Showing 9001 words to 12000 words out of 23360 words
hankalina wurin don ganin mai shigowa,ganinsu Aunty
Asma'u da Daddynsu Iman ne yasa wani farin ciki ya lullubeni, don ganinshi danayine ya
tabbatar mun yana raye, karasowa wurina sukayi tare da tambayata ya jiki, a hankali na amsa
idona akanshi Saboda ganin fuskarshi da bandeji, ganin haka yasa Aunty Asma'u ta juya tafita,
ganin fitar tane yasa shi karasowa bakin gadon ya zauna.
Kallonshi nayi hade da tambayarshi me ya samu cikin jikina,anan yake fadamin kasancewa
wurin faduwa cikina Yaya bugu,shine aka min C.S aka ciremin babyn,amma sun sata a
Incubator (kwalba) saboda watanta bakwai ne da sati biyu.
*_A gurguje_*
Satina hudu a Asibiti tukunna aka sallamoni da ni da Jaririyata wadda taci sunan mamar
Daddynsu wato rukayya(ruhaima), duk cikar dakin Ummy ba wanda yazo dubani, haka ma dana
dawo,Su Aunty Hanna ne kawai da Aunty Fatima suka zo dubani,amma Aunty Amina ko lekowa
batayi ba domin ta min barka sabanin haihuwar su Ilham da duk da bama magana tana min
barka,Ammyna ma bata zo ba sai dai ta sanar dani Alhaji ne ya hanata Zuwa.
Kwananmu biyu da dawo wa Alhaji yazo gidan,a lokacin Daddyn Iman na nan, dukkanmu ya
tara mu a dakin Yaya Farooq,anan ya yanke hukuncin akan Daddynsu Iman ya dena shigo mai
gida,Amma ni bazai iya cewa in bar gida ba,sai dai in zai ganni,ya ringa zuwa bakin GIDAN ya
kirani,in kuma ya na ganin ba haka ba ya tattara ni yaje ya kama min haya,sannan ya min
kashedu in zan je Gidanshi kar in yadda in shigo mai da Jinin Tasi'u,hakanan Alh ya kakkabe
Rigarshi ya kara gaba,ba tare da ya saurari ban hakurin da muke yiba.
Aunty Amina ko kamar ta zuba ruwa a kasa tasha na wannan hukuncin da Alh ya
yanke,sabanin Yaya Farooq da jikinsa yayi sanyi.
Haka Daddynsu Iman ya shirya kayansa tare da diremin ATM card dinsa ya wuce Kudan tare da
min Alkawarin zaije yayi shawara da Iyayensa don samun mana mafita.
Bayan tafiyarshi da kwana biyu ya kirani ya sanar dani zai wuce lagos,don sunyi shawara da
iyayenshi akan ya barni anan kafin ya karasa gininshi (kasancewa yana gini a kaduna).
A wannan zaman da nayi ba karamin bakin ciki nake kunsa ba,don Aunty Amina bata da aiki
sai na yada min da habaici, saukin tama Iman ta girma,don da ita nake hira in bata je school
ba.
Ruhaima nada wata hudu akayi bikin Yaya Ibrahim da ya auro matarshi daga Abuja,bikin ba
karamin kashe kudi akayi ba,inda har mutanen unguwa suka fara tambayar aikin da Yaya
Ibrahim din yakeyi,anan naji Aunty Hanna na cewa wai Yaya Aminu ne ya daukeshi suna hakar
Gold,nan ma sai da suka yita sakin habaici na sunyi mana fintinkau bamu da yanda
zamuyi,shima dai Alhaji ya bashi Gida anan unguwar.
Bayan bikin ne da sati uku, Daddynsu Iman ya kirani akan in shirya kayan mu don zai zo ya tafi
damu kasancewa ya samu scholarship na yin M.sc a Dubai kuma damu zai tafi don harda Gida
aka bashi acan.
