Showing 6001 words to 9000 words out of 23360 words

Chapter 3 - GIDAN-NAGOGGO-BY-Fateeyzah_.pdf

Fateezay   

28 Jun 2025

1261


_Bismillahir rahmanir rahim_


*_Page_* 1⃣2⃣


Ganin jinin na bin kafata yasa Tasi'u ya kara rikicewa,ihun dana kuma saki ne ya dawo dashi
hayyacinsa,daukan key din motar yayi tare da sunkuta ta yayi waje dani,sa key yayi ya bude
motar ya kwantar dani a back seat ,shiga driver seat yayi ya figi motar a guje,Da taimakon
Allah muka isa ABUTH dake Tudun wada saboda reckless driving da yayi,yana parking ya
kuma sunkuta ta da gudu ya shiga cikin Asibitin dani,da gudu nurses sukakarbeni a

hannushi,daganan kuma ban san abunda ya faru ba sai farkawa nayi naganni daure da drip a
hannuna,ga cikina ya na min wani matsiyacin ciwo,gefen damana kuma Tasi'u ne a
zaune,wanda kallonshi da nayi sai da na shiga cikin firgice,don fuskarshi da idon shi yayi wani
irin da alamun yasha kuka,juyin da cikina yayi shiyasani fasa ihu,da sauri ya juyo gareni,irin
kallon daya watsa min shiyasa na manta da ciwon dana ke ciki,don in idona bai min karya
tsanata na gani a idon Tasi'u.

Har gari ya waye,yana zaune a inda yake bai kuma kallon bangaren da nake ba ballantana insa
ran zai mun magana,ni kuma na kasa mai magana saboda wani tsoronsa da ya shigeni.

Sai around 7,tukunna naga ya tashi yana jan kafa ya fada toilet din dakin, sai da yayi kusan
minti biyar tukunna ya fito da alamar alwala yayi,fita yayi daga dakin.
Zafin dana ji a hannuna ya dawo dani daga gajeran tunanin da na shiga,drip din dake hannuna
ne ya kare har ya fara dawowa da jini,yunkirin tashi nayi amma na kasa.

Turo kofa akayi aka shigo,Tasi'u ne da doctor,da sauri suka karaso wurina ganin yanda jinine
ke dawo cikin cedar,cire min drip din yayi tare da"sorry madam,bamu zo da wuriba".kada kai
kawai nayi.
Wurin karfe takwas sai ga Aunty Asma'u tazo,lokacinne kuma naji Tasi'u yake mata sallama zai
je ya dadi.
Tunda na kwanta Asibiti ba wanda yazo agidan sai Aunty Zeena,shima bata dadeba ta tafi,naso
tambayar Aunty Asma'u datake jinyata Amma itama ba fuska,Tasi'u ko a Asibitin yake Wuni
amma ko magana bata shi ya tsakaninmu don ko na masa bai amsawa.

Sai da na kwana biyar A Asibiti sannan akayi discharging dina,direct GIDAN Alhaji aka wuce
dani,dakin Ammyna Auto Asma'u ta kaini nayi wanka,sannan muka je parlourn Alhaji wanda duk
yaran gidan,masu aure,da marasa shi duk suna parlourn,ina hada ido da Ammy ta sakar mun
harara,saurin dauke kaina nayi tare dajin wani takaici ya rufeni,har na samu wuri na zauna ba
wanda yamun magana sai ido da kowa ya zuba min,Aunty Amina na hango zaune a gefe tayi
tsiru tsiru,duk alamun rashin kwanciyar hankali ya bayyana a fuskarta.

Mun kusa minti goma da zama sai ga Alhaji da Tasi'u sun shigo,samun wuri sukayi suka
zauna,sannan Alhaji ya dago Fuska a hade ya yaficeni da hannu,take cikina ya kada haka na
tashi jikina a sanyaye,ina zuwa na tsugunna a gabanshi,baiyi wani jinkiri ba ya tsinkeni da mari
........





More comment,more typing

*Comment*
*Vote*
*Like*
*Share*






*Fateeyzah* ✍



*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story_)*


*_Written by fateeyzah_*


Wannan page din naki ne,Aminiyar kwarai,sahibata,is easiest to cut my hand than to loose u as
a friend, *SOPHIE* *MUHAMMAD* *BUBA*‍❤‍‍❤‍ (The potential banker and the financial
analyst),Allah ya barmu tare har *CBN*(insha Allah),Allah kuma ya nuna min auranki da
*ABDULJABBAR*❤
*Fateeyzah* *novel* *group* inaji dadin addu'ar ku ako da yaushe,ina godiya.

