Showing 15001 words to 18000 words out of 39554 words
da zuwa daddy nayi murnar
ganinka
Yace nima haka kakata ya magidan naki tace kowa lafiya yaja hanunta sukayi sama
Laila dadi yakasheta ganin yadda Hakeem ya nuna murna daga yarshi guda daya
Suna shiga falon kamshi hade da sanyin AC ya doki hancinsu
a falon suka zauna meenat tazauna kusa da daddynta yana tambayarta rayuwa
Husnah tana daga bedroom
Hakeem yadauki wayarshi yakira husnah yace baby kina ina kifito ga 'yarki ta isofa muna falo
tare
Husnah tace ganin zuwa nima inan ina bedroom ne
Ta kashe wayar ta
Meenat kuwa takaici yakamata ganin yadda ubanta yake kashe wa wata banza murya wai
harda kiranta baby
Husnah tafito cikin yanayin tafiyarta medaukar hankali tana murmushi tace Ashe ma sun iso
Hakeem yajuyo jin kamshinta murmushi yazuba mata
Ita kuwa meenat jin muryar kaman tasan inda tasan muryar nan tayi saurin juyowa itama
aikuwa sukakyi eyes to eyes da juna cikin tsananin rudewa meenat tace nashiga uku
Asmau meyakawoki gidan mu
Husnah tayi murmushi kawai tace sannu da zuwa ya hanyar tazo tazauna daf da Hakeem
Meenat cikin tashin hankali ta buga wa husnah tsawa tace meya kawoki gidan nan
Tajuya gurin daddynta tace tadurkusa tadafa gwiwowinsa tace dan Allah Daddy karkace min
asmau ce matarka dan Allah kace min ba ita bace
Yace kina Haukane Amina wani irin magana kikefa matata ce fa
Jin abinda daddynta yace yasa tafa sa wata uwar kara tafadi kasa sumammiya
Husnah tayi kanta tana jijjagata
Jinkara daga sama yasa su Laila dasu hajiya rukayya suka hauro a gigihusnahSuna shigowa
sukaga meenat kwance a kasa kanta a hanun husnah
Tana yayyafa mata ruwa
Suby ta bangaje husnah tace matsa dallah dangin mayu
Daga zuwanta ankama mana ita
Laila kuwa batayi watata ba badauki hanu ta tsinke Husnah da mari dai dai fitowar Hakeem
daga kitchen dinsama dan dauko ruwa mesanyi a kwara ma meenat
aikuwa yasaki robar ruwar akasa baiyi watata ba ya damko Laila yazabga mata mari har sau
uku hajiya rukayya da suby suka saka salati
Hajiya rukayya tacewa wa suby yimaza kije kikira hajiyarsa tazo
Suby tatafi bangaren mummyn Hakeem dan kiranta
Hakeem kuwa da sauri yasa hanu yadago husnah yana rarrashinta Husnah tafashe da kuka
tace
To mena mata zata mareni
Yace kiyi hakuri baki ga na dau hukunci ba
Ya kwantar da Husnah ya akirjinshi yana rarrashinta
Laila kuwa hanu tasa akai tace yanzu saboda wannan yarinyar kamanta da rayuwar 'yarka
Kamareni saboda namata abinda yadace
Meenat dake kuka sosai a hanun hajiya rukayya tace
Asmau kincuceni kincuceni kirasa Wanda zaki aura sai baba na
Wallahi sai kinbar gidan nan inba haka ba zankasheki wallahi ta tashi daga kwanciyar datake
Hakeem yace Ashe rashinkuyarki yakai haka
Zaki dubi tsabar idona kice zaki kashe matata
tobari kiji akan matata dagake har uwarki dama Wanda yake da hanu wajen daga mata hankali
zan Baku mamaki wallahi
Yaja hanun husnah sukayi bedroom
Ya rufo ko
Hakeem yadago fuskakarta yace kiyi hakuri kinji ko bamai sake mai maita abinda ta tayi akanki
ina fatan kinji ko
Husnah tadaga kai yace yauwa my sweet
amma daman meenat kawarki ce
Husnah tace nifa bansanta ba ma a school sosai sai lokacin da akabata prefect
Hakeem yadaga kai yace OK
Nasan aikin kakan kane zata zugata zanyi maganinsu
Mummy tashigo falon tace wai meyake faruwa ne agidan haka
Meenat tanaganin mummy ta taso da gudu ta rungume mummy tace Granny Dan Allah kisa
daddy yasaketa
Wallahi zuciyata zataiya fashewa
Mummy tace wai mekefaruwa ne
Laila tace bata labarin komai
Mummy tace ina suke
Laila tace yajata zuwa dakin yabata hakuri
Mummy takira wayar Hakeem yadauka tace kufito falo dukanku ina da magana daku
Hakeem yakamo hanun husnah zuwa falon
