Showing 6001 words to 9000 words out of 30182 words

Chapter 3 - ZURFIN CIKI Book 3 end by halima Abdullahi K Mashi .pdf

da rabi
tana jiran shigo warshi shiru, waya tadauka ta
rubuta mishi sako da cewa. Ya abba don Allah
kadawo ni dai tsoro nake ji. Ya karanta yayi
murmushi, azuciyarshi yace, don ita ya kwafe,
yayi dunkunan yana son kudin don ya sai mata
akwati da kayan shafa zuwa kayan ciki. Share ta
yayi sai kusan sha daya darabi sannan yatashi
tare da sallamar yaran, haka nan itama sai daya
hado mata duguwa rigarta ta shadda wadda
dama anriga anyi sirfani ajikinta. Dakin bishira
yasoma lekawa, bacci yadauketa sosai agefen
gadon take da alamun baccin yazo mata ba cikin
shiri ba. Abba yayi murmushi tare da cewa, wa ya
fada miki ana cin bashin bacci? Ina zaton matar
nan jiya bata runtsa ba, yau gashi yazo ba shiri.
Har ya gyara mata kwanciya itama 'yar ya gyara
ta amma bishira bata farka ba, don haka yakashe
mata wuta yafita. Yaso kashe injin amma garin
da zafi gashi basu kawo wutar nepa ba, gidan
yarufe yazo ya tura kofar ummi data rufe. Karar
kofar ne ya farkar da ita amma bata motsa ba,
tun daga kofar yatsaya yana kallonta, can
tsakiyar gadon takwanta bata dora kanta saman
filo ba. Amma tana manne da filo daya akirjinta
fuskarta yake kallo, a jikinta taji kallonta yakeyi.
Kusan minti 4 sannan ya aje ledar hannunshi.
Shirin bacci yake amma yakasa daina kollonta,
shikanshi yana mamakin wannar jarababben son
dayake ma ummi, duk da dakewar dayake don
kada yabada kanshi amma sai yadinga jin wani
abu yana fisgarshi. Tamkar yafito mata da zallan
sonshi gareta, tsoronshi inta gano kila tarainashi.
Kadan-kadan takan bude ido ta saci kallonshi, sai
daya gama komai a tunanin ta ya kwanta a
gadon amma sai taga yadauki filo yakwanta a
kan kujera. Haka suka rayu har tsawon sati daya,
ranar yabar dakin ummi ranar kuma tasoma salla,

ita ko bishira satin nan tayi shine tamkar
mahaukaciya sabon kamu. Ranar kuma da abba
yadawo dakinta bata runtsa ba shima bata barshi
ya runtsa ba, daga bisani dole yabar dakin
yakoma falonta yakwanta. Haka gidan yaci gaba
da kasancewa, in Abba yafita ummi bata da
sauran sakewa saboda zagi da habaicin bishira.
Wani sa'in har da kawayenta, ko makota 'yan
jam'iyarta su shigo suyi tayi, ummi bata kula su.qnovels / ZURFIN CIKI book 4 part 8
ZURFIN CIKI book 4 part 8
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:50
Duk abinda bishira zatayi kada takulata. To ita
duk bawannan bne damuwarta ba, damuwarta
ynda Abba sam yaki nuna sha'awarta gare shi,
duk dayasan tana sallah, hka nan duk lokacin
dakwananshi yajuyo kanta sai dai ya jefa filo
akan kujera ya kwanta. Takasa gane ma'anar
hakan, tun tanajin dadin ynda bai nemeta ba
saboda tsoronsa da take harta dawo tasoma jin
haushi. Ita ma fa mutum ce cikakka mai lafiya,
sannan tana kwana daki daya da san kacecen
abun sonta ya ya ba zata damu ba? Sai dai tayi
wa kanta alkawarin a yau in zasu shekara ahaka
ba za ta taba yi masa tallar kanta ba ma'ana
baza takai masa kanta ba. Sai dai zatayi masa
kyale- kyale taga karshen girman kai, ta kosa su
hadu da fati don ta bata sakon kananan kaya
tasiyo mata don ta bata labarin cewa ta kwashe
su a wambai. Kwananta goma taso ma girka, duk
tsawon kwanakin nan abincin siyarwa dana
umma suke ci, domin bishira taki dafa abinci.
Ranar da zata fara girki ta haukata gidan da
kamshi, tuwon shinkafa miyar shuwaka, tasan
Abba nason tuwon shinkafa. Tun kafin ya dawo
yamata waya ta aika shagonshi, 'yan shago sun
ci suna santi, haka nan ya gayyaci abokansa
kofar gida ya shimfida musu tabarma suka ci tare
da lemu, zobo da kunun aya. (reall ehem tazubo
mun nawa na koma 1 site ina kimtsa cikina lolx)
ga nama ya wadata a ciki, abba yaji dadin yanda
abokanshi sukayi ta santi, safiyar ranar kuma
kunun gyada ta musu da kosai. Duk wannan
abincin da ummi keyi bishira ko a harshenta ta ki