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_Page_*1⃣3⃣.

Marin da yamun sai da yayi sanadiyar dauke war jina� na wasu dakika alokacin da jina ya
dawone,na tsinci Alhaji na magana cikin matsinancin fushi"wai bahijja yaushe zakiyi
hankaline,wace irin dakikiya ce ke,duka duka shekarunki goma sha takwas a duniya amma har
kin iya shan magani don ki zubar ciki(duka ' yan parlourn suka dau salati don yawancinsu basu

sasan dalilin da Alhaji ya kira wannan meeting din gaggawar ba)sai da parlourn yayi shiru
tukunna,sai nan Alhaji ya cigaba da bambami wanda ayanxu bazan iya tuna wa duka ba,ranar
na sha zagi don Allah komawa yayi kamai wani bamaguje,sai da ya gaji don kansa sannan ya
umurci Tasi'u yabani key din dakina in tashi in tafi don yana son magana dasu,haka na karfi key
na tashi na fita hawaye na bin idona,haka na kama hanyar gida ba tare dana damu da kallon
da mutane ke bina dashi ba.

Ina shiga gida na hadu da Aunty Zeena ta fito part dinta,ganin yanayin da nake ciki yasata
karasowa da sauri tana tambaya ta mai ya faru,amma nakasa bude baki in bata amsa haka ta
jani har part dinmu ta karfi key din hannuna ta budemin dakin muka shiga ta zaunar da ni akan
two seater,direct fridge dina Ta nufa ta dauko min maltina mai sanyi ta bude min ta kafa min
abaki,batare da bata lokaci ba na shanye tas,sai databari na dan wuta,sannan ta kuma
tambaya ta mai ya faru,kwashe duk abinda ya faru nayi na fada mata tun daga maganin da
Aunty Amina ta bani har abunda ya faru a gidan Alhaji,nan ta hau salati tare da fadin lallai biri
yayi kama da mutum,saurin kallonta nayi tare da tambayar mai ya faru?.
Gyara murya tare da fadin"ana sauran kwana biyu ki kwanta a Asibiti naji Aunty Amina na waya
tanan bayan window bedroom dina tana cewa kamar ma ciki gare ki,bansan dai da wanda take
wayaba amma nadai ji ta ambato sunanki ina kyautata zato indai bada Aunty Hauwah take
waya ba to da mamy ne takeyi,to tunda naga su Mamy sunzo nidai jikina bai bani ba banzo dakin bane saboda Aunty Hauwah kinsan na samu matsala da ita saboda salma
lokacin bikinki"?
Nace "ai ban sani ba"
Tace"abunda ya faru shine yaya Farooq ne ya dinko mana dogayen riguna na shadda ni da
salma,sai ya kasance dankwali daya ne shine sai na dauki dan kwalin sai ya kasance na salma
ba dan kwali,kinsan namiji da yakai mata kayan sai Ummy ta tambayeshi ina dankwalin,sai ya
ce mata wai guda daya ne kuma na dauka,to bansan yanda akayi ba sai ga salma tazo wai in
bata dankwali,ni kuma na ce bazan bada ba,shine fa ta fara fadamin bakaken maganganu,ni
kuma naga bazan jura ba na mareta,to bayan ta tafi ne sai ga Aunty Hauwah tazo wai rama
mata mari,nan fa muka fara cacar baki sai ga daddyn Abdul(Yaya Farooq) ya shigo shine fa da
yaji abunda ya faru ya bata rashin gaskiya".
Na numfasa tare da fadin"Allah ya kyauta,ni yanxu matsalata Yaya Tasi'u,bansan yanda zan
bullo mai ba don fushi yake dani sosai,saboda tunda na farfado a Asibiti bai mun magana ba"na
karashe magana tare da goge hawayen da ya sulalo daga idona.

"Daurewa zakiyi ki kaskantar da kanki ki basa hakuri amma kar ki yarda yasan da sa hannun
Aunty Amina a wannan lamarin saboda in ya sani abun zai fi kamari"cewar Aunty Zeena.

