Showing 21001 words to 24000 words out of 39554 words
nayi kewarsu saura ya shamsu zaizo shima yasameni yamin alkawarin zai
dinga zuwa sosai yana ganina Amman bai cika ba
Husnah tace wallahi danwake zanci da dambu da kuma tuwan alkama
Kubra ta rike baki duk acikin ki kekadai tace sosai makuwa
amma dai yanzu tuwon nake bukata tukun
Anty kubra tace OK bani minti na muna da miya daman tuwon kawai zanmiki
Husnah tace yauwa matan yaya daga ke bawata
Husnah taci tuwo sosai umma da kubra sunyi mamakin
Umma dai murmushi tayi itakadai tasan dalilin murmushinta
Duk abinda takeso shi ake mata agidan su
Yaya shamsu kafin yadawo sai yatambayeta abinda take sha'wa ya taho mata dashi
Ranar da zata tafi tun azahar YOUNG PROFESSOR ABDUL HAKEEM ABUBAKAR
Ya isa kano gidansu husnah yazarce direct danshi jinshi yake kaman bashi da lafiya Dan kwana
biyun datayi bata nan
Saida yaci abinci agidan shida ya shamsu kafin suka wa ummu sallama suka fito suka dau
hanya
Hakeem yakasa boye zalamrsa akanta saida. Yayi parking a gefen titi
Komeyasa oho
Suna isa Hakeem yayi parking yazago yabude wa husnah kofa duk abinda kefaruwa a idon
meenat da suby Dan suna lambun gidan suna hutawa
Takaici Yakama meenat tace wallahi anty suby danasan husnah zata auri daddy Dana wallahi
da banbar hajiya taje gurin maganin ba
Yanzu gashi nibada bash itakuma da auren ubana har bayaganin kowa sai ita
Suby tace ai wallahi zamu koya mata hankali basu rufe bakiba Hakeem yadauko bag din
husnah da Yakama hanunta suka shiga ciki
Suna zama husnah ta ce wayyo Prince zansha nun tsamiya zansha kuma nagaji dayawa
beside ni idan nayi ma balle nashaba
Cikin sauri yazauna kusada da ita yace kobakida lafiya ne Dan naga kincan minfa sosai
Hanu takai ta lakuce hancinshi tace nidai ba abinda yake damuna
Kawai kasamomin kunun tsamiya
Waya yadaga yakira Ahmed yace kana gidane yace a
Hakeem yace kasa Aisha ta min kunun tsamiya zanzo na dauka
Kafin Ahmad yayi magana Hakeem yakashe wayarshi Dan yasan sai yamishi tsiya
Hakeem yajuya yaga hartafara bacci a mota gabadaya ma baccin tayi
Tashi yayi yamatsa kusa da yakura mata ido sosai
Can zuciyarshi tace anya yarinyar lafoyarta kalau kuwa
Yadauki waya yakira family doctor dinsu macen yace tazo da kayan aikinta
Yafada mata abinda yake zargi tace OK tagane gatanan zuwa
Hakeem cikin tsananin farin ciki yayi sujjadar Allah yatabbatar mishi da abinda yake zargi
Next page
Your comments is needed fans
Love all
踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN : 潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤
潤潤潤潤
潤潤潤
潤潤
潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
踫踫踫踫踫踫踫
FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION
(F.C.T.W.A)
HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION
潤I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Aisha Ibrahim ina matukar jin dadin comment din ki
wallahi keep it up ina alfahari dake over my sister 踫踫踫踫踫踫潤
潤AKWAI LOKACI 潤
潤PAGE 143 to 145潤
Bayan gwaje gwaje da likita tawa Husnah ta tabbatar mishi husnah tana dauke da cikinshi
Cikin tsanin farin ciki hakeem yace alhamdulillah Allah nagode maka da cika min burina cikin
gaggawa
Allah kasauketa lafiya likita tayi murmushi tace gaskiya wannan babyn zaiga gata prof irin
wannan doki da murna haka
Yayi murmushi tare da rungume husnah ajikinshi tunda likitar tafada cewan ciki ne da ita
Ta rufe Idan kaman me bacci
Ita kanta takasa sanin meyasata jin kunyar
Hakeem yace wa likita kizuba ido kiyi kallo aranar da Queen dina ta haifamin baby a ranar zan
