Showing 15001 words to 18000 words out of 23360 words
Chapter 6 - GIDAN-NAGOGGO-BY-Fateeyzah_.pdf
inci sabanin da kafin a sace
mun keke girkina nakeyi daban.
Anyi bikin Yaya sadeeq lfy,inda sai danayi danasanin zuwa don duk inda nabi su Aunty Mamy
nuna ni suke suna ga
bazawarar gidansu, washe garin bikin da sassafe nabar gidan don banason Alhaji ya ganni
saboda baison nazoba.
Biki da sati daya Yaya Arsala(dan Hajiyar Sokoto) ya kirani awaya yace in shirya in tafi sokoto,
nan ko nayi ta murna don nasan ko ba komai zanci in koshi.
*SOKOTO*
kamar yanda na fadi Hajiyar sokoto yaya take wurin Alhaji su biyu kadai ne awurin Hajiya Kaka,
farkon auranta tayine a Kudan inda ta haifi Yaya Kabeer(mijin Aunty Amina) daganan sai suka
rabu da mijin tayi aure a sokoto ,mijinta shahararren mai kudi ne kuma mai sarauta,wanda a
farkon auransu lagos a ka kaita saboda acan yake kasuwanci tana da yara takwas dashi, Aunty
Atika,Yaya Arsala, Aunty huzaima, Aunty zainab, Aunty Aisha, Yaya Alamin(wanda Aunty
zubaida ta aura kafin su rabu), Aunty shafa'atu da Aunty zuhura dukkansu sunyi aure sun
hayayyafa don akalla hajiya nada jikoki hamsin da hudu, ban taba ganin family masu zumunci
irinsuba dasu da 'ya'yansu kansu a hade yake, family ne da kowannensu yakeji da naira don
duk cikinsu ba mai auran talaka, kuma kowanne business sukeyi sosai ba matan ba,ba mazan
ba, hakan yasa kowa yake ji da kanshi a cikinsu.
Mijin hajiya Alhaji sammani kafin ya mutu yabar dukiya da yawa bacin gidaje,da gonaki har
kuma tsabar kudi, hajiya na zaune ne a Gidan Alhaji Arsala, don tunda ta gama aurarwa ya
zamana ita kadai ce a gida,sai ya sai wani karamin fili dake gefen gidanshi ya gina mata
3bedroom flat,sai ya zamana in kinshigo gate din gidan part dinta na hannun dama na Yaya
Arsala na hannun hagu dashi da matarshi da 'ya'yanshi shida biyu mata, hudu maza.
Tunda nake ba a taba karramani irin yanda akamin a sokoto, ina zuwa na tarar da an waremin
daki daya a part din hajiya an zuba min set din italian bed,ga plasma tv, Ac, center carpet da
sauran kayan bedroom.
Zamana a Sokoto,zama ne mai cike da FREEDOM inci,insha abunda nakeso duk wani jin dadin
rayuwa na sameshi a sokoto nan danan ni da khaleel hasken mu ya fito muk kara wani kyau
don duk wanda yasan mu shekara daya baya zuwa yanxu yasan mun canza, anan ma na
cigaba da sakata ina samun kudin kashewa, banda wata damuw don ko duk Gidan mu daga
Ammy sai 'yan dakinmu suka san ina Sokoto,don Yaya Arsala ne yace kar a fadama Alhaji don
yasan zai iya hanani Zuwa.
Watana you a Sokoto akayi karamar sallah,mun samu kaya dani da khaleel sosai, don ni ina da
kala goma, khaleel na da shabiyu, don duk cikin 'ya'yan hajiya kowa sai da yamini kayan
sallah,anyi sallah da kwana biyu sai ga Yaya Farooq yazo gaida Hajiya aiko nan yayita
mamakin ganina, ni kuwa tsurewa nayi don nasan dole zai fada ma Alhaji.
Anyi sallah da sati biyu na yaye khaleel,sannan na daukeshi na kaishi kaduna na mika ma
ubansa daga nan na wuce zaria, ina zuwa Alhaji yace in wuce in bashi wuri in koma inda na fito
tunda sanda yace in bar yaron banji maganarsa ba, sannan wai don na rainashi da munafunci
irin na Ammy dani na dauki kafa na koma sokoto ba tare da mun sanar maiba haka ina kuka
nabar gidan,don bakinciki ko Gidan Aunty Asma'u banjeba na wuce park na hau motar Sokoto.