Nace"zanyi kokari Allah ya daurani kanshi"
Tace" amin,amma Bahijjah ina mamakin Aunty Amina,ban taba tunanin zata aikata haka
ba,shiyasa Aunty Hanna tace min inyi taka tsantsan da ita don green snake ce under the green
grass,duk ita take kitsa musu duk iskancin da sukeyi"
Nace "Allah ya kyauta nima dai nayi saurin sakin jiki dasu"
Tace"gaskiya kam,bari in kawo miki,Abinci don nasan baki ciba"fita yayi daga dakin.

Sai da tayi minti biyar sanna ta kawo mun abinci tare da fadin"kici kisha magani,bari inje
inshirya su Abdul zasu tafi islamiyya hudu tayi".

Sai da naci Abincin, nasha magani,sannan na wuce Kitchen don in dafa ruwan wanka,ina
tsugunne sai ga Aunty Amina tayi shigo,motsin ta danaji ne yasa ni dago kai,muna hada ido ta
watsa mun harara sannan ta bude dakinta ta shiga.

Anan na zauna har ruwan yayi zafi na juye nashiga nayi wanka.
Bayan na fito wanka ne ina zaune ina shafa mai sai ga kiran Ammy ya shigo ta phone dina,cikin
sanyi jiki receiving tare da sallama,na gaisheta ta amsa tare damun ya jiki,sannan tayi gyaran
murya tare da cewa"Bahijjah na kira ne ki fadamin gaskiyar abunda ya faru don zuciyata taki
amincewa ke kika zubar da cikin sunna,saboda nasan baki da wayewar da har zaki aikata
haka".
Nan na kwashe duk abunda ya faru na fada mata,salati tayi tare da fadin"Amma Amina bata
kyautaba,girman ta baida amfani,ita da ya kamata ta tsawata miki,Amma ita ta aikata haka,Allah
shi kyauta kuma banaso Tasi'u yaji maganar nan saboda duk lalacewa dai 'yar uwarkice".
Nace"insha Allahu Ammy bazai jiba".nan dai tamin sallama tare da jamun kunne akan Aunty
Amina.

Juyowar da zanyi kawai muka hada ido da Tasi'u,yanda naga idonshi ya kada yayi jane ya
tabbbatar mun da ya gama jin maganarmu da Ammy,take naji gabana ya fadi,juyawa naga yayi
cikin tsananin fushi ya fice daga dakin,hankalina naji ya tashi don bansan hukunci da zai yanke
ba. Ji nayi yana ta kwada ma Aunty Amina kira tare da bugun kofar dakinta.




Don jin yanda zata kaya a *GIDAN* *NAGOGGO* sai ku jira next page.


More comment,more typing



*Comment*
*Like*
*Share*
*Vote*

*_Fateeyzah_*✍




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*



*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*

*_Written_ _by_ _fateeyzah_*


*_Jinjina gareki 'yar GIDAN DC,Hauwah A Abba(mrs Mur)Allah ya bar kauna_*❤.

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_Page_* 1⃣4⃣ *_to_* 1⃣5⃣

Jin kiran da yake mata ne yasa gabana ya fadi, ban tsaya dogon tunaniba na yi hanyar fita
dakin, fitowa ta yayi dai² da bude kofarta, tsaye tayi tare da watsa mai hararara hade da
cewa"wai kai Tasi'u me ke damunka ne kake ta kwala mini kira sai kace wani mahaukaci, kaje
kaji da abinda mahaukaciyar matarka ta yimaka, ba kazo ka sauke fushinka akaina ba,ai bani
na kashe zoman ba,rataya aka ban"ta karashe maganar tana yamutsa Fuska.

Gyara tsayuwarsa yayi tare da yamutsa fuska yace"ba wannan ya kawo niba,nazo ne in miki
gargadi hade da kashedi ki fita daga harkar matata, don naji abunda kikayi na bata magani ta
zubar min da ciki,to wallahi ki shiga taitayinki,in ba haka ba zan nuna miki true color dina, don
naga Alamar baki da mutunci,(ya tsaigaita da magana for 3seconds,sannan yaci gaba)kuma
daga yau na yanke alakar da ke tsakaninku".
Yana gama fadin haka yazo ya wuce ta gefena ya shige daki,niko ina tsaye kamar mutum
mutumi,don na kasa ko motsi,ita ko Aunty Amina jikinta a tsanyaye taja tsaki ta shige dakinta
hade da turo kofa,haka naja kafata hade da dafa bango na shige daki.