yi abinda za bakowa mamaki
Kuma kema fa baza abarki ba zaki ga goron albishir a account din ki
Likita tayi murmushi tace kai amma nagode Allah yafito mana da wannan babyn lafiya
amma Yakama ka kawota hospital gobe Dan mumata scanning a tabbatar cikin wata nawa ne
Dan kasan lokacin da zakafara tsammanin babayn ka
Hakeem yace ai bazan bari sai gobe ba yanzu zamu biki muje Nagani da idona
Doctor tayi murmushi tace ina jiranku to
Hakeem cak yadauki Husnah zuwa bedroom yasamata kataton hijabinta
Sannan kuma ya sunkuya wai ta hau baya
Husnah taga dagaske yakeyi fa
Taware tace a a Dan Allah Prince kabarni maka ganin bamu kadai bane
Hakeem yace ai ni mutane da maganarsu bai cika damuna ba ko agaban mummy zan iya
goyanki ballantana 'yata
Husnah tace naji inkai bazaka ji kunya ba aini zanji
Ta kwasa dagudu tabar dakin
Yafito hankalinshi a tashe yace Dan Allah baby kidaina gudu karki samin baby yagaji
Husnah tatsaya cak taki juyowa
Ya tako ya iso har gurinta yajanyota jikinshi yace oya mutafi ko kinga doctor tana jiranmu a
waje
Cikin shagwaba husnah tace tun ba aje ko ina ba kafara nuna min iyakata ko
Shine zaka ce wai kar babyn ka yagaji
Wato ma bani bace damuwarka babyn ne ko
Cikin murmushi Hakeem yajuyo da ita suna fusakanta juna yace Haba baby kema kinsan you
are my one and only
Taya za ayi nace bandamu damu da lafiyarkiba
ai dake da abinda yake cikin ki
Inkincire mummy da daddy to kune rayuwata kune komai nawa
Husnah tace nidai banyarda ba
aikuwa sai ganin prof tayi gwiwa biyu agabanta
Cikin sauri itama tayi kasan takama hanunshi tace la nifa wasa nakema
Yayi murmushi yaja hancinta yace kinji tsoro kenan tace sosaima wace dasa zuciyata kneeling
a kasa ai dole tsoro yakamani yayi murmushi yatashi yadagota cak
Dakyar tabashi hakuri yabarta ta tayi tafiya da kanta
Bayan scanning da akayi wa husnah aka ta babbatar musu da tana dauke da cikin sati bakwai
wato getting to two months kenan
A gurin Hakeem yadauki wayarshi yakira mummy da daddy yasanar dasu
Mummy kaman tayi tsuntsuwa tazo taga 'yarta husnah haka take ji
Tayi murna sosai haka ma daddy
Dan mummy hafsat kam ma cewa tayi tundaga can zata fara sayayyar kayan jarirai
Daga hospital sai gidan su Aisha da Ahmad Hakeem yayi dasu
Suna zuwa kuwa Aisha takawo mai kunun tsamiyar dakan yazauna kan carpet ya hada mata
sosai tasha kuwa duk sunyi mamaki
Ahmad yace amma natayaka murna abokina Allah yaraba lafiya
Aisha da itama haihuwar ko yau ko gobe
Tayi murmushi tace Allah sarki 'yar kanwata Allah yasaukemu lafiya ko
Husnah tace anty nifa bani da komai
Wasa fa yaya yake muku
Aisha da dariya yaso barke mata tace sosai Nagani kuwa
Wannan tulun kunun da kika shanye ai kowa yasan bake kadai bace
Husnah tayi murmushi tace ai saboda ina sone shiyasa
Hakeem yace sannu da kokari madam kema kina fama da kanki mun hada kida aiki
Tace bakomai wallahi bana ma son zaman
Nan Ahmad da Hakeem sukafita
~~~~~
Bayan sati biyu duk wannan abinda kefaruwa na maganar cikin nan baizo kunnen su Laila ba
Husnah zaune a falonta mai kamshi da sanyun Ac
Kaman daga sama taji murya kaman na anty kubra
Da sauri ta tashi taduba anty kubra ce kuwa tasha kyau cikin wani tsaddan less Dan shima ya
ashamsu yanzu kudi yazauna mishi sosai shiyake juya dukiyar husnah Wanda tabashi ragamar
komai a hanunshi
Kuma shiyazama manager a company Hakeem
Husnah tayi tsalle ta rungume anty kubra tace wayyo anty na wallahi naji dadin ganin
Anty kubra tace kai Husnah bakida hankaline wayafa miki meciki tana tsalle haka husnah
