Showing 15001 words to 18000 words out of 26773 words

Chapter 6 - Ido A Duhu Book Free Complete By billy S Fari.doc

kuma na gefensa tsaye wasu sun jingina a jikin motar ita kuma Felicia saman motar ta haye tana yan hare-hare hango Nu'aymah da Janaam dake tafe daga can nesa, yau abakin gate driver ya ajiyesu don zai wuce da Nihla makaranta ya ajiyeta shiyasa suka tako ?asa, tunda Nu'aymah ta hango Umar Farouk ta faWaWa fara'arta tana murmushin jin daWin ganinsa. Janaam kuwa sai harara take aika masa da ita daga shi har yan matan nasa ta cikin ni?ab, Felicia na ganin sun kusa karasowa ta diro daga kan mota tana cewa, "Zan koyawa yaran can hankali yau". Ba tare da Umar Farouk ya Wago ba ya ce, "waya aike ki ne? Wannan aiki na ne ba na Waya daga cikin ku ba". Yana gama faWar hakan ya fito cikin motar ya tunkaro inda su Janaam ke nufowa, yana kawowa ya tare gabansu fuskar nan tasa a haWe ba Wigon annuri ko Waya akai, cikin daburcewa da farin ciki Nu'aymah ta fara ?o?arin yi masa magana yai saurin dakatar da ita ta hanyar Waga masa hannu idanuwansa na akaina, cikin dakewa na sake haWe rai duk da ina cikin ni?ab, "faWamun ke yar gidan uban waye? Me kike ta?ama dashi da har kike jin kanki ke wata ce? Kin san hatsarin da ke cikin shiga sabgata ba tare da nine na so hakan ba?" Umar Farouk ya faWa yana sake matso ni, ?in matsawa nayi baya don babu alamun jin tsoro atattare dani nace, "And so?" ina jefa masa wani mugun kallo a lalace mai cike da tsana da kuma reni, ran Umar Farouk ne ya sake Saci ya juya gefe yana shafa kansa, ban an kara ba kawai na ji ya Wage mani ni?af ya fizge tare da wurgi dashi gefe, tashin hankali! Abinda na faWa kenan cikin zuciyata idanuwana na canja kala saboda tsananin Sacin rai, ina Wagowa ban tsaya wata-wata ba na Waukesa da wani zazzafan mari, shekarata uku kenan a makarantar yanzu muna shekarar ?arshe semester ta farko, tunda nake ban taSa cire ni?af Wina ba, nasan da yawa a makarantar kai a class Win mu ma ko za'a kashesu basu san yadda fuskata take ba, shine yau saboda jakanci na Umar Farouk zai kware mani fuska a tsakiyar makaranta saboda yana jin shi wani ne, nunasa na shiga yi da yatsa cikin matsanancin Sacin rai ina cewa, "Ni ba karya bace kamar wuWancan karnukan dake bibiyarka Umar Farouk, ba kuma wulakantacciya bace da zaka yi tunanin zan iya zuba idanuwa ka wulakanta ni, idan kana tunanin zaka iya tozartani a cikin makarantar nan to a shirye nake dana tozartaka fiye da haka kaima saboda kai ba ubana bane, ba kuma kai ka halicceni ba balle naji tsoronka kamar yadda sauran mutane ke ji, ina tunanin kuWi ubanka ya biya maka ya kawoka makarantar nan ai ko?, to haka nima kuWi ubana ya biya ya kawo ni don haka banga dalilin da zai sa in dauki reni ga kowa ba, hmmm! Wai da kake Waukar kanka wani kana tunanin duk mai hankali zai ji tsoronka ne bayan kai da yan daudu ba kuda maraba! kana namiji amma kana Suya a bayan mata har kake tunanin zan ji tsoronka? Never walh". Na kare maganar cikin zare idanuwa kafin naja hijab Wina na rufe fuskarta dashi sannan na bar wajen na nufi class ina jin zuciyata na mun ?una, Nu'aymah da gaba-daya ta ruWe sai kawai ta dauki nikaf Winta ta bita a baya.
Umar Farouk kuwa tamkar an dasa shi a wajen haka ya kasa motsawa kuma ya kasa Wago kai, ya rasa me yafi yi masa zafi tsakanin marin da Janaam ta sauke masa da kuma kalaman data faffaWa masa, dariya ya soma yi yana imagining wai kamar shi za'a yiwa haka, wata dariy?r ya sake yi sannan ya juya ya nufi wajen motarsa da yan matansa ke gun sake da baki ganin abinda ya faru, wanda y?na juyowa gaba-daya suka sha jinin jikinsu don sun san tsaf zai juye akansu, book Winsa kawai ya ciro cikin motar ya rufe sannan ya nufi class, yan matan na ?o?arin rufa masa baya yai saurin dakatar dasu yai tafiyarsa abunsa.
Lecture ake yi amma gaba-daya hankalinsa baya wajen sai kallon Nu'aymah data mayar da ni?af Win ta yake yi da wani irin mugun mamakin abinda tayi masa, ana gamawa ya fito ya ja motar sa ya fice daga makarantar ba tare daya damu dayin lecture Win dake gaba ba.
Ni kuwa ina kalle da Nu'aymah dake son yi mani magana akan abinda ya faru amma nayi mata banza, ganin bata ga fuska ba yasa ta sha jinin jikinta har muka gama lecture Win wunin ranar ba tare data cemun uffan ba, bayan mun tashi muna tafe na kalli yadda duk tayi wani sanyi nayi murmushi haWe da cewa. "Wai Aymah lafiya naga duk kin yi wani sanyi sai kace marar lafiya?" Nu'aymah ta Wago kai ta kalleni na Waga mata gira haWe da cewa, "Meye?" Ta sauke ajiyar zuciya ta kalleni sannan tace. "Besty kin bani tsoro, anya kece kuwa?" Na haWe girar sama da ?asa kafin na bata amsa nace, "Me kika gani? Wani abun ne ya faru?" Tana kokarin bani amsa muka ga motar Nu'aymah ta tsaya agabanmu, Ya Nu'aym ne na gani bayan ya zuge glass fuskarsa Wauke da murmushi, bansan dalili ba ganinsa kawai yasa naji Sacin ran da nake ciki ya gushe, "Sannunku yan mata, ina zuwa?" Ya faWa yana Waga mana gira cikin sigar zolaya, dariya duk muka sa kafin Nu'aymah ta buWe gaba ta shiga ni kuma na buWe baya na shige...