A ranar ne kuma *GIDAN* *NAGOGGO* suka tashi da wani tashin hankali inda aka kama Yaya
Ibrahim dalilin satar motar da yayi ta wasu 'yan India da suke yi ma Yaya Aminu Aiki, wanda
kafin wani lokaci maganar ta zagaye unguwa,ranar dai su Ummy sun shiga tashin hankali ni
kuwa ko a kwalar rigata,don a ganina Alhakinmu ne ya fara kamasu,don ko Jaje ban ma kowa
cikinsu ba,anan dai su Alhaji,Yaya Baffa da Yaya Farooq sukayita ciku² har sai da suka fito
dashi, sannan Alhaji ba wani mataki da ya dauka akan hakan,sai ma fushi dayayi akan abunda
Yaya Aminu yayi na kama Yaya Ibrahim din da yasa akayi.
Wani satin na zagayowa, Daddynsu Iman yazo ya kwashe mu kuka tafi Kudan,kwanan mu biyu
anan muka wuce lagos inda zamu yi sati biyu kafin mu wuce Dubai.
Satin mu daya sai ga kiran Yaya Farooq,ina dauka ya fara duramin zagi akan tunda na zabi
mijina akan su in zo in kwashe kayana daga Gidan,bai jira cewa naba ya kashe wayar,
hankalina ba karamin tashi yayi ba da jin zancensa,dialing din Number Yaya Farooq nayi amma
yayi rejecting,nan na fashe da kuka,sai da naci kukana na gaji sannan na yanke Hukuncin kiran
Aunty Asma'u.
Bayan na kira Aunty Asma'u ne take sanar dani yanxu suka gama meeting a kaina anan Gidan
Alhaji,ana take fadinmin wai sarki ne da Mahaifin Tasi'u suka zo bama Alhaji Hakuri akan
matsalar dasuka samu da Tasi'u,shine bayan sun gama tattaunawa ya dauki waya ya kira Tasi'u
yace mai ya samu lokaci kafin mu tafi Dubai yazo a musu sulhi da Alhaji,shine shi kuma baisan
wayar a speaker take ba yace wai ai a share Alhaji da 'ya'yansa duk munafikai ne(wannan shine
ruguntsimi), anan Alhaji yace to ya sakanmai 'yarsa,shine yace ai tun da abin ya faru yaso
sakina,amma na roke shi ya rufamin asiri kar ya sakeni saboda bazan iya zaman Gidan Alhaji
ba.
Tana gama min wanna bayanin naji zufa tana keto min,na rasa a inda zan sa kaina,don Alhaji
shima sai da ya kirani yace kar in kuma zuwa mai Gida in dai akwai Auren Tasi'u a kaina.
Ruguntsimi kenan,
Shin Bahijjah zata bi maganar ko kuma zata bi Tasi'u domin tafiya Dubai?.
Amshoshin tambayar nan zata zo a page na gaba,wanda anan ne zamu ci gaba da Asalin
labarin.
Ayi hakuri da Errors saboda banyi Editing ba.
Kar ku manta comment dinking,shine karfin gwiwa ta.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*Fateeyzah* ✍
*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*GIDAN NAGOGGO FANS*
*Mmn Abdoulaziz*
*Queen candy*
*Hassinat Muhammad*
*Fadiey*
*Rabi'atu Y*
*Sharifat niamey*
*Saudah*
*Fa'iza Auwal*
' *yar Asalee*
*Zainab zee*
*Fatima imilan*
*Maman farhiyya*
*Munlex*
*Hafsat s bello(maman fadila)*
*Meerah*
*Adizatou zanna*
*Ummu farha*
*Amina Sufi usman*
*Maman safwan*
*Nazma*
*Maryam*
*Zabba'u Abdulrahman*
*Mrs Annur*
*Mrs Yarima*
*Maman Deeja*
*Aisha jibril(Aj)*
*Innah sharrif* , *da sauran wadanda baku ji sunanku(sorry sai next page) dukkanku barka da
jumma'a,ina jin dadin comment dinku,ina godiya.*
*jinjina gareku 'ya'yana fadila,khaleefa,Affan Allah ya raya minnku*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page2⃣1⃣to2⃣5⃣_*
A ranar haka na wuni cikin tashin hankali,don ko girkin dare na kasa daurawa, sai dai
cornflakes na hada ma su Iman suka sha sannan sukayi bacci, niko ko ruwa na kasa sawa a
bakina , haka nayi ta zaman jiran Tasi'u ya dawo saboda nata kiran phone dinshi amma baya
dauka daga baya ma sai ya kashe wayar.