Tunda na dawo daga sokoto ko hajiya ta shiga gyarani don kullun addu'arta insamu miji anan
inyi aure ko na samu kwanciyar hankali.
Satina biyu da dawowa daga zaria sai ga Aunty zubaida tazo wadda kallo daya zaka mata
kasan kwakwalwar tata da matsala,nan dai hajiya tayi ta neman mata magani don abin nata
kamar asiri saboda wani zubin lafiya wani zubin cuta.
Ana cikin hakane kuma kawu Muhammadu ya kirani yake sanar dani dakin da akasa kayana ya
fadi,sundai kwashe kayan amma duk wasu sun fashe, dana sanar da Yaya Arsala sai yace in
shirya in tafi in duba kayana, dazan wuce sai ya hadani da Aunty zubaida in kaita wurin mai
magani da ya samu nan kaduna.
Bayan naje na duba kayana wanda duk wani kayan kitchen dina da kujera sun lalace,kayan
gado kawai na tsira dashi, daganan nan kuma muka nufi gurin mai magani da Aunty Zubaida.
Bayan mai magani yayi mata tambayoyi yace mun aljanu aka turo mata,kuma ba shiganta
sukayiba,shafenta sukeyi,sannan wani dan uwa na jikine yasa a tura mata, sannan makaryinsa
sai dai a maida ma wanda ya turota........kakakarakara,asirin wasu ya kusa tonuwa.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*Fateeyzah*✍
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment,to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page4⃣1⃣to4⃣5⃣_*
Daukar waya nayi na kira Yaya Arsala na sanar dashi abunda mai magani ya fadi, sai yace
adai yimata magani amma kar ace za a maida ma wani tunda yace cikin 'yan uwane, anan dai
malam yace maganin na sati biyu, hakan yasa Yaya Arsala yace in zauna harsai angama
maganin sai mu dawo tare.
Kwana na biyar a kaduna na shirya na tafi ganinsu Iman, tarba akamin ta mutunci kamar yanda
aka saba, kuma naji dadin yanda sumayya take kula dasu especially khaleel dana ga ya zamo
wani kato kuma ya dada wayo(rainan madara), suma su Iman da ka gansu kasan suna jin
dadin zaman gidan,nayi mamakin yanda yaron bai manta dani ba don yana ganina ya taho da
gwarancinsa yana cewa yummy(mummy), wannan karan harta umma ta sakarmun fuska don
haka tayi ta jana da hira, nan dai na basu chocolate din dana saimusu na dawo Gidan Granny
cike da kewarsu.
Washe garin ranar da naje wurinsu Iman sai ga kiran Tasi'u, ina dauka muka gaisa yake
tambayara ashe nazo kaduna, nace mai kwanana shida kenan, nan dai yayi ta jana da surutu,
tun ina biye mai har na gaji nayi mashi sallama.
Bayan kwana uku,ranar na tashi da kewar yarana , hakan yasa na daidaici lokacin tashinsu
break na shirya na tafi school dinsu, nan dai na gansu mukayita hira tare da daukar hoto, harsai
da aka kada bell na komawa class tunkunna nabarsu suna daga min hannu,nima ina daga
musu.
