Showing 3001 words to 6000 words out of 26773 words

Chapter 2 - Ido A Duhu Book Free Complete By billy S Fari.doc

tayi mai Wan nisa kafin ta isa police station Win, tana fitowa ta fara haWuwa da d.p.o ya fito da alama masallaci zai je don an soma kiraye-kirayen sallah magrib, sanin ko ita waye yasa ya nufi wajen ta, fuskarta ba walwala suka shiga gaisawa ta faWa masa abinda ke tafe da ita, da kanta yayi mata jagora zuwa ciki yanayi mata bayanin abunda ya faru da suka sani. Bata iya cemasa komai ba har suka shiga ciki ya buWe mata office Winsa ta shiga, sallah ya faWa mata zai je ya yi amma yasa a fito mata dashi sannan ya wuce wajen sallah. Police biyu ne suka rirri?osa suka shigo office din dashi, gaba-daya an bubbuge masa fuska ta kumbura saboda dukan da yasha, shiyasa ko tafiya baya iya yi sai da aka rikosa don duk dukan daya sha akan ya faWi waya turosa ya yi kisan ya?i cewa uffan, da sauri ta taso tana kallon halin da Wan nata ke ciki idanuwanta na kawo kwalla. "Me kuka yiwa yarona haka? Kenan kashewa kuka tashi yi ko?". Ta faWa a tsawace tana zaro idanuwa tana kallon police Win, gaba-dayansu babu wanda ya tanka mata suka ajiye sa ?asa sannan suka fice daga cikin office Win,? kuka ta fashe dashi ta zube ?asa tana shafa fuskarsa da kamanni da gaba-daya an sauya masa su tana cewa, "Me kaje ka aikata haka ka jefa kanka cikin wannan halin, don Allah kafada mani baka aikata abinda ake zarginka dashi ba". Hannunta ya cire daga kan fuskarsa da take shafawa dake matu?ar yi masa zugi ba tare daya ce komai ba, ri?e hannun tayi sosai tana kallonsa ta ci gaba da cewa, "Kayi mun magana my son me yake faruwa? Da gaske ne ka aikata laifin da ake tuhumar ka dashi?" Nan ma bai ce komai ba ya juyar dakai gefe tamkar baya son jin kalaman mahaifiyar tasa, "Shikenan ko ka aikata ko ma baka aikata ba babu abinda zai sameka, jikina yana fadamun sharri akayi maka don haka ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru". Haka taci gaba da suruttanta har ta ?arasa ba tare daya ce uffan ba, jiki ba ?wari ta mi?e don dama tasan za'a yi hakan, zafin ransa bazai taSa bari ya iya sauraren kowa ba ko da kuwa itace har sai lokacin daya huce, police ne suka sake shigowa suna sanar da ita lokacin da aka Wibar masu ya ?are, daga nan suka sake Waga sa suka mayar dashi cikin cell suka rufe, ita kuwa kwalla ta share ta dauki handbag Winta ta fice daga police station Win ba tare data sake yiwa kowa daga cikinsu magana ba..
*******
Tunda ta shigo cikin gidan take kuka ta kasa yiwa kowa bayanin abinda ke faruwa, sai da taga ran mahaifiyar tata ya soma Saci sannan cikin shesshekar kuka ta shiga faWa mata halin da ake ciki, sallallami ta shiga yi tana faWin."Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un amma wannan yaro ya cuce mu, muna zaman zamanmu zai jawo mana tashin hankali da fitina, yanzu ke kina ganin akwai wanda ya isa ya fitar dake a wannan case Win, ai ya bar mana baya da kura don babu wanda ya isa ya kare ki sai Allah". Yayan yarinyar da shigowar sa kenan yace. "Tabbas akwai ?alubale a gabanmu domin yanzu haka da naje sallah baki ji maganganu dake tashi akan wannan maganar ba, don haka na shiga ban Wauka ba bata fidda Sarawo sai dai muyi addu'a ko meye Allah ya kawo mana shi da sau?i". "To Amin ya rabbi, sai dai ai ita gaskiya gaskiya ce, sannan mai ita yana tare da Allah, wannan kukan ba maganin da zai yimaki tunda mai afkuwa ta afku kuma agaban idanuwan ki, kalubale dai ne ya riga ya fuskanto mu sai muyita addu'a". "Shiyasa kika ga bana son ala?ar ta da mutanen gidan amma kina ganin laifi idan ina cewa ta dena shige masu, to gashi yau abinda shiga gidan ya haifar mata da bamu san inda abun zai tsayawa ba". Ita dai mahaifiyar ta su kasa cewa komai ta yi sai uban tagumi ta buga tana tunanin dole fa idan za'a yi bincike zai zo takan yar tata tunda komai akan idanuwanta ya faru.