Direct Bedroom na nufa don ina kyautata zaton acan zan sameshi,ina shiga na ganshi zaune a
gaban mirror dafe da kanshi,wurin shi na nufa gwiwata a tsanyaye na zube a gabanshi tare da
kai hannuna kafarshi,ban zata ba naji saukar mari a kumatuna, saurin sakin kafarshi nayi don ji
nayi duniyar na juya min don tun da nake ba a taba min marin daya shigeni ba irin
wannan,saboda masifar shigata da yayi na kasa kuka sai sauke ajiyar zuciya nake,ganin yana
kokarin mikewa yasa naja baya da sauri,ji nayi ya damkoni,da sauki kulle idona ina jiran saukar
wani marin,sai jinayi yayi hugging dina hade da fashewa da kuka,nima kukan na saka tare da
kankameshi,haka mukayi tayi babu mai lallashi.(Allah sarki Bahijja yanxu kika fara
kuka).

Sai da mukayi kukan mu muka gaji tukunna muka kwanta kowa na sakin ajiyar zuciya,anan
bacci ya daukemu wanda sai kiran sallar magariba ne ya tashemu(kasancewa jikin gidanmu
akwai masallaci),tashi yayi ya fita ba tare da ya tanka munba.

Sai wurin karfe Tara ya dawo hannunshi dauke da takeaway wanda ledan ke dauke da tambarin
chicken republic,yana ajiyewa ya kuma fita sai gashi da plate da fork,fridge ya bude ya dauko
maltina guda biyu yazo ya ajiye akan center Table,takeaway ya bude hade da juyewa a plate
gasasshiyar kaza ce wadda taji hadi,haka ya ringa yaga ya na samun a baki hade da maltina
sai da nace mai na koshi, tukunna ya fara cin nashi.
Sai da ya gama ya tattara kayan yakai kitchen hade da daura ruwan wanka aka gas,tukunna ya
dawo daki ya kunna TV hade da kamo tashar Mbc Action yana kallo,zuwa nayi na durkusa a
gabanshi tare da kamo kannunshi na rike ina zubar da hawaye hade da fadin"Yaya Tasi'u
bansan da wata irin kalma zanyi amfani wurin baka hakuri ba,amma don Allah ina rokon ka ka
yafe mini ko na samu sassauci acikin Zuciyata ba,domin wallah fushinka a gareni zai iya sa in
shiga halin da yafi wanda na tsinci kaina kaina yanxu a ciki,wallahi nayi nadama ji nake na
tsani kaina tunda har zan iya saba ma mahaliccina,sannan kuma na yaudari mijina wurin zubar
mai da jininshi"na karashe magana hade da fashewa da kuka.

Hannu yasa ya sharemin hawaye tare da sauke numfashi yana fadin"komai ya wuce Bahijjah
amma ki sani abinda kikayi ya fara sani shakku akan kina sona kuwa,don da kina sona da baki
yadda an baki maganin da kika zubar min da jinina ba,amma innayi la'akari da auren hadi aka
mana,sai inga kamar an miki dolene wurin aurena,saboda tun kafin auremu ban taba ji kin bude
baki kin fada min kalmar I LOVE YOU a bakiba koda bata kai ZUCIYA ba"

Nayi saurin cewa"Wallahi yaya ina sonka,sharrin shedan ne kawai hade da zugin su Aunty".

Yace.shikenan ya wuce sai ki kiyaye gaba sannan ki dukufa wurin rokon Allah yafiyar abinda
kika aikata,sanna daga yau bake ba Aunty Amina ban yadda ki ringa shiga dakinta ba ko wata
magana ta hadaku mai tsawo,abunda na yarje miki shine yimata sallama ko gaisuwa".

Nace.insha Allah zaka sameni da bin umurninka".

Kamoni yayi yai hugging dina tare da fadin"shikenan Allah ya miki Albarka,amma ya kamata a

canza mun suna daga Yaya ya koma Sweetheart ko baby,tunda yau dai an tabbatar mun da
ana sona".