ALLAH KA JI?AN IYAYEN MU=?O?
[6/15, 3:18 PM] Qee's Queen=?x?: *IDO A DUHU*

? ? ? ?? *NA*

*BILLY S FARI* =؎?

Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 10.

Sai da Ya Nu'aym ya tada motar ya hau titi sannan ya juya yana kallon Nu'aymah yace, "Aymah why are you so Cool? Me yafaru ne?" Juyowa Aymah tayi tana kallona na haWe rai tare da kauda kaina gefe, sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta kallesa naji tace. "Ba komai Ya Nu'aym kawai na Wan gaji ne". "Ehm..wai haka ne Janaam?" Ya tambaya yana kallona ta cikin madubi, murmushi na saki tare da cewa. "Eh tunda haka ta faWa maka Ya Nu'aym, ina wuni?" "Lafiya kalau, ya lectures?" "Alhamdulillah". Na amsa masa ina kallon waje ta cikin glass Win motar dake gefena, daga haka babu wanda ya sake cewa komai har muka iso gidansu, har zan fita yai saurin dakatar dani yana cewa. "No bari na ajiyeki gida". Kasa yi masa musu nayi duk da bana son Ya Jameel ya ganeni saboda yawan ja mini kunne da yake yi akan shige masu da yake ganin kamar ina yawan yi. "Besty sai gobe ko?" Nu'aymah ta faWa bayan ta fita tana Wago mani hannu, Nima hannun na Waga mata sannan Ya Nu'aym ya ja motar yabar wajen.
Shiru kake ji ba wanda ya sake cewa wani abu tsakanina dashi kafin can ya Nu'aym yace. "Janaam in sha Allah gobe da safe zan bar ?asar nan, kiyi ha?uri na saSa alkawarin cewa zan baki kwanaki kiyi tunani akan soyayyata, hakan ya faru ne saboda matsa mini da su Abba keyi akan na koma hankalinsu zaifi kwanciya, bayan haka akwai ayukka masu tarin yawa dana baro daya kamata ace na koma Win duk da ba hakan naso ba". Shiru ya Wanyi yana driven a hankali tamkar wanda baya so ya isa inda zai je kafin yaci gaba da cewa.
"Janaam ina so kifaWa mini gaskiya idan har kina da ra'ayi akaina". Cikin jin kunya na saukar da kaina ?asa ina tunanin amsar da zan bashi, idan har nace zuciyata bata son Ya Nu'aym to nayi ?arya, sai dai ina tunanin ya yi wuri na amshi tayin soyayyarsa cikin kwana biyu har sai na gama fahimtarsa da sanin ko waye shi." "Please Janaam kice wani abu mana". Na ji ya sake faWa haWe dayin parking adai-dai lokacin da muka iso ?ofar gidanmu. Tsoron kar Ya Jameel ya rutsani yasa nayi saurin fitowa cikin motar ina cewa, "Na amince ya Nu'aym". Ina gama faWar hakan cike da jin kunya na shige gida da gudu ina jin zuciyata na wani irin bugawa da sauri da sauri".
Nu'aym kuwa Janaam na faWin hakan ya rintse idanuwa yana yiwa Allah godiya, tabbas ranar yau na Waya daga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tarihin rayuwarsa da bazai iya mantawa da ita ba, kalamai ukun data furta nata amince dashi sun matukar sanyaya masa zuciya, kofar gidansu ya ?urama idanuwa tamkar wanda ke jiran fitowar ta kafin ya saki murmushi ya ja motarsa yabar wajen.