ALLAH KA JIKAN IYAYENMU =?O?
[6/15, 3:18 PM] Qee's Queen=?x?: *IDO A DUHU*

? ? ? ?? *NA*

*BILLY S FARI* =؎?

Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 4.

? ?? A gurguje na fito daga cikin Wakina ina sa?ale jakar da nake zuwa makaranta da ita, Amatul-Alim cikakken sunana kenan da iyayena suka raWa mani amma suna yi mani la?ani da *Janaam* sunan da kenan akafi sani na dashi kuma ake kira na dashi, sauri nake yi ri?e da ni?af a hannuna ina ?o?arin Waurawa akan fuskanta don na kusa makara, na kuma tabbata Nu'aymah ?awata da muke wucewa tare a motarta ta fito tun Wazu ni kaWai take jira, hakan yasa ban damu na tsaya karyawa ba na nufi hanya, Muryar Mamah? baki tana cewa, "A'ah! Janaam ina zuwa bakiyi kari ba". Da sauri na juyo na ?araso wajen ta ina cewa, "Mamah na makara zan tafi sai na dawo, kin san halin mutuniyar tana can tana jirana, yanzun nan zaki ji tafara yimun horn idan ta gaji da jira". "To haka zaki fita baki karya ba". Na juyo kamar zanyi kuka jin muryar yayana dake fitowa daga ta sashensa yana faWa, cike da girmamawa nace, "Ina kwana Ya Jameel?" Fuskarsa a sake ya amsa mani yana murmushi haWe da ?arasowa wajen yana cigaba da cewa. "Lafiya ?alau Janaam, me yasa kullum bakya son yin kari kafin kifita? So kike yi wani ciwon yazo ya shige ki ki tada mu tsaye?" "Kai ma ka faWa, kullum faWan da nake yi da ita kenan akan fita ba kari amma bata ji!" Mamah ta faWa tana kallona, sai dana daura ni?ab Win dake hannuna akan fuskata sannan na Wage sa nasa? hannu cikin flate Win da Mahmah ta zuba abun karyawar da zata ci na Wauko yankan soyayyen arish Waya na tura abaki sannan na ciro tissue dake kan table Win ajiye na goge hannuna ina cewa. "Afuwa ya Jameel gashi naci, in Sha Allah kuma na dena yin hakan bazan sake ba, amma dai yanzu zan tafi saboda 10 zamu shiga lecture kuma mintuna kadan ya rage ta buge, mun kusa makara kuma kasan halin mutuniyar". na faWa haka tare da ficewa daga falon cikin Wan Waga muryarya ina yiwa Mamah sai na dawo, "To adawo lafiya kiyi addu'a kiyi addu'a kafin kifita?". "Ok Mamah bye". "Bye Janam ki kula da kanki".
Ina fita kai tsaye gidansu Nu'aymah na nufa, cike da natsuwa nake tafiyata har na ?araso cikin gidan, dai-dai lokacin Nu'aymah na kokarin fitowa da mota ta maka maka mani harara, dariya na saki daga cikin ni?ab Wina na ?arasa wajen ina faWin, "Tuba nake yi muje ko?" Ina shiga sai ga yayanta Nu'aym ya fito cikin shirinsa yana gyara clip Win hannun rigarsa, knocking Win glass din ?ofarta yai ta danna glass Win ya zuge, "Fito ki koma baya Aymah". Ya faWa fuskarsa ba wasa, Nu'aymah ta Wan turo baki tana cewa, "School fa zamu je ya Aym". "Na ce baza ku je bane? Fito mana nace". Ina ganin Nu'aymah zata fita nima nafara ?okarin fita yai saurin dakatar sani, "No ki zauna abunki". Ya faWa yana zaunawa inda Nu'aymah ta tashi tare tada motar muka bar wajen, cike da natsuwa yake driven duk da yadda ya fahimci sauri muke yi mu isa school, dukkanin mu babu wanda ya iya cewa uffan daga ni har ita, Allah ya gani ba ?aramar takura naji ba zamana a wajen, a hankali ya juyo yana kallona nayi saurin kauda kaina gefe, "Morning Janaam". Na ji muryarsa ta daki kunnena duk da maganar yayita can ?asan ma?oshi tamkar baya son maganar. Ban iya amsa shi ba don nasan ya yi hakan ne saboda ban gaishesa ba. Shiriyar ajiyar zuciya ya sauke a sirrance yana sake ri?e steering wheel Win motar haWe dayin gyaran murya yace.