Sai wurin karfe sha biyu tukunna ya shigo gida alokacin har na fara gyangyadi don karar rufe
kofar shi ne ya tasheni, kallon da na watsa mai ya sa jikinshi sanyi da jan kafa ya karaso
wurina hade da fadin"bahijjah mai ya faru, tunda nake da ke ban taba ganin kin min mafificin
wannan kallon ba".
Na kalleshi fuskata cike tab da hawaye nace"dole kace haka mana, tunda kasan abun da
kayi,haba Daddynsu Iman koda Alhaji sa wuka yake yana yankan naman jikinka ai bai kamaci
zagi a wurinka, ko ba ka aurena ai akwai dangantaka ta jini, amma wai har kai zaka iya bude
baki ka kira Alhaji munafiki, aiko kaga ka cancanki wannan kallon daga gare ni " na karashe
magana ina goge hawayen dake fuskata.
Riko hannuna yayi tare da fadin"wallahi Bahijjah ba abunda ya faru kenan ba, nasan dai
Alhajinmu ya kirani yace mun shi da sarki sunzo sun samu Alhaji sun bashi hakuri akan abunda
ya faru, shine Alhaji yace yana bukatar inzo saboda akwai maganar da yake so yayi a gabana
shine fa nacemai bazan samu zuwa ba saboda ina shirye shiryen tafiyar mune, to kinji yanda
muka yi dasu,kawai kuma sai ga Yaya Baffa ya kirani yanata zagina wai na zagi Alhaji, tunda
bansan mutunci ba in sakeki, ni kuma nace mai ina sonki ne shi yasa ban sakeki ba, amma da
bana sanki da ba mu kai wannan lokacin a tare ba".
Ajiyar zuciya na saki tare da fadin"kar kaga laifina hatta Aunty Asma'u abunda ta fada min
kenan, amma me yasa da na kira wayarka ba ka dauka ba daga baya kuma ka kashe wayar
gabaki daya"na karashe da tambayarsa.
Sakin hannuna yayi sannan yace"wallahi sanda kika kirani ina meeting ne kasancewa yau nayi
handing din komai ga sabon manager da aka kawo".
Hausawa nace wa tsakanin miji da mata sai Allah,a wannan dare muka shirya da ni da Tasi'u
don ni aganina abunda ya fada min shine gaskiya sabanin abunda Alhaji da sauran ' yan uwana
suka ce.
Sati na zagayowa,jirgin mu ya tashi zuwa Babban birnin Dubai wato Abu Dabi city, zaman mu a
Dubai zama ne mai cike da FREEDOM hade da jin dadi,banda wani tashin hankali ko fargaba,
don duk na manta da wani tashin hankali a Nigeria,don daga Ammy sai Aunty Asma'u kawai
nake waya don nasan ko na kira Alhaji dauka zaiyi ba.
Kasance wa in Daddynsu Iman ya tafi school sai yamma yake dawowa,sai ya neman ma Iman
da Ilham school acan,inda akasa Iman a nursery two,Ilham kuma a pre nursery,ni kuma sai ya
neman mu wani school na fashion designers, wanda anan na koyi yanda ake dinka jallabiya da
veil.
Shekara mu daya da wata biyu acan muka tattaro muka dawo Nigeria inda muka sauka a
Lagos,kwanan mu biyu muka yo Arewa inda Daddynsu ya ijiyemu a zaria shi ya wuce kudan.
Wurin karfe biyar keke napep ya sauke mu a bakin gate din Gidan Alhaji,nan na nemu Almajirai
suka daukar mun trolleys dina suka shigan mun dasu gidan,ni kuma na biyar mai keke napep
kudinsa na kama hannun yarana muka shiga ciki.