ci, cewa ma tayi ita fa kowa tayi girkinta don
baza ta ci abincin ummi ba. Kuma ba shegiyar
dazatai wa girki, hakan yayi wa ummi dadi don
nata ganin ta bakin tsohuwa ce, da ta ce ko kwai
bishira tadafa shine dai dai a cikin bawo to baza
ta iya ci ba bare wani abinci. Sun zauna tsawon
wata daya ahaka ummi bata taba leka ko kofar
gida ba, tana kewar ummanta gara ma tsohuwa
duk ranar juma'a in tadawo masallaci takan biyo
gidan taga takwararta. Dakinta Abba yake
yagama karyawa ya shirya zai tafi aiki, ummi ta
kalle shi tana son tambayar zuwa gidan umma
tna jin tsoro. Ya dubeta kamar kina son cewa
wani abu ko? Ta ce am dama inaso inje gida in
gaida su umma, yajuyo yadubeta suka hada ido.
Gabanta yafadi, ta sunkuyar dakanta, yace a'a
tadaga ido takalle shi, wani kunci taji aranta, ga
matanshi nan yini take garari a layi bata ko
tambaya amma ita ta tambaya shine ma zai
hanata? Ya dauki jakar shi, ta mike ta rakashi
har tsaka gida tare da yi masa addu'ar Allah
yatsare, yini tayi da takaici dama haka mata suke
ji in an hana su zuwa anguwa? Daran ranar zai
koma ga bishira don haka bata san dawowarshi,
tana kwance kan doguwar kujera tana karanta
littafin hausa ( naleka muku kozanga sunan
littafin amma bangano mukuba) kamshin turaren
shi ne yasa tasan yashigo, don littafin yadauki
hankalinta. Ta amsa sallamar daya sake yi tare
da mikewa zaune, yana sanye da kananan kaya
tamkar wani dan saurayi, yayi kyau a idonta
kamar ta rungumeshi. Tace sannu dazuwa yace
yawwa, dauko mayafinki muje tazura takalma
bayan tagoge sannan ta ciro mayafi, yace a'a
dauko hijabin. Ta maida ta dauko hijabi tafito
sannan yakulle kofar, saida suka fita waje sannan
yadubeta, hannu rabbana zakije musu? Tace yaya
Abba toni bani da kudi ai. Sukabi ta wani super
market suka sai sabulai da turare, akafa suke
takawa sannu ahankali suka jero duk da cewa
bawata hira suke ba, Abba ne yake amsa waya
jifa-jifa na jama'a masu sonshi. Tun daga nesa
suka hangi mahaifansu suna cin abinci a inda