"Aymah meke damun ?awarki ne? Ko azumin magana take yi?" Nu'aymah dake baya ta turo baki kamar zata yi kuka tace, "Don Allah Ya Nu'aym kabar wannan maganar ka taka mota, wallahi mun kusa makara kuma duka laifinta ne". Nu'aym ya sake juyowa yana kallona, ni har mamaki yake bani yadda yake son kallon nawa duk da rufe fuskata take, ?asa nayi da kaina ina wasa da yatsun hannuwana naji yace, "Wai haka ne Janam?".? A maimakon na amsa masa sai na tsinci kaina da cewa, "Please Ya Nu'aym mun makara fa?" "Am sorry". Ya faWa yana Wan taka motar, da haka muka iso school, yana yin parking Nu'aymah ta Salle marfin motar tafita tana faWin, "Bye Ya Nu'aym" "Bye Aymah". Ya faWa yana Waga mata hannu, na Salle marfin zan fita Nima yai saurin dakatar sani ta hanyar cewa, "Janaam ina son yin magana dake, gashi tun da na dawo ?asar nan banda wani lokacin kaina kuma jibi zan koma". "Kayi ha?uri muna da lecture yanzu in ba so kake a hanani shiga ba kaga Nu'aymah har ta wuce abunta ta barni". Daga haka ban jira cewar sa ba na fito na nufi cikin hall Win da zamuyi lecture, ina jin idanuwansa akaina amma ban iya juyowa har na shige ciki, Alhamdulillah ko da na shiga har lokacin malamin da zai mana lecture bai zo ba, na zauna ina sauke ajiyar zuciya haWe da mamakin to wace magana yayan Nu'aymah ke son yi dani.
Bayan mintuna biyar da zamana sai ga malamin ya shigo yana bamu hakuri akan delaying da yayi, awa biyu muka dauka muna lectures kafin ya gama ya fita, bamu fita ba sai da Nu'aymah tasa na sake yi mata bayanin karatun da muka gama sannan ta Wago ta kalleni tana cewa, "Janaam muje capteria wlh yunwa nake ji". Kusan haka take a wajena yunwa nake ji sosai, don haka muka mike tare muka fito, muna fitowa idanuwana suka sauka akan Umar Faruk a can gefe shi da ?awayensu da duka mata ne sai abokinsa namiji ?waya Waya riko, yan matan sun zagaye su sai fira suke yi suna dariya shi kuma yana tafewa dasu, kallo Waya nayi masu na janye idanuwana saboda a kaf faWin makarantar babu wanda na tsana kamarsu, bani ?aunar abinda zai haWa ni dashi koda kuwa alkhairi ne saboda yadda ya Wauki kansa acikin makarantar, baya ganin mutuncin kowa kuma baya shakkar wulakanta kowa cikin mutane, ciki kuwa hadda malamai saboda yana Wan Wan wani babban attajirin mutum dake faWa aji a gwamnati mai ci yanzu, mata sune abokansa aduk inda yake baka rabashi dasu, yana taka duk wanda yaso sannan ya daukaka wanda yake so ba tare da an taSa dakatar dashi ba a makarantar, duk da wuWannan Wabiu nasa kuma ba kaWan 'yan mata ke sonsa ba saboda kyan da Allah yayi masa da kuma iya wanka, uwa uba tarin arziki da yake dashi da kana kallonsa zaka san shi Win ba Wan gidan ?ananan mutane bane. Umar Faruk wankan tarwaWa ne wato chocolate colour, yana da manyan idanuwa masu launin ja kuma a shanye suke tamkar mai jin bacci, haka kuma yana da dogon hanci da loSawar kumatu musamman idan yayi dariya duk da ba kasafai ya fiye yinta ba, yana da matsakaicin tsawo da kuma murWaWWen jiki dake nuna yana motsa jiki, na fahimci duka hakan ne lokaci Waya saboda yadda 'yan mata ke yawan zancensa.