_( rabuwar aure wallahi bata da dadi,especially in akwai yara a tsakani,sai yara su taso
kamar marayu gasu dai suna da iyaye duka,amma rashin iyayen a wuri daya matsala ne duk
yanda wata zata kula miki da 'ya'ya ba kamar yanda ke zaki kula dasu ki basu tarbiyya ba,inma
aka hadu da mai rikon mara kirki sai tayi ta azabtar da yaran, amma kuma wani auren
rabuwarshi shinr maslaha kamar wannan na Bahijjah mai cika da matsaloli wanda har takai
babu ganin girma da mutunci tsakaninsu, Allah ya tsare ya kara dangana, hakuri da soyayyya
tsakanin ma'aurata ya shiya mana 'ya'yanmu,shiriya ta tafarkin addinin musulunci,Ameen)_
Ina tafiya ina kokarin maida kwallar dake shirin futowa,kiran sunana da akayine yasa ni saurin
juyowa,Yaya Mahmood na gani(yaya Mahmood cousins yake wurina, amma dangantakarsu tafi
kusa da Tasi'u), nan dai na karasa muka gaisa sannan ya tambayeni hala su Iman nazo gani na
amsamai da eh,nan dai yayi tamin fada na zubar da zumunci tunda na rabu da Tasi'u ko kira
banayi a gaisa nan dai nayi ta kawo excuses, sannan muka yi sallama muka rabu.
_(Haka mutane suke,su suke zubar da zumunci amma insun ganka suyita borin kunya wai
bakason zumunci)_
Bayan kwana biyu, ina zaune ina shafa ma Aunty Zubaida magani, kawai sai ga kiran Alhaji ya
shigo wayata, take gabana ya yanke ya fadi, don nidai a wurina kiran Alhaji ba Alkhairi bane a
wurina, sai da wayar ta kusa katsewa tukunna na dauka cikin rawar na dauka tare da karawa a
kunne hade da sallama, ya amsa sallamar tawa tare da fadin "uban mai ya kaiki kaduna?" yayi
mini tambayar hade da hargagi.
Cikin rawar baki nace"naje kai Aunty Zubaida wurin mai magani ne daga nan kuma na duba
kayana da akace ginin dakin ya fadi"
Cikin daga murya yace"Bahijjah yaushe kika fara karya?, kuma karyar ma kirasa wa zakiyi
mawa sai ni"
Cikin sanyin jiki nace" wallahi Alhaji ba karya namaka ba,kafi kowa sanin ko yankani za'ayi indai
na........"bai bari na karasa maganaba ya yanke kiran.
Haka ranar na wuni suku²,don duk iya tunani na na kasa tuna laifin dana yi ma Alhaji.
An gama yima Aunty Zubaida magani,inda abin nata yadanyi sauki, kwana biyu muka kara
muka kama hanyar Sokoto.
Bayan mun huta tukunna Hajiya da Yaya Arsala suka kirani palour,jin kiran sai da gabana ya
fadi don nasan ba lafiya ba, ina zuwa yay Arsala ya fara magana cikin bacin rai"Bahijjah kinsan
maganganu da tijara da kika jama na cikin dangi kuwa?".
Jikina na karkarwa nace "A'ah".
Yace"maganganu nata yawo cikin dangi akan kinje kin samu Tasi'u kina kuka akan ya maida ke
dakinki, hakan yasa yace muki bazai maida kiba don Allah yace inkin koma bashi bake, Amma
wai sai kikayi hugging dinshi kika ce wai ya maida ke zaki zauna dashi yabar maganar
Alhaji,shine yanxu muka kiraki muji gaskiyar magana don na kasa gasgata haka".
Cikin matukar razana na zayyane musu abunda ya faru, ina fadi ina kuka,don tunda nake ba'a
taba mun irin wannan sharrinba.
Take Yaya Arsala ya kira Alhaji ya zayyane mai abunda ya faru, nan Alhaji yace abar maganar
zai zo da babbar sallah.
Anyi sallah da kwana biyu su Alhaji suka zo Sokoto, bayan sun ci abinci sun huta aka fara
meeting wanda duk akaina akayisa,nan dai aka maida magana akamana sulhu da Alhaji(dani
da Aunty Zubaida)nan dai Alhaji
yace ya hakura sannan yace kowa ya zama shaida ko bayan ransa na koma Gidan Tasi'u bai
yafemun ba.
Kwanan su biyu tukunna yace mu shirya yatafi damu don canma zaria meeting din zamuje
muyi.
A ranar da muka dawo ba karamin farinciki na tsinci kaina ba saboda ko ba komai ranar na
shiga gidan Alhaji batare daya koreni ba, kwana mukayi muna hira da Ammy don rabon da mu
zauna muyi hira batare da wata fargaba ba shekara goma kenan.