suka saba. Alhaji babba dakarami. Cikin zumudi
ummi ta ce, yauwa gasu alh. Abba yaje haka
zakije musu da rawar kanki ko? Cikin shagwaba
tace, wanne rawar kai nayi toni yaya Abba? Yace,
na gani kinayi kamar zaki kwasa da gudu, kafin
tayi magana sun iso gurin dukkansu suka zube
akan tabarmar daga gefe. Abba ne yasoma cewa,
sannunku alh. Alh. Yace, a'a kune? Alh karami
yace, uwata harda ke? Tace, eh ina yininku?
Sukace lpy lau. Alh. Karami yace, uwata kunanan
lpy ba wta matsala ko? Ta ce, ba komai alh..
Yace to Allah yyi maku albarka, ya azurtaku da
'ya'ya ma su albarka wadanda kuma zasu biku.
Abba yace amin suka hada baki da Alhaji babba,
alh babba yaci gaba da cewa, Abba ya hakurin
shirmen ummi kuma? Ince dai bawata matsala?
Abba yakalleta mun gode Allah alh, amma bwata
matsala, ummi tamike dazumudi bari a karasa.
Tun daga soro take kwala ma umma kira. Umma
tce, A'a muryar wa nake ji haka? Ummi tashigo
da gudu ta cakume umma, tsohuwa tafito tana
fadin lale. Dakin tsohuwa tasoma shiga suka
gaisa sannan tadawo dakin umma, sun gaisa
umma tasake mata nasiha, ummi tace umma ni
matsalata daya matarsa. Kullum saitayi min
habaici tana zagina wata rana r harda kawayentaRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 9
ZURFIN CIKI book 4 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:54 Ita ko bishira
gidan su umman bashir ta tafi dakuka wiwi, tace Abba yamata duka takan sun taka hakkinta sun
fita ranar girkinta. Tayi magana ummi ta mata tsaki shi kuma yazo yazo yahauta da duka,
umman bashir tace duka! Duka akan ummi? Tabdi, tashi muje gurin wadanda suka daure masu
gindi. Umma na kokarin shiga daukin alhaji taji sallamarsu sama-sama, gabanta yafadi ta amsa
tare da dawowa baya. Sahura tace to suwaiba, abinda kuka shiirya yasoma tasiri. Abba yayi wa
bishira shegen duka saboda 'yarku, umma tace haba sahura, yaya ki ke irin wannan maganar?
Mu ne zamu sa Abba ya cutar da iyalinsa? Sahura kiyi nazari. Alhaji yafito, me yafaru ne ni kejin
hayaniya suwaiba? Umma tace, oho. Sahura tace, bishira fada musu. Nan bishira ta shaida
masu yanda ta tsara ma umman bashir, alhaji yadaga waya yakira Abba, Abba yana dagawa
alhaji cikin zafi yace Abba maza kazo yanzun duk in da kake. Abba yace to alhaji, ummi ta mike
zan bika tsoro nake ji ni daya, cikin zafin rai yace abin daki ke tsoro ya cinye ki, ya fita fuuu.
Cirko-cirko ya same su a tsakar gida, sai muryar sahura kake ji tana rashin mutunci. Alhaji
karami yadawo gidan shi sai ya jiyo muryar sahura a can gidan, ya nufi gidan don haka kusan
tare suka shiga gidan da Abba. Alhaji cikin bacin rai yafada Abba da fada, abba bai katse shi ba
har sai daya kai ga tambayarshi cewa me yasa yayi mata duka? Yace, banyi mata duka ba
alhaji marinta kawai nayi, umma ta ce mari kawai ne Abba? Alhaji karami yace, to kan wane