A hankali na ci gaba da saukowa akan matattakalar wajen da muka gama Waukar karatun ina ma Nu'aymah magana, jin shiru bata amsa ni ba ya sani Wago kai da niyar sake yi mata magana, abun mamaki sai na hangota a can matakalar farko ta saki baki tana kallon gefen da su Umar Faruk suke tana faman kallonsa, takai ci ne ya kamani na Wan tsaya ina kallonta nima kafin na koma na ri?o hannunta muka shiga saukowa ina cewa, "Wlh Aymah bakiyi ba! Na rasa meye abun kallo a can". Nu'aymah dake yi tana juyawa tana kallonsa tace, "Baza ki fahimta ba Janaam, gayen can na matu?ar burgeni wallahi, ba don nasan halinsa ba tsab zai iya disgani da na je mun zama Friends ni dashi, Allah Janaam yana matu?ar burgeni sosai". TaSe baki nayi bayan mun sauko ina cewa, "Lallai ba kida aiki Aymah, meye abun burgewa atattare dashi, bakya ganin dabi'unsa da halayyarsa ne? Ai sam ko kusa bai dace daya shiga rayuwarki ba don Allah tun wuri karki fara, mutum bai da aiki sai faWin rai da zama cikin mata sai kace wani Wan daudu". "Hmm! Bazaki gane ba, ai Wlh ni ko gaisawa ce mu ri?a yi dashi hakan ba ?aramin faranta raina zai yi ba,". Nu'aymah ta faWa tare da juyawa gefe, hango motar ta a inda mukayi parking Wazu tayi, tayi saurin taSo ni tana faWin."Bar wannan zancen Janaam dama ya Aym ya bar mana motar anan bai tafi da ita ba?" Na juyo na kalli motar haWe da cewa. "Gashi kin gani, amma nima ban san bai tafi ba gaskiya tunda bai bani key ba yana hannunsa, kin kuma san idan yasan anan zai bar maki ita dole ya bani key Win yace na wuce maki dashi". "Zo muje" Nu'aymah ta faWa tana jan hannuna muka nufi wajen motar, tamkar wanda idanuwansa ke kanmu muna isowa wajen ya zuge glass Win gefensa fuskarsa Wauke da murmushi yana cewa. "Har kun fito". Nu'aymah ta zato idanuwa tana kallon sa haWe da cewa, "Can't believe wai da gaske kai ne yaya ka tsaya jirana? Muna fa da lecture Wi 2-4". Ni kuwa a zuciyata mamaki ne yakama ni kar ace ya tsaya ne akan maganar daya ce yana so yayi dani? Ai kuwa sai ji nayi yace wa Nu'aymah. "Malama bake na tsaya jira ba, ?awarki Janaam nake son magana da ita shiyasa ban tafi ba". Nu'aymah ta taSe baki tana haWe rai take cewa. "Dama ai na sani, kinga Janaam bara naje na samo mana abinda zamu ci, kai kuma ya Aym gaka gata amma ka sani dole sai ka biyo ta hannuna na buga maka stamp, idan ba haka ba na hana a saurareka". Nu'aym ya saki murmushi haWe da ciro kudi a aljihunsa ya mi?a mata yana cewa, "Eh na dai ji, karSa ki ?ara ki sawo maku abu mai kyau, in dai ke nasan halinki yanzun nan sai kije ki kwaso maku harkar kayan za?i da snacks, kuma sam basa maganin yunwa don haka kawai kiyi maku take away Win abinci mai kyau". Nu'aymah na dariya ta karba ta wuce, shi kuma ya Wan le?o daga cikin motar yace, "To Ranki shi daWe shigo daga ciki muyi magana". "A'a ya Nu'aym nan ma ya isa". Na faWa ina jin ?irjina na wani bugawa da karfi, murmushi ya yi ya fito cikin motar shima ya jingina a jikinta kamar yadda nayi sannan yace..