Washe gari,Alhaji ya hada meeting wanda duk wani dan gidan sai daya halatta, nan dai Alhaji
yayi mana nasiha tare da nuna mana muhimmancin zumunci, da alama dai mazan jikunansu
sunyi sanyi don har gafarar Ammy suka roka sabanin matan da sai wani cika suke yi suna
batsewa.
Satina daya a zaria na fara shirin komawa Sokoto,ba yadda Ammy bata yi daniba akan in bari
akwai buki a gidan Aunty jummai dake katsina(kanwar Alhaji dasuke uba daya ita zata aurar da
danta)amma naki,don gaba daya dan zaman gidan da nayi naji zaria ta fitarmun a rai,haka na
shirya kayana na koma Sokoto.
Daga nan Sokoto ma Aunty shafa ce kadai taje bikin, itama kwananta biyu ta dawo.
Ina kwance da dadddare sai ga kira ya shigo wayata,ganin number ba suna yasa naki daga
wayar, sai da aka kira so uku tukunna nayi picking, muryar babban magidancine ya bugu
kunnena, jin hakan yasa na gaisheshi cikin girmamawa, bayan mun gaisa tukunna yayi gyaren
muya tare da fadin"Bahijjah nasan baki gane mai magana ba,sunana Alhaji Suleiman,ina zaune
ne a garin kano,inada mata biyu da yara hudu, ban taba ganinkiba amma na karfi number ki a
wurin kawunki ne Alqasim da yake kano, abunda ya faru shina naje biki katsina ne kasancewa
Mamar Aunty Jummai kanwa take a wurin babana,to anan naga 'ya'yanki kakarsu taje da su
bikin,to gaskiya yaron sun bani sha'awa anan na tambayi Aunty umma(kanwar Aunty Jummai)
yaron waye,anan dai ta bani labarin ki da abunda ya faru dake ba,gaskiya anan naji na kamu da
sonki, ban yi nauyin bakiba na fada mata ina sonki, anan dai ta fada ma Alqasim da mijinta
sabitu kasancewa sabitun yaya nane uban mu daya, shine sai Alqasim ya bani numberki"ya
karashe magana cikin sanyi murya.
Nan na rasa bakin magana don jin maganarshi nayi kamar saukar aradu,sai da yayi gyaran
murya sannan na dawo daga guntun tunanin da na tafi tare da cewa"ya za ayi baka ganniba
amma kace kan sona?, don kaga 'ya'yana bai zama hujjar daza ka amince dani ba.
Ajiyar zuciya yayi tare da fadin"ina nan zuwa Sokoto sati mai zuwa saboda akwai wani abokina
senator dazai kara aure, in nazo zan karaso wurinki".
Hmm ya kuke ganin,don da alama Bahijjah ta samo babban fish,abokin senator fa.
Sorry for the errors ban yi editing ba.
*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*
*_Fateeyzah_* ✍
[4/17, 12:47 AM] ~Fateeyzah✍✍: *© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)_*
*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*
*_Written by fateeyzah_*
*_Bismillahir rahmanir rahim_*
*_Page4⃣6⃣to5⃣0⃣_*
Haka dai mukayi sallama dashi, yabarni inata sake² don ban dauki maganarshi da wani
muhimmanci ba,don a ganina daga gani 'ya'yana kawai batare da ya ganniba sai yace yana
sona.
Washe gari kuma sai ga Aunty Umma ta kirani,bayan mun gaisa again dai maganar Suleiman
tayi mini,tare da gargadina kar in basu kunya don suna son nuna ma Tasi'u da magoya
bayanshi nafi karfinshi da har zai min sharri wai naje ina kuka ya maidani, bayan mun gama
magana da ita ta umurceni da in kaima Hajiya wayar, nan dai nakai ma Hajiya wayar, bansan
yanda suka Kare ba ,don ina bata wayar na juyo dakina ita kuma Hajiyar bata cemin komai ba.
Tunda ga ranar Suleiman kullun sai ya kirani so hudu, tun ban saki jiki da shiba,har nazo na
yi,Suleiman namijine da ya iya tattali don yadda yake nuna min so bazakiyi tunanin ya ajiye
mata biyu ba har da yara hudu.