tarufe ido tace anty nifa banida komai
Kubra tace ai Allah zata sake magana husnah taja sukayi part dinta
Laila dake zaune jin abinda anty kubra tace
Ya mugun daga mata hankali sosai
Tace kai ina karya ne wallahi ba zaki taba haihuwa gidan nan ba matsuyaciya
Meenat ce tafito daga part dinsu
Dauke da glass cup a hanunta na drink
Sai mummynta na hawaye
Sai Takaraso a tace meyafaru kuma mummy
Suby tace wannan 'yar talakawar ce wai cike ne da ita
Meenat batasan sanda tasaki cup din hanunta ba
Tace karya takeyi wallahi bata isa ta haifi wannan Dan iskan cikin nata agidan nan ba
Tayi hanyar dakin husnah suby tayi saurin tarota tace inazaki
Meenat kibarni naje anty suby wallahi sai namata dukan dazaisa cikin yazube inga tafadi
Suby tace idan kikayi haka daddynki zai dauki babbar mataki akanki
Kibari mubiyo musu tabayan gida
Ina tabbatar muku husnah bazata haifi cikin nan ba
Nan dai suby taringa basu shawarwari
Husnah takawo wa anty kubra gashashshan namar kaza da drink saikuma fruit
Ta zauna kusada anty kubra
Anty kubra tace anya wannan husnah ummace kuwa
Kinganki kuwa kinyi fresh dake kaman ba mai cikiba
Husnah tayi murmushi kafin tayi magana wayarta yayi kara tana dubawa taga Prince ne cikin
shagwaba ta amsa sallamar
Anty husnah baki kawai tasake tana kallon husnah yadda tazage tana soyayya da mijinta ba
alamar kunya cikin kawarewa da iya wa Hakeem yace to ya antyn mu
Husnah tace LA ya akayi kasan tazo yayi murmushi yace karkidamu ki isar min da gaisuwa na
kafin mukaraso yanzu
Husnah tace kukaraso kaida wa kuma
Yace naki fada yayi murmushi yace bani baby na muyi hira naji abinda take bukata
Murmushi husnah tayi tace anty nan
Yace kibani baby muyi hira
Taga dagaske yake
Tayi murmushi ta kashe wayar
Sai da tagama taga anty kubra tazuba mata ido
Kubra tace anya wannan Husnar ummace kuwa towai Husnah ina kunyar ne wannan soyayya
haka
ai sai kisa yakasa aikin
Husnah tayi murmushi tace anty kenan wallahi tun inajin kunyar ya Hakeem wallahi har na
daina
Dan shi baruwanshi ko agaban waye baya kunyan nuna min soyayya
Anty kubra tayi murmushi tace to ai gwamma dai da kika nuna mishi kema kwararriya ce fanni
kula miji kar kiyarda kece zaki kunyar wasu
Husnah tace wallahi anty kaman kinsan ni
Wallahi Allah yagani tsoro suke bani kawai nuna musu nakeyi kaman bana jintsoronsu
amma wallahi suna ban tsoro
Anty kubra tace ai karkisake Susan kina tsoronsu
Wato ita meenat din har yanzu bata sadudaba duk da irin jarabawar data gani na rayuwa
Husnah tayi murmushi tace wallahi anty sai abinda yakaru inda kikasan zata kasheni agidan
nan haka take min
Dam tana tsoron daddynta ai da abinda zata min dayafi haka daga ita har uwarta
Anty kubra tace ai sai kigodewa Allah ma mijin ki nasonki
Husnah tayi murmushi tace ai ni wani zubin har tsoron nuna min son dayakeyi gabansu nakeyi
Anty kubra tace inbanda abinki ai hakan shine zaisa duk sukone da ruwan jikinsu
Nan dai anty kubra tayi ta bata shawarwari zaman duniya
YOUNG PROF da Ahmad da ya shamsu sukayi sallama suka shigo falon
Masu falon ne hakimce abinsu
Suby da meenat suka gaishesu amma banda madam laila
Direct dakin husnah suka shiga
Wani kamshi ne yadoki hancinsu yasa farin ciki a zuciyar Hakeem yasan kadan daga aikin
husnah bata zama ba kamshi
Husnah cikin tsananin murna tace LA yaya shamsu daman harda kai kukazo shima ya shamsu
Cikin tsananin farin cikin ganin 'yar kanwar tashi
Yayi murmushi yace ai daman mamaki nakeson baki
Sosai husnah take murna ganinsu