dalili ma zaka mare ta? Abba ya koro musu komai, ya kara da cewa, wannan har zata ce an
mata tsaki, zata yi duka ni wane irin zagi ne bata min ina hakura darajar iyayenta? Ya nuna ta,
wallahi in kika kai ni bango zaki koma gidanku don bazan iya ba na gaji, nan kuma su alhaji
suka shiga bashi hakuri. Ita kuma suka bata rashin gaskiya, sai dai duk da haka umma tai masa
fadan kada ya sake daukan ummi ranar girkin bishira ya fita da ita, yace to. Umman bashir taja
bishira zo muje ai dama nasan baza suga laifin 'yar su ba. To wllh marin da yamiki ki tabbata
bashine. Ko nan da yaushe ne ki rama shi kan ummin, in ba haka ba duk da banice uwar data
haife kiba sai na tsine miki. Alhaji karami yace, to katuwa mara lissafi, ke dai kinji haushin
rayuwarki, to ki sani duk randa ta rama duka akan ummi ni kuma akan ki zan rama wa ummin
inga ta tsiya. Alhaji babba yace, kada kai ma kazama su mana aminu. Tsohuwa tace, gskiya ne,
in har tazama silar dukan ummi itama sai ya mata taji. Umma tace, a'a duk abin ba zai kai haka
ba insha Allahu, kai dai abba kayi ta hakuri sannan kadaina sa hannu kana dukan mace. Yace,
umma dukana fa tayi, sai kace wani soko zan tsaya mce tna dukana, umma tace, to ai tace
ummi taje duka, yace ummin 'yarta ce? Alhaji yace, tafi gidan kahadasu kayi masu nasiha, Abba
yace ai baza ta tsaya ba, wannan yarinyar fa sai dai addu'a ni in nagaji kawai hakura za ayi,
umma tace bana son jin wannan zancan, alhaji karami yace ai gskiyarshi ne, shi yasan irin
zaman dayake da ita. Alhaji babba yace, ai kuma darajar mahaifinta za aduba, da mutuncinsa,
Abba yace ai dama alhaji ni banda mahaifinta da tuni nayar da kwallon mangwaro na huta da
kuda. Umman tace je ka gida Allah ya kyauta. Nan dai ya musu sallama yanufi gida. Ummi da
gske tsoro ne da ita, da rana in ba kowa bta damuwa, amma da dare tfi son tdinga jiyo motsin
bishira koda habaicin dta sabayi mata. Soro taje ta tsaya tana yi tana leka waje, can ta hango
bishira, don haka takoma daki ta kullo kofa aranta ta ce kada tazo tayi min duka. Ummi tna
jiyota lokacin data shigo tana cewa wllh kan yarinya zan rama marina, wannan dole ne koba
dade saina ramashi. Abba kan bai nufo gida ba, shagonsa ya wuce lokacin goma ta gota, yaran
sunyi shirin tafiya, don haka ya amshi makullin ya shiga shagon saman teburin da suke yin
yanka da guga ya hau ya zauna. Tagumi ya zuba hummu biyu tare da sauke wata ajiyar zuciya
mai karfi, me yasa ummi ta furta kalmar data tuna mishi cewa bata sonshi? Sakankancewa
dayanda ummin kenuna mishi yasa shi jin kamar sonsa take ashe dai shi yake shermenshi. Ya
tuno wani labari yaya tabaji na wani mutum da aka ara masa mata wadda bata sonsa, tazo
tazauna dashi tsawon shekaru kuma tayi masa biyayya matuka. Ga 'ya'ya sun haifa yaran sun
yi girma sosai, suma sun zama magidanta, sai wata rana mutumin nan suna hira da matar, yace
oh, wance dafa ba kya sona, yanzun gashi harmun tsufa kin manta dawata kiyayyah.
Tadubeshi, inji wa yace maka na manta? Biyayya kurum nake maka amma har gobe bana
sonka. Abba yajinjina kai, lallai dole ne ya nutso, yadaina tunanin ummi tana sonshi kokuma
zata soshi, shidai da kaddarar sonta tafada mishi sai yayi ta addu'a Allah ya bashi hakurin jure
zama da ita ahaka. Bai san adadin lokacin daya dauka awaje ba kuma baisan adadin tunanin
dayayi ba. Daga karshe yarufe shagon yanufi gida. Ganin yanda garin yayi tsit shine yasa shi
kallon agogon hannunshi, daya da minti shabakwai, lallai lokaci yatafi. ZURFIN CIKI book 4 part
10
ZURFIN CIKI book 4 part 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:55
Yanufi dakin bishira aranshi yce da wanda yake
kinka gara mai sonka ko mahaukaci ne. Gdon