******
"Umar Farouk wai lafiya tun safe daka dawo school kazo ka shige Waki ka rufe ?ofa baka fito ba? Me yake damun ka ne?" Mom dake tsaye bakin kofar Wakin Umar Farouk tana bubbuga wa ta faWa cike da damuwa, mayarta ta kusan bakwai kenan tana yi masa knocking amma bai buWe ba, yanayin da yaji muryarta yasa shi tasowa ya buWe kofar tare da juyawa ya koma ciki, "Umar Farouk lafiya kake?" Ta faWa tana shigowa cikin Wakin, sinne kai ya yi ?asa don gani yake tamkar idan aka kalli fuskarsa za'a hango marin da Janaam tayi masa, a hankali yace, "Momy kaina ne yake Wan yi mini ciwo amma is ok now na ji na samu sau?i". "Are you sure Umar Farouk?"."Yes Momy yunwa dai nake ji bari na watso ruwa sai na fito naci abinci". Ya faWa tare da barin wajen don baya son ta sake jefo masa wata tambayar, ruwa masu sanyi ya sakarwa kansa sosai har na tsawon minti biyar kafin yayi wankan ya Waura towel ya fito, tsaye yai gaban mirror yana ?arewa kansa kallo, kyakkyawar fuskarsa zuwa murWaWWun damatsan hannunsa, faffaWan ?irjinsa zuwa cikinsa dake nannade ya fidda wasu layoya, coily hair Winsa ya shafa yana sake ?urawa fuskarsa idanuwa, da sauri ya rintse ido tunowa da marin da Janaam tayi masa yana sake jin saukarsa akan fuskarsa kamar lokacin, wata ?ara ya saki haWe da du?awa yana ri?e gashin kansa da hannu biyu tamkar zai cire sa, kamar ni wannan yarinyar zata mara kuma nakasa yin komai? Wacece ita? Ya faWa cikin ransa yana jin zuciyarsa na sake yi masa zafi, tabbas ta taro wasa mai kyau tsakanin shi da ita, ya ji daWin da ita ce ta fara buga wasar, don haka dole suci gaba da bugata har lokacin da Waya zai yi nasara tsakanin su. Jin Momy na kiransa daga palour ya sashi mi?ewa yana faWin, "Momy yanzu nan zan fito".
Da?yar ya iya tsayawa ya shafa mai ya samu kaya marasa nauyi ya saka, har ya Wauki comb zai gyara sumar kansa sai kuma ya fasa ya Wauki turare kawai ya fesa jikinsa sannan ya fice zuwa paloun, a can ya tadda abincin da Momy ta shirya masa kafin ya fito, zaunawa ya yi don sosai yake jin yunwa bazai iya jira ta dawo ta zuba masa ba, abincin ya buWe ya zuba ya ci ya ?oshi sannan ya koma ciki ya Wauko key Win motar sa da wayar sa ya fice zuwa part Winta. Sai daya gaisheta sannan ya ce mata zai fita, addu'a tayi masa tana sauke ajiyar zuciya tare da jin daWin fitar da zai yi, ko ba komai tasan zai Wan wartsake idan ya haWu da abokanansa,
Umar Farouk ko daya fita lambar Felicia da Billy yan matansa ya kira su zo su rakasa buga table tennis da yake zuwa yi duk mare ce ko kuma basket Ball, cikin mintuna biyar sai gasu sun iso ko wace taci gayu a tunanin ta ita kaWai ya kira, nan fa suka shiga kallon kallo da yan harare-harare tsakaninsu, Umar Farouk bai bi ta kansu ba ya buWe gaban motar da sauri Billy dake kusa ta shige, dole Felicia ta buWe baya ta zauna tana rufe ?ofar da ?arfi, shi kuma ya tayar da motar yabar wajen ba tare daya cewa Waya daga cikinsu ko uffan ba.