Muna kusa kai Gidan,naga Almajiran da na bama kayana na tsaye a farfajiyar Gidan,gefe daya
kuma ga Alhaji,Ummy,Ammy da wasu daga cikin yaran Gidan a tsaye,ganin irin kallon da Alhaji
yake watsamin ne yasa na kasa ci gaba da tawo wa,nuna ni yayi da dan yatsa tare da fadin "kar
ki kuskura ki karaso wurinnan in baso kike na bata miki rai ba,ai dama an fadamun kin
dawo,shiyasa na kasa na tsare don nasan dole zakizo, toh ki bude kunnan ki kiji wallahi bazaki
shigo mun gida da auren Tasi'u akanki ba, inkin ga na kuma bari kin shigo gidannan to kinzo
min da takardar sakine,don haka na baki minti buyu ki tattara kayanki da yaranki ku bar min
Gida kuma kar ki sake inji kinje wani gidan dan uwa, sannan kayan dakinki na baki nan da sati
daya kizo ki kwashe in ba haka zan zubar dasu a waje,kinji dai na fada miki"
San ya juya ga 'yan gidan tare da fadin" ku kuma ku wuce muje",haka ya tasa su a gaba suka
shige cikin falonsa,ina gani Ammy idon ta cike da hawaye tana waiwayoni har suka shige.
Haka ina kuka muka fito Gidan inda nasamu keke napep na muka shiga, sannan na sallami
almajiran na umurci Driver da ya kani motor park.
Muna hanya Ammy ta kirani tana kuka tana ban hakuri sannan ta ja mun kunne akan kar in
sake in ce zan kashe aurena,don ko na dawo Gida bazan iya jin dadin zaman Gidan ba,don ita
ma saboda Kannena take zaune, haka tayi ta bani shawarwari da nasiha, sannan muka ajiye
waya.
Muna karasowa motor park na sallami mai keke napep na kama yarana muka hau motar
Kudan,minkai minti goma sannan motar ta cika muka tashi,a hanya ma Aunty Asma'u ta kirani
ta ringa bani hakuri tare damun kashedin kar in sake in kashe aurena.
Sai bayan magriba muka iya kudan,muna sauka na samu Almajirai suka daumin kayana muka
kama hanyar Gidansu Tasi'u kasancewa babu nisa daga inda aka saukemu.
Muna isa, mukaci karo da Tasi'u a kofar Gida, da mamaki ya tare mu, ya amshi kayanmu
kayanmu sannan na sallami Almajirai muka wuce cikin Gida,yana ijiye kayanmu ya fita domin
yin sallar magariba,mu kuma muka shige dakin mahaifiyarsa(umma).
Bayan munyi sallah hade da cin abinci sannan Alhajinsu ya kirani zuwa falonshi,nan na tarar da
Tasi'u da umma da Alhaji, bayan na gaisheda Alhaji sannan ya tambayeni abunda ya faru na
tawo kudan bacin Tasi'u yace ya barni a zaria, nan na kwashe duk abunda ya faru na
fadamai,nan ko ya fara fada ya dauki waya ya kira Alhaji, yana dauka ya fara surfa mai masifa
kamar haka"wai kai *NAGOGGO* wani irin zuciya gare kane,an bak hakuri amma kaki hakura,
ko Allah ana mai laifi kuma atuba, ballantana kai, to wallahi ka guje randa Allah zai kama ka
saboda hakkin yarinyar nan kaji na fada maka,kuma insha Allahu auren Bahijjah da Tasi'u har
mutuwa" yana kaiwa nan ya kashe wayar bai jira amsarshi ba.
Nan Alhaji ya shiga yi mini nasiha tare da kwantar min da hankali,sannan yace min zasuyi
shawara da Tasi'u suji inda zamu zauna,ranar dai sai kusan asuba nayi bacci.
Kwanan mu biyu a Kudan,Tasi'u yazo ya sameni da murna yake cemin ya samu aiki a NNPC
nanan Kaduna,nan mukai ta murna nan yace mun gobe zai je don sun kirashi,washegari ko yayi
sammako ya tafi kaduna.
