Showing 12001 words to 15000 words out of 23360 words
cikin takardar ba komai na fahimta acikin takardar ba sai
layi biyu da na iya kai duba na kai wati inda ya rubuta
_Ni Tasi'u Ibrahim Kudan na saki matata Bahijjah Ahmad Nagoggo saki biyu_...........nan naji
wani irin jiri ya debe ni da sauri na dafe hannu kujera ana Humaira ta karaso wurina ta taimaka
min na zauna.
Mun kai minti talatin ba tare da mun furta komai ba don kowannan mu yayi nisa cikin tunani,
humaira ta fara janne shirun tare da fadin"Maman Ihsan ya kamata ace kin sanar da gida halin
da ake ciki"
Sai da na dau dan lokaci tukunna nace "haka ne humaira amma kinfi kowa sanin halin dana ke
ciki,ni wayata babu ko sisi".
"Bari in dauko wayata akwai credit"ta karashe maganar tana ficewa.
Cikin minti biyar sai gashi ta dawo ta mikamin wayar tare da juyawa ta fita, jikina na rawa haka
na fara dialing din Number Ammy sai da tayi ringing so uku tukunna ta dauka tare da yin
sallama, cikin Muryar kuka na fara magana"Ammy ya sakeni ba tare da nayi mai komai ba".
Salati tayi tare da fadin"Bahijjah kikace ya sakeki?, mai kika masa?, dama baku zaman lafiya ne
kika boyemu?,oh ni Amina wani irin abune wannan ka saki matar ka ranar sallah".
Jin wadannan tambayoyi daga bakin Ammy yasa hankalina yakuma tashi, nan na zayyane mata
abunda ya faru tun daga daukar cikina har zuwa sakin daya mini, nan Ammy ta kuma zabga
salati tare da fadin"Bahijjah kina da hankali kuwa,duk wadannan abun na faruwa amma kika
kasa sanar da kowa".
Nace"Ammy don Allah kiyi hakuri wallahi banson ya zamana ko yaushe ni nake daga miki
hankali,kuma kinga kema kina ji da kanki, ga matsalar nan gidan, shiyasa naga bai kamata in
kara miki wata damuwar ba"
"To yanxu ina su Iman din" Ammy ta tambaya
Nace"inaga ya kaisu Kudan ne,saboda naga ya hada musu kaya".
"Bari yanxu xan kira Asma'u muji yanda za a yi, don gaskiya bansan yanda zan tunkari Alhaji
da wannan maganar" haka mukai sallama da Ammy na kashe wayar.
Can wurin karfe biyar na ranar sai ga sallamar Yaya Baffa,Yaya Farooq da Aunty Asma'u, suna
shigowa Yaya Baffa ya umurceni da intashi in hada kayana inzo mu wuce, cikin rawar jiki na
shiga daki dan hado kayana, ina cikin hadawa Aunty Asma'u ta shigo tace inje Yaya Baffa na
kirana, cikin sanyin jiki na bita zuwa parlour, ina zuwa na samu wuri na zauna sannan Yaya
Baffa ya fara magana cikin bacin rai "Bahijjah ganin mu da kikayi munzo, Alhaji ne yayi umurni
akan muzo mu tafi dake Saboda Asma'u tazo mana da maganar Tasi'u ya sake ki,Hakika
dukkanmu ranmu ya baci akan abunda ya faru,duk da a baya mu muka nemi daya sake
ki,amma ya nuna mana yana son matarsa,ko yanxu abinda ya bata mana ran baiwuce yadda
Ammy ta fada mana irin wulakancin da ya miki hade da hanaki abinci da yayi,Amma kuma
yanxu Alhaji ya kuma kiranmu akan mubarki anan ki haihu, inyaso inkin yi arba'in sai ki ijiyemai
'yarshi ko 'yanshi ki koma gida".
Nan naji gabana ya fadi in ijiye dana kuma, ai abunda bazai taba yiwuwa ba kenan in bar dana
ko'yata mai kwana arba'in a duniya, ina kokarin magana ne Aunty Asma'u ta girgiza min kai,
ma'ana kar ince koma.Anna Yaya baffa ya tambayeni in bashi Account number na, ina bashi
yayi mini tranfern dubu dari yace inje in sayi abinda nake bukata in kuma akwai wata matsalar
in kirashi a waya, ina ji ina gani suka tafi suka ganni.
