bayan na karya asiri jikinshi ne na mai rukiyya inda Aljananin yake
sanar dani dashi data jikinki tare aka turo su, kasancewa shi ya tsani aljanar jikinki ita kuma
tana sonshi, wannan ne yasa aka turashi jikin Tasi'u don yasa mai kiyayyarki acikin zuciya,
wannan ne yayi musabbabin rabuwar ku wanda kuma Allah yasa zaman aurenku ya kare".
Kafin ya gama maganar nan gaba daya hawaye ya wanke mana fuska, Ammy ce tayi karfin
halin cewa" Allah gafarta malam, ko sun fadi wanda ya turo su"
"Tabbas shi Aljanin ya fadi uwar gidankine ta turo su, naki fadama Tasi'u ne saboda na fison in
gama yi ma ita Bahijjah rukiya itama, don ko asirin da ke jikinki ita tayi shi"ya karashe magana
yana nuno Ammy.
Cikin kidima muka hada baki muna salati,sai da muka kwashi mintina sannan Ammy tabude
baki tace"don Allah malam ina neman wata alfarma na karka fada ma Alhaji ko Tasi'u wanda
yayi wannan abun don nasan wannan maganar ba karamin tashin alkali zata jaba, ni na barta
da Allah, Allah ya saka mana, don insha Allahu da sannu zata girbe abinda ta shuka".
Malam ya amsa"da insha Allahu baza suji wannan maganar ba,wannan dalilin ne yasa nace su
bamu wuri, don na saba samun irin wannan case din naku, yanxu ke zan hada miki magunguna
da ruwan magarya, indai kina amfani dashi da izinin Allah komai zai warware, sannan ke
Bahijjah zamu miki rukiyya kema insha Allahu komai zai daidaita, yanxu bari in kirasu su shigo
ayi a gabansu"ya karashe magana ya na kokarin tashi".
Bayan su Alhaji sun shigo ya nuna musu toilet din dake parlourn a kan su shiga su dauro
Alwala, da ya bayan daya mukayo Alwala,sannan malam ya ibi wani ruwa daga cikin wata jarka
ya watsa min akai, sannan ya bama Ammy wani turare ta shaka mun, tunda ta shakamun
bansan inda kaina yake ba.
Wurin la'asar na tashi na ganni akan gadon Granny, kokarin tashi nayi amma na kasa don jinayi
duk jikina kamar an mini duka, jin muryar Ammy da nayi daga falo yasa na fara kwala mata kira"
Ammy, Ammy".
Cikin hanzari ta shigo dakin Granny na biye da ita, kokarin tada ni tayi tare da fadin "sannu
Bahijjah, Goggo dan Allah miko min maganin da malam yace inta tashi a shafa mata"
Cikin sauri Grand ta fita sai gashi ta dawo da wata kwalba ta mikia ma Ammy, karfa tayi ta shafa
mun tare da jero mun sannu, bayan ta shafamun da kusan minti biyar sai gashi inata zufa
daganan kuma sai naji jikina ya canza take naji wani karfi yazo min, ganin haka yasa fara'ar
fuskar Ammy ta karu.
Kwana biyu na kara a kaduna sannan na shirya komawa saboda inaso in biya zaria in kwana
daya kafin in wuce sokoto, kafin in tafi sai da Ammy ta kuma jamin kunne akan kar in sake ko
Aunty Asma'u in fada mata abinda ya faru.
Bayan na kuma warwarewa nasamu nayi wanka hade da rama sallolin da ake bina.
Ina sauka a zaria direct gidan Alhaji na nufa,wanda bayan gaishe², Alhaji ya nemi ganina cikin
sirri a bedroom nashi, bayan na shiga na samu wuri na zauna tukunna ya gyaran murya
yace"abunda yasa nace ina son ganinki ba komai bane illa in nemi yafiyarki akan abubuwan
dana yi muki, hakika Bahijjah ban miki adalci a matsayina na mahaifinki don nasan na cutar
dake, so da yawa sai nayi miki abu amma daga baya kuma sai abin ya zo ya dameni, Amma
daga yanxu insha Allahu kin dena zubar da hawaye saboda ni" ya karashe magana cikin sanyin
murya.