Sai bayan magariba ya dawo,bayan ya yi sallah yaci abinci yake cemin sunce ranar monday zai
fara aiki saboda haka yayi shawara da Alhajinsu akan sai kama mana haya a kaduna kafin ya
gama nashi ginin,nanko naji farinciki ya rufeni, don ko ba komai kafi sakata ka wala anaka
dakin.
Acikin sati naje na kwashe kayana a Gidan Alhaji, tukunna muka wuce kaduna inda ya kama
mana haya a Kinkinau, gida ne mai dauke da Flat biyu kowanne flat yanada 2bedrooms,
kitchen, toilet da store.
A farkon zaman mu, muna zaune ba tare da wata matsala ba,haka ma makociyata wacce take
dayan flat din itama bata da matsala.
Matsalar dana fara facing daga Tasi'u shined dana samu ciki, sai ya nemi in zubar da cikin wai
saboda shi yara uku sun isheshi, ni kuma naki yadda,nan fa yafara min rashin mutunci hade da
gori, sai ya kunle store ya tafi da mukullinshi sai dai makociyata ta bani,su Iman dama ya sasu a
makaranta insuka tafi tun safe sai la'asar sai ya zamana in yaje daukosu sai ya biya dasu ta
restaurant suci abinci,da daddare kuma sai ya dafa musu indome ko ya siyo musu snack su ci
nikuwa bai damuba, haka ya raba daki dani ya zamana yana kwana da 'ya'yansa.
Ranar da bazan manta da itaba,itace ranar wata babbar salla alokacin cikina wata shidda, sai
na sami Tasi'u don in tunatar dashi hakkina daya danne,aiko na ya balbaleni da masifa har da
cemun dama halin 'yan gidan mune rashin kunya ni kuma da abun ya ban haushi sai nace mai
ai munfi 'yan gidansu da suke maneman mata,aiko nan ya tsinke ni da mari yaci gaba da zagina
nima ina ramawa,aiko da ya gaji sai naga ya shiga daki sai gashi ya fito da farar takarda ya
mikomin........
'ka'ka'kara 'kara, sai mun hadu a next page.
Kuyi hakuri na gaji banyi Editing ba.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah_*✍
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*( _Home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page2⃣6⃣to3⃣0⃣_*
Mika min takardar yayi tare da fadin "gashinan sai a kara gaba,ki tafi gidan masu tarbiya
wadanda basa neman mata"yana gama fadin haka ya dauki key din motar shi ya fita.
Take kukan da nakeyi na nemeshi na rasa, jinayi kamar in hadiye zuciya in mutum, aranar na
tabbatar da namiji badan goyo bane duk wanda ta maidashi uba zata mutu marainiya, a ranar
na kuma tabbatar da namiji ko service din MTN ya fishi guarantee, sannan alokacin nadama ta
kamani na yanda na fifita mijina akan ubana, na zabi in zauna da mijina akan mahaifina,a
wannan lokacin nayi danasani da naki bin maganar Alhaji,aganina duk wulakancin da yamini da
hana ni abinci bai isheni ba har sai daya hada ni da saki a lokacin danafi bukatarsa,sannan nayi
danasani na rashin sanar da Ammy da Aunty Asma'u halin da na ke ciki, don ko Granny da
muke gari daya karya na mata nace cikin yazo mun da matsala shi yasa bana zuwa gaisheta
wanda kuma saboda rashin kudin mota ne dalilin, ita kuma ba kafa ba ballantana tazo.
Nakai kusan awa biyu a inda ya tafi yabarni,ba komai nake tunani ba sai rashin sanin abin yi,da
rashin sani wanda zan fada ma maganar nan,ganin shigowar Humaira (makociyata) ne ya bani
kwarin gwiwar tashi na nufeta nayi hugging dinta sannan na fashe da kuka, cikin rikicewa take
tambayata mai ya faru ,kasa bata amsa nayi sai zame jikina danayi daga jikinta na nufi inda na
tashi na dauko takardar na mika mata, karba tayi cikin mutuwar jiki ta warware takaddar,cikin
sanyin jiki tace "inalillahi wa'inaillahir raji'un maman Iman saki har biyu", cikin azama na karfi
takardar daga hannunta na kai duba