Haka naci gaba da rainon cikina cikin kulawar 'yan uwana da Humaira, tsakanina da Tasi'u
kuwa sai dai ido ban shiga harkarshi nima bai shiga tawa, su Ihsan kuma bai dawo dasu ba.
Bayan wata uku na haifo dana da taimakon unguwar zoman da Humaira ta kira mun a bayan
layinmu, duk wanda yaga yaron sai ya yabashi,a ranar ne kuma Allah ya dauki ran Alhajin
Tasi'u.
Haka 'yan uwa sukayi ta kirana suna min barka hade da gaisuwa, sati na zagayowa aka rada
ma yaro suna ibrahim khaleel,ba wani taro akayiba ,amma duk 'yan gidanmu da surukan gidan
sunzo illa 'yan dakin Ummy, ba laifi an tara mana kaya ni da khaleel, Tasi'u ko khaleel kadai yai
ma kaya niko ko kyale bai min ba.
Nayi arba'in da kwana daya sai ga Yaya Baffa yazo wai Alhaji yace in ajiye ma Tasi'u danshi in
bishi mu tafi gida.
Please manage.
Shin Bahijjah zata ijiye danta ta tafi ko zata zabi danta akan Alhaji?
Sai mun hadu a next page.
*_Fateeyzah_*✍
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
_*(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)*_
*GIDAN NAGOGGO*
*_( A true life story)_*
_*Written by fateeyzah*_
*Godiya gare ku real Fateeyzah novel group,ina jin dadin comment dinku ako da yaushe
especially maman Abdulaziz,Aisha jibril(Aj),yar Asalee da sauran members ina yinku.*
*Da masu kirana,da masu text ina yinku,naga tsakonninku na gode da nunamin kulawa da
kukayi.*
*Hafsat .s.bello(maman fadila) thanks for the visit,gskiya na ga alama ke babbar fan ce ta
GIDAN NAGOGGO, ina godiya*
*Aisha jibril(Aj)thanks for the call,Allah kara zumunci.*
*Sis Zuby Allah ya kara sauki,yasa kaffarane*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page3⃣1⃣to3⃣5⃣_*
Take naji hankalina na tashi,don kwata² na manta da maganar Alhaji na in na haihu zan
barmai yaron, tsawar da Yaya baffa ya daka munne ya dawo dani daga gajeran tunanin dana
tafi tare da fadin "don Allah Yaya Baffa kayi hakuri, bazan iya barin khaleel ba in tafi,don Allah
ka taimakeni ka rokon min Alhaji ya barni da dana"na karashe maganar ina zubar da wasu
zaffaffun hawaye.
Wata harara ya banka min tare da fadin "wai ke Bahijjah wata irin kafaffiyar yarinya ce,duk
wulakancin da Tasi'u ya miki ba ki gani ba,amma har yanxu kina nan nanike da dansa,mufa
gata muke so mu miki amma kinki ganewa, kinsan ko daya sake ki sai da muka sha artabu da
Alhaji kafin ya bari muka zo wurinki,amma kike nema ki watsa mana kasa a ido".
Dago kaina nayi a karan farko na kalleshi tare da fadin"wani irin gata ne wannan nasan rabani
da d'ana mai kwana arba'in da biyu a duniya, wanda ta dalilinsa na samu kaina a cikin halin
dana ke ciki,ta dalilinsa na rasa ubansa da yayyinsa, a yanxu in ka cire Ammy ba wanda
nakema son da nake ma khaleel a duniya, don haka in baza ka iya yimin taimakon dazan
kasance da d'anaba ka tafi ka barni kawai"na karashe magana cikin daga murya.