Hakeem yace lalle ma baby wato kinga ya shamsu kin manta dani ko
Ahmad yayi dariya yace kai Dan uwa wasane ballantana su biyu kawai
Kokaima dakana da kanwa haka zaka nuna jin dadin ganin ta alokacin da kuka hadu bayan kun
Dade Baku haduba
Young prof yayi dariya yace wayafada maka duk shakuwarsu
ai yanzu munfi shakuwa Dan nasan kozaba zatayi yanzu
Ya mu'allim zata dauka
Ya kalleta kobahakaba Queen dina
Husnah tashi tayi tabar gurin zuwa dining Dan hada musu komai
***********
Hajiya suwaiba tawa bokanta magana akan aikin datakeso yamata
Shine yabasu tabbacin sai sun zo dakansu baya son aika
Shiyasa da hajiya rukayya da hajiya rukayya suka shirya tafiya zuwa karbo maganin daza a wa
husnah cikin yazube kuma ta haukace tabi duniya
******
Bayan wata daya da sati biyu
a yaune ake sa rai da dawowar su daddy da mummy
Husnah tagama gama hadawa su mummy abincin su mai rai da lafiya kusan kala hudu banda
drinks kala kala
Da su farfesun kaji gasunan dai
Hajiya suwaiba da hakiya rukayya sundawo wajen satinsu uku kenan yau suke son aiwatar da
nufin su akan husnah
Husnah da Hakeem sungama shiryawa kasancewar ranar girkintane
Har sunfito zasuje air Port dauko su mummy Sai taji kanta yasara mata tadafe kan nata
Hakeem dake bayanta yayi saurin karasowa yakamata
Yace yadai Queen tace kai nane yake ciwo
Yace o to sannu kinji kizauna kawai zanje na daukosu
amma barin kawo miki magani kisha kafinko
Duk wannan abinda me faruwa a idonsu meenat
Hajiya rukayya takashe mata ido daya
Meenat ta tashi da sauri tace daddy kaje kawai zan kawo mata maganin
Kaman daga sama yaji maganar abakin amina
Kafin yayi magana wayar daddy ya shigo wayar Hakeem
Hakeem yace sun sauka baby
Husnah tace badamuwa kaje kadauko min mummy na nafi bukatar ganinta akan maganin ma
nasan idan naganta shikenan
Yace show tace show yace OK take care of your self tace I will
Ya fita meenat ta faikace idon husnah ta balla mata harara
Husnah tadago ido ta kalli meenat
Meenat tayi murmushi tace sannu anty na barin kawo miki magani
Meenat tayi saurin barin gurin
Husnah tayi murmushi tace hmmmm
Meenat tadawo tace gashi husnah takarba tace nagode sosai
Meenat tace ba godiya ai yiwa Kaine
Husnah takarba taduba ruwan da kyau taga bai mata ba
Ta ajiye meenat ta ce ya kuma zaki ajiye bayan na kawo miki Dan kisha kisamu lafiya
Husnah tace ai naji ma kan yayi sauki sosai
Meenat tace bangane ba kina nufin bazaki kishaba kenan
aikuwa su madam laila da suby suka taso
Suby tace kedan ubanki karki ba kisha
Husnah tace ubana fa kikace Dan bakisan darajar naki ubanba
Kafin husnah takarasa magana meenat takai mata mari
Tashakota tace kokisha ko wallahi kici. Ubanki
Kafin meenat takai karshen magarta husnah ta wanka mata wani gigitaccen mari
aikuwa Laila da suby suka rufu akanta duka ta kota ina
Kaman sun samu jaka
Tun husnah na Neman taimako har takasa
Laila tadago husnah data Riga ta galabaita ta kaimata naushi aciki
Wani gigitaccen kara Husnah tayi
Tazube kasa sumammiya yayi dai dai da shigowar
Prof da mummy
Next page
Your comments is needed fan's
Love all
踫踫踫踫踫踫踫踫踫踫
[05/05, 10:18 PM] UMMU AFAN : 潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤潤
潤潤潤潤潤
潤潤潤潤
潤潤潤
潤潤
潤
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Story & written
By
The special writer
UMMU AFAN
踫踫踫踫踫踫踫
FIRST CLASS TECHNOLOGIES WRITERS ASSOCIATION
(F.C.T.W.A)
HOME OF QUALITIES AND TRUSTED WRITER'S OF THE NATION
潤I DEDICATE THIS PAGE TO YOU Umulkhairi Mahmoud ina alfahari dake over my sis
comment dinki yana kara min kwarin gwiwa keep it