*******
Fitowa ta wanka kenan naga wayata dake kan standing mirror na haske da yake a silent na sakata, ?arasowa nayi na Wauka ina zaunawa gefen katifata haWe da Waga kiran duk da sabuwar lambace na kara a kunnena. "Amincin Allah ya tabbata agareki matata". Naji an faWa cikin wata irin sanyayyar murya mai cike da natsuwa, wadda ta tabbatar mini da cewa Ya Nu'aym ne, murmushi nayi haWe da cewa. "Tare dakai ya Nu'aym, ya ka isa gida Wazu?" "Lafiya ?alau kyakkyawata, Allah yasa ban tasheki bacci ba?" "Ko Waya, idan ma kayi hakan to girmanka ne." "Godiya nake yi, dama nakira naji muryarki ko zan samu nayi bacci mai daWi, baccin da nake da tabbacin daga shi bazan koma yin bacci mai daWi ba kuma". "Saboda me ya Nu'aym?" Ya Wan sauke ajiyar zuciya sannan naji yace, "saboda zanyi nesa da masoyiyata abar kauna ta, Janaam ni fa a yadda naso iyaye su shiga maganar mu kafin na tafi, son samu ma ace har aure an daura mana in Wauke ki na tafi dake don samun cikakkiyar kulawarki, sai dai yanzu lokaci ya ?ure da bazan samu wannan damar ba, zan yi hakuri na fara renon soyayyaki tayi girma tare da rassa a zuciyarki har zuwa lokacin da zan sake dawowa, nasan a lokacin ma kun kammala karatu sai na shigo da karfina ayi komai a gama ko kuwa?" "Idan haka ka tsara Shikenan ba laifi, amma a son samu na mu samu cikakken lokacin da zamu fahimci juna, watanni basu fi takwas ba ya rage mu ?are school, gashi nisa ya sanya katanga a tsakaninmu da baza mu samu damar kasancewa tare ba akoda yaushe, Ni ina ganin yayi wuri lokacin idan iyaye suka shiga maganar". "But amma hakan ya dace Janaam indai har da gaske muke son juna". "Haka ne, amma muna bukatar lokaci sosai domin yiwa soyayyar mu kyakkyawan ginin da bazai rushe ba agaba." "To Shikennan zan jira har wannan lokacin, amma ki kula mini da kanki, ki killace mini gangar jikinki ni kaWai, ki bawa zuciyarki kyakkyawan tsaro wa ni kaWai Janaam, ina sonki ina kuma jin kishi sosai da zan tafi na barki wasu mazan na kalle mini ke a makaranta, na baki amanar kaina Janaam don Allah kada ki barni". Murmushi nayi cike da jin daWin kalamansa nace, "Ka dauka Janaam acikin makafi take karatu da idanuwansu baza su taSa ganinta ba, haka kuma dukkansu guragu ne bazasu taSa zuwa inda Janaam Winka take ba, zan kula maka da kaina har lokacin da zaka dawo in sha Allah". Wata irin ajiyar zuciya mai ?arfi naji ya sauke haWe da cewa, "har kinsa na ji sanyi, abu daya ya rage shine kimun al?awarin bazaki sauya ni ba saboda bana kusa dake". Nayi dariya ina mamakin to wane irin sauyasa zanyi tunda babu wani namiji dake zuciyata face shi, na amsa amsa masa da cewa, "nayi maka alkawari ya Aym daga kai ba ?ari ba kuma canji". "Alhamdulillah nagode sosai Janaam, I will forever love you". "Me too". Na faWa nima don tuni ya gama tsuma ni da daWaWan kalaman sa. Hira mukayi sosai don har ?arfe sha biyu muna ma?ale da juna, A ranar Ya Nu'aym bai barni ba sai daya gama sanyaya ko wace gaSa ta jikina da salon soyayyarsa, ya kuma tabbatar mini shi Win cikakken masoyi ne da a shirye yake ya bani farin ciki na har abada, hakan yasa na mi?a masa dukkanin yarda da kuma soyayyata, na kuma amince ya ja ragamar rayuwata har zuwa lokacin da zamu kasance cikin inuwa Waya a matsayin miji da mata...