Yanayin yanda nayi magana da hargagi da kuka yasa jikinsa yayi sanyi tare da fadin "Bahijjah
kinsan halin Alhaji, inya zartar da hukunci ba wanda ya isa ya saba, Bahijjah duk irin rashin
jituwar dake tsakanin 'yan dakinmu da naku baki ji bakin cikin damuka tsinci kanmu ba da
mukaji sakin da Tasi'u ya miki, wannan ne dalilin dayasa mukayi confronting din Alhaji lokacin
da abun ya faru, dakar muka shawo kanshi akan muje mu dauko ki amma da sharadi inkin
haihu da zaran kinyi arba'in zaki maida mishi danshi, wanda daga baya kuma ya canza shawara
akan abarki anan, in kinyi arba'in din kya ijiye yaron ki dawo gida, a yanxu basan yanda zan
tunkari Alhaji akan ya barki ki koma gida da..... "Ringing din wayar shine ta katse mai magana,
cikin sauri yayi receiving din wayar tare da sata a speaker, muryar Alhaji ne ta doki kunnena
wanda dalilin haka yasa 'yan hanjin cikina kadawa, Yaya Baffa ne yayi mai sallama tare da
fadin" an wuni lafiya Alhaji"
Daga can bangaren Alhaji ya amsa tare da fadin " lafiya lau Baffa, kun tawo ne Saboda kunake
jira, don inason zuwa ta'aziya".
Saida Yaya Baffa ya kalleni, tunkunne ya kwashe duk yadda mukayi ya sanar da Alhaji, nan fa
Alhaji ya fara bambami, nan dai ya ringa bala'i, sannan daga karshe yace ma Yaya Baffa ya
taho ya kyaleni sannan ya shaidamin kar in sake in tako gidanshi batare dana maida dannan
ba.
Inaji ina gani Yaya Baffa ya tafi tare da cemun in mai kwatancen Gidan granny zaije ya sanar da
ita in yaso sai in koma wurinta da zama kafin su samo mafita.
Bayan fitarshi da awa biyu sai ga kiran Ammy inda take fadin mu Yaya Baffa ya kirata ya fada
mata komai,sun yanke hukunci zan koma Gidan Granny da zama, don haka gobe Aunty Asma'u
zatazo ta rakani Gidan, nan dai tayi mini nasiha tare da fadin wannan karan zata kai karar Alhaji
wurin Hajiyar Sokoto don ta gaji da irin abinda ya kemun.
Bayan na gama waya d Ammy ne kuma sai ga kiran Yaya Baffa inda yace min in turo account
number na, take ko na tura wanda anan yamin transfer dubu dari, kiranshi nayi don in mai
godiya anan yake cemin ya turamin ne don in samu sana'ar yi, nan dai shima yamin nasiha
sannan muka yi sallama.
Nan na zauna inata mamakin Yaya Baffa,don dai nasan da ba haka yakeba, don shima nuna
mana tsana yake kiri kiri, ina cikin wannan tunanin sai ga Humaira ta shigo nan dai na fada
mata yanda mukayi da su Yaya t Baffa,nan da muka fara kukan rabuwar.
Wurin karfe takwas na dare,sai ga Tasi'u ya shigo ya hada kayanshi dana yara da duk abinda
yasan mallakinsane yayi ta futa dasu,sai daya gama sannan ya miko min key tare da fadin in na
kwashe kayana na kulle ma masu gida dakinsu,bai jira cewata ba yasa kai ya fita ya barni da
tunani.
Ina zaune a inda yabar ni,ina ta juya maganarsa acikin kwakwalwata, don na kasa fahimtar inda
ya dosa, sai ga Humaira ta shigo cikin sauri tana kwala min kira, ganina zaune a parlour yasata
karasowa wurina cikin hanzari tare da cewa" Maman Iman kinji abunda na jiyo kuwa(na girgiza
mata kai)wai sauran sati uku bikin Daddynsu Iman".
Bakina na rawa nace mata"da gaske Humaira ko dai jita² kikaji kan cewa zai yi aure"
"Wallahi da gaskene don mai gidana ya fada mawa, na ma manta, yaufa ya tare a sabon
gidanshi tare dasu Iman da ummanshi", take naji cikina ya fara juyawa,nan danan naji wani
zazzabi yana son rufeni,ban san har yanxu akwai son Tasi'u a raina ba sai da naji maganar
aurensa, sannan gidan dana zabi plan da kaina shine wata zata shiga bani ba,nan dai naji wani
irin kishi ya rufeni, ganin halin da nake ciki yasa Humaira tafara lallashina tare da min
nasihohi,sannan ta tashi ta fita.