ALLAH KA JIKAN IYAYENMU =?O?
[6/15, 3:18 PM] Qee's Queen=?x?: *IDO A DUHU*

? ? ? ?? *NA*

*BILLY S FARI* =؎?

Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 5.

"Janaam ya lectures Win? Ina fatar dai laifina bai sa aka hanaki shiga ba?" Na Wanyi murmushi daga cikin ni?ab Wina haWe da cewa, "Ko Waya ya Nu'aym". Ya amsa da alhamdulillah yana gyara tsayuwar sa, shiru ya Wanyi kamar mai wani nazari kafin yai gyaran murya yaci gaba da cewa, "Bansan ta wace fuska zaki kalli maganar da nake so muyi dake ba, amma ina rokonki daki taimaka ki yi mani kyakkyawar fahimta, kin sani ni ba mazaunin ?asar nan bane amma ba tun yau ba nake jin ?aunarki da soyayyarki acikin zuciyata, duk tsawon tazarar dake tsakaninmu dake, da yadda mukayi nisa ban taSa jin ?aunarki ta ragu a zuciyata ba, dake nake kwana kuma dake nake tashi araina har zuwa wannan lokacin". Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya kafin yaci gaba da cewa, "Ina sonki Janaam so mai tsanani da bana jin zan iya rabuwa dake, ina fatar samun alfarmar so a wurin ki ba tare da kin bari nasha wahala ba". Shiru nayi ?irjina na wani irin duka da jin kalaman yayan Nu'aymah saboda ganin rashin cancantar tarayyarmu dashi, ita kanta Nu'aymah lokuta da dama duk da kasancewar muma muna da namu rufin asiri dai-dai gwargwado nakan yi ?o?arin nisanta kaina da ita, soyayyar da take yimani tasa ko nayi hakan zata sake janyo ni cikin jikinta da kuma rayuwarta, mahaifina har ya rasu mutum ne mai matsakaicin ?arfi, saSanin nasu mahaifin dake da matu?ar tarin arziki shiyasa ban fiye shige masu ba, muhimmancin da Nu'aymah ta nuna mani ina dashi a wajenta tare da bani matsayi mai gima shiyasa na saki jiki da ita sosai har ?awancen namu yayi ?arfi ta yadda zaka iya cewa gida Waya muke. taya kuma yanzu yayanta zai zo mani da zancen wata ala?a ta soyayya tsakanina dashi! Jin nayi shiru ina wannan naz??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????arin ya sashi cewa. "Janaam bazan maki dole ba nace sai kin amshi soyayyata yanzu-yanzu, zan baki lokaci kiyi tunani, idan kin amince dani sai na baki amanar zuciyata duka kiyi yadda duk kike so da ita, jibi zan koma ina fatar zaki bani izinin sake tuntuSarki naji ra'ayinki kafin na tafi". "Shikenan ya Nu'aym ba damuwa Nagode ". Na faWa ina ?o?arin barin wajen, "Ina kuma zaki tafi tunda ?awar taki bata dawo ba?" "Zan jira ta ne daga can". Na nuna masa wani gurin da muke zama ni da ita, kasa bari yai na ?arasa wajen ni kaWai sai dai muka tafi tare yana cewa, "Nagode ma Allah daya sa kike rufe kyakkyawar fuskar nan taki Janaam, ba don haka ba da nikam na shiga uku". Nayi dariya haWe da cewa, "Shiga uku fa kace Ya Nu'aym, na meye?" Ya Nu'aym dake kallon yanayin cikin makarantar tamu a natse yace, "Baki ga yawan samarin dake cikin makarantar nan taku ba? Ai inaga da zasu san yadda Allah ya kyautata halittar ki da kuma kyan da kike dashi da ban samu damar tsayawa tare dake ba don na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login