Cikin karayar zuciya wanda duk wanda yaji muryata yasan dauriya kawai nake nace" na yafe
maka Alhaji,amma nima don Allah ina neman yafiyarka, don nima na saba maka na tsallake duk
wata magana taka".
Yace"Bahijjah ba komai Allah ya yafe mana gaba daya, abu na gaba kuma shine Tasi'u yazo
mini da wata magana akan yanaso a maida auranku, to amma sai na nuna masa yanxu haka
da sa ranar wani akanki, to dayake a gaban sarki mukayi sai yace a bari aji ta bakinki ,in zaki
koma gidan Tasi'u ne ki rike yaranki sai aba ma shi Suleiman hakuri, inkuma Suleiman din kika
zaba shi kenan don dai wannan karan bazan miki doleba kamar wancan karan".
To Bahijjah fans sai ku zabar mata miji a karo na biyu tunda Alhaji ya baku zabi.
Ina Suleiman fans banda son kai,haka kuma Tasi'u fans.
Insha Allah saura page daya na gama novel dinnan saboda azumi ya gabato.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah_*✍
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_Page 6⃣1⃣to7️⃣0⃣_*
Cikin tsarkewar murya nace"don Allah Alhaji kayi hakuri da abinda zan fadi, na zabi auran
Suleiman akan komawa Gidan Daddynsu Iman, don ko na koma zan ringa kallonshi da irin
wulakancin da yamun duk da ba a hayyacinsa yayi ba, sannan su Iman sunyi dace da uwar
riko, don nasan sumayya na kula dasu dai² gwargwado".
(Lol duk kun bude kunne kuji zabin Bahijjah, to dai ta zabi naku nikuma ta ajiye nawa my
Tasi'u).
Cikin sanyin jiki Alhaji yace"Allah yasa haka shi yafi zama Alkhairi, su kuma yaran Allah ya
shiryasu".
Cikin jin kunya na amsa da"Amin".
"Ina zuwa Bahijjah"Alhaji ya fada tare da mikewa ya nufi drawer da ke dakin, bayan 'yan
mintoci kuma ya nufo ni da kudi a hannushi, mika min yayi tare da fadin" Bahijjah ga
gudunmawata nan a matsayina na mahaifinki, kije ki sayi abinda baki da dashi, sannan zan kira
'yan sokoto in musu godiya don Ammynki ta fada mun sunyi miki kayan daki".
Cike da murna na karfa tare da fadin "nagode Alhaji, Allah yasaka da alkhairi ya kara girma.
Fuskarshi cike da fara'a yace "Amin Bahijjah,Allah yayi miki albarka, yaushe zaki wuce
Sokoto?"
Ina mirmushi nace" Amin Alhaji, gobe zan wuce".
Ya mike tare da fadin" Allah shi kaimu,bari in tafi masallaci naji an fara kira" ya karashe magana
yana fita.
Bayan nabar dakin Alhaji, Gidan Aunty Asma'u na wuce don magana nacina na kosa inje in
fada mata yanda mukayi da Alhaji, da sallama na shiga Gidan, da gudu Aunty Asma'u tazo ta
hugging dina tare da fadin" wallahi yanxu nake zuci² kiranki" ta fadi fuskarta cike da fara'a.
Nace" gani nan nazo ai, nima bakina cike yake da magana, wallahi Aunty Asma'u yau ji nake
kamar an mini kyautar Aljanna, wai yau ni Alhaji ya nemi yafiyata har da samun Albarka,
wanda tun dana taso nayi Wayau ban taba jin wata kalma mai dadi da Alhaji ya jefeni da ita ba"
na karashe magana cikin zubar da wasu zafaffun hawaye.
Idon Aunty Asma'u cike da kwalla tace" Bahijjah ba kuka zamuyi ba, godewa Allah zamuyi don
nima jiya Alhaji har gidan nan yazo ya nemi yafiyarmu nida baban Amira, Ammy ma tace ya
nemi yafiyarta, kinga wannan babban ni'ima ce daga Allah".
Nan dai na nuna mata kudin da Alhaji ya bani, itama tayi ta murna tare da yima Alhaji addu'a
sannan tace zata kirashi Tayi