Daukar waya nayi nakira Ammy tana dauka na sa mata kuka tare da fada mata abinda naji
daga bakin humaira.
Gyaran murya tayi tare da cemin"Bahijjah mun riga mun sami wannan labarin, Alhaji ne yace
kar a fadamiki, don tunda Tasi'u ya sakeki da sati biyu aka samasa rana da wata yarinya anan
kaduna,don ko su Iman ba kudan ya kaisu ba suna nan gidansu amaryarsa"
Cikin rawar murya nace" Ammy duk kunsani kuka kasa sanar dani?, a ganina Ammy koda
Alhaji yace kar a fadamin ai ke bai dace ki'ki sanar daniba"
Cikin sanyin jiki Ammy tace"Bahijjah kiyi hakuri don sanar da ke baida amfani, mutuwar auranki
bakaramin rikici yaja a dangiba wanda yaja rarrabuwar kawunansu, a ranar da kika sanar dani
Tasi'u ya sakeki, saina kasa sanar da Alhaji don nasan duk abunda zai biyo baya ba mai dadiba
ne, sai na yanke shawarar kiran Baffa na fadamai wanda cikin tashin hankali ya hado kannisa
suka samu Alhaji suka fada mai, cikin bacin rai yace shi ba ruwansa, dakyar suka shawo kan
Alhaji inda ya yadda su Baffa su daukoki, bayan tawowarsu wurinki ne sai Alhaji ya dauki waya
ya kira Babban Tasi'u ya sanar dashi abunda ya faru, amma budar bakin shi sai yace ya sani,
don shi farin ciki ma yake Tasi'u ya rabu dake saboda wai Tasi'u yace rikemai riga kikayi kikace
in ya cika cikin uwarshi da ubanshi ya sakeki, shine shi kuma ya sakeki, haka dai yaci mutuncin
Alhaji a waya, wannan dalilin ne Alhaji yace a bari ki haihu anan,don bazaki kawo mai jinin
Tasi'u gida ba, wallahi bahijja ko da mahaifin Tasi'u ya rasu muka je gaisuwa bakiga irin
wulakancin da 'yan gidan suka mana ciki kuwa har da ummanshi, wannan dalilin ne yasa Alhaji
cewa ki ijiye khaleel ki dawo gida, don dacan ya sake shawara akan in kinyi arba'in ki dawo gida
da khaleel inyaso inkin yayeshi kya maida shi".
Cikin kuwa nace"Ammy tabbasa biri yayi kama da mutum don tunda Tasi'u ya sakeni wani dag
gidansu bai taba kirana ba, don ko lokacin da Alhajinsu ya rasu da na kirasu nayi musu gaisuwa
yanda suka amsa mini kamar akwai wani abu, ni kuma sai na dauka mutuwarce ta taba
su,Ammy ayau na tabbatar da Alhaji abunda yayi shine daidai, don haka zan ijiyemai danshi in
dawo gida tunda dai abun rashin mutunci ne".
Ya kuke gani,shin Ammy zata yadda Bahijjah ta ajiye danta mai kwana arba'in da biyu a duniya
ta koma gidan Alhaji?
_Sorry fans insha Allah daga next page zamu dawo cikin labari don jin yadda auren Bahijjah
na biyu zai kasance._
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*Fateeyzah*✍
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace, joint of entertainment and to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*Ta'aziya*
*Inalillahi wa inna illayyir raji'un.*
_Ina mika ta'aziyata zuwa ga ummu salma daya daga cikin member na_ *HIKIMA* *WRITERS*
*ASSOCIATION* , _na_ _rashin danta(naeem),wanda ya rasu ranar kamar haka
11/04/2020,muna rokon Allah ya jikanshi,ya gafarta masa yasa masu ceton mune,ameen._
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page3⃣6⃣to4⃣0⃣_*
"Kul Bahijjah, ki dena fadin zaki ijiye mai dansa, kina ganin abinda ya faru da zubaida
sakamakon rabata da danta da Alhaji yayi dan wata biyu,ranar kakarta t kawota gurin Alhaji
take fadamai, yanxu haka Asibitin mahaukata ake karbat mata magani, don doctors sunce
tunanin 'yayanta yasa kwakwalwarta ta tabu, don haka ki barshi da Allah duk abunda yayi, yai
ma kansa, sannan na san ki da kulafacin 'ya'ya don Allah kicire 'ya'yan nan aranki, sannan
karkiga garinku daya kiyi ta daukar kafa kina zuwa gidan, don bansan abunda za ayi ta kananan
magannanu akai, sannan kinsan irin gidan dazaki koma zama, don haka ki kama bakinki, ba
ruwanki da gulma da tsegumi irin na family house"haka dai Ammy tayi tamin nasiha sannan
mukayi sallama.