Mummy ta kalli husnah tace 'yata dama kunsan junane da meenat
Husnah ta girgiza kai tace a a mummy
Ina dai ganinta a school dinmu
amma gaskiya bawani sani na mata ba
Amina tace karya kikeyi kifada musu gaskiya
Granny wallahi babbar kawatace a school nasanta tasanni cin amana ne kawai ta auri babana
na
Dan Allah daddy karabu da ita wallahi kawatace komai namu tare mukeyi
A school
Taya zatayi tazama kishiyar uwata
Hakeem yace kewai bakida kunya ko oya get out of here stupid girl
Dasauri meenat takama husnah
Tace wallahi kifada musu gaskiya
Dan wallahi bazan taba barinki kizauna agidan a amatsayin kina auren baba na ba
Husnah ta kalli mummy
Mummy tace was husnah kiyi hakuri kinji husnah
Koma dakinki kizauna kawai
Husnah tace to mummy
Tajuya zata fita amina ta fincikota ina zakishiga gidan ubanki ne
Ko anfada miki nan ma scholarship akeci kamar yadda kikasamu har kika yi makaranta mekyau
Kafin husnah tayi magana taji wasu gigitaccen mari da duka tako ta ina
Daddynta yace Ashe bakida kunya matata kikefadawa haka Ashe zaki iya fadawa uwarki kenan
Laila tace kadaina hadani da wannan jinin mayun
Mummy tace wai maiyasa hakane
Towaima menene dalilin dazaku dage
Saiya saki matarshi
Ke meenat idan kawarkice shiya haifeta
To bari nafada muku bawanda ya isa yatakurawa yarinyar nan agidan
Idan kinsan rigima zakiyi da matar mahaifinki kiwuce kikoma gidanki
Hakeem yace mummy rabudasu dasu duk zanyi maganinsu koma jeki huta abinki
Mummy tawuce zuwa part dinta
Amina tasauka kasa dagudu tana kuma mecinrai sosai
Hajiya rukayya tace gaskiya gidan nan ba adallaci
Laila tace bakomai Allah zaimana sakayya Dan yana ji kuma yanagani
Hakeem yajuya yamaka mata wani uwar harara yace idan kikasake ambatar Allah sainabuge
bakin ki wallahi kinsan Allah zaki dinga abinda kukeyi
Ya juya yashiga bedroom dinshi yaga husnah kwance tana kuka
Yasunya dai dai kunanta yamata rada
amma taki shiru cak yadauketa zuwa bathroom
Tare sukayi wanka saida ya tabbatar ta huce sannan suka fito daga bathroom din dakanshi
yashiryata zai mayar mata dakayan data cire tarike hanunshi tace zanje nasa wasu
Yace wadannan bayanzu kikasaba tace ai idan nayi wanka bana son maida Wanda cire kobaiyi
datti
Yace duk yadda kikeso haka za ayi amma saikin gama shirya ni kinsan zanfita magriba tadaga
mai gira tace angama sweet
Tsaf tashiryashi cikin wani farin jallabiya kowa yaganshi yasan yanada kwanciyar hankali
Zaifita tace bakajiba yatsaya yana kallonta ta tako tazo har inda yake
Tayi tsalle manna mashi kiss tace I LOVE YOU
Murmushi Hakeem yayi yakamota yace I love you too
Ya rungumeta tsam a kirjinsa
Yadago kanta ya hade bakinsu guri daya yashiga kissing din sosai sun Dade a haka
Hakeem sai dayaga hankalinshi na shirin barinjikinshi yasaketa da kyar
Dan yaji anakiran sallah yace mune kikaini nasake auwala
Murmishi husnah tayi taja hanunshi zuwa bathroom Dan taga rigima yakeji
Sai daya sake alwala kafin nan ya manna mata kiss
Yayi waje
Murmushi tayi tabishida kallo
Meenat kuwa tana can falo tana kuka
Laila tace kifada min gaskiya meenat a ina kika San wannan yarinyar yanayin kukanki yaban
tsoro fa
Kaman akwai wani Abu akasa
Cikin kuka meenat tace mummy wallahi kawatace nasanta tasanni
Kuma wallahi nayi alkawarin bazata kwana agidan nan ba
Yayi dai dai da saukowar husnah daga sama daga ita sai karamin tawul zata je part dinta tasa
kaya ne
Duk suka bita da kallo
Next page
Your comments is needed fans
Love you all
踫踫踫踫踫踫
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN : 潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤
潤潤潤潤
潤潤潤
潤潤
潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
踫踫踫踫踫踫踫
FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION
(F.C.T.W.A)
HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION
潤I DEDICATE THIS PAGE TO YOU ABDUL AZEEZ (KHALEEL) & HAJARA (YUSRAH)
INA ALFAHARI DAKU 'YA'YANA NAKAINA ALLAH YA RAMINKU DA IMANI
踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫
潤AKWAI LOKACI 潤
潤PAGE 138 to 140潤
HUSNAH takallesu tayi murmushi tace sannunku da hutawa
Meenat tazabura zata biyota
Hajiya rukayya takamota tace rufamana asiri
Mezaki mata
Meenat tace kibarni naje na nuna mata ita karamar Mara kunyace hajiya
Laila tace karuwai ba inba karuwa ba mezaisa tasauko daga ita sai karamin towel
Husnah tayi murmushi tace
Dadin abin aduk inda kiga karuwa saikunga abokin tambadewarta
Kaman yadda kuka ganshi yasauko yayi masallaci yanzu
So kuringa sanin abinda zakufada Dan bakusan abinda za'amayar maku ba
Kekuma daughter meenat
Mekike tunanin zakimin duka na zakiyi ko
Lalle kuwa Ashe zaki iya dukan ubanki kenan
Mara kunya kawai
Kifito fili kifada musu abinda kike boyewa fa
Ta kallisu hajiya rukayya tace tabbas meenat kawata tace kamar yadda tafada muku
Sauran bayani zata muku
Tawuce abinta cikin part dinta
Daga Laila har hajiya rukayya baki sukabita dashi
Cikin kuka meenat tace kunganiko dakunganiko nafada muku kawatace
Wallahi dakun barni naje naci ubanta
Laila tace rabu da ita dole musam abinyi tunda abin yakai haka
Hakeem nafitowa daga massalaci yaga motar Ahmed
Yakarasa gurin motar
Ahmad tafito yace kaganni kenan Hakeem yayi murmushi yace ai inafitowa naga motarka
Yace mukarasa ciki mana Ahmad yace a a mushiga mota kawai muyi maganar
Nan suka shiga Hakeem yaba wa Ahmad labarin komai zuwan meenat
Ahmad yasauke numfashi yace kasan mena fahimta a wannan labarin
Hakeem yace saika fada
Ahmad yace Husnah tasan meenat zai iya yuwuwa kawartace kaman yadda meenat tace
Akwai dai dalilin dayasa husnah taki nuna tasan meenat
Yakamata ka lallabata tafada maka komai
Hakeem yace hakane nima naso nafahimce hakan
amma maizaisa meeanat ta dage ita saina saki matata
Akan husnah zansaba mata wallahi daga ita har uwarta dansu suke Dada bata min yarinya
Ahmad yace a dama aibazaka rabuda matarka saboda
Wannan daliliba
amma inaso kasani fa akwai takaici kawarka ta auri mahaifinka
Dole meenat zataji ba dadi
Hakeem yace kuma husnah bata taba sanin nineahaifin meenat ba sai ranar dataga ta a hoto
amma naga tayi murmushi Dana tambayeta murmushin metake tace min bakomai
Ahmad yace ganiba tabbas akwai wani Abu
Hakeem yace kwarai kuwa amma nasan yadda zanyi zangano koma menene
Nan sukayi sallama da Ahmad
Shikuma Hakeem yatsaya a massalaci don sallar isha
Husnah tashirya cikin wasu arnar kayan bacci masu matukar kyau tafeshe jiki ta da turare
Takoina yadau kamshi ta hada gashinta guri daya da ribbon
Kafin tabude fridge din kitchen dinta tadau fruit salad din data hadawa mijinta tadauki dogon
hijabinta tasaka
Tadauki abinda zata dauka tayi waje tayi sama abinta cikin farin ciki
Hakeem yadawo daga massallaci yabi wajensu mummy
Mummy tace Dan Allah kaba wa husnah hakurin abinda tagani yau
Mutanan basuda imani fa
Ni anya bazan fasa tafiyan nan bakuwa
Hakeem yace saboda mezakifasa mummy
Mummy hafsat tace sunban tsoro ne ai karama susata agaba
amana ce fa a hanunmu idan muka bari wani Abu yasameta Allah bazai barmu ba
Yarinyace karama
Hakeem yace karkidamu mummy
Insha Allah ba abinda zaifaru mummy
Mummy tace shikenan Allah yadada karewa yace ameen
Mummy tace tashi kaje gurin matarka kabarta itadai
Yama mummy saida
Yana Shiga falon baiga kowaba
Ya wuce saman shi
Yanashiga kamshin ta yadaki hancinsa
Tana zaune kafanta daya kan daya
Rigar mesharara ce sai yana da siririn hanu sannan kuma dai dai cinyarta yatsaya ba abinda