Sunne kai nayi ina dariya,a wannan daren yaya Tasi'u (awsweetheart) ya nuna mini soyayya
don hatta wanka sai da yamin kafin mu kwanta.
Sai da ya kara kwana biyu tukunna ya koma Lagos ya barni da kewa.

Tunda ga abunda ya faru,sai ya zamana ko na gaida Aunty Amina bata amsawa ,yaranta ma
basa shiga harkata,sai ya kasance ina zaman kadaici a gidan don itama Aunty Zeena ta samu
admission a A.B.U,yaran Aunty Amina kuma in suka tafi school tun safe sai yamma.
Da naga zaman ya fara isata sai na fara zuwa gidan Alhaji in a rage wuni,nan ma a rana ta
hudu Alhaji ya koroni yace na cika yawo,bayan nan Kuma su Aliyu suka fara zuwa suna tayani
hira in sun dawo makaranta,nan kuma Aunty Amina tace in sunzo wai suna mata rashin kunya
basu gaisheta,daga nan Alhaji ya hanasu zuwa.



Bayan shekara biyar,A lokacin inada 'ya'ya biyu duka mata, Amina(Iman) da maryam(Ilham) da
kuma cikin na uku.

A lokacin da cikina ya kai wata takwas ne mai afkuwa ta afku, abinda ya faru shine ana sauran
kwana biyu sallah Daddyn su Iman ya dawo daga Lagos, sai na dafamai ruwan wanka na kai
bathroom,nashiga daki in dauko sabulu, kawai ina fitowa sai naga Aunty Amina ta zubar da
ruwan ta jefo min bucket dina waje, ni kuma naga bazan iya daurewa ba sai na tambayeta
dalilinta nayin haka, budar bakinta kawai sai ta cemun gani tayi wanda aka kai ruwan dominshi
ba gidan ubanshi bane, ni kuma kawai da abun ya bata mun rai sai nace mata shima naga
wannan mai jan GOLF(Mijinta) din ba gidan ubansa bane, ina fadin haka na shige kitchen
domin in kara dafa wani ruwan, kawai sai jinayi an rufeni da duka da wata zabgegiyar bulala,
ihun dana kwala shi ya fito da Daddyn su Iman, yana fitowa yaga abunda yake faruwa bai yi
wata² ba ya tsinketa da mari, shikuma dai² Yaya Farooq ya fito shi da Aunty Zeena, yana
karasowa baiyi wata² ba ya tsinke Daddyn sun Iman, nan suka kaure da dambe, kasancewa
training din soja daban yake haka, haka Yaya Farooq yaringa kwala Daddyn su Iman da
kasa,ganin yana niyyar yin kisa yasa na fita GIDAN da gudu ina neman taimako,ina fita nayi
kicibus da Alhaji zai shiga masallaci,ganin yanayin yanda na futo ne yasashi tambayata lafiya,
kasa bashi amsa nayi,sai dai nuna mai cikin gida nayi da hannu,a dai² lokacin ne mukaji an saki
wani ihu, da gudu muka karasa cikin gida,muna zuwa na tarar da Daddyn su Iman a kwance
baya motsi da gudu na karasa wurinshi ina jijjigashi ina kuka,amma kwata² bai motsa ba nan na
kwala ihu tare da faduwa kasa tim........

Alqur'an na gaji da typing

*Comment*
*Like*
*Vote*
*Share*











*_Fateeyzah_*✍




*HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*


*GIDAN NAGOGGO*
*_(A true life story)_*


*Written by fateeyzah*

*_Jinjina gareki sharifat niamey,Allah yabar kauna❤_*


*_Allah ina rokonka ka*_ *_kara daukaka*_ *HIKIMA WRITERS* *ASSOCIATION* , *_ka_*
*_karemu daga sharrin mahassada_*.


*_Bismillahir rahmanir rahim_*


*_Page_* *_1⃣6⃣to2⃣0⃣_*

Tunda na fadi bana cikin hayyacina sai washe garin ranar na farka na ganni a Asibiti, shafa
cikina danayi ne naji ba komai yasa hankalina tashi, nayita kokarin mikewa amma na kasa.

Nakai kusan minti goma da farkawa amma ba wanda ya shigo dakin, hakan yasa ni cikin tunani,
don zuciyata cike take da tambayoyi, wanda na rasa wanda zai amsamin.

Turo Kofan da akayine yasa ni maida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login