Washegarin ranar, wurin karfe goma na safe sai ga Aunty Asma'u tazo, nan muka samo
Almajirai suka tayamu kwashe kaya sannan muka rankaya har da Humaira sai dan bushiya
Gidan Granny.
Daki guda aka waremun a shiyar Granny,inda anan akasa mun kayana,suka gyara min daki
kamat wata amarya,sannan bayan la'asar suka tafi suka barni,wanda munci kuka da kyar
Granny ta rabamu(lol su Bahijjah masu idon kuka)
.
Kudin da Yaya Baffa ya bani,shine na dauka na siya keken dinki hade da materials,na fara
dinka gowns mai kamar jallabiya inasa stones,sannan ina dinka kimono,kasancewa dan
bushiya akwai gidan masu kudi, Sai ya zamana ina ciniki sosai don da kaina nake shiga gida²
ina masu talla.
A bangaren zamana a gidan,banda wata matsala da kowa,ban shiga shirgin kowa ,in mun hadu
a tsakar gida kuwa gaisuwa ke shiga tsakanin mu,in ko ban fito ba sai mu dade basu sani a ido
ba.
Su Iman kuwa, so biyu ina zuwa dubasu, nan na tarar yara sunyi kyau sunyi bul² kamar 'ya'yan
turawa don Amayar Daddynsu na kula dasu kuma Tasi'u yanxu kudi ya zauna mai sosai don
dakaga irin dukiyar da aka sama gidan kasan mai gidan ya jiku da naira, ko da naje nasamu
tarban mutunci a wurinshi da kuma Amaryarshi mai suna Sumayya don har mukai exchanging
din number sukace zasu ringa kawo mun su,aiko so biyu suna zuwa sumin yini ranar da ba
makaranta.
Gidan Alhaji ko so uku ina zuwa,wanda so biyu ya barni na shiga shima sai da nakai khaleel
Gidan Aunty Asma'u,ana ukun ne yace indai bazan maida khaleel ba kar in kuma shigo min
gida, haka nayita kuka tukunna nabar Gidan na koma Gidan Aunty Asma'u na kwana, washe
gari kuma na koma kaduna, wanda ina zuwa kuma na tarar da abin tashin hankali, barayi sun
shiga dakina sun dauke min keken dinki da naira dubu ashirin,take hankalina ya tashi haka
akayita min jaje, faruwar haka na shiga cikin wani hali, wanda ya zamana komai sai an taimaka
min dashi saboda rashin sana'a, yau da gobe sai Allah, ganin suma masu taimakona sun fara
gajiy yasa na fara sa'kar hannu,ba laifi ina ciniki, da haka rayuwa taci gaba, yau da dadi gobe
akasin haka.
A lokacin dana cika shekara daya a Gidan granny,sai autan su Ammy yazo zaiyi aure, kuma
dakin danake da dakinshi yakeso ya hadama Amaryarsa, hakan yasa na koma dakin Granny,
kayan dakina kuma aka kai ajiya makota. Gani haka yasa na kira Ammy a kan maganarmu ta
baya da tace zata yima Hajiyar Sokoto magana, shine tace in bari in hajiyar tazo bikin Yaya
sadeeq da za ayi zata mata magana.
Haka dai na cigaba da zama a gidan Granny cikin hakuri don ji na nakeyi a takure, don abinci
ma sai an kawo ma Granny daga wurin 'ya'yanta sannan nake sami