A cikin satin nan nayi wani irin sabo dashi, wanda nake ji kamar mun yi shekaru tare, don wani
irin zafaffan so nake masa wanda nima bansan lokacin daya shigeni ba, don a wannan lokacin
na tabbatar da son dana yima Tasi'u kadan ne akan wanda nake yi ma Suleiman.
Week na zagayowa kamar yanda yayi alkawari sai gashi yazo,kallo daya zaka masa kasan
akwai 'yan gidan rana(naira),wanda yasha shaddar shi gezna sai kyalli takeyi,chocolate color ne
gashi giant,duk inda ake neman namiji, Suleiman yakai har ya wuce, nan dai na sauke shi a
falon hajiya sannan na fara kawo mai su snacks da abinci dana tanada donshi,sai daya cika
cikinsa sannan ya shiga ya gaida hajiya da Aunty suwaiba(matar yaya Arsala)sannan muka
dawo parlour muka dasa hira, duk da yawancin hirar shi yakeyi don ni daga eh sai a'ah.
A dan zaman da mukayi na fahimci Suleiman mutum ne mai saukin kai, ga sanin ya kamata nan
dai ya tabbatar mun shifa da gaske yake,don in so samune in aka tashi saka rana a saka wata
daya, haka dai mukayi ta hira har Yaya Arsala ya dawo suka gaisa nan ya sanar da Yaya Arsala
yanaso ya turo iyayensa amma kafin nan yanaso inje inyi HIV da Genotypes test nan dai nan
dai Yaya Arsala ya amsa mai da zanyi kuma shima yanaso yayi bincik, inyaso in ya kammala ya
turashi wurin Alhaji, anan dai sukayi sallama dashi.
Dawo wa gurina yayi mukayi sallam, ya kirgo 30k ya bani tare da fadin ga kudin hira Kya sa
kati, nan dai nayi godiya tukunna namai rakiya ya tafi don jirgin karfe hudu zai bi zuwa kano.
Bayan sati daya naje nayo test inda result ya fito HIV Negative, Genotypes kuma AA, nan nayi
snapping na tura masa shima ya turo min nashi wanda the same thing ne da nawa.
Bayan sati biyu yaya Arsala ya gama bincike sannan ya kira Alhaji ya sanar dashi nan dai Alhaji
yace ya waliyi na, amma aje Kudan a daura aure, nan dai ya tsayar da ranar sati biyar.
Suleiman dubu dari uku ya bani in hada lefe, sannan danace mai zanje kaduna in gyara kayana
ya bani dubu hamsin(wanda nayi karya nacema Yaya Baffa dubu goma ne)naki fada mai
gaskiyane sabodah nasan sai ya fada ma su Aunty Amina.
Bayan nanne ya zamana in nakira Alhaji bai daukar wayata,ni kuma danaga baya dauka sai na
dena kiransa.
Biki yana sauran sati uku shine na shiryo don in gyara kayana,wanda na biya gidan Alhaji yayi
mini koron kare batare da nasan abunda nayi masa ba.
*BACK TO STORY*
Nauyayyar ajiyar zuciya na saki yare da goge hawayen dake idona, jin an tada kiran sallar
magariba ne yasa na mike da sauki na fito,a kofar daki na taradda Granny na alwala kallona
tayi tare da fadin "sannu hakima,sai yanxu kika tashi daga baccin asara, ai da niyata inna gama
alwala inje in tashe ki da ruwan sanyi"ta karashe magana tana miko min butar hannunta.
Karfa butar nayi yare da fadin"ni ba bacci nayiba,tunanin rayuwar gidanmu nayi".
Tabe fuska granny tayi tare da fadin"rayuwar gidanku har abin tunawa ce, ai wannan mai hancin
kamar biro itace matsalar gidanku,amma da *NAGOGGO* zai gane daya bincike rayuwar
gidanshi"ta karashe magana tana shiga daki.
Inayi sallah isha'i naci abinci nayi shirin bacci na haye gadon Granny na kwanta,kamar jira yake
sai ga kiran Suleiman, nan dai muka gaisa sannan yake cewa "wai darling