yahau tagefe ya kwanta suka saka muhibba
atsakiya, ummi kuwa duk tsawon lokacin nan
tkasa bacci domin bata ga shigowarshi ba. Idonta
biyu har sai daya shigo ta leka ta windo tana
kalloshi har yashiga dakin bishira ya rufo kofa,
sannan ta kwanta tare dayin ajiyar zuciya. A fili
tace ina ga fa har dani alaifin nan, amma bari
gari yawaye inba shi hakuri durkusa ma wada ai
ba gajiyawa bane. Bishira tafarka cikin dare taga
Abba kwance hannunsa na dama dore kan jikin
'yarsu, ta tsura mishi idanu tana son mijinta
sosai. Ban dahaka data kaishi koto ya bata
takardarta koda mahaifinta xaimata baki
sanadiyar haka, amma shi yanzun yadaina sonta.
Takai hannu tadora a kumatunshi, ahankali
yabude idanu, suka kura majuna ido yace bishira
me yasa kike yin abinda zai samu mu samu
sabani bayan kinsan sone ya hadamu?
Idanuwanta suka kawo ruwa, Abba dane ka soni
kaji dani har alokacin ina ganin ba Wata mace
data kai ni dacen gwanin iya soyayya. Amma
yanzun duk ka zuba ni a kwandon shara har kana
marina saboda ummi. Ya ce, a'a ba sbd ummi na
mare kiba, saboda kin dukeni ne amma kiyi
hakuri. Banason kina zubar da kanki a gurinta,
yawan fadanku zai sa raini ya shiga tsakaninku,
ni kuma ba zan so ta rainaki ba. Kuma da kin
kwantar da hankalin ki ummi fa ba wai tana sona
bane, ita fa an matsa ma tane, kuma su umma da
kike zagi na rantse miki masoyan kine. Ta ce
tokai kana son ummi ne ? Ya dan yi jim, sannan
ya ce ai dai kin san yanda auran namu da ita
yakasance bagatatan bai dace ace kinma tsaya
yin wannan tambayar ma. Tadan yi shiru, zancen
nan ya shige ta bakamar yanda ta zata da farko
ba, ko dadin baki zaimata? Sannan ta tuno da
ranar da fati tazo. Ta labe taji koza suyi
zancenta sai taji suna ta hirarsu, acikin harar fati
ke cewa wai kuwa ya kuka kaya ne ummi? Nasan
yanzun ai kin warke, kema kin goge. Ta ce
damefa? Fati tace, a'a ki gane mana, batun
kwanciya. Ummi tace, kin san cewa yaya Abba ko
gadona bai taba kwana ba? Fati tace kai haba?

Ummi tadinga yimata rantsuwa, tuno da wannan
sai bishira ta yarda mijinta ma baya son ummi,
don haka sai ta saki murmushi. Yace, tunanin me
ki ke yi? Tace da ina ga kamar dadin baki kake
min, amma dana tuno naji ummi tana fadama fati
wai baka taba ko kwanciya a gadonta ba, bare ka
hada jiki da ita sai na yarda. Abba ya zaro ido, a
ina kika ji suna zancan? Ta ce, a'a tazo mata
rakiyane naji suna maganar a soro. Abba ya
girgiza kai. Bishira tace, kuma da gske hakane,
yakai hannu yakama nata tafin hannun, wannan
wani sirri ne tsakanina da ummin. Ynda ba zan
fada mata komai tsakanina dake ba, haka itama
zan sakaya nata sirrin, tadai fahimci hakane, don
haka sai ranta yayi mata dadi har ma ta baiwa
Abban kanta a daran. Ynda taga yna rawar jiki ya
tabbatar ma ta ba wani angwanci da yayi, don
haka zuciyarta fes ta wayi gari. Duk da cewa
abba ya tashe ta cewa taje tayi wanka harda
Allah yahadata amma tayi niyar baza tayi hakan
ba sai gari yayi haske. Ummi ta fito don tanuna
mata cewa Abba ya kwana da ita. Bishira an dafa
ruwan tea an kai falo sai wannan rawan kai ake
yi. Sai data lura ummi ta dauko tsintsiya tasoma
sharar gidan kamar yanda tasaba, sannan tafito
da buta aka nufi bandaki, kai ko dankwali babu
aka yiwanka aka fito. Gashi yna ta digar ruwa,
ummi ta fahimta kuma tagane cewa tayi hakan
don ta nuna mata ne. Kuma taji zafi aranta
kamar ynda bishiran taso, ta amma azuciyar ta
sai tace na banza jiya nan yakora miki mari.
Lokacin da abba ya shigo gidan tagama shara
tana kwashewa, bai ko dubeta baya shige falon
bishira, kan ummi yasake daurewa, me yake
faruwane haka da zafi? Ta tambayi kanta. Data
koma daki tagumi ta zabga tana tunani ita da
suka yi kaca-kaca ma sun shirya bare ni? Kamar
tabi shi har falon bishiran ta gaida shi, amma sai
tafasa. Tazuba ido taga zai bar gidanne ba tare
daya leko dakinta ba? Sun gama karin
kumallonsu tsaf yayo wanka don tafiya gurin aiki,
sai dai kayan dazai saka suna dakin ummi. Ya
fito yanufi dakin. Ciki- ciki yayi sallama ita kam

tsoro ne ya tsirga mata, tasake tambayar kanta
mekuma yafaru? Ta amsa tare da gaida shi. Nan
ma a ciki ya amsa, yadauki kayan sai dazai fita
sannan yace ba kya bukatar komai ko?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login