ALLAH KA JIKAN IYAYEN MU =?O?
[6/15, 3:18 PM] Qee's Queen=?x?: *IDO A DUHU*

? ? ? ?? *NA*

*BILLY S FARI* =؎?

Arewabook:-billysfari
Wattpad:-billyfari9

? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 11.

Tun da asubar fari wayar Ya Nu'aym ce ta tashe ni daga bacci, mirginawa nayi tare da mi?a hannuna a jikin socket na ciro wayar dana saka a chargy da zan kwanta jiya. Cikin magagin bacci na Waga kiran tare da kai wayar a kunnena nayi sallama, sautin muryarsa naji ya ce, "wake up kyakkyawata, me kike har yanzu baki tashi ba gashi na gama shiri zan tafi". "Da wuri haka Ya Nu'aym?" Na faWa ina ware idanuwana daga baccin da nake tare da mi?ewa zaune, murmushi Nu'aym ya saki jin abinda ta faWa yana cewa, "Morning kin tashi lafiya?" "Lafiya ?alau kai fa?" "Ehhh to alhamdulillah zance don nasha mafarkanki har ba iyaka jiya, ciki kuwa hadda na munyi aure kin haifa mini kyawawan yara masu kama dake." Cikin jin kunya na yaye bedsheets Win dana lulluSa dashi na sauko da ?afafuwana ?asan katifata ina cewa, "Kai ya Nu'aym!" "Kai ya Nu'aym." Shima ya faWa yana kwaikwayon muryata tare dasa dariya, nima dariyar nayi kafin na mi?e ina cewa. "Bara nayi sallah sai muyi waya". Cike da amsa umurnina ya katse kiran ni kuma na shige toilet na Wauro arwala na fito na saka hijabina tare da shimfida abun sallah na tayar, ko dana gama ban bi takan wayata ba har sai da nayi azkhar Wina na kammala na gyara Wakina, lokacin kusan ?arfe bakwai da wani abu, na nufi Wakin Mamah ina buWe wayata, message Winsa ne na gani har guda biyu sun shigo, na farko na fara buWewa na karanta, Wauke yake da tarin kalamai na so da ?auna da suka jefani a cikin shau?i marar misaltuwa, na biyun kuma sake jaddada mani irin kewata da zai yi yake haWe da yi mini bankwana, nan take nima na ji cewa tabbas zanyi kewarsa duk da ba wani sha?uwa muka yi dashi ba. Text message na rubuta masa nima ina mai yi masa addu'a tare da fatan Allah ya saukesa lafiya sannan na tura ina sauke ajiyar zuciya.
Da ma zaune na isko Mamah tana karatun alkur'ani na zauna zaman jiran ta ?arasa, tana kammalawa ta Wago kai tana cewa. "Janaam har kin tashi?" "Na tashi Mamah ina kwana, an tashi lafiya?" Tana rufe al?ur'anin ta amsa mini da "lafiya ?alau Janam , halan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login