ba gani a jikinta
Ga sambala balan cinyoyinta masu tsantsi da laushi
Da kuma daukar ido
Cikin yanga da Jan hankali ta taso tarungumshi
Hakeem sumane kawai baiba saboda gaskiya shigar ya kayatar dashi sosai
Nan da nan kwadayinshi yatashi akanta
Sosai ya matseta ajikinsa
Yana shin shinnanta yamata rada akunne tayi murmushi tace saikaci abincinka
Yace ai nakoshima Ganin wannan wanka ma ai wadatar dani sosai
Husnah takama hancinsa tace naki wayon ta matsa cikinshi tace ji cikinka bakomai kaman wani
silipas
Shima dariya yayi yashafa cikin nata yace harkura zatace wa kare maye
Ji cikin kifa
Tace aini hallittace duk abinci da zanci cikina bazai tashi amma kaifa idan kaci abinci sosai
katoto cikin ka yakema
Hakeem yayi murmushi yadauketa cak dining dakanta tayi feeding dinshi
Shima yabata kafin suka tashi zuwa bedroom wanka suka fara
Indai suna tare komai tare sukeyinsa
Shiyasa wani shakuwa metsanani yashiga tsakanin su takama idan baranar kwananta bane
Hakeem cikin kunci da kewa yake
Sosai yasamu abinda yakeso agurinta tacire mishi duk wani damuwar dasu meenat da uwarta
suka sashi
Sai da komai yakammala sannan Hakeem yadawo hankalinshi
Cikin tsananin son matarshi yarungumeta
Shikanshi yasan tana kokari dashi sosai bata taba hanashi kantaba
Duk da yasantana wahala sosai danshi din yasan Jan gwarzo ne
Yana rumgume da ita ya kalli beautiful face dinta ya manna mata kiss abaki
Nan yashiga tunanin abinda yasa husnah taki amincewa tasan meenat
Yasan tabbas akwai wani Abu haka kawai husnah bazata nuna mata haka
Kuma yana da tabbacin husnah ce da gaskiya
Dan yasan halin 'yarshi sarai
Agogo yaduba yaga time shabiyu darabi nadare
Badama yakira ya shamsu yanzu amma zaibari zuwa gobe yakirashi yamishi tambaya
Yarungemeta sosai ajikinta sosai ahaka bacci yayi awungaba dasu
Dasafe bayan husnah da Hakeem su shirya cikin shigata alfarma
Cikin wani rantsatstsan less
Maroon colour yayi matukar kyau tasaka farin mayafi da farin takalmi
Shima Hakeem cikin dark maroon shadda
Yayi balain karbarshi
Husnah kuwa ta maka wata dambareriyar sarka tasaka na zinari
Tare suka fito zuwa kasa
Meenat suka hada ido husnah tasakar mata harara
Itakuma husnah tasakar mata murmushi
Meenat tace ina kwana daddy
Yace lafiya qalau
Suby ma tagaisheshi ya amsa yace wa meenat bataga antynta bane bazata gaisheta ba
meenat tayi shiru
Husnah tayi sauri tace Dan Allah sweet kabarta bakomai wallahi watarana zata gane
Hakeem yafita abinshi
Husnah takalli Laila tace mama zamuje kai mummy air port sai mundawo kafin suyi magana
tafita
Laila kuwa inbanda kallon takaici ba abinda take bin su dashi
Shiyasa ma Hakeem yayi banza da ita sukayi waje zuwa part din mummy
Mummy tace ina suke subazasuzo muyi sallama ba
Hakeem yace muje kawai mummy Daddy yace a a ke 'yata kiramin matata muyi sallama
Husnah tayi murmushi tace to daddy
Tasan meenat yake nufi kenan
Tawuce zuwa falonsu tace amina Hakeem daddy na kiranki kafin amina tace wani Abu husnah
tajuya abinta
Meenat tace wallahi mummy idan nabar yarinyar nan nacutu
Laila tace kedai kwantar da hankalinki kije kiji medadin zaimiki kidawo
ai nata yazo karshe agidan nan
Meenat tana zuwa falon daddyn Hakeem yace haba amaryata shine bazakizo nagankiba muyi
sallama
Meenat ta kakalo murmushi tace yahakuri grand wallahi kaina yake ciwo yace asha kinsha
magani kuwa meenat tace nasha yace to Allah yakara sauki ko
Wannan in Allah ya dawo damu lafiya
Zanzo hargidan ki kinji ko 'yar albarka
Meenat tace to grand Allah yadawo daku lafiya yaciro cheque yayi signed yabata na zunzurutun
kudi jar 1 million
Sosai meenat tayi godiya tafita
Dan bata San Ganin husnah da ubanta
*****
Da yamma Hakeem nazaune shikadai a